Page 9
by @sanazty
WUTAR ƘAIƘAYI
Wattpad@SaNazdeeyah_
_Arewabooks@sanazty
Facebook@SaNaz Deeyah
Tiktok Handle: Habibtyn Habibi👸💍🦋
Youtube: ***
Facebook page: ***
KARAMCI WRITERS ASSOCIATION
[karamci tushen mu'amula ta gari]
Book 1
```🆓Page 9```
Rai a ɓace ya wuce ɗaki, bai daɗe ba sai gashi ya fito haka ya saka kai ya fita ya bar ta cikin tashin hankali. Tana durƙushe a ƙasa har ta yi kuka ta gama sai hawaye kawai dake fitowa jefi-jefi, maƙotanta biyu suka doka sallama. Baki kawai ta motsa dan muryarta taƙi fitowa; su ma jikinsu a sanyaye suka shigo suka zauna.
"Sadiya dan Allah kiyi haƙuri"
Hannu ta saka ta goge hawaye sannan ta ɗan yi murmushi wanda iyakarsa leɓe.
"Sannunku da zuwa."
"Yawwa, kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki."
Sun mata kara sosai domin sun zauna har bayan magriba sannan suka tafi, Sadiya hankalinta a tashe yake sosai ta kasa sukuni ta kasa sakin jiki haka har aka yi isha'i tana zaune tana zulumin abinda zai je ya dawo.
"Ina take algungumar" Shi ne abinda ta ji lokacin ta gama yi wa yara shimfiɗa. Fatima da Maryam ne suka shigo sai wata ƙanwar Umma mai suna Aunty Adawiyya. Sadiya na fitowa tsakar gida kawai taji an rufeta da duka ta ko ina, tun tana ƙoƙarin kare kai har ta kasa jikinta gabaɗaya sun mata lilis bakinta kuwa har ya fashe haka suka barta a kwance tana numfarfashi. Najma na gabanta tana jijjigata ita kuma Ihsan tuni ta yi bacci, tun tana iya gane abu har ta daina saboda dukan da suka yi mata.
***********
"Hajiya sai dai fa ku yi haƙuri amma ba zamu iya ba da beli ba sai dai ku dawo zuwa gobe idan wanda ya shigar da ƙara ya yafe, amma ba a ba mu damar beli ba"
"Officer dan Allah ku taimaka wallahi tana da larurar hawan jini"
"Amma ta san da haka take rashin kunya?"
"Haƙuri za kuyi dan Allah"
"Gaskiya ba zai yuwu ba"
Har zai ƙara magana Umma ta ce "Rabu da su Yazid, mu je kawai"
Kallon Umma ya yi sannan ya ce "Yakumbo Bahijja bata da lafiya"
"Yazid zama anan ƙarin cin mutunci da ƙasƙanci zai ja mana, saboda talaka ba su ɗauke shi a bakin komai ba"
Kallon ɗan sanda ya yi sannan ya juya kawai ya fita rai a ɓace Umma ta mara masa baya.
"Yazid!"
Ya ji ta kira sunansa dan haka ya tsagaita saurin da yake, ita kuma ta ƙaraso gabansa ta kalle shi sannan ta ɗan kauda kai.
"Ka haƙura da wannan yarinyar indai ba da gwal aka ƙerata ba, kai ko gwal ce ita ai babu amfanin tarayya da abin da zai cutar da kai."
"Umma ba laifin Sadiya bane, saboda ni ban ga alamun ta san shi ba."
"Yazid na tabbatar da ta san shi dan ni na ga hakan da idona ba labari aka bani ba."
"Umma maganar ba ta nan ba ce, mu samu mu fitar da Yakumbo dai tukun."
****** ******
Yawo yake a tsakar ɗakin kafin ya juyo ya kalli Lawisa dake zaune kan sofa.
"Shiyasa na ce miki muje tare saboda bana so a samu matsala amma sai kika kawo min wani banzan uzurinki."
"Yaya ka yi haƙuri dan Allah wallahi ni da na san haka za ta faru da da kaina zan karɓa na kai."
"Hmmm! Ban taɓa ganin saunan miji kamar nata ba, wallahi darajar aure kaɗai ya saka ban wanka mishi mari ba, saboda idan na mare shi abin kan ta zai koma."
Ɗan zaro ido tayi sannan ta ce "To alhamdulillah tunda baka yi marin ba, amma fa wallahi da mun shiga uku, so kake ya fassaraka?"
"Na nawa kuma, ai sun yi kuma sai na shiga kotu da ita"
"Yaya Affan abi abin nan a hankali wallahi idan Mommy ta gane abin da muka aikata za a iya samun matsala"
Shiru ya yi tare da zama gefen gado ya saka hannu a fuska rai ɓace.
"Yaya!" Lawisa ta furta a sanyaye.
Ɗago ido ya yi ya kalleta.
"Ka yi haƙuri ka ba da damar a sallameta"
"Ba zan iya ba, sai na ɗauki mataki, domin da kwarto ta kirani bayan ko ina saurayi ban yi ba bare yanzu"
"To ni dai na gama shiri yanzu zan tafi, idan naje duk abin da ake ciki sai mu riƙa waya"
"Kin dage dai amma da kin bar ni naje da kaina"
"A'a duk da nan Kano ne amma za a iya samun wani wanda ƙila an masa transfer daga can yazo nan, ko kuma wani wanda ya san case ɗin ka acan Yola gara dai naje"
"Har tsawon wane lokaci kuke so na ɗauka ba tare da na sake ba?"
"Ko iya haka ma ai ka sake tunda kana zuwa ko ina."
"Ni fa yanzu babu komai a tare dani duk wani evidence da muke da shi yana gurin Nashwa kuma sun kashe ta sun karɓe komai to kina tunanin me zan iya yanzu, amma da ace ina da hujja a kansu ko ɗaya ce wallahi da sai na tona musu asiri"
"Allah ya ji ƙan Nashwa"
"Amin ya rabbi."
Tare suka jera suka fito, suna shirin fita Mommy ta sauko daga sama. "Ina zuwa kuma?"
Gabaɗaya suka jiyo suka kalleta.
"Ni fa ban gane me kuke nufi ba anya babu abinda kuke ƙullawa kullum sai na ganku tare"
Murmushi Affan ya yi sannan "Mommy ko mene za a ƙulla ai za ki sani"
"To ina kuma zaku tafi?"
"Lawisa ce za ta fita, ni ina gida babu inda zan je"
"Sabon salo ne yasa zaka rakata mota?"
Sai lokacin Lawisa ta ce "Kai Mommy"
"Kin ga Lawisa sai kin dawo" Ya furta yana juyawa ita kuma ta yi murmushi.
"Mommy an kirani emergency call daga asibiti so zan je na ji"
"Okay sai kin dawo. Kai kuma ƙaraso dama ina son magana da kai"
Suna zama ta kalleshi "Affan ka daina maganar aure ko?"
Ɗan murmushi ya yi sannan ya ce "Mommy ba haka bane, kece gabaɗaya kin yi min takunkumi"
"Affan kenan, yanzu dai ba wannan ba, ka ga dai tunda aka ɗauke Badriyya yau ku san wata huɗu kenan babu wanda ya sake kira, ko saki ma basu nema ba to shi ne na ce me zai hana mu nemesu ka sawwaƙe mata kawai"
Mommy ya ƙurawa ido dan gani yake kamar ba ita ba, bai taɓa tunanin za ta faɗi wannan maganar ba, ta cigaba da cewa "Na yi magana da ɗayar ƙawar tawa anan Kano suke zaune akwai yaranta biyu, ina so ka je ka gansu sai ka zaɓi wadda ta yi maka a ciki, sannan na yi magana da wani director abokin mahaifinku ne tun yana raye mahaifinku ya hidimta masa har ya kai wannan matsayi na Director anan wata jami'a so ya ce akwai slot da aka ba shi ya kuma saka sunanka, so at anytime za a iya nemanka"
Zama ya gyara sannan ya ce "Mommy amma mene fa'idar sakin Badriyya?"
"Saboda haka suke buƙata"
"Mommy dan Allah kiyi haƙuri mu ɗan ƙara masu lokaci, saboda ni na san Badriyya tana sona."
"So na hauka dai, duk wannan bala'in ba ita ce ta jefamu a ciki ba"
"Mommy duk da haka ina neman alfarma ki bani dama na kirasu na kuma yi magana da ita kafin yanke hukunci"
Shiru ta ɗanyi rai ɓace.
"Please Mommy"
"Na ji ba damuwa na baka dama."
"Thank you Mommy"
"It's okay. Yanzu dai yaushe zaka je gidan Hajiya Bilkisu"
"Mommy yaushe kike so na je?"
"Ko zuwa weekend jibi asabar ko kuma lahadi"
"Zan je ranar Sunday insha Allah"
"To shi kenan Allah ya kaimu"
"Amin ya rabbi."
******** *******
A hankali ta fara buɗe idanuwanta da suka mata nauyi, kallonsu ta fara yi ɗaya bayan ɗaya, Saddiqa da Surayya ne a kanta, sai Yazid.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." Ta furta hankali sannan ta kai dubanta ga hannunta da aka sakawa drip.
"Sadiya sannu" Saddiqa ta faɗa, sannan ta kalli Surayya, ki kira Dr kice ta farka.
Ɗan lumshe ido ta yi ta ji kanta yana juyawa sosai, sai kuma ta buɗe ta fara ƙoƙarin tashi zaune, Saddiqa ce ta taimaka ta zauna sai kuma ta fashe da kuka, a daidai lokacin kuma Surayya ta shigo tare da Dr.
"Kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki."
"Aunty ina su Najma?"
"Suna wurin Mameey"
Kallon Dr ta yi ta ce "Dan Allah Dr ka sallame ni yau." Ta sake fashewa da kuka.
A kan ta ya tsaya sannan ya ce "Kar ki damu zamu baki sallama idan muka ga yanayin jikinki amma dole sai kin kwantar da hankalinki."
Goshinta ya sha bandeji ga kuma gefen bakinta da ciwo.
Yana gama dubata ya ce "Kiyi haƙuri zamu saka miki drip idan ya ƙare sai a sallameki" Sai daya ɗauko ruwan ya saka mata sannan ya fita.
"Yazid kayi haƙuri amma zan iya samun matsala da duk wanda ya yi wa 'yar uwata wannan abin" Surayya ta yi maganar rai a ɓace.
"Surry kar na ƙara jin kin yi magana"
"Haba Aunty Saddiqa ki duba ki ga abin da suka mata fa, wannan wane irin abu ne, tun da Aunty Sadiya ta aure shi ba ta ƙara samun kwanciyar hankali ba."
"Surayya idan kika ƙara magana wallahi sai ranki ya ɓaci"
Shiru ta yi tana ƙara ɓata rai, kawai ta juya ta fita.
Saddiqa ta kalleshi ta ce "Ka yi haƙuri Yazid ka san Auta sai a hankali"
Murmushin yaƙe kawai ya yi tare da cewa "Babu komai."
Shiru ya ɗan biyo baya ƙafin ya ce "Aunty Saddiqa ina neman alfarma"
"To ina jinka"
"Dama game da Yakumbo da aka kama to sun ƙi sakinta dan a station ma ta kwana, sai yau ya ce sai ta ba shi haƙuri a bisa ɓata suna da ta masa sannan ta bawa Sadiya haƙuri. To kuma ga Sadiya a kwance a asibiti shi ne na ce ko zaki saka baki su saki Yakumbo wallahi tana da hawan jini, ta ba shi haƙurin ma ya ce lallai sai Sadiya ta haƙura zai ba da damar a saketa"
"Subhanallahi, waye wannan?"
"Wani ne wai Sadiya na kama da tsohuwar budurwarsa."
"Kuma sai me? Kama da wane ai bata wane."
"To haka dai ya ce, ni dai fatana a saki Yakumbo Bahijja."
"A saketa dan Allah ni dama ban ji haushin abin da ta yi min ba" Sadiya ta furta a sanyaye tana kwance a gado.
Saddiqa ta kalli Yazid ta ce "Ka kira a waya zan yi magana dasu."
"Nagode" Ya faɗa sannan ya kira wayar. Lawisa ce ta ɗaga suka yi magana da shi sannan ya ba Saddiqa wayar ta sanar mata da Sadiya ba lafiya amma ita kanta ba zata so a riƙe wani a dangin mijinta ko wani makusancin shi, sannan da kanta ma ta faɗa a sake ta dan haka su yi haƙuri komai ya wuce"
Sai da Lawisa ta kira Affan da ƙyar ta lallaɓa ya yarda aka saki Yakumbo.
Bayan Kwana Biyu
Har zai fita daga gida Umma ta dakatar da shi, ya tsaya yana kallonta kafin ya sadda kai ƙasa.
"Yazid ko dai ka fara shan wani abu?"
"Umma babu abin da nake sha"
"Yakumbon ka fa tana asibiti amma kuma ka ƙi ɗaukar mataki akan abin da matarka ta saka wani banza ya mata."
"Umma wallahi ni a ruɗe nake a wannan lamarin, itama Sadiya har gida aka je aka mata duka, kuma 'yan uwanta na zargin Fatima da Maryam ne, ga ta a asibiti"
"Ok so kake ka faɗa min cewa ba zaka iya rabuwa da karuwar yarinyar nan ba"
Ɗan lumshe ido ya yi, dan har cikin ransa sai daya ji wani iri da aka kira Sadiya da wannan suna. "Umm...." "Dakata Yazid wallahi a wannan gaɓar zan iya yin fito na fito da kai idan baka rabu da wannan yarinyar ba."
"Umma zan rabu da ita amma dan Allah ki bari sai ta samu sauƙi"
"Shi kenan Allah ya kaimu."
Da ƙyar ya iya cewa "Amin."
Yana fita kai tsaye gidan wan mahaifinsa ya nufa, wanda shi ne waliyyinsa a lokacin bikinsa da Sadiya. Ko daya je a ƙofar gida ya same shi da almajiransa. Bayan sun gaisa ya ce masa ya shiga ya gaisa da 'yan gida. Tunda ya kalli yanayinsa ya san akwai matsala dan haka yana shiga ya miƙe ya bi bayansa.
Suna zaune a zaure Yazid ya zayyana masa duk irin abubuwan da suke faruwa.
"Assha! Garin ya duk haka ta faru amma ba ka zo ka sanar dani ba Yazid?"
"Baffa na ɗauka zan iya kashe wutar amma abin ya ci tura"
"Subhanalillahi, yanzu ya jikin nata?"
"Da sauƙi tunda jiya ma har tana iya cin abinci da kanta"
"To Allah ya bata lafiya yasa kaffara ne, kuma insha Allah da yamma zan je na samu mahaifiyar taka, daga nan kuma zan yi ƙoƙari naje asibiti na dubata"
Kai Yazid ya gyaɗa.
"Dan Allah irin haka ta faru a riƙa sanar mini da wuri"
"To Baffa insha Allah"
Baffa da yamma kuwa ya samu Umma kamar dai yadda ya alƙawaranta kuma ya zaunar dasu tare da Yazid da ƙannen nasa. Dukkansu babu wanda ke fara'a dan sun tabbatar zuwansa ba zai zama alheri ba.
"Kenan ƙarana ka kai gurinsa?" Umma ta yi maganar rai a ɓace tana kallon Yazid.
"Ai ya isa ya kawo ƙarar saboda ni mai faɗa ne aji a gidan nan tun da ni wan mijinki ne"
"Hmmm!" Ta sauke numfashi tana ƙara haɗe rai.
Kallon Fatima da Maryam ya yi ya ce "A cikinku wace ce taje ta daki matarsa."
"Baffa ƙarya take saboda mu bamu zuwa gidan sa ba dan babu abin da zamu tsinta a gidan" Maryam tayi magana rai ɓace.
Hannu ya watsa mata sannan ya ce "Kin ci gidanku, gidan ɗan uwanki kike cewa babu abinda za ki tsinta"
Baki ta turo bata sake cewa komai ba. "Wannan ba daidai bane, duk irin abubuwan da kuke ina sane ƙyalewa kawai na yi amma lokaci ya yi da zan ɗauki mataki akan hakan" "Baffa abubuwan sun fara yawa ita...." "Idan kika sake magana sai ranki yayi mummunan ɓaci. Ku bar yaro ya samu nutsuwa da iyalinsa."
Sai lokacin Umma ta sake cewa "Ba zai yuwu mu bar yarinya tana abin da take so, dan haka dole ne ya rabu da ita ko kuma ya ƙara aure."
"Idan ya ƙara auren kina ganin wadda za a kawo muku alheri zata haifar ko kuwa idan ya saki matarsa kina ganin shi ne sauƙi ko kuma jindaɗinku, mene ribarki akan haka?"
"Ni kaɗai na san irin abubuwan da nake fuskanta, dan haka ni dai na ba shi zaɓi."
Duk yadda Baffa yaso ya nusar da su amma suka kasa fahimta haka ya haƙura ya tafi ya ƙyalesu da mummunan ƙudurinsu.
Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting.
VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:
Guda 1: ₦500
Guda 2: ₦900
Guda 3: ₦1400
Guda 4: ₦ 1800
Za'a turo kuɗin ta wannan account.
Acct no: 6370370016
Acct name: Halima Salahu Adamu
Bank name: Fidelity Bank
Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number ***
Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number ***.
Shaidar biya ta wannan wannan number ***
lLITTAFAN SUNE:
1-WUTAR ƘAIƘAYI
2-WA'ADI.
3-A CIKIN IDO..
4-TAZARAR SO
#FITATTUHUƊU2025
#WUTARƘAIƘAYI
#SaNaz_deeyah