Barrister Hibba

Barrister Hibba

by @nusybee143

💥 BARRISTER HIBBA💥

✍️alƙalamin Nusaibat ibraheem rimi (Nusy bee)

بسم الله الرحمن الرحيم

Littafin BARRISTER HIBBA mallakin Nusy bee ne,kuma ƙirƙirarren labari,idan hali ko yanayi yazo ɗaya da na wani/wata,to a rashin sani ne

Sadaukarwa:na sadaukar da littafin BARRISTER HIBBA ga makaranran litattafai na ƴan amana 🥰 kune ƙwarin gwiwa ta kuma farin ciki na

Page 1

LEKKI PHASE 1,LAGOS STATE, NIGERIA

"Yes come in"aka amsawa mai knocking ƙofar"

Shga tayi cikin office ɗin,cikin girmamawa take gaida wadda take zaune a office ɗin

Matashiyar budurwa ce,wadda zata iya kai shekaru 27-28,fara ce kyakkyawa,amma kallo ɗaya nayi mata na ga alamun ba bahaushiya bace, tafi kama da ƙabilar igbo,sanye take da suit kamar dai yadda aka san lauyoyi,kunnen ta ɗaya jone yake da Ear pod,ta mayar da hankalin ta sosai kan computer da alamu abu mai muhimmanci takeyi,a haka ta amsa gaisuwar sakatariyar tata

"Ma'am,you have a guest"a cewar sakatariyar tata cikin girmamawa

"Who is he or she?"ta sake tambaya batare da ta kalle ta ba still

"Barrister awwal Nuhu tofa"ta sake bata amsa

Sai da ta ɓata kusan minti guda kafin tace"let him in"

"Alright ma'am"ta faɗa tana rissinawa sannan ta juya ta fita

Mintuna biyu tsakani barrister Awwal ya shigo da sallama,ta amsa masa tana ɗan sakin fuska kaɗan,kuma har yanzu idanun ta na kan computer ɗin ta,bai damu ba ya samu waje ya zauna,don ya san zaiyi wuya idan ba wani abu mai muhimmanci takeyi ba,ya san ta sarai bata ɓata lokaci akan shirme

Ta kai kusan mintuna goma kafin ta gama Abinda takeyi,ta ɗago da ɗan murmushi tana faɗin"welcome barrister"

"Weldone barrister! I hope you are doing good"

"Absolutely barrister! I'm hoping you are well prepared for our next case"

Ɗan murmushi yayi yace"You know everything barrister Khadijat,komai yana hannun BARRISTER HIBBA AIYO,and for now bata ƙasar,i spoke to her last week about the case tace min tana sani"

Barrister Khadijat ta girgiza kanta tana ɗan murmushi tace"don't misperceive her, definitely tana shirya wani abu ne behind,and Ni da Kai mun sani,aikin mu babu yarda da juna, beside, barrister hibba bata cikin nau'in mutane masu yarda da mutum"

"All I want shine muyi winning case ɗin nan Khadijat,amma ina shiga tashin hankali idan na tuna har zuwa yanzu bamu da evidence akan Hajiya Fatima da ƙanin ta Suraj,gashi sam ba'a san inda Rahama take ba, gashi barrister aiyo tace tana da ayar tambaya akan abokin Alhaji Ja'afar shuwaki, Alhaji adam doguwa,tunda tace hakan definitely akwai abinda ta gani,You know who barrister aiyo is"

Murmushi sosai barrister Khadijat tayi tace"I know barrister aiyo sosai, definitely bata yin abu a banza,for now dai We should wait for her presence, I'm very sure zuwa next week zata iso, I know barrister aiyo,she knew what she is doing"

"Alright barrister,sai mun haɗu a can ɗin, yaushe zaki je ke?"

"I will wait for aiyo's call,yadda tace haka zanyi"

"Okay,see you soon, thanks barrister"Barrister Awwal ya faɗa yana miƙewa

"Okay barrister, thanks very much"ya faɗa yana ficewa,ita kuma ya mayar da kai ga computer ɗin ta ta cigaba da aiki

AIYO MANSION,ALI MUHAMMAD KABO AREA, RAILWAY ESTATE

Samari ne sun kai su ashirin a ƙaton compound ɗin suna ta hirar ayyukan su,da alamu dukkan su ma'aikatan gidan ne,shi kaɗai ne yayi shiru yana bin su da kallo,yana mamakin abinda suke faɗa akan mamallakiyar gidan wadda shi dai tunda ya fara aiki tsayin kwana arba'in da uku kenan yau bai taɓa ganin ta ba

Mas'udu yaji yana cewa"ai wallahi matar nan bana jin zata gama da duniya lafiya,tunda nake ban taɓa ganin mace mai girman kai da ɗagawa irin ta ba,kamar ita ɗin wata tsiya ce,yo mace gandareriya kamar wannan babu aure mai akayi kenan, tsakani da Allah fa ilyasu"

Wanda aka kira da ilyasu,wanda shine mai wanki da gugar gidan yace"ashe dai bani kadai nake wannan tunanin ba,Ni fa gaba ɗaya dukiyar tata ma tsoro take bani,yo magana ta Allah fa mas'udu,bana jin idan halal take ci zatayi waɗannan munanan ɗabiun,Ni mamaki ma nakeyi yadda mahaifiyar tasu bata da kataɓus akanta,sai abinda tace ce takeyi, tamkar itace ƴar,ita kuma hamshaƙiyar itace uwar"Aminu mai wanke mota ya kwashe da dariya yace"kaji ka kuma,to menene sirrin idan ba kuɗi ba,kasan ance kuɗi ƙare magana,ba don kuɗin ba zaka ganmu anan ne?"

Mas'udu yace "hakane fa, gaskiya dai Allah yasa muyi kuɗi mu huta da wulaƙancin matar nan"

Har ilyasu ya buɗe baki zaiyi magana horn mai ƙarfi ya katse shi,a guje
Mas'udu ya miƙe ya nufi kantamemen gate ɗin ya hangame shi,wata rantsatstsiyar BMW ta danno Kai a hankali,kai tsaye ta nufi parking space,shima mas'udu ya koma wajen zaman shi,in da dukkan ma'aikatan sukayi shiru suna zazzare idanu,kowa na ƙoƙarin ganin wanda zai fito daga motar,ciki har da shi da yake ɗan danna wayar shi yana ɗan kallon inda motar ta gama daidaita parking a fakaice

Kusan a tare suka fito, identical twins ne waɗanda a ƙalla zasu kai shekaru sha tara zuwa ashirin,farare ne sosai, waɗanda sunji gayu har sun gaji,sanye suke da wasu designer blouses masu uban sun tsada sky blue,kowaccen su ta ɗora ƙaramin mayafi akan ta fari,hatta da agogon hannayen su iri ɗaya ne, faɗar sunyi kyau ma ɓata lokaci ne,da sauri Jabir,wato shugaban ma'aikatan gidan ya ƙaraso da fara'a ya rissina yana musu sannu da zuwa,ɗaya daga cikin su ce ta amsa,ɗayar kuwa kallo ɗaya tayi masa ta cigaba da danna wayar ta

Mai amsawar ta dube shi cikin ɗan sakin fuska tace"kace an ɗauki sabon driver ko?"

"Hakane ranki ya daɗe,gashi can ma,idan kinyi min izni sai a kira shi"no ba sai ka kira shi ba,zan shiga cik na shirya,idan yaso sai ka kawo shi na ganshi"

Cikin girmamawa yace"okay ma'am"bata tsaya sauraren shi ba ta bi bayan ƴar uwar ta wadda zuwa lokacin ma ta kusa isa balcony na gidan

Da sallama suka shiga parlourn, wadda ta fara shiga ta juyo ta dubi ya bayan tana faɗin"ARWA anya bazamubi yaya ba? I'm missing her,kuma duk lokacin da muka zo hutu I'm just feeling somehow idan na shigo gidan nan anytime Yaya bata nan"wadda aka kira da Arwa ta ɗan yamutsa fuska tana faɗin"Ni tun ina damuwa da al'amarin yaya har na daina,bana gane gaban ta da bayan ta,kuma mutum bai isa yayi tambaya ba,ranshi ya ɓaci, don't ever try to follow her MARWA,yanzu yaya zatayi disgracing ɗin ki ta saka ki a mota ki dawo Nigeria,ta ƙarasa faɗa tana shigewa ɗakin ta

Wow!ɗakin kamar na Sarauniya,an narka dukiya,hatta da tissue box dake kan ɗaya side drawer abin kallo ne, ba'a maganar bed side lamp, furnitures da sauran su,bata tsaya tunanin komai ba ta rage kayan ta ta ɗaura towel ta shige haɗaɗɗen banɗakin nata

Kusan lokaci guda suka fito ita da twin sister ɗin ta, dukkan su kayan shan iska ne a jikin su,na Arwa farar singlet da wando three quarter,kanta babu ɗan kwali,ita kuma Marwa farar top ce a jikin ta da blue jeans dogon wando,itama dai kan nata babu ɗan kwali,sai wayar ta ƙirar iPhone latest version a hannun ta,ita kam Arwa ko wayar bata dauko ba,dama ita waya bata dame ta ba 

Kai tsaye upstairs suka nufa inda nan ne part din mama,ya haɗu babu laifi, sai dai abin mamaki ko rabin dukiyar da aka kashewa ɗakunan nasu bai kai ba,a parlourn ta suka same ta tana waya da abokan kasuwancin ta,tana ganin su ta katse wayar,da fara'a ta miƙe ta rungume su tana faɗin" ƴan biyu kyautar Allah,an sha makaranta,nayi kewar ku,babu ku babu babbar yaya"suna murmushi su duka, Arwa,wadda tafi magana tace"mu ma munyi kewar ki mama,ga karatu da saka zafin kai"murmushi mama tayi,ta koma wajen zaman ta, su kuma suka rissina suna gaishe ta

Mama tace"wannan karon yayar ku ta daɗe,rabon ta da daɗewa kamar haka tun tana karatu"Marwa tace"maybe ko wani uzuri ya riƙe ta"mama tace"hakane,to Allah ya dawo da ita lafiya"suka amsa da ameen

Da daddare a ɓangaren mama suka ci abincin dare kafin kowacce cikin su ta wuce nata luxury room ɗin

Washegari da misalin ƙarfe tara na safe, dukkan su suna sanye da riguna dogaye marasa nauyi,kalar sea green da scarf shima sea green, Arwa ta kira Jabir ta bashi umarnin yazo tare da sabon driver ɗin da yayi employing ba da daɗewa ba

Da kamar mintuna biyar suka danna intercom, Arwa ta basu izinin shigowa,suka shiga da sallama,kafin Jabir ya zube akan carpet,shima sabon driver bashi da zaɓin da ya wuce na bin bayan Jabir,amma zuciyar shi cike da mamakin wai kamar shi yake rissinawa waɗannan yaran da ko autar su ta girme su,kuma a haka ma Arwa ce ta amsa, Marwa kam wayar ta ce a hannun ta tana chatting,ko ɗaga kai ta kalle su batayi ba

Arwa ta amsa gaisuwar su sannan ta mayar da kai ga baƙon driver ɗin tace"da farko yaya sunan ka?"

Yayi jim kamar bai ji ba,sai da Jabir ya zungure shi,can ƙasa ya amsa,"suna na MUYASSAR"

"Wow!nice name"a cewar Arwa"to malam Muyassar nasan zuwa yanzu Jabir ya sanar da kai aikin ka a gidan nan, driving maman mu,sai ni da twin sister na,idan yayar mu ta dawo aikin ka zai fi yawa, kasancewar ta ma'aikaciyar wajeje da yawa,abinda muke so kawai ka kasance ka riƙe aikin ka da mutunci, saboda mu da maman mu matsalar mu mai sauƙi ce,amma yayar mu bazata taɓa ɗauka ba ko da wasa, lokacin zuwan ka by 8:00am ne,ƙarfe 5:00pm ka tashi,amma idan yayar mu ta dawo har bayan Isha'i zaka iya kaiwa kana aiki,amma zata biyaka na overtime da zakayi mata"

Bayanin ya fara yiwa Muyassar yawa,sai jinjina ikon wannan baiwar Allah yake wadda ko a hoto bai taɓa ganin ta ba a tsawon zaman shi a gidan,ɗagowa yayi yana faɗin"babu laifi idan banyi overtime ba?Ina nufin ita yayar taki idan ta dawo ta bukaci ƙarin lokaci ba laifi nace a'a?"ba iya Arwa ba,har Jabir da Marwa wannan karon sai da suka kalle shi,kafin Arwa ta cigaba da magana Marwa tace"kawai ka saka a ranka yayar mu kakeyiwa aiki malam!tana da right da zata ce ka shirya ku bar kasar not even  overtime,idan kana da ra'ayin aikin fine, idan baka da ra'ayi hanya a share take,zaka iya komawa inda ka fito"ta ƙarasa tana nuna masa hanya fuskar ta a haɗe

#Nusy_bee