Barrister Hibba

Barrister Hibba

by @nusybee143

💥 BARRISTER HIBBA 💥

✍️ Nusy bee

Page 3

Yana kallon kiran su Mifra yana shigowa a wayar ummin nashi amma bai ɗaga ba,daga baya ma sai ya danna musu busy ya kashe wayar,a lokacin gaba ɗaya ya manta da wata Hibba da alwashin da ya ɗauka akanta, saboda tunawa da matar shi abar ƙaunar shi wadda ya rasa ta shekaru biyu da suka wuce a haihuwar ta ta biyu,tabbas yaso Namra, Namra ta so shi, soyayyar da suka yiwa juna ba kaɗan bace, family ɗin su har tsokanar su sukeyi Layla da majnun,yau gashi a doron duniya amma babu Namra,kuma ya san samun kamar Namra a rayuwa abu ne mai wahala,mace ce selfless,mai kirki da damuwa da damuwar wasu,a kowanne lokaci damuwar shi tana gaba da tata, shiyasa yake jin har abada bazai samu mace kamar Namra ba

Jiki a mace ya miƙe ya bar office ɗin ba don lokacin tashin shi yayi ba,sai don babu wani aiki da zai iya ƙara yi yanzu


ALI MUHAMMAD KABO AREA, RAILWAY ESTATE, KANO STATE

"Mtseeeeewwww,dalla malama kiyi ki fito,You are wasting my time,kizo kiyi ta sme sme kina ɓata wa mutane lokaci,haba!"a cewar Marwa cikin fusata

A kaikaice Arwa ta kalli Marwa tana faɗin"dalla malama kar ki dame ni,ki bar ni naga shiryawa a nutse,kar ki rikita min kai"

"Okay in tsaya ki cigaba da ɓata min lokaci, wallahi zanyi tafiya ta,yamma tana yi kuma kin san yaya ta hana mu yin yamma a waje"

"Mtseew sai kiyi ai,ƴar wahala"

"Ni kike kira ƴar wahala? wallahi bazan sake tafiya da ke ba,aikin banza kawai"daidai nan mama ta iso wajen tana faɗin"to Tom and Jerry,kun fara raba halin ko?ku dai Allah ya shirye ku,ban san ranar da zaku girma ba wallahi"

"Tun ɗazu fa na sanar mata zamu je shopping,kin gani wai sai yanzu take shiryawa fa,na mata magana zata fara min rashin kunya"

Arwa tayi shewa tace "sai dai uwar rashin kunya,idiot ke yanzu a mentality ɗin ki kece babba akaina ko?"Marwa tayi kan Arwa da duka,mama ta riƙe ta ta fara faɗa"wato a gaba na zaku cigaba da raba hali ko?to wallahi idan baku kama kai kun daina shiririta ba zan kira yayar ku in faɗa mata,don bazan iya tashin hankali ba"Arwa dai bata sake magana ba,ta ɗauko tsadaddiyar jakar ta irin ta Marwa,dama kayan jikin su ma iri ɗaya ne,wasu tsadaddun English wears ne riga da skirt sai mayafi da suka ɗora, Marwa tayi gaba Arwa ta bi bayan ta tana faɗin"mama sai mun dawo"

Suna zuwa lokacin Muyassar ya fito da mota yana jiran su, kallo ɗaya yayi musu ya ɗauke kai,don har yau bai manta abinda Marwa tayi masa ba,gashi dukkan su ba gane su akeyi ba ballantana ya ware wadda tayi masa ya ajiye ta a gefe,babu wadda ta damu da shan ƙamshin shi,don Marwa ma wayar ta take dannawa, Arwa ta dube shi fuska babu yabo babu fallasa tace"maya global house zaka kaimu,zamuyi shopping ne"batare da ya kalle su ba yace"to ba matsala"

Sun hau titi sosai,wayar Marwa tayi ƙara,da zumuɗi ta ciro wayar daga jaka,don ringing tone da ta saka wa mai kiran ta dabam ce,itama Arwa cike da zumuɗi ta ƙara matsowa, Marwa ta ɗaga,a tare suka haɗa baki suna kiran"miss You so much Yaya,how are you doing?"

"I'm good,how was your holiday?"

Marwa tace"is not funny doing holiday without you and Maryam, please come back Yaya"a shagwaɓe take maganar

Ɗan murmushi matar tayi tace"I'm coming soon, where is Arwa?"Arwa tayi karaf tace"I'm here Yaya,how was little?"

"She is missing you, what are doing now?"

Arwa tace"maya global house muka nufa,zamuyi shopping ne"abinda ta fara faɗa ne ya sanya su kallon juna cikin mamaki da takaici,don faɗa takeyi ta inda take shiga ba ta nan take fita ba,a ƙarshe ta tabbatar musu da kar su je ko'ina su koma gida

Muyassar yana gaba yana jinsu, zuciyar shi cike da mamakin wannan ji da kai da isa irin ta yayar tasu,da alamu bata bar kowa, Arwa ce tace"driver ku koma gida kawai"cikin ƙunar rai tayi magana

"Sai muyi shopping ɗin online kawai, tunda yaya tace mu koma gida"a cewar Marwa

Har suka je gida babu wadda ta sake magana saboda takaici,amma still basu ji haushin yayar tasu ba,suna fitowa kowacce ta wuce ɗakin ta

ANNASTRASSE, FRANKFURT CITY, GERMANY

Ƙaton luxury room ne da ban taɓa ganin mai kyau da haɗuwar shi ba,daga kan royal bed, cupboard,hatta da su bed side lamp rantsatstsu ne,duba na nakai kan kantamemen gadon,wanda aka shimfiɗa masa farin bed sheet ƙal,ta lulluɓa da farin duvet,dogon gashin ta da ya sha gyara da kula ya zuba ya rufe mata fuska,a hankali naga tana ƙoƙarin buɗe idanun ta,zaunawa tayi kan gadon tana karanta addu'ar tashi daga bacci a zuciyar ta,ta kai a ƙalla mintuna biyar kafin ta sanya hannayen ta ta mayar da gashin ta bayan kunnuwan ta,sai a lokacin na samu ƙare mata kallo

Tsananin kammanin ta da twins Arwa da Marwa na gani,sai dai ita bata kai su haske ba,kai tsaye baza'a kira ta fara ba kuma baza'a kira ta baƙa ba,tashi tayi ta sauko daga gadon,daga yanayin tafiyar ta na fuskanci cewa the lady is unique and classy,Kai tsaye banɗakin da ke cikin ɗakin ta shiga,ta kai aƙalla one hour kafin ta fito, shiryawa tayi cikin riga da wando track suit farare masu tambarin ƙungiyar wasan ƙwallon ƙafa ta PSG,ta ɗaura scarf a kanta ta ɗaura agogon ta na diamond sannan ta fice daga ɗakin

Ɗakin kusa da ita ta buɗe ta shiga,wow!ya haɗu sosai amma bai kai nata ba,daga can gefe ɗan madaidaicin gado ne,sai dai tsadadde ne sosai, yarinya ce wadda aƙalla zata iya kai wa shekaru biyar zuwa shida, a kallo ɗaya mutum zai tabbatarwa kanshi yarinyar baturiya ce,yanayin kalar fatar ta da gashin kanta,ta nutse a tsakiyar gadon ta sai bacci take peacefully

Tun tashin ta batayi murmushi ba sai da tayi arba da lovely soul ɗin tata,tayi murmushi sosai kafin ta matsa kusa da ita ta fara bubbuga pillow ɗin ta tana faɗin"time up baby!it is getting late,wake up!wake up sweetheart!!!"

A hankali yarinyar ta fara buɗe blue eyes ɗin ta, murmushi ta ƙara yi tana faɗin"say your dua best friend"ɗan murmushi yarinyar tayi tana karanto addu'ar tashi daga bacci,bayan ta gama ta miƙe zaune,ita kuma ta kama hannun ta har bakin toilet,cikin Yaren German tace mata"kiyi alwala kiyi sallah,zan yi miki wanka,yau zamu wuce UK wani aiki,daga can zamu wuce Nigeria"

Tuni yarinyar ta wartsake cikin Yaren German itama take faɗin"zamu ga su Aunty twins?

Da murmushi cikin harshen turanci tace" of course dear,our flight is in next two hours, please be hurry"daga haka ta fice daga ɗakin

Tana komawa ɗakin ta wayar ta ta fara ƙara,sai da ta ɓata sakwanni kafin ta ɗaga batare da tace komai ba

A ɓangaren Barrister Khadijat ta soma magana don ta san halin mutuniyar tata

"BARRISTER HIBBA AIYO! I hope you are doing good!"

Yatsina fuska Hibba tayi tana faɗin"I'm normal,how was your husband and children?"

"They are all fine, barrister,it is about that case,you are not saying a word"

Yatsina fuska tayi tace"yeah! I'm aware, everything is moving smoothly, don't bother yourself, and, don't say a word to barrister Awwal tofa"

Murmushi mai sauti Barrister Khadijat tayi tana faɗin"Hibba kenan,do you said anything to me ne da kike tunanin zan gayawa wani?"

Hibba tace"na dai faɗa miki,don't say anything to barrister tofa, talkless of another person"tana kaiwa nan ta kashe wayar ta,ta jefar kan gado sannan ta wuce wajen kayan ta ta zari abubuwan ta masu amfani ta zuba a ɗan ƙaramin akwati

Ƙarfe takwas da mintuna goma sha bakwai suka fito daga gida ita da yarinyar ta,sanye suke da jacket ta sanye manya manya, Hibba ce ke jan akwatin yayin da ta riƙe hannun Maryam,kai tsaye Frankfurt airport suka nufa,basu kara awa guda a Frankfurt ba jirgin su ya ɗaga zuwa manchester na ƙasar United kingdom (England)

Suna sauka basu ɓata lokaci ba kai tsaye suka wuce saint Mary's hospital da ke nan manchester,sai da hibba tabi dukkan ƙa'idojin asibitin sannan akayi leading ɗin ta zuwa ɗakin wadda take buƙatar gani,duk da ɓata mata lokaci da query da ta amsa bata wani damu ba

#Nusy_bee