WUTAR ƘAIƘAYI

Page 5

by @sanazty

WUTAR ƘAIƘAYI

Wattpad@SaNazdeeyah_

_Arewabooks@sanazty

Faceboo@SaNaz Deeyah

Youtube: ***

KARAMCI WRITERS ASSOCIATION

[karamci tushen mu'amula ta gari]

Book 1

```🆓Page 5```

Sun fi mintuna biyu zaune babu wanda ya tankawa wani, sai dai Sadiya hawaye kawai ke zuba a fuskarta.

"Sadiya"

Ta ji ya kira sunanta a sanyaye, ta ɗago ta kalleshi idanuwanta har sun fara canja launi.

"Dan Allah ka da ki rabu dani wallahi ba zan iya rayuwa babu ke a ciki"

Ba ta ba shi amsa ba haka zalika ba ta bar kuka ba.

"Na yi miki alƙawarin ba zan taɓa bari ki wulaƙanta ba, kuma na san Mameey tana fushi ne amma za ta sauko saboda tana sonku"

"Ina tsoro Yazid"

"Kar ki zaɓi rabuwarmu saboda ba zan iya rabuwa da ke ba, dan Allah ki tausaya min" Ya furta yana haɗe hannayensa.

Haka ya yi ta roƙonta har ta ji cewa za ta iya bin sa, duk da tana cikin fargabar furucin Mameey, amma rayuwa da mijinta da kuma yaranta ya fi mata komai.

Tana cikin haɗa kayansu Mameey ta shigo.

"Sadiya haɗa kaya kike za ki bi miji?"

Ɗagowa ta yi da rinannun idanuwanta ta kalli Mameey.

"Kiyi haƙuri Mameey bana so na raba kan yarana dan Allah Mameey ki fahimc...."

"Dakata, tunda dai haka kika zaɓa ya miki kyau, Allah ya barku tare ke da shi." Tana gama faɗa ta juya.

**********

Ko da ta shiga gidan ta yi mamaki sosai da ta gan shi a tsaftace, kuma an gyara bayin sannan an sake musu rufi.

Sai bayan sun huta ne take tambayarsa inda ya samu kuɗin da ya yi wannan aikin, anan yake sanar da ita sauran kuɗin aikin da aka mata ne ya haɗa ya yi gyaran gida.

Shiru ta yi idanuwanta cike da ruwan hawaye dan ƙiris suke jira su zuba.

"Sadiya kiyi haƙuri, ki ɗauki dangana Allah ya sa mai ceto ce, ke kuma Allah ya baki lafiya me ɗorewa"

"Ban taɓa yin wahalar labor kamar na wannan cikin ba, ashe bama zamu rayu tare ba"

Ta saka yatsa tana goge hawaye.

"Haba Babyna, dan Allah ki bar kuka, insha Allah zamu samu wasu" Jin haka ya saka ta lumshe ido cikin jindaɗi, duk da suna da yara kuma suna cikin matsi na rayuwa amma hakan baya hanasu shan soyayya.

Ranar cikin farin ciki da annashuwa suka kwana, duk da ɗinkin ta bai gama warkewa ba amma dai sai daya daɗaɗa mata ya kuma mantar da ita damuwar da ta taho da ita daga gida.

08:00am

Tana gaban murhu tana dafa ruwan shayi sai ga shi ya fito ya ƙarasa inda take. "Maman Najma ni zan tafi kasuwa."

"Haba Abban Najma ya za ka fita baka karya ba"

Murmushi ya yi sannan ya ce "Kar ki damu nima zan samu abu a waje na ci, amma kin ga na yi rana yanzu"

Miƙewa ta yi tana kallonsa.

"Dama akwai abinda nake son baka, amma tunda yanzu ka yi rana sai mu bari sai gobe idan Allah ya kaimu."

"Allah ya kaimu"

"Amin Abban Yara Allah ya tsare hanya"

"Amin Babyn Baby"

****** ******

"Saddiqa a haka kike tunanun zan cigaba da haƙuri da Sadiya bayan ba ta jin magana ta kuma ba ta san kima da darajata ba" Mameey ta yi maganar cikin ɓacin rai.

"Mameey dan Allah kiyi wa Sadiya uzuri, ni na san tana yin haka ne saboda yaranta ba ta so ta fito kuma ace za a ƙwace mata yara"

"Haba Saddiqa ai ban san meyasa da ke da Faruq sam baku ganin laifin Sadiya sai kuce wai na yi mata uzuri, wane uzuri ne ban mata ba, dole sai ta tura kan ta inda ba a yi da ita."

Faruq zama ya gyara sannan ya ce, "Mameey dan Allah kiyi haƙuri"

"Ni fa ina ganin mijin nan nata asiri ya mata, haba wannan wane irin so ne?" Cewar Surayya.

"Babu asirin da ya yi mata, kema idan kika yi aure kika haihu za ki gane irin yanda ɗa yake a zuciyar mahaifiya" Saddiqa ta faɗa tana kallon Surayya.

"Amma dai kin san ko yaran Sadiya sun kai dubu zan iya riƙewa ko?"

"Mameey za ki iya amma kina da tabbacin 'yan uwansa za su yarda su bar mata yaran? Musamman ma mahaifiyar shi da ba ƙaunarta take ba"

"To sai ta bar musu dama ai ba dasu taje gidan ba."

"Mameey kema fa kina jin zafin yadda Sadiya ke shan wahala a gidan Yazid duk da cewar Yazid yana ƙaunar Sadiya, to ya kike tunanin Sadiya za taji idan aka ƙwace yaranta aka damƙa a hannun da babu kulawa?"

"Shi kenan tunda kun zaɓi Sadiya sama dani, taje ga miji nan ai dama itama miji ta zaɓa sama da mahaifiya" Tana gama faɗa ta tashi rai ɓace ta bar parlourn.

Faruq ya sauke ajiyar zuciya tare da faɗin "Aunty Sady dai ƙaddararta ce a haka, kuma naga da ita da Uncle Yazid gabaɗaya suna son junansu ya kamata both family ɗin su bar su su yi rayuwarsu mu bisu da addua"

"Ai ƙiyayyar Yazid a gurin Mameey fa ta daɗe Faruq"

"Na sani Aunty Saddiqa amma tunda har da yara ya kamata Mameey ta haƙura."

Sai lokaci Surayya ta ƙara soma baki a maganar ta ce, "Ni fa bana son Yazid ɗin nan, dama tun farko ba su dace da Aunty Sadiya ba, ni wlh ban san me ta gani ba"

"Ki rufa mana baki mara kunya kawai"

"Daga faɗar gaskiya"

"Ke har wata gaskiya ne da ke"

"Kai kuma Faruq ka kiyayeni wallahi"

"Oh ni dai kike so kice na kiyaye ki"

"Kin san dai ba zan taɓa faɗa miki haka ba Aunty Saddiqa."

Tana gama maganar itama ta miƙe ta wuce. Saddiqa ta girgiza kai tare da cewa "Allah ya kyauta."

****** *******

Kuka sosai suke yi ita da Ammi sai da suka yi mai isarsu sannan suka tsagaita.

"Amma gaskiya baku kyauta mana ba da kuka kasa faɗa mana gaskiya"

"Yanzu ai ga shi kun sani, kuma a baya da mun faɗa muku gaskiya ai ba zaku iya protecting ɗin ta ba."

"Haba Malama, ita ɗin fa 'yar mu ce jininmu" Ammi ta furta rai a matuƙar ɓace.

Abbu ya yi saurin cewa "Mariya kiyi shiru ba abin faɗa bane, tunda dai tana raye mu godewa Allah, da fa har mun fitar da rai da ita."

"Wannan ai mugunta ce, kalli yadda Badriyya ta koma, wata takwas kana ɗaki, kawai dai so sukayi su kwantar da ita kamar yadda shima Affan yake a kwance"

"Wace irin magana kike faɗa haka Mariya?"

"Komai ma, taya za ki ɗauko mutum ki ajiye wata takwas a ɗaki kuma ba wani ciwo yake ba, to wallahi sai na ɗauki matakin shari'a dake."

Murmushi Mommy ta yi sannan ta ce, "Wannan shi ne babban kuskuren da za ki tafka a rayuwarki, muddin kika bayyana cewar Badriyya da Affan suna raye"

Lawisa dai bata ce komai ba, sai ma faɗuwar gaba da taji ya risketa.

"Badriyya tashi mu tafi, wallahi Affan ko ɗan gwal ne kin gama aurensa, kuma Allah ya isa bamu yafe ba"

Sai a lokacin Badriyya ta saki wani sabon kuka, duk yadda taso ta bar gidan amma a yanzu sai taji bata so, duk da a gidan ma ba wani haɗuwa suke da Affan ba, amma a yanzu ta san in ta tafi za ta ƙara yin nesa da shi ne. Sai dai duk yadda taso amma iyayenta suka turje har sai da suka tafi da ita ba tare da Affan ya san wainar da ake toyawa ba.

Dare

Tana ajiye masa abinci ta kalleshi taga idanuwansa a kanta suke, zama tayi tare da faɗin "Ko dai kana buƙatar wani abu?"

"Ina Nashwa?" Ji ta yi gabanta ya faɗi, dan maganar Nashwa kawai ake mata ta ji ranta ya sosu, saboda ta san ba za su taɓa dawo masa da Nashwa ba.

"Yaya bata nan, Nashwa tana Kano mu kuma muna nan Abuja, amma insha Allah next week zamu koma Kano"

"Meyasa Nashwa bata zo tayi jinyata ba, ko ba a sanar da ita dalilinta na samu haɗari ba, ita ta takura sai anyi dinner kuma a hanyar zuwa muka samu accident, shin ba a ɗaura auren ba?"

"Yaya baka da wata cikakkiyar lafiya, ba a so ka riƙa doguwar maganar so dan Allah ka yi haƙuri a hankali za ka san komai"

"Yaushe? Ina so ku sanar dani gaskiya na ga sai ɓoye-ɓoye ake min"

"Yaya calm down ka dai warke sosai sai ka gaji da ganin duk wanda kake so gani"

Murmushi kawai ya yi, ita kuma ta miƙe ta fita.

Kai tsaye bedroom ɗinta ta wuce, tana shiga ta faɗa gado tare da fashewa da kuka, sai kuma ta miƙe tana share hawaye ta janyo waya.

"Ai na ɗauka ɓatan hanya kika yi Lawisa"

"Haba dai"

"E mana, na sanki ba ki da zumunci baki neman mutane, ke ko a group ma baki yin magana."

"Wallahi abubuwa ne suka kwaɓe anan Rayyana, amma dai in komai ya lafa zan dawo normal"

"It's ok. Ya kike ya gida da kuma Mommy?"

"Lafiya lau. Dama na kirana ne na tambayeki"

"Ke nan dai ba zumunci kika kira a yi ba"

"Har da zumuncin ma"

"Faɗi gaskiya dai"

Murmushi ta yi sannan ta ce "Gaskiyar kenan"

"To ina sauraronki"

Zama Lawisa ta gyara sannan ta ce "Ina wannan wadda kika ce tana kama da matar da Yayana zai aura lokacin da na saka pre wedding pictures ɗinsu?"

"Oh na gane, ai an ɗan kwana biyu ƙila ma har ta kusa haihuwa ko?"

"Ina fa, kin san ko bikin ma ba ayi ba ta rasu sai shi kuma Yayana ya haɗu da cutar paralysis"

"Subhanallahi! Amma baki taɓa faɗa ba Lawisa"

"Rayyana abubuwa sun caɓe mana wallahi bani ma da wannan nutsuwar social media ma ai ɗauke mata ƙafa na yi"

"Allah sarki, Allah yajiƙanta da rahama, ya jikin nasa?"

"Da sauƙi sosai"

"Allah ya ƙara masa lafiya"

"Amin ya Allah. Dama cewa na yi idan babu damuwa ko za ki haɗani da mai kama da Nashwa, kuma ki turo min hoton ta "

"Kin san mene matsalar?"

"A'a sai kin faɗa"

"Matar aure ce yaranta har biyu, na ukun ma dan baizo da rai ba C.S aka mata a gida tayi jinya dan munje mun dubata, kin san a time ɗin na ce miki dan dai taku siririya ce kuma tana da ɓular hanci da fashin goshi da sai na ce Sadiya ce, to itama Sadiyar yanzu ta zama siririya"

"To amma ba kin ce min ƙawarki ba ce?"

"E, ƙawata ce auren wuri ta yi"

"Oh Allah sarki"

"But duk da haka ina son contact da kuma hotonta in babu damuwa"

"Gaskiya bani da ko ɗaya amma anjima insha Allah zan leƙa gidan nasu sai na karɓar miki number, hoton ne dai ban san ya za ai ba"

"Ko da dabara ne a lokacin a ɗauka please"

"Shi kenan zan jarraba"

"Nagode sosai Rayyana"

"Haba karki damu."

5 Months Later

Jin knocking ya saka ya yi saurin ɗaukar hoton ya mayar ƙasan pillow, a daidai lokacin Mameey ta kunno kai cikin ɗakin, sai da ta ƙarewa ɗakin kallo sannan ta zauna gefen gadon.

"Mene yake damunka Faruq?"

"Babu komai" Ya faɗa kansa a ƙasa.

"Faruq ka san kai baka isa kayi min wayo ba ko? Dududu nawa kake?"

"Mameey idan akwai ba zan ɓoye ba"

"Amma Dr ya faɗa min damuwa ce ta yi maka yawa shiyasa jininka yake hawa, ya kuma sanar min in akwai abin da ake maka to a daina, ka faɗa min ko dai wani yana maka abin da baka so?"

Kai ya girgiza sannan ya ce "Mameey kawai stress ɗin karatu ne"

"Karatu?"

Ya gyaɗa kai.

"To ai friend ɗinka ya ce min tsawon wata guda baka je school ba, ko kaje baka shiga lecture, wani lokacin kuma baka shiga school ma, anan kuma ka ɗauki mota ka fita, shin canjin nan na mene? Me ke faruwa?"

"Mameey ƙarya yake min"

Ya furta yana ƙoƙarin dira daga gadon.

"To ina kuma zaka je?"

"Ina son zuwa gidan Aunty Saddiqa ne"

"To ai shi kenan, ita ƙila ka faɗa mata gaskiya" Ta faɗa sannan ta miƙe ta bar masa ɗakin.

Hoton ya janyo ya ƙura masa ido, sannan ya rungume hoton ya lumshe ido yana jin kansa na ƙara zafi da tafarfasa, da sauri ya miƙe ya mayar da hoton inda yake ɓoyonsa sannan ya faɗa toilet. A gurguje ya yi wanka ya shirya sannan ya fita.

Mameey ta yi mamaki da taga bai karɓi key ɗin mota ba ya fice haka abinsa, anan ta fahimci lallai damuwarsa mai yawa ce. Waya ta ɗauko ta kira Saddiqa.

"Mameey da yanzu nake shirin zuwa, ina wuni"

"Lafiya lau, ya kike?"

"Alhamdulillah"

"Yanzu nake shirin zuwa na duba jikin Yaro, na ji Surayya ta ce har yanzu jikin nasa babu daɗi"

"Ni ai lamarin Yaro har tsoro yake bani, yanzu yake ce min ya tafi gidanki shiyasa na ce bari na kirawo ki"

"Nan ya taho kenan"

"E haka dai ya ce min"

"To shi kenan bari na jira shi"

"Yawwa idan yazo dan Allah ki riƙeshi ya sanar miki abinda ke damun shi"

"To shi kenan."

****** ******

A zaure ya tsaya yana sallama, tana daga ɗaki ta ji sallamar Faruq ta fito tsakar gida tare da amsa masa sallama.

"Yaro shigo mana sai kace wani baƙo" Ta faɗa tana tsaye daga ƙofar ɗakin.

"Ashe za ki ɗauki murya."

"Haba to ni ko a mafarki ai ba zan kasa shaida muryarka ba Yaro"

"Gaskiya Aunty Sady ki daina ce min Yaro, ni fa na isa aure, kin ga yarinya nan" Ya faɗa yana nuna Ihsan da ta fito, sannan ya ƙarasa gami da miƙa mata ledar da yayi masu tsarabar chocolates da fancy biscuits."

"Ka san dai ba zata iya riƙewa ba ko, duk mene ka siyo haka mai uban yawa?"

"Babu ruwanki, yarana na yiwa tsaraba" Ya faɗa yana fito da chocolate ya bawa Ihsan sannan ya kama hannunta suka shiga parlourn.

"Thank Allah kuna da nepa"

"E basu daɗe da dawo da ita ba, ga zafi ana yi, ai mukam muna nan muna shan OX ɗin daka saya mana, da yanzu muna ta fama da mafici"

Murmushi ya yi tare da faɗin "Najma tana school?"

"Ana can sun kusa tashi ma."

"E, 12 ta kusa"

"Za ka ci dambu?"

"Aunty Sady ni kome kika bani ai ci zan yi"

"Ok. Bari na zuba maka, dama akwai magana a baki na"

"Kema har an faɗa miki kenan"

"Kuma baka so na sani ko?"

"Faɗa ne ni bana so"

"Ai dole mu yi maka tunda mun girmeka"

"Kai Aunty"

"E mana."

Sai daya gama ci ya sha ruwa sannan ta kalleshi a nutse ta ce "Yaro wallahi ka rame, kuma kallo ɗaya za a yi maka a gane kana da damuwa, ni na yi mamaki ma daka zauna ka ci abinci sosai anan dan cewa aka yi baka cin abinci ma"

Shiru ya yi kafin ya ce "Aunty Sady ni sunana Faruq"

"To na ji, faɗa min mece ce matsalar?"

"Ko da na faɗa miki baki da maganinta"

"Ina da shi dan ko shawara na baka na san na yi maganin wani ciwon"

"Hmmm!"

"Dan Allah ka faɗa min Faruq"

"Aunty Sady akwai wacce nake so, kuma wallahi lokaci ɗaya na ji kawai sonta ya shige ni ba tare da na yi aune ba, Aunty na san kin san so tunda naga irin son da kike wa Uncle Yazid, to ni kuma wadda nake so na san ba zata taɓa sona ba, shiyasa nake son yaƙi da zuciyata na ga na cire son amma abin ya gagara" Sai ganin hawaye tayi a kuncinsa, abin ya bata mamaki sosai.

"Faruq kuka akan mace?"

"Ni kaɗai na san yadda nake ji."

"To wace ce?"

"Mene amfanin faɗar, bayan ba za ki iya convincing ɗinta ta so ni ba? Kawai a barni a haka"

"Ka faɗa min, na maka alqawarin ko ɗiyar waye zan jarraba"

"Za ki iya?"

"Sosai ma"

Shiru ya yi yana kallon gefe guda na tsawon second 30 kafin ya juyo ya kalleta.

Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting. Sannan ina maraba da duk wanda suke so a tallata musu hajarsu, a cikin littafin, ko kuma a facebook da tiktok ku tuntuɓi wannan lambar ***

VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:

Guda 1: ₦500

Guda 2: ₦900

Guda 3: ₦1400

Guda 4: ₦ 1800

Za'a turo kuɗin ta wannan account.

Acct no: 6370370016

Acct name: Halima Salahu Adamu

Bank name: Fidelity Bank

Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number ***

Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number ***.

Shaidar biya ta wannan wannan number ***

lLITTAFAN SUNE:

1-WUTAR ƘAIƘAYI

2-WA'ADI.

3-A CIKIN IDO..

4-TAZARAR SO

#FITATTUHUDU2025

#WUTARKAIKAYI

#SaNaz_deeyah