Barr Hibba
by @nusybee143
💥 BARRISTER HIBBA 💥
✍️Nusy bee
Page 4
Da sallama suka shiga VIP ward ɗin,matar da a ƙalla zatayi sa'ar twins ta ɗago da murmushi a fuskar ta tana amsawa,cikin farin ciki take faɗin"sannu da zuwa Aunty Hibba,dama Dr Leonardo ya gaya min kece kika kawo ni,gashi da naji sauƙi sai ban ganki ba"itama Hibba murmushi tayi ta zauna a kujerar da ke facing ɗin ta tace"yaya jikin?"
"Jiki na alhamdulillah na samu afuwa"
"To Allah ya ƙara sauƙi"ta juya ta kalli Maryam da ke ta kallon jaririn hannun matar,wanda bai fi wata biyu da haihuwa ba, Hibba tayi murmushi,cikin harshen German tace"angel babu gaisuwa ne?"murmushi Maryam tayi, idanun ta yana kan babyn tace cikin Yaren Hausa,wadda ita taji matar tana yi
"Ina kwana"mamaki ya ƙamar da matar,don wallahi bata taɓa tsammanin tana jin Hausa ba,amma sai tayi murmushin ƙarfin hali tace"lafiya lau dear, what's your name?"
"I'm Maryam Muhammad"ta ba ta amsa tana murmushi
"Wow! fantastic name, that's my mother's name,to Allah ya albarkaci rayuwar ki mama na"tana washe baki ta amsa da"ameen,Aunty ki bamu baby kinji,kinga Mamie na bata da baby"sukayi dariya su duka, Hibba ta janyo ta ta rungume tana faɗin"bani da wata baby bayan ke,amma idan na samu wata kin yarda ke ba favourite ɗina bace?
Kinga kafin ke twins sune favourites ɗina, Amma yanzu kece,baby yana zuwa kuma shi ne,do you agree?"
Haɗe rai tayi tana girgiza kai,dukan su sukayi murmushi, Hibba ta ja kumatun Maryam tana faɗin"that's my girl!"sannan ta kalli maman babyn tace"to maman baby,Ni zan wuce,ina so na duba wasu ayyuka da nakeyi anan manchester,daga nan zan wuce Nigeria gobe,so be ready,in Sha Allah everything will be alright"hawaye suka zubo a fuskar ta,tace"babu abinda zan ce miki Aunty Hibba sama da Allah ya biya ki da aljanna maɗaukakiya,na gode na gode Allah ya magance miki dukkan damuwar ki ya baki miji mafi alkhairi a gare ki"murmushi kawai Hibba tayi ta ja hannun Maryam suka fice daga ɗakin tana faɗin"be ready"
SALFORD QUAYS, MANCHESTER, ENGLAND
Hibba ce zaune da ear pod a kunne,gaban ta computer ce da waya,abu take saurara,bayan wasu mintuna tayi wani murmushi da ita kaɗai ta san ma'anar shi,sannan ta fara magana a kausashe
"A halin yanzu tunda bana ƙasar ni da ƴa ta babu waɗanda suka rage da zai bibiya sama da ƙanne na,abinda bai sani ba sai da na cancanta sannan ake kira na da COBRA!lamɓo nakeyi don cafke abokin hamayya, kazalika bana barin baya da ƙura,wayace masa Ni mahaukaciya ce da zan karɓi Shari'a kamar wannan sannan nayi wasa da rayuwa ta ko ta wani a kusa dani?ya ɗauka da holoƙon kai na kai wannan matsayin?"shiru tayi alamar saurare kafin ta ja tsaki tace"sanin kanka ne bana tsoron ƙwari irin shi,asalima insecticide nake tanada na musamman don irin su,in Sha Allah shari'ar nan ta zo ƙarshe, I don't care who the stupid is"ta ƙara yin shiru kafin tace"yeah yanzu shirye shiryen da nakeyi kenan,in Sha Allah Ina nan dawowa"daga haka ta kashe wayar ta kalli wayar sai ta fashe da wata iriyar dariya, lokaci guda kuma ta gintse tana kallon wayar fuska a haɗe tace"bari na gama da shugaban naku,kaima da sannu zan dawo kanka"ta girgiza kai cike da ƙunar rai,ita fa a yanzu ko me mutum zaiyi baya bata mamaki, kuma bata shakkar kowa,kuma bata jin zata ragawa wani har abada ma kuwa,bazata taɓa yiwa duk wanda ya shiga hannun ta sassauci ba,wannan alƙawarin ta ne
Da yamma ta shirya Maryam cikin track suit irin tata mai tambarin ƙungiyar wasan ƙwallon ƙafa ta PSG,ƙafafun su sanye da fararen canvas,sun Sanya baby hijab,ta ɗauki wayar ta suka nufi harabar gidan ta shiga rantsatstsiyar motar ta ƙirar Lamborghini suka bar gidan
Sunyi yawo sosai,don har gidan aminiyar ta Clara wadda ta kasance abokiyar aikin ta a UK sai da suka je,sun tattauna sosai akan aiki,a lokacin sun tuna da Helen har ƙwallar tuno ta sai da sukayi,daga nan Hibba ta ɗauko Maryam suka dawo gida
Kwanan su uku a manchester kafin Hibba ta wuce London,ta London suka bi zuwa ƙasar mu ta gado Nigeria
A Murtala Muhammad airport suka sauka, kasancewar saukar dare sukayi kawai Hibba tayi hiring ɗaki a hotel kusa da airport ɗin,washe gari da safe tayi musu boarding jirgin da zai tashi ƙarfe sha ɗaya sannan ta kama hannun Maryam ta kira musu bolt suka nufi lekki phase 1
LEKKI PHASE 1, LAGOS STATE, NIGERIA
Cike da tsananin mamaki barrister Khadijat ke kallon aiyo da sakatariyar ta tayi mata iso, Hibba batayi mata kallo biyu ba ta nemi waje ta zauna bayan ta ɗauko water bottle ta bawa Maryam,sai a lokacin ta ƙara kallon Khadijat tana faɗin"ya dai?"
"Aiyo,You really surprised me"murmushi Hibba tayi tace"i hope everything is fine"
"Alhamdulillahi,ya ayyukan?"
Kafin Hibba ta amsa Maryam ta gaishe ya cikin girmamawa, Khadijat ta amsa da fara'a tana tambayar ta Germany, Maryam bata wani ja magana irin ta yara masu surutu ba,don itama ta samu training mai kyau daga Wajen Barrister Hibba
Barrister Khadijat ta juya wajen Hibba tace"kin zo a daidai,don in less than one week za'a cigaba shari'ar nan,amma abin tashin hankalin har yanzu ba'a san inda Rahama take ba,ina tsoron kar su Hajiya Fatima su kashe ta"
Hibba ta yatsina fuska tace"ko ma me sukayi mata bazasu sha ba,sannan basuyi a banza ba,for now dai I have no enough time, flight ɗin mu will take off few hours later,so all I can say to you is get prepare,zaman court nan da three days, everything will be alright in Sha Allah"daga haka ta miƙe, Maryam ma ta miƙe
Barrister Khadijat ce ta rako su har bakin building ɗin in da bolt take jiran su,suka shiga ta mayar da su airport
ALI MUHAMMAD KABO AREA, RAILWAY ESTATE, KANO STATE, NIGERIA
Yau tun sassafe aka tashi da gyaran gida, Jabir ya maimaita dokokin gidan kamar yadda ya saba a duk sanda mamallakiyar gidan zata dawo,ya tara ma'aikatan ya maimaita musu cewa,yana daga cikin dokar ta bata son hayaniya da yawa,bata son ɓata lokaci a komai,dole a daina zaman hira saboda bata da yarda,sannan bata son wasa, Muyassar dai zuwa yanzu ya ƙagu ya ga wannan uwar iko da isa da mallakar,don yaga bayan dukiyar da uwar me take taƙama da har ta mayar da mutane bayi
Ƙarfe uku da mintuna goma sha biyar daidai,a lokacin gidan yayi shiru ba kamar yadda aka saba kaiwa da kawowa a gidan ba,mama ta saka masu aikin ta sun gyara cikin gidan anyi girke girke na musamman an jera su a babban dinning room na gidan, Marwa da Arwa kuwa kamar suyi hauka don tsananin farin ciki,as usual sunyi shigar su iri ɗaya,na riga da skirt na atamfa,hatta da ɗauri iri ɗaya sukayi, exactly dai identical twins ɗin su
Wato Barrister Hibba akwai CAPACITY😁to maji ma gani dai,wannan isar da jin kan ina zasu je oho,a ɓangare ɗaya ma'aikatan gidan Hibba na takaicin dawowar ta,ƙannen ta na murna,mu kuma muna so mu ga iyakar tsawon CAPACITY ɗin nan nata
#Nusy_bee