29
by @gureenjoh
KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
Zuhraa
Hamrah
Igiyar Rayuwa
Noor Iman
Ruwan Sama..
Lelewal
GAMON JINI paid
And Now
Kowa Ya ga zabuwa..
PAGE 29
FREE BOOK
"What do you think old lady?"
Ya watsa mata tambayar bayan ta ɗauka ko sallamanta be amsa ba.
"Assalamu Alaikum warahmatullah"
Ta sake cewa, karamin kwafa yayi yace
"Wa'alaikumussalam warahmatullah duk yadda kike so ki kauce maganan nan baze kaucu ba, what do you think? Karki manta fa hidayah is my worker, she's under me I see no reason da zaki yi involving ɗin ta cikin mess ɗin wanchan mutumin"
Tace
"Raed ina yini?"
Haushi ne ya kama shi, ze kashe tace
"Allah kana hanging call nan zan saɓa maka Raed, wai kana dauka baka da mafadi ne kab duniya? Don na faɗa mata labses ɗinka wani abu ne? Mahaifinka na kwance a chan rai a hannun Allah ko kudin kunun da ze sha babu kana zaune a matsayin multi billionier ba abun kunya bane a wurinka?"
Dariyar rainin hankali yayi, yana tuna clearly a sadda yake gaban mahaifin nashi da bin mawanki yake samu yaci wani lokacin ma haka ze yini ya kwana be ci komai ba.
"Kunya!! Wow hmmm, the last time I checked da bakinshi ya ce na kara Haɗa sunana da nashi be yafe ba so it's up to him.. I just call to tell you hidayah bata san mutumin nan ba, bana kuma so ta sanshi in one way or the other bcs he always end up hurting duk wadda ya mu'amalance shi da alkhairi, and am very sure a labarin da kika bata she end up shading tears I don't like that... Good night"
Yana kai nan ya kashe Wayanshi.
Washegari kusan ya fita da sassafe don bayan abunda zasu yi akwai Private jet da ya saya don ya gaji da bin public abubuwa alhali yana da kuɗin yin na kanshin, yana so ayi launching ɗinta a gaban shi Sam ya sake mantawa da birthday ɗin Farrah..
Suma da suka tashi school hidaya ta tarkata su suka tafi, bayan sun tafi ta kira Rashida dama tun jiya suka yi magana ta zo da masu Deco, they decorated parlorn saman so perfectly yayi matukar kyau, ita da Rash suka yi berbie cake sbd Farrah na kaunar berbie, shima kaman ka lashe don kyau da tsaruwar da yayi, snacks da Chinese rice mara yawa sukayi da kuma pepper chicken da kuɗin da hamza ya bata na Kasar suka yi anfani wurin sayo en abubuwa kaɗan da babu a gidan.
Wanka suka yi suka sauya kaya, a cikin kayakin da yake sassayawa yaran ta zaɓarwa kowa kayan sawa, birthday girl kuma ta cire mata wani purple gown me kyau da crown, suna isowa kuwa Rashida ta tare su a ƙasa, a chan suka yi wanka kowa ya saka kaya, crown ɗin bata sauko dashi ba.
Suna fitowa zasu haura se gashi nan ya shigo yana sauri don daga Airport ya tuna birthday ɗin, saɓanin ɗazu da kayan ball ne jikinshi yanzu Ash suit ne da red tie da ƴar ciki itama red, da gudu suka je suka mishi oyoyo, ya shafa kan Farrah dake tura baki yace
"am so sorry my princess, happy birthday"
Dukawa yayi yayi mata peck a goshi yace
"I love you today and always"
Murmushi ta saki yace
"u look good... Lemme go and freshen up se ki zabi duk inda kike so muje se mu je right?"
Kai ta gyaɗa, suka nufi sama don tuni Rashida ta haye.
Dulum suka ga saman dama asali shi wutan shi romantic light ne da dinner light, dukda sun fi anfani da romantic one ɗin be da haske sossai, sede yanzu Dulum dukun.
"Miss hidayat! Aunt Rash!"
Norah tayi kiran sunan, bata rufe baki ba haske ya gauraye parlorn.
Rashida da Hidayat suka fito suna tafa hannu suna yiwa Farrah
"happy birthday to you...!"
Suna sauke first verse Norah da Aisha da ma Raed suka karɓa suna mata tafi, idanunshi zube kan hidayat da tayi wani irin kyau cikin Ash gown da ta sanya, turtle neck ne hakan yasa hula turban red kawai ta sa a kanta se wani fancy earring ta ɗan yi light makeup da red hot lipstick kafafunta sanye da wasu flat takalma masu taushi red.
Sossai tayi mishi kyau and it was like a coincidence shima Ash ne jikinshi and red, Farrah tayi farin ciki ba kadan ba, dukda home party ne su ya su sede yayi kyau matuka, hidayat ta ɗauko crown ta saka mata, sun sha hotuna a 15 pro Max ɗin Raed wadda ko sau daya be yarda hidayat ta fita daga ciki ba daga nan Farrah ta yanka cake ta fara ba hidayat tayi mata kyakyawar runguma tace
"thank you miss hidayat.. I love you"
Tana murmushi tayi hugging ɗinta back tace
"love u more baby girl"
Ta juya ta ba Raed shima haka ta mishi kan ta ba Norah da Aisha da Kuma junior da yake ta so ya rusa cake ɗin, sossai ya sakar mata idanunsa masu rikita lissafinta so yake ta kalleshi sede taki Sam don tana jin kwayar Mayun idanun nashi a kanta.
A hankali yace
"thank you!"
Se ta ɗan ɗago ta kalleshi tare da sakar mishi murmushi wadda yayi sanadiyar lobawar duka dimples ɗinta so Masha Allah, kasa dauke idanu yayi daga kallonta, yarinyar nan ta mishi illah! Illar da baya Tunanin yana da magani.
Abinci suka ci wadda kaɗan kaɗan ne amma different varieties da snacks, daga nan ya shige yaje yayi wanka, ya sauya da kananun kaya suka yi la'asar, ya so su fita sede Farrah tace miss hidayat party is ok.
Shi kaɗai ya sake fita ya sayo gifts ya dawo wadda seda ya sayawa hidayat wani diamond necklace me shegen kyau, ita kuma birthday girl sabon laptop da headphone me kyau, Norah da Aisha ma duk ya saya musu abu.
Ko da Rashida zata tafi kudi ya baiwa Norah ta kai mata wadda a kudin Nijeria sun kusa dubu ɗari shidda zuwa bakwai Don 500dollars ne.
Miss Mary ce ta tattare parlorn yayinda Paul yayi wanke wanke, suna zaune a ɗakinta da Farrah da Junior yayinda Norah da Aisha suke ɗakin Norah suna abunda ya shafesu call ɗin hamza ya shigo mata..
A natse ta ɗaga suka gaisa jin yanayin muryarshi kaman be da lafiya yasa ta tambaya
"ya hamza fatan kana lafiya? Naji voice ɗin ka is sounding somehow"
Yace
"eh hidayat! Bani da lafiya I was admitted ma"
"Subhanallah! Meke damunka?"
"Stress ne ya haifar min da fever but am getting much better"
"amma meyasa kake stressing kanka dayawa har haka yaya?"
Yace
"Toh ya kike so in yi hidaya? Uhm? A duk sadda zan tuna kina gidan wannan ɗan kwallon se gabana ya faɗi ina tsoron rasaki, sannan a nan zainab bata barni na sha iska ba the moment haihuwar ta na ƙaratowa the moment take ɗaga min hankali akan sunan da na yiwa kaina alkawarin sawa"
Shiru ta ɗan yi kan tace
"amma yaya ai na gaya maka ka kwantar da hankalinka, be kamata kana pressurizing kanka akan waennan kananun magunganun ba, zainab kuwa ba sunan hajiya bane?"
"No! Sunanki nake son saka wa"
Wara idanu tayi a zuciyarta tace ai dole zainab ta ɗaga maka hankali, soyayya kaɗai ma da take ga muna yi ta hanani zaman lafiya da call bare kuma ka sakawa ɗiyar ta sunan wata buduruwarka.
"Amm yaya hamza a nan gaskiya ban ga laifin zainab ba! It's unfair mana ina ga har yanzu baka san menene kishi ba a wurin mace, babu macen da zata yarda da wannan duk haƙurin ta kuwa kayi hakuri ka barta ta sa sunan da ya mata please!"
Shiru yayi, tace
"kaji? Please"
Yace
"Toh naji na amince, yanzu dae bar maganan zainab ya namu maganan?"
"Yadda kace in Shaa Allah"
"Toh na ce daga Abba ya samu sauki saboda 100% goyon bayanshi na tare damu, yana karasa warkewa in Sha Allah zaki zama matata"
Murmushi ta saki tace
"yanzu am engaged kenan?"
Yace"
Morethan that ma, ni a wurina kin riga kin zama tawa"
Dariya ta ɗan yi tana kallon Farrah da ta tashi da gudu ta fice kaman wacce aka kore ta tace
"Ohk ka gaida Abba"
Yace
"in shaa Allah! Thanks take care"
Ta sauke wayan tana me kishingiɗa da pillow, hannunta ɗaure bisa kan shafaffen cikinta da bazaka taɓa cewa ƴaƴa har uku sun zauna ciki ba, hamza is something else ta rasa menene ke hana shi kwantar da hankalinshi in har dae abu da ya shafe ta ne, ba wai tana da niyyar yaudaranshi ko wani abu ba sede tana jiye mishi idan Allah be qaddareta a matsayin matarshi ba!
Kwarai zata iya aurenshi ta zauna dashi da iyalan shi lafiya ta auri Yusuf ta zauna da Yusuf ma na kusan shekara goma da daaɗi ba daaɗi bare hamza da yake matukar son ta?.
Da gudu ta shigo ɗakin bata damu da zaune yake yana aiki a system hannunshi ɗaya rike da waya yana call jingine da pillows ba ta haye gadon tare da jan hannunshi dake rike da system ɗin tace
"Daddy! Daddy! Miss hidayat wants to leave us"
Da sauri ya kalleta yace
"what??"
Yarinya kam se hawaye sharrrr, katse wayan yayi tare da sauke system ɗin ya kamo hannunta
"Farrah explain why did you said she wants to leave us?"
"Dad this guy we called Daddy hamza he want to take her away from us! She's promising to marry him ahhh I can't believe this"
Ta karashe da zabga tagumi tana cigaba da hawayenta.
Kallonta kawai yake ganin kaman be ɗauki maganan serious ba Dukda a nashi ɓangaren he's in Morethan shock yasa tace
"Daddy this is a big problem, he wants to take her away from us!"
Cikin wani yanayi yace
"Ohk baby! U know what am gonna do? I will talk to her not to leave us ok?"
System ɗin ta rufe tare da matsarwa ta fara jan hannunshi
"dadd come with me and talk to her..."
Da kyar ya samu ya lallaɓa ta ta kwanta anan bacci ya ɗauke ta, se ya mike ya fara safa da marwa a cikin ɗakin, be taɓa jin fargaba da tsoro irin wannan ba har rawa rawa zuciyarshi yake yi, a hankali ya kai hannunshi aljihun wandon jikinshi ya fiddo wani gidan zobe me tsananin kyau black, da babban yatsanshi yayi anfani ya buɗe wani diamond ring hadadde ya bayyana se kyalli yake, shafa kai yayi ya sake rufewa.
Wannan dare haka ya kwana be iya runtsawa ba cikin Tunanin mafita, daga karshe kuma ya tsayar da mafita guda ɗaya.. Idan har be yi working out ba yana da Plan B baya Tunanin kuma ze faɗi.. gab asuba kuma aka kira su akwai wani training haka ya fice da wuri.
Ko da ta shirya su suka tafi school ita yau ma bata je ba, kasancewar revision suke yi suna gab da fara exams, bayan ta gama ayyukan ta karatu ta zauna tayi ta dubawa daga karshe ta sake gwada layin Ummi kaman yadda kullum take yi sede bata same ta ba.
Abincin rana ta ɗaura musu bayan ta sauke tana fitowa parlor taji Paul na magana, da sauri ta juya wurin kofa yake ce mata oga ya ce ta shirya ta zo ze kaita wani wuri.
Tambayar yaran tayi yace lafiyansu ƙalau suna school, ɗaki ta shiga bata tsorata ba sbd ta san dae baze taɓa cutar da ita ba, don haka a natse ta shirya cikin wani riga da skirt na material me taushi da tsada wadda a dinke yazo, hannun dogo ne sede yana da tsagu zuwa gwiwan hannu, kayan ya zauna mata sossai, ta ɗaura dankwalin sossai ya haske fuskanta kasancewar kayan ruwan powder ne.
Milk veil ta yafa da milk shoe se handbag shima milk bayan ta saka fashion dan kunne milk, se ta saka sarkar da ya saya mata jiya, fuskanta ba komai banda kwalli da pink lip balm me haske.
A natse ta sauko tana duba agogon da ta ɗaura na Apple watch me gold hand, yaran suna da ɗan sauran lokaci kan su tashi don haka bata damu ba ta fito, Paul da kanshi ya buɗe mata bayan katuwar farar GLK ɗin ta shiga ya rufe tare da zagawa ya tayar suka bar kofan gidan...
****
"Wai Alhj me nayi maka ne? Bayan Duka shekarun nan da ka kwashe a kwance ina fama da wahalar ka in ci kashinka in ci fitsarin ka da abunda zaka saka min kenan bayan farkawarka? Ai ko me nayi maka ban cancanci haka daga gareka ba Alhj bare ma babu abunda nayi maka"
Ta karashe cikin masifa, idanu ya zuba mata yana kallo, chan yace..
"Kika ce babu abunda fa kika min? Toh ba dole kiyi ba tunda ke kika zaɓarwa kanki? Ko kin manta kece sanadiyar wannan ciwon nawa?"
Wara idanu tayi tace
"Wallahi ba de ni ba, kaima ka san sanadiyar ciwonka ba ni ba kam karka ɗaura min... Ah to"
Tana kai nan ta juya fuuu ta fice, da kallo ya bita, Hajiya bazata taɓa chanzawa ba a duniyan nan, Allah ya bashi lafiya shine rokon shi don yana da babban Burin da yake son cimma a duk ranar da cikakken lafiya ta same shi, lumshe idanunshi yayi yana ambaton Allah..
#Vote
#share
#comment
🖤Gureenjo🖤