KULSOOM

TWO

by @oumameer2671

          💝 KULSUM 💝

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

    CHAPTER TWO

  

    Saida ta ƙare masa kallo tsaf, sannan ta taɓani wanda ni gaba ɗaya hankali na baya wurin yana kan wayata da nake duba chart.

  “Kulsum kinga Guy ɗinda idanuna suka ganemin kuwa? Ko dai gizau ne yake mini?”

Sai a sannan na ɗago nima ina kallon direction ɗinda itama take kallo nace.

"Wane ne shi?”

Harara ta maka min tace.

“Kulsum you are not serious, Khaldun Zurmi ɗin ne baki saniba?”

With serious attention nima na sake kallonsa murya ta na shaking nace.

“Da gaske kike”

Maimu tace.

“Wallahi shi ne, ke muguwar banza ce  wallahi. Ki daina ƙureshi da wannan kallon haramun ɗin kiyi abu na masu aji mana”

Sunne kaina nayi still ina ƙara kallonsa a kaikaice kuma itama din shi take kallo.

Numfashi na sauke a hankali tare da kallon Maimu nace.

“what should we do Maimu? naga fa ko kallon inda muke bayayi duk tsabar ƙure adakarmu, ji ma wani irin shan ƙamshi da yake tamkar wanda yake jin warin mutane”

Dariya tayi ƙasa ƙasa sannan tace.

“Kulsum girman ajinsa ya wuce duk yadda kike tunani,wallahi mata da yawa masu aji waɗanda suka fimu komai ba su ishesa kallo ba, duk da muɗin masha Allah ba laifi, amma yanzu ke kije ki gwada sa'arki mu gani...”

Zaro ido nayi tare da dafe ƙirjina tamkar wadda aka ce tayiwa sarki ƙarya na ce.

“Haba Maimu, kema kin san ba zan iya ba....”

Nodding ɗin kanta tayi tace.

“OK! Wannan damar ko zata wuce mu kenan”

Na ce.

“why did you say so?”

Maimu tace.

“Saboda ke ce da an kalle ki za'a ga jiki duk madara, komai naki so masha Allah Kulsum babu namijinda zai kalle ki bai sake ɗaga idanuwa ya ƙara kallonki ba. Gidan  masu kuɗi ne kawai Allah bai ƙaddari zaki fito ba, amma ke ɗin kalar masu ƙumbar susa ce. Da gwaji jirgi ya tashi saboda haka ki je mu gani”

Jin yanda take ta kurantani yasa naji kaina ya ɗauki hayaƙi, domin ni kaina nasan  cewa Allah ya bani baiwar kyau wanda ko gasar sarauniyar kyau za'a je to zan iya zuwa nima a fafata dani. Saboda haka ba tare da dogon nazari ba na miƙe Bag ɗina na maƙale a hamata ta na doshi inda yake zaune kaina tsaye.

  Duk da akwai waya riƙe a hannunsa hakan bai hana shi duba tsadadden agogonda ke ɗaure a tsintsiyar hannunsa ba. Lokaci ɗaya ya saki ɗan siririn tsaki tare da kara ƙaramar wayarsa a masarrafar jinsa. Jin ba'a amsa ba daga ɗayan ɓangaren yasashi  sake jan tsaki a karo na barkatai ya ajiye ta akan table ɗinda yake gabansa.

Zaunawa nayi akan kujerar da ke damansa zuciyata kamar zata fasa ƙirjina ta fito saboda tsoron kada ya wulaƙantani a bainar nasi.

Murmushin ƙarfin hali na ƙirƙiro na ɗora akan fuskata nace.

“Hi!”

A daƙile ya ɗan kalleni kaɗan sai kuma ya kawarda kansa murya can ciki yace.

“Hi!”

Ƙara gyara zamana nayi still Ina Murmushi nace.

“Alamu sun nuna kana jiran wani ne ko wata,shi kuma ya saɓa maka alƙawari, ta dalilin hakan ne yasa fushi ya samu matsuguni akan wannan Kyakkyawar fuskar mai cike da haiba da kuma kamala. Lallai da zan haɗu da wannan bawan Allah to tabbas saina yi masa hukunci dai-dai da laifin da ya aikata”

Ba laifi yanzu ya ɗan sassauta daga ɓacin rai zuwa sakin ɗan ƙayataccen murmushinda daga gani kasan zantukana sun yi tasiri a zuciyarsa.

A hankali ya buɗe bakinsa yace.

“And you, what brought you here?”

'ƴar dariyar nasara ce ta suɓucemin ba tare da yin wani nazari ba nace.

“Saboda Kai”

Sake kallona yayi sai kuma ya girgiza kai yace.

“I doubt”

Ɗan zaro ido nayi nace.

“Why?”

Yace.

“Banyi da kowa zan haɗu da ke ba, ba kya cikin schedules ɗina na yau I guessed”

“Haka dai kace...”

Ringing ɗin wayata yasa na zura hannuna a jakata na ɗauko, Maimu na gani a gaban screen din hakan yasa na ɗan waiga ta side ɗinta kaɗan na kalleta sai kuma na ɗauke kai, saboda bana fata wani abu yazo wanda zai yi sanadiyyar shiga tsakanin wannan firar da muke mai cike da nishaɗi.

Jin har ta tsinke ban ɗaga ba ya kalle ni yace.

“Laifin me nayi miki kike nema na?”

Kai tsaye na ce.

“Aure za muyi”

Sai yanzu ya ɗago Kyakkyawar fuskarsa cikin 'ƴan daƙiƙunda basu wuce goma ba ya ƙare mini kallo tsaf.

Ƙirjina sai dukan uku-uku yake tamkar ana mini lugude akai. Ga wani shirunda ya ratsa tsakaninmu ba wanda ya sake furta ko kalma ɗaya.

Jin ƙarar shigowar message yasa nayi saurin dubawa. Maimu ce, abinda ta rubutomin shine.

"Da alama kin samu shiga, to kada ki tsaya sanya, ki yi duk yanda zakiyi ki ga kin sameshi a hannu"

Ɗan murmusawa nayi nima na rubuta mata.

"In sha Allah ya faɗo hannu"

"Duk da haka nasan halin samarin zamanin nan sarai, wallahi muddin bai lashi zumarki ba to tabbas ba zaki taɓa yin tasiri ba a cikin zuciyarsa.

  Shiru nayi zuciyata na ƙyamatar abinda Maimu take shirya mini.

  Ganin convoy yasa na saki baki ina kallon ikon Allah. Ban ankara ba sai ganin nayi ya miƙe muryarsa na faɗin.

“we will talk later”

Hakan yasa nima na miƙe na nufin gun Maimu.

“Maimu ban fahimci abinda last message ɗinki yake nufi ba, Sai ya lashi zumata as how?”

Ɗan siririn tsaki ta ja sannan ta kalleni tace.

“Wallahi muddin bakiyi abinda nace ba to zaki tsaya kallon ruwa ne kwaɗo ya miki ƙafa, mace sai son harakar wayewa amma bata waye ba. Irin wannan muddin haɗuwar farko baku ɗinke ba, to wallahi a kwandon shara zai watsa ki kuna rabuwa, ke da shi sai dai kuma a lahira... ”

Gyara zamana nayi da kyau ina kallonta nace.

“Bana tunanin zai min haka Maimu a yanda naga ya karɓeni”

Girgiza kai tayi tana faɗin.

“Wallahi Kulsum ba zaki san kinyi sake an yimiki sakiya ba sai kin bari Khaldun ya suɓuce miki, kuma wallahi har abada har gaban abada ba zaki taɓa sake samun irin sa ba ke ko masinjansa ba zaki samu ba....”

Ta haka sai da Maimu tasan yanda ta cusa min ƙazamin tunaninda ya kai ni ya baro.

 

Ganin motacin sun fara haramar tashi yasa na bar wurinta na koma gunda ya barni zaune. Da yake kuma shi ɗin ɗan halak ne sai gashi ya dawo inda nake ya kalleni yace.

“I will go and pray Magrib, I will be back”

Daga haka ya wuce bayan an idar da sallah ko sai gashi still ya sake dawowa,kallona yayi yace.

“Muje”

Kamar wata raƙumi da akala haka na tashi na bishi. Wata rantsatstsiyar mota ya nufa kai da gani kasan naira ta koka. Driver na ga ya sauko ya buɗe sai yayi min alama da in shiga ba musu ni kuma na faɗa,shima ya zagaya ɗayan ɓangaren ya shiga.

Shiru ne ya ratsa tsakaninmu na 'yan mintuna daga nan ya kalleni ya ce.

“Ina muka nufa”

Kaina tsaye kamar wata wadda uwarta tace jeki kya gani haka nace mishi.

“Duk inda muka nufa, ni ɗin gaba ɗaya mallakinka ce sai yadda kaso  zakayi dani”

Wani irin razanannen kallo ya jefeni da shi ni kuma idanuwana sun riga da sun rufe ban iya na hango hakan ba a ƙwayar idonsa.

Ɗan runtse idonsa yayi sannan ya buɗe ya kalleni yace.

“Hotel?”

Ina murmushin nasara nace.

“Duk inda kake so”

Fita yayi ya ƙwanƙwansa ƙofar drivern nasa bansan maganar mi suka yi ba ni dai naga ya shigo mazaunin driver shi kuma drivern ya kama gabansa. Har muka isa inda zamu Maimu na ƙara jan kunnuwana akan kada na yarda na kofsa. Ashe tozarci ne ke can yana jirana bani da masaniya.

  Jin muryar Innata a kaina yasani dawowa daga duniyar tunaninda na afka tana faɗin.

“Kulsum daga ina kike? Ba sai da naja kunnen ki nace kada ki wuce ƙarfe bakwai ba a gidan nan?”

Babu shiri nayi saurin haɗiye kukanda nake tare da miƙewa zaune ina goge hawaye nace.

“Innarmu kin san fa wurin dinner yanda yake, duk yadda aka so ba za'a fara biki ba sai wuraren tara na dare, wallahi da fara bikin nan ko taƙamaimen minti talatin banyi ba na fito ga abin hawa da wahala, da ƙyar na samu mashin ɗinda ya kawo ni”

“To kin dai ga Innani ta ganki sai ki nemi kalmomin kare kanki wurin malam gobe da safe domin ni dai ba ruwana kada ma ki kuskura ki Kira suna na”

Daga haka ta fice ta barni nan abin duniya yabi ya dameni. Allah Allah nake gari ya waye in ji mi Maimu zata faɗamin kuma.

    

                 OUM AMEER