KOWA YA GA ZABUWA…

28

by @gureenjoh

KOWA YA GA ZABUWA...

   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.             

         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:

Zuhraa

Hamrah

Igiyar Rayuwa

Noor Iman

Ruwan Sama..

Lelewal

GAMON JINI paid

And Now

Kowa Ya ga zabuwa..

                      PAGE 28

FREE BOOK

Assalamu Alaikum barkanmu da warhaka, fatan duk muna cikin koshin lafiya, kwana biyu kun jini shiru lafiya ta ƙalau wallahi I was extra busy ne, I was occupied ta yadda ko online bana hawa se in ya kama so waenda suka min messages zan yi reply in na karasa natsawa kuyi hakuri! Waenda suka kirani kuma na gode🙏 Allah ya bar zumunci

"Nace ku min bayani dallah dallah!!"

Ya daka musu tsawa a karo na babu adadi, gabaɗaya rayuwarshi be taɓa samun sukuni ko na miskala zarratin ba, komai yanzu baya mishi daaɗi, komai baya sa shi farin ciki, bakin cikin da yake kwasa da yaran cikinshi abu ne da baze faɗu ba.

A tsorace suka fara bayani dallah dallah sace sace da ake ta mishi sune suke yi suke rabawa tsakaninsu, yadda zarah ta sace kudadenshi suka ɗaurawa Mairamu, yadda suka yi ta Haɗawa Raed tuggu yana ɗaukan munanan mataki a kanshi.

A hankali wani irin sanyi ke rarrafowa yake lulluɓe shi kwarai laifi me girma ya aikatawa ubangiji da ya jarabceshi da waennan matayen, wacce ita ce jin daaɗin duniyar shi yayi silar mutuwar ta da hannayenshi, abunda yake taɓa mishi zuciya shine har karɓar diyya yayi amma yaronta ko biyar be amfane shi da kuɗin ba a Tunanin shi mamanshi shi take kashewa kudadenshi da suke ɓata.

Yunkurawa yayi da nufin rufe su da dukan mutuwa sede jininshi da ya hau a take ya saka ya yanke jiki yayi wani irin faɗuwa, ihu suka kurma dukansu uku suka yo kanshi da gudu, ganin mummunan yanayin da yake ciki yasa suka fita suka nemi taimako aka zo aka yi asibiti dashi.

Tashi ɗaya bayan dogon bincike likitoci suka tabbatar da irin faɗuwar da yayi da yadda jikinshi ya hau fiye da ƙima ya samu paralyze komai baze iya yi da kanshi ba.

Sun sha kuka a lokacin kam, kwananshi goma a asibitin yana cin wuya don ko magana a karkace yake fitowa, su kuwa tun suna jinyar da ɗan daaɗin rai suka fara mishi kawai na dole, don suna yi suna mita, ko Daadida basu kira sun sanar da ita abunda ke faruwa ba har aka sallamo shi ya cigaba da cin baƙar wuya saboda rashin kula.

****

Kira yake yana sakewa sede be same ta ba, haka baƙin ciki na cinshi ya dawo asibitin ya cigaba da kula da Abban shi zuciyarshi ba daaɗi, yana jin tsananin ciwo da idan har aka ce ya rasa hidayat babu abunda ze hana shi mutuwa, hawaye ke cika idanunshi yana maidawa shi karan kanshi be san wani irin soyayya bace wannan.

"Ham....za!"

Muryar Abba cikin Crack ya kira sunanshi saboda bacewa da yayi cikin tunani.

Da sauri ya mike ya iso kusa shi tare da kama hannunshi se hawaye sharrrr

"Abba yau Kaine ka kira sunana da bakinka? Ashe zan sake jin amon sautin muryar ka da kunnuwa na? Alhamdulillah ya Allah!"

Shafa kanshi Abba yayi a hankali yace

"menene? Yake damunka"

A rarrabe maganar ke fitowa.

Da kyar ya iya tsayar da hawayen shi yace

"Abba hidayat ce take so ta kashe ni! Abba na rasa me ke damuna a kanta anya ba wani sakamako bane soyayyar nan? Abba wallahi ji nake kaman zan yi hauka..."

Kuka ya ci karfin shi.

"Kana... Kaiwa Allah kukan ka kuwa?"

Girgiza kai yayi yace

"Abba Bana samun natsuwar yin ibada yadda ya dace, Abba na san hakkin aure na kuma san ina tauyewa zainab hakokkinta saboda masifaffen soyayyar da nake yiwa Hidayat amma na kasa controlling kaina in ba kaina natsuwar da ta dace..."

Rike hannunshi yayi da kyau yace a wahalarce.

"Ka natsu! Ka tsaida hankalinka wuri guda kaji? Ka roki ubangiji ka kuma lazimci karatun Alqur'ani zaka samu natsuwa in shaa Allah"

Kai ya gyaɗa Abban ze sake magana aka budo kofa ko ba'a faɗa mishi ba ya san wacece hakan yasa ya saki hannun Hamza tare da lumshe idanunshi.

Da kallon rashin fahimta duk suka bishi sede ba wadda yace komai saboda ba'a so ana takura mai amma fa abun akwai alamar tambaya ita kanta hajiya ta kula da yadda yake share ta tunda ya farka ko kallon second biyu be taɓa mata ba.

****

Kan a tashi wasan nan seda kowa ya san Raed junior don gefe wurin zaman en kwallon ya zauna dashi ya ajiye shi kan grass carpet, yaro kam ya ruga ya je ya fara tura ball dake zaune daga gefe incase in na ciki ya samu matsala a sauya shine dalilin ajiye shi, da kyar yake tura ball ɗin se hankalin players da suke waje ya koma kanshi suna ta murmushi in aka tambayi sunanshi kai tsaye yake cewa

"Raed junior" cikin wani irin alfahari, wannan shine takwararsa na farko, lokaci lokaci se ya kalli inda take ya saki murmushi Dukda bata Kallonshi bare ta san yanayi kanta a ƙasa.

A ɓangaren ta kuwa zurfi cikin tunani tayi, bata taɓa jin abu makamancin wadda taji ba a jikinta ɗazu, eye contact da suka Samu ya bata wani saƙo me girma ga duk sassan jikinta har yanzu a jikinta take jin wasu abubuwa da suka dinga shiga idanunta a sadda suke kallon junan suke ratsa jini da jijiyarta, menene hakan da har yanzu sukuninshi ya ƙi barin ta?

Lumshe idanu tayi tuna yadda ya sake protecting dignity ɗinta cikin jama'a be bari an kalli gashinta ba wadda shima yake al'aura ne a gareta tunda musulma take.

Wasa wasa wasu sabbin abubuwa ne suke shiga tsakaninsu a cikin ruwan sanyi, kan su bar Belgium Seda suka sha yawo da kalle kalle, cima kuwa babu abunda basu ci ba a garin se abunda Allah ya haramta.

A duk lokacin da ta kalli kanta ta kuma kalli yaranta taji yadda junior ke tashi babu Kalmar hausa ko guda a bakinshi taji yadda Aisha take mance ta iya hausa wani zubin ko ita Hausar ya fara mata wahalan yi se tace ina Yusuf yazo yaga yadda rayuwa ta koma mata? Lokuta dayawa ta kan kalli Raed taji duk duniya shine namiji mafi girman ƙima a rayuwarta saboda ya mata abunda babu wadda ya mata a duniya, yana ƙaunar yaranta fiye da yadda uba ze kaunaci yaranshi..

Hakan yake bata kwarin gwiwar tsayuwa tsayin daka da jajircewa bisa ilimin addininsu kuma Alhamdulillah ba karamin kokari suke ba tunda Allah ya riga ya sa musu kaunar addinin.

"Rash...!"

Ta kira sunan cikin kosawa don tunda suka haɗu take ta maganan hotunan su da yaje viral ita kuwa a duk sadda taji maganan har tsikar jikinta take tuna moment ɗin.

"Ke komai zaki ce Kice, kin san Allah you were the real definition of perfect couple, na rantse baki ga yadda kuka bada kala bane"

Duk yadda ta so hana kanta blushing Seda tayi, ta kau da maganan da

"kin san ya hamza yana ta fushi a kan hoton nan? Duk yadda na mishi bayani ya kasa fahimta, sincerely bana son irin yadda yake yi it's like rashin yarda.."

Ajiyar zuciya Rash ta sauke tace

"in dae har kin san zuciyarki na son Raed it's high time ki gayawa hamza yayi hakuri, a gaskiya bana so ki sake komawa rayuwar wahala da bakin ciki wadda kika yi a baya ma ya isa, Raed kanshi a waye yake, rayuwarshi duka irin na Turai ne sannan labarinku na kamanceceniya ina ga ko don wannan Zaku rungumi juna ku baiwa yaran ku kulawar da ta dace"

Ajiyar zuciya ta sauke tace

"wannan fa ke kike Tunanin nan Rashida shi Raed ɗin ya taɓa cewa yana so na ne da zan kori ya hamza? No, I Will pray idan hamza Allah ya zaɓa min zan zauna lafiya da family ɗinshi in shaa Allah"

A wurin suka bar maganan suka shiga wata.

A gajiye ta dawo gidan Allah ya taimake ta yau ma kaman tunda suka dawo a waje ya sayo musu abincin rana so bata yi girki ba, bayan sun gama karatun yamma wadda shi be samu yayi ba sbd meeting da ze yi attending suka zauna hira.

"I almost forgot! Na san Dad ma wallahi ya mance Farrah tomorrow is ur birthday"

Cewar Norah cikin mamakin yadda suka so sha'afa.

"Wow.. Farrah is turning 7 tomorrow it's a call for celebration"

Hidaya tayi maganan fuskanta cike da fara'a, nan fa Farrah ta fara tsalle wai ita ta girma, Aisha ce tace

"nima mama ai I will be 7 soon ko?"

Hidayat tace

"yeah but Farrah ta baki almost 3months"

A take rikici ya barke Farrah wai se Aisha ta dinga ce mata big sis tunda ta girme ta, hidayat da Norah de se dariyar su suke tayi.

"What's so funny?"

Yayi maganan bayan ya shigo don ko sallamar shi basu ji ba, tsagaita dariyar da take tayi, idanunta dake sparkling na ɗan ruwa da ya taru a ciki sbd dariya ta ɗaura a kanshi, ɗauke nashi yayi ya maida kan Norah da take bashi labarin abunda yake faruwa.

Murmushi kawai yayi yace

"nima I almost forget tomorrow is my little angel born day, I will think about how we celebrate"

Se lokacin Hidayat tace

"welcome sir"

Yace

"thank you"

Daga haka ya saki hannayen Aisha da Farrah da yake rike da yana tambayar Junior, Norah tace yana bacci.

Wucewa yayi ɗaki don yana so ya ɗan yi wani aiki kan magrib maybe da safe zasu yi team trip wadda a bus na players ne dayake ba nisa zasu yi ba.

Aikin ya riƙe shi sossai magrib ya fito yayi ya sake komawa har ze shige tace

"Sir! Do you need anything?"

Kallonta ya ɗan yi yace

"just coffee"

Kai ta gyaɗa ya shige, ita kuma ta tashi tana instructing yaran da suyi karatu tana zuwa.

Kitchen ta shiga tana jujjuya yadda zatayi approaching ɗinshi da maganan dake cin ta wadda shine abu na karshe da zata so taga ya gyaru a rayuwar shi, honey coffee tayi ba me sugar ba, tayi cup ɗin yayi looking so good daga ido ma bare in ka kai baki.

A karamin tray ta ɗauka ta nufi ɗakin sanye da free bubu se karamin chantley vail ba hula kanta tubkakken gashinta ya taimaka wurin riƙe gyalen da kyau ya fito da fresh and smooth face ɗin ta da babu komai bisa kai.

Da sallama ta shiga yana zaune yana duba abu lokaci lokaci kuma yana ɗan rubutu, she feel it's not the right time to bring this up but ya zama dole tayi maganan bcs she doesn't want it to be late for him, ajiyewa tayi ya ɗan ɗago ya bata quick glance tare da cewa

"thanks"

Ya maida kanshi kan aikin, se ta gyara tsayuwa ba tare da ta tafi ba, jin har lokacin tana tsaye ne yasa ya sake ɗagowa yace cikin husky musculine voice ɗinshin nan

"akwai wani problem ne?"

Kai ta gyaɗa, yace

"sit"

Tare da nuna mata bakin couch na ɗakin, zama tayi tana fuskantar shi kanta a ƙasa tana karatun kuda, kan ta Haɗa confidence tace

"Amm Daadida called..."

A take yanayin fuskanshi ya sauya yace

"what?? Why? When did you knew each other?"

Ya haɗo mata duka tambayoyin.

"Am sorry we knew each other not so long after na fara aiki, the truth is Dukda tunda na zo na fuskanci irin kalar rayuwar da kuke na saka a zuciyata dole ku gyara kuma Zaku gyara sede before taking any action or measure,one respectful day Daadida ta kira and ba kowa a gida I picked with salam, shine abunda ya ja hankalin ta tayi murna sossai and made me take a promise na saita rayuwarku."

Dakatawa tayi ganin yayi relaxing bayanshi jikin pillow tare da lumshe idanu Fresh kafanshi Kal Kal kaman wadda baya taka ƙasa a harɗe bisa gadon kaman yadda hannayenshi suke rungume a kirjinshi, ba tare da ta jira yayi magana ba ta cigaba

"wasu abubuwan na ban tsoro ba wai na tsoratarwa ba, sede I was confused how can a muslim wadda yake amsa suna musulmi ba ze iya yin komai daidai a addinin shi ba? daga karshe to clear my doubts na nemi ta bani labarinka and..."

Yadda ya buɗe idanunshi da suka rine a take ya zube bisa kanta ne yasa tayi shiru tana maida kanta ƙasa.

"She gave u?"

Ya watsa mata tambayar.

Kai ta gyaɗa tana me satar Kallonshi, se ya maida idanun ya sake lumshe wa ranshi sossai ya sosu kawai he doesn't like the fact da za'a ke Kallonshi da idanun tausayi bisa past ɗinshi, yana ganin yanzu ya riga ya wuce wannan mataki baya Tunanin kuma ko da za'a Haɗa en gembu karankatakap babu wadda ya isa ya ɗaura ɗan yatsa a kanshi se idan shine ya bada dama bare ayi maganan su Badi'ah. He got billions of dollars ba ma Nairas ba shiyasa yake jingine baabin rayuwarshi na da kaman ba'ayi ba.

"Am sorry!"

Tayi exclaiming.

"Did you helped saboda wanchan wicked mutumin?"

Ya watso mata tambayar ba tare da ya kalleta ba, daga muryarshi zaka san ranshi yayi daci.

"Please don't address him like that, he's ur fathe....."

"Hold on!!! Just hang on there..!"

Ya faɗa da ɗan faɗa faɗa Dukda yadda yake kokarin calming kanshi saboda ita ce, da wani ne yana da tabbacin da yanzu police da zasu raba su su kuma yi musu tsakani sun iso.

"Am sorry!"

Huci me karfi ya fesar tare da sa hannu ya shafa kanshi yana me dunkule hannun, cikin muryar da ta fara mishi wahala yace

"answer me"

Tace

"no, I helped because of Allah(SWT) abunda kuma ya kara min hakuri da juriya is because u also helped me! u are my life savior so in one way or the other I have to find a way da zan maida ko da da kaɗan ne cikin dumbin alkhairinka gareni.."

Bakinta dake motsi a hankali yake fidda kalmomi masu kama hankali da natsuwa kawai yake kallo, chan yace

"thanks! But as from now bana so ki sake alakantani da wadda ya jima da yanke alaka dani for decades ago, u can leave"

Yayi maganan tare da maida hankalinshi kan system ɗinshi Dukda idanunshi da suka nuna kwantaccen bacin rai me wuyar fassaruwa.

Bata da wani option se na bin umarnin shi, ajiyar zuciya ta sauke bazata gaji ba kuma bazata karaya ba Dukda ko kadan bata ji daaɗin saka shi a mood da yake ciki yanzu ba sede dole zata cigaba da kawo mishi maganan har ta samu ta shawo kanshi.

Tana fita ya sake nannauyar numfashi tare da ture system ɗin, ko yace ze cigaba da aikin karya yayi, coffee ɗin ya ɗauka ya kurba tare da lumshe idanu yana jin yadda daaɗin shi da gardinshi ke bi mishi ko ina ga sanyi da ya ɗauka.

"Daadida!!!" Yayi exclaiming yana hautsina fuska se ya janyo Wayanshi ya danna mata kira.

#Vote

#share

#comment

                 🖤Gureenjo🖤