Matar Khalees
by @nusybee143
*****MATAR KHALEES*****
✍️Nusy bee
Page 5
Cikin abinda bei wuce mintuna sha biyar ba aunty Bintu da babbar ƴar ta intisar mei kimanin shekaru goma sha bakwai suka iso, cikin murna mai yawa intisar ta rungume meema tana faɗin"wow! aunty meema you are highly welcome, gaskiya munyi missing ɗin ku da yawa"ta dubi hafeez fuskar ta ɗauke da murmushin farin ciki tana faɗin"uncle hafeez yau a gari?ai munyi tsammanin mutanen Malaysia sun riƙe mana kai"
Ɗan murmushi hafeez yayi sannan yace"ina!kuna raina intisar,kawai time ne baya samuwa,amma kuma ai auntyn ku tana zuwa ko?"
"Eh haka ne,to yanzu dai kuzo muje gida, Mamie na ta shirya muku delicious and wonderful dish"
Mima ta wuce gaba tana faɗin"kuzo muyi sauri,a gajiye nake ni"suka ɗunguma suka shiga motar,aunty Bintu taja suka tafi gida
Basu samu damar zama cin abincin ba sai da sukayi sallar maghriba,suna cin abinci suna hira,anan aunty Bintu ta sanar dasu batun auren Deeja
Cikin madaukakin mamaki Mima tace"kamar a mafarki?Deeja tayi aure kullum mukanyi waya ko chat amma ta kasa sanar dani?"
Aunty Bintu tace"kin santa da zurfin ciki,kuma ina zargin akwai matsala ne,duka duka fa kwananta arba'in da shida da yi mata aikin zuciya akayi mata auren fa"
Hafeez ya gyaɗa kai yace"lallai babu mamaki,to ina tsohon mijin nata?"
Aunty Bintu tace'yana nan"
Kuma suna haɗuwa dashi?"a cewar Mima tana tsare ta da ido
"Sai dai idan bataje gidan Mamie babba ba,kuma bikin a gidan mamien za'a yi"a cewar aunty Bintu
"Yayi aure ne?"hafeez ya tambaya
"Tun kafin su rabu da Deeja "a cewar Mima"wata fitsararriya mara kunya mara tarbiyya"ta ƙarashe maganar tana yatsina fuska
"Ke Mima!ina raba ki,a ina kika san bata da tarbiyya?"a cewar aunty Bintu
Murmushin takaici miman tayi tace"a bar maganar kawai aunty"daga nan suka sauya wata hirar
A ranar Mima ta kira Deeja ta sanar mata da saukar su,ihun murna ta rinƙa yi,tace"oh!leemo nayi missing ɗinki da yawa,ina my baby Mee'ad?"
"Tana wajen abban su ita da munib"
"Yayi kyau,to yaushe zaki ƙaraso?"
"Oho miki,mara mutunci kawai,kiyi aure amma ki kasa sanar dani?"
"Uhm!"da story sosai Mima,sai mun haɗu kawai,yaushe zaki zo?"
"It is better mu haɗu a gidan bikin, saboda abban Mee'ad ya matsa min gobe,jirgi zamu bi zuwa azare,don mu gaida ammin su"
"Okay,babu matsala, yaushe zaku dawo?"
"Jibi in Sha Allah,Kuma a gidan bikin zan sauka"
"Okay babu damuwa,Ni da gobe nace zan je,amma yanzu na fasa sai jibin"
"Haba ke kuwa,meyasa?"
"Mu haɗu a jibin kawai,da stories"
"Okay Allah ya nuna mana da alkhairi"
"Ameen"sukayi sallama
A ranar Deeja cikin farin ciki ta kwana,walwalar ta ta bawa Khalees mamaki ƙwarai, saboda irin tarin matsaloli da ta tsinci kanta a ciki basa bata damar yin walwala kamar kowanne mutum,amma sai sabgar ta takeyi cikin farin ciki,shi kuma Khalees jin kai irin nashi ya hana shi tambaya
Washe gari da safe daga office Kai tsaye wajen kitso da ƙunshi ta nufa,ai kuwa aka tsantsara mata kitso, dogon baƙin gashin ta ya amshi ƙananan kitson,lalle ja da baƙi ya amshi chaculate fatar ta,tayi kyau sosai ga wani haske da ta ƙara a ƴan kwanakin nan
A ranar bata koma gida ba sai shida saura ƴan mintuna,tun sanda mai gadi ya wangale gate ta hango khalees yana ta faman Safa da marwa, fuskar shi ɗauke da alamun damuwa,amma ganin shigowar motar ta sai ya tsaya cak yana kallon ta batare da yace uffan ba, fuskar shi har yanzu a ɗaure take
Kai tsaye parking space ɗin gidan ta nufa bayan ta daidaita parking ɗin motar ta fito tana ɗan satar kallon Khalees ɗin,ko uffan ba tace ba tayi nufin wucewa cikin gidan
"Daga ina kike?"
Batare da damuwa ba ta bashi amsa,"naje kitso da ƙunshi ne"
"Shine sai yanzu?"ya faɗa da ɗan ɗaga murya
Ganin hankalin mutanen da suke yiwa gidan hidima ya fara dawowa kansu ya sanya ta furta"I'm sorry"da sauri ta wuce cikin gidan
Ta fito wanka ta ganshi a bakin gado,har yanzu fuskar shi babu walwala,hakan bai dame shi ba,ta zauna a gaban madubi ta fara gyara kanta,sai yanzu Khalees ya ƙare mata kallo ganin tayi kyau sosai,amma duk da haka bai fasa faɗar abinda ya kawo shi ba
"Ban amince ki rinƙa zuwa ko'ina kina haura la'asar a waje ba,idan haka ta kuma faruwa rai zei ɓaci"bei jira amsar ta ba ya miƙe ya fice daga ɗakin
Wayar ta ta ɗauko daga jakar ta,miscall shida ta gani,shaf ta manta cewa ta sanya ta a silent,duk misscall shidan Khalees ne,a fili ta furta "oh!wato jin kai bazai bar shi yace"ya kira ni ban amsa ba ko?"
Washe gari ta kama juma'a,kuma a ranar zata tafi gidan bikin,sai zumuɗi take tayi,Khalees yana kwance yana kallon yadda take ta farin ciki, gaba ɗaya sai yaji ya shiga damuwa,wato farin ciki takeyi Saboda saboda zata nisance shi?"
Da yaga zumuɗin yaƙi ya ƙare sai yace"Malama haukan ya isa haka,idan kika matsa ma wallahi sai na hana ki"
Kallon shi tayi cike da mamaki,ganin ya ɗaure fuska ya sanya ta ɗauke kanta ta cigaba da abinda takeyi, zuciyar ta cike da mamakin shi
Ƙarfe bakwai da mintuna arba'in ta kammala shirya komai,a lokacin tuni Khalees ya wuce wajen aikin shi,ta loda akwatunan ta a Boot taja motar ta ta nufi wajen aikin ta
Sha ɗaya da minti bakwai wayar ta ta fara ƙara,tana dubawa,sunan Mima ta gani,da sauri ta ɗaga tana faɗin"sister leemo ya?kun sauka lafiya?"
"Lafiya lau sister deejo,mun dawo fa"
"Da gaske don Allah?"a cewar ta cikin farin ciki
"Wallahi kuwa,yanzu haka ma gamu a airport,aunty Bintu zata ɗauke mu"
"To Allah ya iso daku lafiya,Ni ina wajen aiki"
"Okay to mu haɗu a can ɗin kawai"
Don Allah a rinqa bani qwarin gwiwa ta hanyar,like, comment,da share
#Nusy bee