Barrister Hibba
by @nusybee143
💥 BARRISTER HIBBA💥
✍️ Nusy bee
Page 2
Wani irin kallo ya watsawa Marwa,wadda tana gama magana mayar da kanta ga waya tayi,ya ɗauke kanshi yana jinjina rashin tarbiyya da rashin sanin darajar mutane irin ta wasu yaran masu hannu da shunin
Shiru wajen ya ɗan ɗauka na wasu ƴan sakwanni, Jabir sai gumi yake yanko masa,don ya sani sarai ba'a yi musu magana biyu akan dokar yayar su, Arwa ce ga cigaba da magana"bazai yiwu kayi denying aikin yaya ba muddin ta bukaci kayi ƙarin lokaci,ai dai an gaya maka nawa za'a baka ko?"
Danne ɓacin ranshi yayi yace "eh har an bani albashin farko ma"
"Alright, Allah ya bada Sa'a,zaku iya tafiya,ga wannan"ta miƙa musu dubu ashirin ashirin
Da sauri Jabir ya dafe yana ta godiya,shi kuwa Muyassar baiyiwa kudin kallo biyu yace"na gode, I'm okay with my salary"ya fice daga parlourn, Jabir ya bi bayan shi
A compound Jabir ya tsayar da Muyassar yana faɗin"kai!kar ka janyo wa kanka matsala,ka godewa Allah da ba shugabar tasu bace"
Cikin ɓacin rai Muyassar yace"da nayi me?don kawai nayi tambaya?"
"Baayi musu tambaya, musamman wadda ta saɓa da ra'ayin su,ka kiyaye Muyassar"gajeren tsaki Muyassar yaja ya wuce wajen zaman shi,yana jiran lokacin tafiyar shi ya tafi gida,don ya bar ammin shi jikin nata na ƙoƙarin tashi
Ƙarfe biyar nayi ya miƙe,yau saboda ɓacin rai ko sallama baiyiwa abokan aikin nashi ba ya fice daga gidan,a bakin gate Allah ya taimake shi ya samu adaidaita sahu ya wuce zuwa unguwar su gandun albasa
Har ɗakin ammi yayi sallama,tana zaune a gefen gado ta amsa masa,ya shiga ya zauna akan daddumar da ya gani a shimfiɗe, cikin girmamawa ya gaishe ta,ta amsa ta ɗora da faɗin
"Yassar ka dawo?"
"Na dawo ammi,ya na same ku?"
"Lafiya ƙalau,ya aikin?"
"Aiki alhamdulillahi,ya jikin naki?"
"Jiki alhamdulillah,mun samu afuwa"
"Ammi ina zeenat?"
"Zinatu ta je dubiyar ƙawar ta nan gidan malam dallatu,amma ba daɗewa zatayi ba,nasan duk inda take Yanzu tana shirin dawowa,ko ta taho ma"
"To Allah ya dawo da ita lafiya"
Shiru ya ɗan ratsa ɗakin,kafin ammi ta dubi Muyassar tace"Yasar ya dai?"
"Me ya faru ammi?"
"Na ganka ne ba yadda na saba ganin ka ba"murmushi yayi yace"hoo ammi,da da wata matsala ai zan gaya miki,ke dai kawai ki sanya ni a addu'ar ki, Allah ya dafawa rayuwa ta,yanzu dai an siyo miki maganin da na rubuta miki?"
"An siyo min Yasar,har ma nasha, Allah yayi albarka"yayi murmushi,kafin yace komai zeenat ta shigo da sallama
Suka amsa,cikin girmamawa ta durƙusa ta gaida Muyassar,ya amsa yana faɗin"ya mai jikin da aka ce kin je dubiya?"tayi ɗan murmushi tace mai jiki alhmdllh,ta ji sauƙi"
"To Allah ya ƙara sauƙi,zan samu abinci?
Kafin tayi magana ammi tace"amma Yasar ka cika ganganci, menene dalilin da yasa kake son zama da yunwa bayan kasan yadda kake fama da ulcer?na San dai ana baku abinci ko?"
"Ammi abinda suka dafa ne bana ci, shiyasa"
"To shikenan, Allah ya kyauta,zeenatu kawo masa abincin"babu musu zeenat ta fice don kawowa yayan nata abinci,ya bi ta da kallo cike da tausayin ta,da yana da yadda zaiyi da ya inganta rayuwar ta fiye da yadda yakeyi yanzu
MAITAMA,ABUJA, NIGERIA
"Dr Ahmad wai meyake faruwa ne?wannan matar meyasa har yanzu baayi mata aikin nan bane?na kagu su bar min asibiti saboda Waɗannan family ɗin nata were so annoying,I detest seeing them in my hospital"cikin ƙunar rai yake maganar
Wanda aka kira da doctor Ahmad yayi ɗan murmushi yace"sorry doctor,you Know the policy,nayi bincike sosai,and naga akwai possibility na magani zai iya narkar da ciwon,no need of surgery,ka rinƙa daukar komai da sauki Dr HAMMAD, everything that happens will definitely comes to an end"
Yatsina fuska Dr Hammad yayi batare da yayi magana ba,ya fara duba x-ray ɗin da aka kawo masa few minutes ago
Har Dr Ahmad ya miƙe zai fice sai kuma ya juyo yace"sir!Dr Khaleed yayi min magana akan aikin da zamu je muyi next week a asibitin su,but unfortunately something bad happened to Dr zahraddeen"
Ɗagowa yayi ya kalli Dr Ahmad na wasu few minutes kafin yace"what happened to him?"
"He has been arrested"
"What!for what reason?"a cewar Dr Hammad cikin daga murya
"I have no idea sir,har zuwa yanzu bamu samu dalili ko ɗaya da yasa aka kama shi ba,amma mun samu sunan wadda ta saka aka kama shi"
Shiru Dr Hammad yayi yana kallon shi,kafin yace"wacece?"
"BARRISTER HIBBA AIYO, Dr mukhtar yayi kokarin magana da ita but unfortunately she is not willing to listen to anybody,she even switch her phone off"
Shiru Dr Hammad yayi yana kallon Dr Ahmad cikin tsananin ɓacin rai,shi bai taɓa ganin arrogant kuma stubborn girl irin wannan yarinyar ba,ya daɗe yana fatan ta shiga boundaries ɗin shi ya karta mata rashin mutunci,yanzu gashi ta kawo kanta har inda yake,yayi wani murmushin mugunta ya kalli Dr Ahmad yace"this girl didn't know who Zahraddeen is to Hammad,Amma zan nuna mata hakan a aikace ba a baki ba,ka bar case ɗin a hannu na,ai yanzu ance bata ƙasar ko? I think zan bi ta har ƙasar da taje nayi mata abinda ko da wasa akace ta kalli Zahraddeen ta harare shi ma bazatayi ba, ballantana har ta kulle shi"
"No sir,ba girman ka bane Please,ka bari ta dawo,naji Dr Safiyya tace nan da next week zata dawo"
"Allah ya dawo da ita lafiya,she will know who I am,I will teach her a memorable lesson"Dr Ahmad yayi murmushi yana jinjina masa sannan ya fice daga office ɗin
Komawa Dr Hammad yayi jikin kujerar da yake zaune yana tuna wata haɗuwa da sukayi da hibba aiyo,a asibitin su Dr Khaleed, asalima wajen shi tazo,bai taɓa ganin mace mai ji da kai da ɗagawa irin ta ba,bata ɗauki wulaƙanci ko ƙasƙanta ɗan adam a bakin komai ba,ya tuna yadda tayi embarrassing ɗin shi a gaban mutane,sannan ta wuce cikin kwanciyar hankali ta shige motar ta ta tayar ta bula Masa ƙura
Murmushi mai ciwo yayi yana faɗin"nayi miki alƙawari sai na wulaƙanta rayuwar ki,sai kinyi kuka da idanun ki kinyi dana sanin zuwa duniya,da HAMMAD ABDULLATIF kike magana,zaki raina kanki tabbas"ya ƙarashe yana dukan tebur ɗin gaban shi
Kira ne ya shigo wayar shi,ganin mai kiran da sauri ya ɗaga wayar da sallama,amma sai yaji hayaniyar yara suna faɗin"daddyyyyyyy! happy birthday!!"take ya nemi duk wata damuwa da ke ranshi ya rasa,yay murmushi yana lumshe sexy eyes ɗin shi yace"Weldone sweet angels,how are you doing?
Mifra ce tace"alhamdulillah, Daddy when are you coming back?we really missed you badly, where is Nihla?"
"I'm here daddy,Mifra ce take ture Ni tana so ta hana Ni magana da kai"
"Wallahi daddy ƙarya takeyi min,mumu kawai"
"You hear daddy Mifra is calling me mumu"a cewar Nihla da Muryar kuka, Hammad ya dafe kanshi yana jinjina rigima irin ta twins ɗin nan nashi,zuwa can yace"is okay please,in Sha Allah I'm coming back very soon,but idan kunsan faɗa zakuyi I will rather continue my work,don Zane ku ma zan rinƙa yi"Nihla tace"we are sorry Dad"Mifra ma tace"we are very sorry,we apologize"
"Good girls,now Ina Ummi na?"
"Daddy bata nan,she forgot her phone that's why we use that opportunity to call you"a cewar Mifra uwar surutu sama da twin sister ɗin ta
"Daddy mu Ina momyn mu?kace tayi tafiya kuma har yanzu bata dawo ba,we really missed her so much"
Kamar saukar aradu haka Hammad yaji maganar Nihla,har wani jiri yake ji,babu shiri yace"I will call you back"yayi azamar kashe wayar batare da ya jira amsar su ba
Hoton matar shi Namra da ke kan fuskar wayar ya tsurawa idanu,take idanun nashi suka ciko da ƙwalla,a hankali ya shafa hoton yana faɗin "Allah yaji ƙan ki da rahama Honey, Allah yayi miki kyakkyawan masauki a aljannatul fidaus, haƙiƙa ke ɗin ta dabam ce,samun mai maye gurbin ki abu ne mai wahala"
#Nusy_bee