Barrister Hibba
by @nusybee143
💥 BARRISTER HIBBA 💥
✍️Nusy bee
Page 5
Mota ce ƙirar Lexus ta dakata a bakin gate ɗin,cikin nutsuwa akayi wani dogon horn sau ɗaya,a guje mas'udu ya je ya buɗe gate ɗin,sai da gaban shi ya faɗi ganin motar,cikin sauri ya matsa,motar mai baƙaƙen glass ta taho a slow ta shigo zuwa harabar gidan,har wani rissinawa yakeyi amma bai ga alamun mai motar ta san yayi ba, wannan ba baƙon abu bane don kuwa an saba,yana kallon ta ta nemi waje a ƙaton parking lot na gidan inda motoci Masu suna motoci suke kusan guda ashirin a parking lot ɗin
Maryam ce ta fara buɗe motar ta fito cikin farin ciki,sanye take da doguwar riga wadda kaɗan ta haura gwiwar ta kalar baby Pink,kanta sanye da hat red colour wadda akayi wa kwalliya da flowers baby Pink,takalmin ta ma baby Pink ne,a guje ta shige cikin gidan tana dariya tana ƙwalla kiran twin aunties
Hibba ce ta fito daga motar,as usual sanye da track suit farare tas masu tambarin ƙungiyar wasan ƙwallon ƙafa ta PSG,ta Sanya baby hijab fari tas,kafar ta sanye da sneakers,idanunta sanye da farin medicated glassesta zagaya ta buɗe back seat ta ɗauko ƙaramin akwatin ta,ta wuce cikin gidan ko kallon ma'aikatan gidan da ke ta mata sannu da zuwa cikin girmamawa batayi ba
Muyassar ya bi ta da kallon mamaki,sannan ya bi ma'aikatan da ke dawowa bakin aikin su da satacciyar gwiwa da kallo, mas'udu da Aminu sai zancen suke jajantawa,suna la'antar wannan mata mai shegen girman kai da ɗagawar tsiya
A balcony suka haɗu da twins,ihu sukayi a tare suka rungume ta,da murmushi ta rungume su duka,sun kai tsayin mintuna biyar kafin su sake ta su ja baya suna kallon ta suna haki,ɗan murmushi tayi ta ja hannun Maryam,suma suka rufa mata baya
A babban parlourn gidan suka iske mama tana saukowa daga sashen ta,da tsananin farin ciki ta zo ya rungume Hibba tana faɗin"idon ki kenan Hibba?wata kusan shida babu ke Babu alamar ki? gaskiya wannan karon ayyuka sun miki yawa,kina cin abinci ma kuwa?duba fa,duk kin bi kin rame"murmushi Hibba tayi tace "mama ina cin abinci, stress na aiki ne kawai,bari nayi refreshing na dawo"bata jira cewar mama ba ta wuce nata part din Wanda yafi na kowa tsananin kyau da tsada
Tsawon mintuna arba'in kafin ta fito,sanye da riga da wando,rigar ta Jersey ɗin PSG ce,sai baƙin wando,kanta babu ɗan kwali, baƙin dogon gashin ta ya sauka har dokin wuyan ta,wayar ta ce a hannun ta tana dannawa,da alamu chat take yi
Har ɗakin mama ta bi ta suka gaisa,ƴan biyu ma shigowa sukayi suka gaishe ta,sannan suka ɗunguma baki daya zuwa dinning room
A ƙa'idar ta ne,babu mai magana idan ana cin abinci,don haka bayan Bismillah babu abinda ake ji sai ƙarar cokula a plate,duka duka abinda taci bai wani taka kara ya karya ba,ta miƙe ta koma parlourn,bata wani juma ba babyn ta ta biyo bayan ta,suma ragowar da ɗaiɗai da ɗaiɗai suka fito
Zama suka yi suka fara hira,a nutse ta kalli Marwa tace"Fatima I hope kina samun medical attention sosai game da larurar ki"shiru Marwa tayi,zuwa can tace"eh yaya,kawai....."
"I hate any excuse,jikin ki,for now I know kin aqn ciwon kanki,so do what suit you"daga haka ta mayar da kanta ga wayar hannun ta tana kallon livematch na PSG da Liverpool da take ɗan kallo bayan ta kashe ƙarar
"I'm sorry sister"banza tayi mata, Arwa tace"Please sister"ta watsa mata wani kallo,Marwa ta fashe da kuka,sun tsani yayar su tayi fushi dasu,mama tace"ayi haƙuri,ciwon ma alhamdulillahi,tana kiyaye dokokin da zasu tayar Mata dashi,ko lokacin da na kai musu ziyara a makaranta banga alamu tana wasa da ciwonnata ta ba"murmushi tayi tana girgiza kai tace"mama kar ki yi depending ɗin ta,don babu mai sake daga min hankali"mama tace"dama wazei ɗagawa babbar yaya hankali,ayi haƙuri dai"tayi murmushi,nan suka canja hira
Arwa ta kalli Hibba tace"yaya last week Nafi'u yazo,amma na sanar masa cewa bakya ƙasar,yace idan kika dawo na shaida masa"
"Ki sanar masa"Hibba ta faɗa a taƙaice,still idanun ta na kan wayar ta
"To yaya,sai....um...tace don Allah ki taimaka mata yaron ta bashi da lafiya za'a mayar dashi asibiti, bata zo ba amma ta kira ni"sai zare idanu takeyi, Marwa sai hararar ta takeyi don ta san zata iya ɓallo musu ɓacin rai ta hargitsa musu farin cikin da suke ciki na dawowar yayar tasu,zata iya barin ƙasar a yau ma
Tuni ƴar fara'ar da ta rage a fuskar Hibba ta ɓace,don ta gane wadda Arwa take nufi,amma sai ta dake fuska tace"wacece?ki fito kiyi min bayani zainab"
"Uh...uh... maman su fauziyya"
Ɗauke kai Hibba tayi batare da tace uffan ba,daga nan parlourn ya ɗauki shiru,ba Arwa ba,hatta Marwa tana jinjina tsanar da Hibba takeyiwa mutanen nan,duk da cewar sun san dalilin,amma ai dalilin bai hana su cigaba da mu'amala da sauran family ɗin su ba ko da sama-sama ne kuwa
Sun kai mintuna goma suna zaune ba wanda ya sake magana, Hibba zuwa yanzu ta gama kallon da takeyi tana danne dannen ta a laptop,ita kuwa Marwa a waya,mama kuma ya mayar da hankalin ta ga Film ɗin kabhi alvidana kehna da aka saka a mbc Bollywood,itama Arwa pretending tayi kamar kallo takeyi,amma a sace kallon fuskar Hibba takeyi,ba zato ba tsammani yaji tace"stop looking at me that way"babu shiri ta sunkuyar da kanta,tana jin Marwa na mata dariya ƙasa ƙasa amma babu halin masifa don dama Hibba itace maganin su
Kiran sallar la'asar ne ya watsa taron, Hibba ce ta fara miƙewa,Maryam ta bi bayan ta,kafin sauran suma duk su miƙe, kowacce ta nufi ɗakin ta donyin sallah
Da daddare bayan sun gama cin abincin dare Hibba ta kalli Arwa tace"kiyi mata magana,tazo gobe itama"
"To yaya"Arwa ta amsa cikin girmamawa
"Yauwa,sannan ina so kiyiwa Jabir magana zamu tattauna dashi"
"To yaya"ta sake amsawa a ladabce,ita dai Marwa yadda ba'a saka da ita ba itama bata shiga ba
Washegari wajen ƙarfe tara Hibba tana kwance, farkawar ta kenan daga baccin da ta koma bayan ta idar da sallar asuba taji knocking ƙofar ɗakin ta
Ɗan gajeren tsaki ta ja kafin tace a ɗan fusace"who is there"
"It's me Yaya,you have a visitor"taji muryar Arwa. rai a ɓace ta kalli expensive agogon da ke kafe a bangon ɗakin nata,ƙarfe tara da mintuna biyu,bata sake magana ba ta miƙe ta faɗa toilet
Ta kai mintuna aƙalla arba'in da biyar zuwa hamsin kafin ta shigo babban parlourn gidan inda baƙuwar tata take zaune zuru tana jiran ta,gwara ma Arwa ta kawo mata lemo da cake bayan sun gaisa,amma Marwa tana gaida ta bata sake ganin ƙeyar ta ba,Maryam ma leƙen ta kawai takeyi don sai ta ganta kamar wata sabuwar halitta,don bata saba ganin mutane a firgice haka ba
Da sallama ta shigo parlourn fuskar ta tamkar bata taɓa dariya ba,tana sanye da riga T-shirt da skirt,ta Sanya hula a kanta,rai a ɓace ta fara magana batare da ta amsa gaisuwar da matar takeyi mata kamar zata duƙa ba
"Maman fauziyya meye haka?wanne irin zuwa ne wannan fisabilillahi?kin saka a je a taso ni, Yanzu da ace ban tashi ba? saboda Allah bazaki iya jira rana ta ɗaga ba?kinfi kowa zumuɗi ne?"
Sunkuyar da kai maman fauziyya tayi jikin ta na rawa tace"wallahi jikin abdallah ne ya matsa,banda haka da na ƙara bada lokaci,mun buga mun kaɗa bamu samu kuɗin magani ba shine nace bari nazo nan,na san bazaki hana mu ba"ta ƙarashe tana dariyar yaƙe
Tsaki Hibba ta ja sannan ta cilla mata bandir ɗin dubu ɗari a cikin envelope,ta juya don komawa sama tana faɗin"Allah ya bashi lafiya"
Da bala'in sauri maman fauziyya ta cafke kuɗin tana washe baki,tana ta jero mata godiya,ita tuni ma ta shige part ɗin ta
Wajen ƙarfe sha daya da rabi Jabir ya shigo babban parlourn a dalilin kiran da Arwa tayi masa,kan kujera ya zauna Kamar yadda yake tsarin Hibba,ya gaishe ta ta amsa,yayi mata sannu da zuwa,ta amsa sannan yayi mata bayanin an samu sabon driver,kusan watanni biyu baya,batare da ɓata lokaci ba Hibba tace ya gabatar mata dashi
Ya fita babu jumawa suka shigo da Muyassar,sai a sannan ya ƙare mata kallo a kaikaice, yarinya ce gaba ɗaya bazata wuce sa'ar zeenat ƙanwar shi ba,27-28 haka,ɗauke kai yayi bayan ya gaishe ta a taƙaice
Itama a taƙaicen ta amsa masa,sannan ta ɗora da faɗin
"Kaine sabon driver da Jabir ya ɗauka right?"
"Eh nine"ya bata amsa, Hibba ta ɗora"lokacin da aka ɗauke ka bana nan,ina Germany,sisters ɗina kuma suna Abuja schooling,a taƙaice dai,for now da Ni da sisters ɗi na ba mazauna bane,Ni ina aiki da foreign countries su kuma twins suna karatu,muna iya share watanni Bama nan,ita kuma maman mu ba yawan fita takeyi ba,so yawanci ayyukan ka zasu fi yawa idan muna nan,suma sisters ɗi na ba wai suna fita anyhow bane,don haka aikin ka zai fi yawaita idan ina nan,ina da guraren aiki da yawa,daga Kano har zuwa wajen Kano,don yadda ka saba aiki daga 8:00am zuwa 5:00pm,to idan ina nan zaka iya kaiwa har 9:00pm ma, har sama da haka,ina fatan zamu daidaita?"batare da yayi magana ba ya gyaɗa kai
Bata damu ba ta ɗora"anjuma zaka kaini unguwa"ta miƙe tana gyara zaman madaidaicin mayafin ta da ta ɗora a kanta zuwa kafaɗar ta kan doguwar rigar abaya da ta sauya,sai da ta fara tafiya sannan ta juyo ta furta"You can leave"tana gama faɗin haka ta wuce part ɗin ta
Miƙewa sukayi batare da sun ce komai ba suka fita,sai da suka isa harabar gidan sannan Muyassar ya kalli Jabir yace"ina ganin wannan aikin resigning kawai zanyi, saboda idan ta cigaba da nuna iko irin haka zan iya ɗauke ta da mari"
Eh to Hibba ta ɗan haura layi,amma Muyassar indai ka kuskura ka marar mana Barrister ba yarda zamuyi ba🙄kar ma ka manta mune kotu😁🤸
Yau dai anyi post biyu🤗
#Nusy_bee