KULSOOM

ONE

by @oumameer2671

      đź’ť KULSUM đź’ť

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

Chapter 1

          A hankali na shiga zare kayan jikina ina murmushi tare da kallon haÉ—aÉ—É—en mutuminda muka shigo É—akin tare wanda yake zaune kan kujera yana shan abu a Mug lokaci É—aya yana kallon gaban screen É—in wayarsa da yake dannawa. A yanzu zuciyata ta gama sakankancewa da kuma yin amanna akan kururuwar  shaiÉ—an wadda yayi min a masarrafar saurarona tamkar wadda ta shekara ashirin tana goga bariki.

     Without thinking twice na faÉ—a kan lallausan gadon da aka lailaye da white bedsheet, na lafe wuri É—aya tamkar wata jaririyar mage tare da janyo white duvet na É—an lulluÉ“e jikina saboda yanda nake jina a takure.

    Nafi minti goma a haka ina sauraren inga ya miĆ™e shima ya shirya amma sai ma Ć™ara gyara zaman shi yayi tare da miĆ™a hannu ya É—auko Ć™aramar wayar sa dake É“urari dalilin kiran sa da aka yi, a hankali ya kai wayar kunnen shi wanda duk irin nutsuwar da na bada na kasa jiyo abinda yake faÉ—a. Hakan yasa na Ć™ara gyara kwanciyata ina ta saĆ™e-saĆ™e a cikin raina.

Sai da ya kwashe kusan mintuna sha biyar yana magana daga ƙarshe ya tsinke kiran, lokaci ɗaya ya ɗago fitilun ganinsa ya watso su a kaina na kusan 15seconds sai kuma ya kawarda kansa tare da miƙewa tsaye ya zura wayoyinsa a aljihun rigar sa. Kuɗi ya ciro masu yawan gaske wanda ni kaina bansan ko adadin nawa bane ya ajiye kan center table ɗin ba tare da ya sake kallon inda nake ba cikin tsadaddiyar muryarsa mai narke zuciyar mai sauraro yace.

“Take this and leave when you prepared your self. Da kince kuɗi kike nema ta wannan hanyar ba zanyi mamaki ba, amma Kice mijin aure to tabbas ina tantama, kuma idan har ta haka kike tunanin zaki samu mijin aure to be frank you are very wrong, bcoz kin yaudari kanki,mace mai kamala da mutunci killace kanta takeyi ta jira har sai an zo gareta”

  Daga haka ya fice daga É—akin kanshi tsaye.

Tamkar wadda ta samu cutar taɓin hankalinda bata gane komai haka nayi zuru ina kallon shi har ya ɓacewa gani na. Nafi minti biyar ban iya ko hannuna na motsa ba kamar wadda ta kamu da ciwon paralyzed tsabar shock ɗin da ya ziyarci dukkan gaɓɓai da jijiyoyin jikina.

A hankali na sulalo ƙasa tare da sakin wani irin marayan kuka ina tuhumar matacciyar zuciyata akan miyasa ta sakani na aikata wannan irin katoɓarar? Take naji imanina ya dawo lokaci ɗaya nadama marar amfani ta ziyarci zuciyata na fara kiran.

 

“Astagfirullah ya Allah! Allah na tuba ka yafemin, na zo na buɗe jikina ga mutumin da ban saniba ban san ko wanene ba da nufin aikata zina akan dalilina marar tushe marar...”

  Sake fashewa nayi da wani mugun matsanancin kuka ina ta maimaita Astagfirullah.

  Sai da naji tururin da zuciyata ta É—auka ya É—an ragu sannan na miĆ™e da Ć™yar na mayarda kayan jikina daman akwai pant da bra da suka saura ban cire ba.

  Bayan na É—auki Veil É—ina da Bag na nufi Ć™ofa ba tare da na kalli kuÉ—in da ya ajiyemin ba still ina tsiyayar hawayen nadama ga saĆ™e-saĆ™e da yawa da suka taru suka sarĆ™afemini zuciyata.

                             ***

     Tunda ya fito ya shiga motarshi ya rufe ya kasa yin Ć™waĆ™wĆ™waran motsi, gaba É—aya kanshi ya kwance.

    Ya tsorata ya gigita da 'Ć´an matan zamani. Wannan yarinyar kwata-kwata ba zata wuce sa'ar Meerah ba Ć™anwar shi ta uku. Amma ita ce zata Ć™are cikin wannan dirty life É—in 'Wa'iyazubillah!.

  Ya daÉ—e a haka kafin ya iya saita kanshi sakamakon kiran da hajiyar shi ta mishi yaji ya É—an samu releive kaÉ—an sannan ya iya jan motarsa ya bar wurin.

                             ***

  Da Ć™yar na iya kawo kaina titi still ina rairai kuka na kasa dainawa tamkar wadda aka yiwa saĆ™on mutuwa.

Gefe na samu na ciro wayata a Bag É—ina na kamo layin Ć™awata Maimu. Ringing É—aya tayi picking murya  a dusashe tace.

“ Kulsoom ya ne? Ina fata Abubuwa sun tafi dai-dai...?”

Cikin sheshsheka nace.

“Maimu I'm finish.. Mutumin nan ya gama dani Maimu, but amma ai taimaka ta ma yayi...”

  Jin muryarta nayi tana faÉ—in.

“Look Kulsoom, a haka relationship yake farawa, beside kin samu namijinda ko wace macce take mafarkin mallaka....”

Girgiza kai na nayi kamar tana a gabana na haÉ—e wani yawunda naji ya koma min tamkar maÉ—aci nace.

“Maimu babu fa abinda ya faru a tsakaninmu ƙarshe ma nasiha yayimin kuma abinda ya faɗamin shine gaskiya. Wallahi Maimu I'm ashamed of my self, wai kinga yanda na muzanta na tozarta a gaban shi kuwa? Kuma maganar gaskiya I'm blaming you Maimu bcoz kece kika kaini ga duk wannan, ba zan kuma taɓa daina kuka da ke ba...”

Wani irin ɓacin rai Maimu taji ya dirar mata lokaci guda tare da tsuke fuska kamar muna ganin juna tace.

“Kulsoom zaki fara  ko? Ta ina wannan É—in kuma ya zama laifina daga abin arziki? Did I ask him to do that for you?”

Nima cikin ɓacin rai na ɗaga murya cike da ihu nace.

“But you are the causer Maimu , bcoz kece kika bani shawarar cewa.....”

Da sauri  ta girgiza kai tare da kwantar da murya tace.

“Cool down Kulsoom please,ni nasan hanyar da  zamu bi muyi handling É—in Khaldoon, wallahi bai isa ba bcoz ya riga da ya shigo komar mu ba zai taÉ“a iya fita ba, kizo nan kawai ki bari sai gobe mu tsara ta yanda zamu É“ullo mai kafin nan kin samu nutsuwa sai kije gida....”

Girgiza kaina nayi nace.

“A'a, Inna zata yi mini faɗa beside kin san Jarababbiyar grandma ɗinmu tana nan, so I will be going home sai mun haɗu gobe dai”

Maimu tace.

“OK! Bye, ki kula Friend”

“I will”

Kawai na faÉ—a na tsinke wayar.

  Ko da na tura yagalallen Ć™yauren gidanmu wanda tsuwar shi kaÉ—ai ya isa ya janyo hankalin 'Ć´an gidan ba kowa a tsakar gida sai Innani wato kakarmu, tana zaune a Ć™ofar É—akinta tana alwala da alama bacci zata shiga saboda Ć™arfe goma na dare tayi har ta gota da wasu' Ć´an mintuna.

Wuce ta na yi ba tare da na ko kalleta ba na shige ɗakinmu nida ƙanwata Khadija kaina tsaye.

Miƙewa tayi daga alwalar da take ta sage hannu baki buɗe tana kallona har na shige sannan ta buɗe baki tana banbami tana faɗin.

“Amma dai  Kursume baki da albarka, yo naji shegiyar yarinya, ni zaki wuce baki yimin magana ba kamar kinga kashi? To kin yiwa ubanki Sulmanu. Sai Ć™amshi take zubawa kamar wata amaryar da za'a kai É—akin miji Oh ni Zuwaira! Yanzu in yi magana Habiba ta ga baĆ™ina ta ce ina yiwa 'Ć´arta fatan sharri to kuma gashi dai kowa ya gani bata dawo gidan nan ba sai cikin talatainin dare, to ba zan ce komai ba amma Allah ya shirya”

Daga haka ta ci gaba da alwalar da take.

Duk abinda Innani ke faɗi a kunnen Innata saboda bata yi bacci ba, itama ranta ya kai ƙoluluwa ga ɓaci ganin ban dawo ba har goma na dare, sai addu'a take kada Babanmu ya dawo ban dawo ba.

Ni kuma ina zuwa na faÉ—a kan yaloluwar katifa ta na sake fashewa da sabon kuka, ina mai yin nadama a karo na barkatai. Tuni memory É—in abinda ya wakana tsakanina da Khaldoon É—azu da yamma ya shiga dawo min vividly..........

  Zaune muke ni da Maimu a Bilkebab Chops N coffee Eatry mun baza komarmu, domin a zahirin gaskiya ba wani takamammen abinda ya kaimu wurin sai neman mijin aure a namu bahagon tunani. Kuma sai mukayi tsaga da faÉ—i domin babu abin harin mu sai samari ko alhazawan nan masu matsiyatan kuÉ—i.

Muna nan muna Fira sama sama idon Maimu ya hango mana wani the top richest Handsom Guy da ake ji da shi jahar tamu. Saboda a duk faɗin Gusau babu wanda bai san "Khaldoon Umar Farouk Zurmi" Ba. Babban ɗan kasuwa ne wanda yayi fice tun daga gida Nigeria har zuwa sauran ƙasashen duniya.

                OUM AMEER