Chapter 007
by @jeeddah3256
TAREEQ IMAM
Na
Jeeddah Aliyu
Arewabook@Jeeddah3256
007.
Nana tana kwance a ɗakinta tayi rub da ciki tun dawowarta daga school take kwance tamkar marar lafiya, bata da kuzari da walwala ko kaɗan. Duk sanda tai yunkuri ta tashi ta cire school uniform ta watsa ruwa a jikinta sai ta ji wata irin kasala da mutuwar jiki ya lulluɓe ta, abun da Tareeq Imam yai mata a school shi kaɗai ke mata yawo a kwakwalwa. tsawon rayuwarta bata taɓa dawowa daga school ta zauna da uniform a jikinta ba koda na mintuna ɗaya ne. Balle har ta kasa wanka saboda ita ɗin mutum ce mai tsananin tsaftar gaske wannan horu ne daga mamanta.
Jin shirunta ya yi yawa bata fito ba parlour ba bare taci abinci yasa Mama ta nufo ɗakinta, ta ganta kwance ga kuma uniform bata cire ba. Hakan ya haifarwa Mama da faduwar gaba har ta shiga tunani ko Tareeq ya sake taɓa mata ƴa da kuwa a wannan karon ba zasu kwashe ta daɗi ba ita da iyayenshi. Ba zai yiwa ba ya hanawa ƴarta sakewa dole ta kai report a school authorities.
Kusa da ƙafafuwanta Mama ta zauna ta bubbuga ƙafafuwanta haɗi da kiran sunanta "Nana! Ke Nana!"
Mama ta kira sunanta da ɗan ƙarfi
firgigit Nana tayi tare da saurin tashi zaune ko ba ka tambaya ba fuskarta za ta bayyanar maka da damuwar da take ciki.
"Na'am Mama!.
Nana ta faɗa sa'ili da ta jinginar da bayanta ga kan gado.
"Nana ya kike kwance ko school uniform ba ki cire ba ko dai taƙadari yaranan Tareeq ya sake miki wani abu ne?"
Nana tsintar kanta tayi da wani irin mashahurin faduwar gaba ambatar sunan Tareeq kawai da Mama tayi cikin sanyi murya ta shiga girgiza kai tare da faɗin "Ba abin da ya yi min Mama kawai dai bana jin daɗin jikina kamar zazzaɓi ne yake so kamani."
"Subhanalillah! shine ba za ki faɗa min ba kika ƙunshe a ɗaki yaushe kika fara koyon ɓoyemin halin da kike ciki Nana?"
Sadda kai ƙasa Nana tayi tana wasa da ƙaramin zoben zinari da ke maƙale a ɗan yatsanta na hagu "Ba ɓoye miki nayi ba Mama kasala ce ta rufe ni tun ɗazu nakeso na tashi na yi wanka ko na ji ƙarfi jikina amma na kasa tashi."
Nana ta ƙarasa magana tana ɓoye hawaye da ke ƙoƙarin zubo mata. Hannu Mama tasa a gefen wuyanta taji temperature ɗinta.
"Ikon ALLAH! Nana jikinki ba zafi ko kaɗan?"
Mama tai magana cikin mamaki "Eh... Mama kawai kaina ne ke ciwo sai kuma rashin kuzari da nake ji, amma bara nai wanka watakila gajiyar school ce ke ɗibana."
"Shike nan tashi maza ki watsa ruwa ina jiran ki a parlour ki ce abinci idan jikin bai warware mu je asibiti a duba ki banaso zama da ciwo kin ji ko?"
Gyaɗa kai Nana tayi saida ta shiga bathroom Mama ta ji saukar ruwa kafin ta fice daga ɗakin. Cikin ƙanƙani lokaci Nana ta fito ɗaure da blue towel, kaitsaye wardrobe ɗinta ta buɗe ta ciro plain gown na material mai ƙaranci nauyi ta ajje gefen gado kana shiga tsane raguwar ruwan da sukai saura a jikinta turare kawai ta shafa ta zura rigar ta fito parlour.
*******
Hannun Tareeq Hajiya Jamila ta riƙo ta ja shi zuwa cikin ƙaramin parlournta, cikin hikima da kwarewa take masa nasiha kafin ta kira ɗaya daga cikin masu aikinta tasa ta kawo mai abinci kaɗan ya tsakura, dan shi ba ma'aboci cin abinci bane barshi da kayan zaki, kamar shazumame.
"Babana me ya sami wayarka Daddy yace ko ya kira layin ka a kashe?"
"Lafiya ƙalau kawai dai wayar ce banaso kuma Ummi tace ba za a canza min ba shiyasa na rufe ta."
Murmushi Hajiya Jamila tai kafin ta shafi sumar kan Tareeq tare da faɗin "Babana Sarkin rigima yanzu saboda canjin waya zai sa ka haramtawa Daddynka jin muryarka almost a week rabo shi da yai magana da kai, ka kuwa san yadda ka ɗaga mai hankali?"
Zamburi baki ya yi yana gunguni ƙasa-ƙasa
Mommy ta kira Alhaji Imam Wali a wayarta bayan sun gaisa, ya ji lafiyar gidansa ta kara wa Tareeq wayar a kunne shi cikin shagwaɓa ya furta "Daddyna...!
Saukar muryar Tareeq a dodon kunnen Alhaji Imam Wali ya haddasa masa sakin ƙarfaffiya ajiyar zuciya saboda ya yi kewar ɗa nashi ba kaɗan ba.
"My Heir!
"Na'am Daddyna ina wuni?
"Ba zan amsa gaisuwarka ba Tareeq har sai ka faɗa min laifin da nayi da ka kashe wayarka, kuma ka kasa nema na."
Tareeq yai wani ɓata rai tamkar yana gaban Daddy nashi, cikin shagwaɓaɓɓiyar murya ya amsa da cewa
"Daddy ba laifi da ka yi kawai dai banso wayar nan so nake a canza min, kuma Ummi ta ce ba za a canza ba."
Dariya ya yi irin ta dattawa kafin cikin kwantar da murya ya ce "My Heir kai ma kasan waya ba matsala bace zan kira El-yaqub ya kawo maka wayoyi new version har gida ka zaɓi wacce ka ke so.
"Ni Iphone 7 nake so wannan 6 ce an gama yayin ta."
"Shikenan El-yaqub zai kawo ma har gida."
"To amma Daddy ya za ka yi da Ummi tun da ta ce ba za a canza wayar ba, ni gaskiya banaso faɗa nan nata na rashin dalili?"
Tareeq ya faɗa yana wani yatsine fuska tare da turo baki.
"Don't mind her ai ba kuɗinta bane, yanzu dai mu ajiye matsalar waya da ta Amina a gefe tun da na ri ga da na magance wannan matsalar."
Cewar Daddy yana ƙoƙarin kawar da zance Ummi saboda ko kaɗan bayaso ya ji an ambata mishi sunanta yanzu sai mood ɗinsa ya canza.
Fira suka shiga yi tamkar wasu Friends tsawon lokaci suka share akan waya kafin, suka yi sallama sai gafda magariba Tareeq ya baro ɓangaren Hajiya Jamila.
Misali ƙarfe 9:00pm Tareeq ya fito cikin shiri na fita gantalinshi na dare yana tafe yana wani taƙama ga ɗan uban ƙamshin designer perfume dake tashi a jikinshi, a compound ya haɗu da Ya Fadila jingine da motar Isma'eel saurayin ta da za ta aura, ko kallon gefen da suke Tareeq bai yi ba ya nufi parking lot Isma'eel ne ma ya yi ƙarfin hali yimasa magana "Muhammadu Tareeq yau ba ko gaisuwa?"
Banza ya yi dashi tamkar bai ji ba al'hali ya ji shi sarai lokaci amsa mai ne kawai baya dashi.
Ɗaya daga cikin tsadaddun motocin Daddy ya nufa tun da yamma yasa Isa ya wanke masa ita ya yi unlocking kofufin motar ta hanyar danna remote
Fadila ta ankara abin da yake shirin aikatawa ta kalli Isma'eel dake ta faman korafi akan yai wa Tareeq magana bai amsa ba. Cikin sauri ta ce "Kayi haƙuri Babe bani two minutes nai magana dashi da alamun akwai abin da ke damunshi."
Ta ƙarashe magana bata jira amsar da Isma'eel zai bata ba ta nufi parking lot da saurinta "Kai Tareeq ji mana tsaya zan yi magana da kai."
Ta faɗa tun kafin ta ƙarasa gun sa.
Cakk ya tsaya tare da waigowa nan take annurin fuskarsa ya ɗauke.
"Me kake shirin yi ne in short ina za ka tafi da motar Daddy amma sato key ɗin ka yi ba tare da sani Ummi ba ko?"
Ta faɗa sa'ili da ta isa kusa da shi.
Wani irin mugun takaici ne ya lulluɓe shi ya shiga ƙare mata kallo from head to toe kafin ya shiga tata mata rashin mutunci tamkar yana yi da sa'arshi "Wai ke Ya Fadila ba ki da aiki ne sai na gulma? Ya kamata ki sauya hali wallahi."
Cikin matuƙar fusata Fadila ta nuna shi da yatsa "Watch your tongue Tareeq kasan irin maganar da za ka dinga furta min remember I'm your elder sister."
"To hell with you da zamanki elder sister, ke bara ki ji Ya Fadila kar ki ga ina raga miki ki ɗauka ina jin tsoronki ne kasancewar ki gaba da ni don haka ki fita sabgata ba ruwanki da....
"Tareeq!
Fadila ta katse shi cikin tsawa da hargagi kana ta ci-gaba da cewa "Ka zage ni iya adadin da ranka keso amma ba zan taɓa bari ka fita gidanan da motar nan, domin ALLAH ne kaɗai yasan irin masifar da za ka je ka ɗauka mana a gari yaushe ma ka kware da driving da za ka fita da mota?"
"Kutumar ubanan wai kina nufi kece za ki hanani fita da motar da ubana ya zuba kuɗi ya siya?"
Tareeq ya faɗa yana dariya mai cike da reni.
"Kwarai kuwa ko kana mamaki ne?"
"Ba mamaki na ke ba Ya Fadila saboda na daɗe da sani ke ɗin cikakkiyar mahaukaciyar ce wacce bata damu da tattalin lafiyar jikinta ba."
"Duk abin da za ka faɗa go ahead ba zan hanaka ba, fita da mota nan ce dai ba za ka yi ba. Maza ka bani key ɗin hannunka kana ɓata min lokaci kuma ka ga ina da baƙo."
Ta ƙarashe magana tare da tara masa tafin hannunta, sosai Tareeq yake sheƙa dariya sai da ya yi mai isarshi kafin ya ɗage gira sama tare da cizon gefen leɓɓen shi na ƙasa yana kallon Fadila tunani yake ta ina zai fara illata ta yayin da ta shamma ce shi da nufi ta wafce key cikin rashin sa'a yai sauri janye hannunshi, hakan da tayi ba ƙaramin ƙara fusata shi ya yi ba cikin zallar ɓaci rai ya dube ta da idanuwanshi da suka fara sauya launi gami da daka mata tsawa yana faɗin "Ya Fadila I'm warning you stay away from me tun muna sheda juna wallahi-azim idan ki ka yi yunkuri hana ni fita da motar da ubana ne ya zuba kuɗinsa ya siye bai kuma taɓa yi min shamaki da ita ba. To kuwa ba abin da zai hana ni bi ta kanki na taka ki ba abun da za a yi dan na taka banza gwara tun wuri ki yi ta kanki rashin mutuncina ya girmewa naki."
Zaro idanuwa Fadila tayi cikin kaɗuwa za ta yi magana ya ƙara daka mata tsawa yana zare mata manyan idanuwanshi "Don't ever tested my patience just get out of my way."
Wani kallon banza Fadila ta shiga yi masa kafin tayi ƙwafa tare da kyasta yatsunta ya bada sauti ƙasss....ƙasss! "Ka jira za ka ga abin da zai biyo baya kuma In-sha-ALLAH yadda ka yi min sai ALLAH ya ba ka ƴaƴa da za su ma fiye da abin da ka yi min ɗan iska yaro marar tarbiyya ALLAH ya haɗa ka da dai-dai da kai."
"Dallah bani hanya Malama ko uban waye ya faɗa miki zan yi aure balle har na haifi ƴaƴa, sai dai ke ki haifa min nai ta cin ubansu."
Ya ƙarasa magana tare da buɗe ƙofar mota ya shiga yai mata key da ƙarfi ya shiga yin reverse, kamar zai taka Fadila tai sauri yi tsalle ta koma gefe tai tsaye tana kallonshi da idanuwanta da suka fara tara ƙwalla saboda ta ji zafin rashin kunya da yai mata musamman da ta waiga wajen da Isma'eel yake tsaye ta ga hankalinsa ya tattara ne akansu.
A hankali Tareeq ya sauke gilashi yai ƙasa ya leƙo da kansa yai mata waving haɗe da gwalo, ya ƙara figar motar da gudu tuni aka wangale mai gate.
Yana fita kai tsaye ƙofar gidansu Rooney ya nufa horn ya shiga dannawa sai ga Rooney da Lil-prince sun fito cikin shigar english wears, ya kwashe su suka nufi wani farm house na mahaifin abokinsu Sasco can bayan gari wuri daji ne sosai anan za su gudanar da birthday party da Sasco ya shirya wa girl friend ɗinshi.
Fadila tasa gefen gyaleta ta goge fuskarta dashi kafin ta koma wajen da ta baro Isma'eel, tana wani murmushi yaƙe "Babe mike faruwa ne naga kamar kuna sa-in-sa da Tareeq?"
Isma'eel ya faɗa yana kallon cikin idanuwa Fadila tare da karantar yanayi da take ciki.
#Jeedd
ah Aliyu
#Tareeq
#Fadila
#isma'eel
#Rooney
#Lil-prince
#team TareeqImam.