12
💋ƊAN HALAK💋
MALLAKAR
UMMU MAHER(MISS GREEN)🍃
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION📖*
AREWABOOK
https://arewabooks.com/book?id=6631fffa
0eeb3b80f1ef8159
WATTPAD
***
_content=story_info
12
_______Bayan babanmu ya gama banbaminsa da masifarshi, ƙaninshi kawu Jafaru ya shigo gidan da sallamarsa hankalinsa a matuƙar tashe jin cewar an tafi da ƴaƴan yayansa folis tashon. Ganin babanmu yasa ya yi turus baki buɗe ya ce "A a mai zan gani yaya? Ni na ɗauka ka tafi wajen yaran nan kuma sai na ganka a gida zaune hankalinka a ƙwance"?.
Wani kallon banza yabi Jafaru da shi sannan ya ce"hum! yaro baisan wuta ba sai ya taka, uban waye yace su gayyatowa kansu abin da suka aikata yanzu? Ai kasan Allah Jafaru? yaran nan suna dawowa sai dai su nemi wani gidan uban amma ba nan ba, yara sun zama yaran masifa ƴaƴan Allah bani, masu mugun hali irin na uwarsu to ni dai baza su kashe ni ba sai dai su kashe uwarsu".
Sosai kawu Jafaru ya yi mamakin babanmu amma duk da haka yasan yaran ma suna da laifi sai ya ce"haba mana yaya, saboda me zaka dinga binsu da wannan bakin na ka mai dafi gare su? Babu kyau hakan ai, an san dai sun yi kuskure kuma na tabbatar yanzu haka sun gane basu kyauta ba, kawa Allah da manzonsa ka taho mu tafi domin mu gano halin da yaran nan suke ciki"?.
"Jafaru kake kowa? Malam dai ba zai je ba, akan mi zaka takura mishi? Sai kace ubanshi? Ƙaninshi ne fa kai? Amma kake nuna kai kamar kaine babba, saboda haka nima ina bin bayanshi kada yaje don Allah su kashe su ma kowa ya huta".
Mamaki ya kusan kashe Jafaru, dama abin da ake faɗa akan Kande gaskiya ne? Shi dai bai taɓa ganin rashin mutuncinta ba sai yau, tunda shi dai ba mazauni bane yana zuwa lagos da jos siye da siyarwa.
Sosai ya harzuƙa har baisan lokacin da ya fara maida martani kakkausa ba. "Kar Allah yasa yaje, idan bai je mutuwa za suyi? Da ki hana shi da ki barshi duk uwar uban ɗaya ne saboda haka kada kaje".
Bai sake magana ba ya fice a zafafe zuwa gidanshi, domin ya ɗibi kuɗi yaje can caji ofis ɗin. A tsakar gida ya tarar da hansai matarshi, tana zaune gaban fanfon yana ƙwaranyowa sannu a hankali, ita kuma tana wanke shinkafa fara domin yin tuwo. Sosai gabanta ya faɗi domin ko sallama bai yi ba, jikinta yana kyarma ta matsa jikin shi sosai har suna jiyo numfashin juna ta ce"lafiya kuwa Baban Audu"?. Ya maida mata da tambayarta a gaggauce ya ce" Wai dama haka Kande take gurza rashin ɗa'a yaya kuma yana biye mata? tsohuwar alakwakwai".
"Hum me kuma ta yi? Domin mu dai har mun saba da rahin mutuncinta, musamman ma ni ganin cewar kishiyarta mamar Humairah ƙawata ce, shi yasa ko ga miciji bama yi da ita wallahi Baban Audu matar nan muguwa ce, duk ta raba shi da yaransa gashi ita kuma bata haihun ba, ƴan uwanshi ma ɗai-ɗai ne bata rabasu ba"......Tana kaiwa nan ya dakatar da ita wajen cewa"To amma ai baki taɓa faɗamun ba sai yau? Ashe abin har ya kai haka? Kinga irin tsinuwar sa yake jifansu da ita, Yanzu idan bakin ya bisu ya zai yi? Dole ai ba a canjawa tuwo suna".
Taɓe baki tayi, wallahi baza ta bisu ba tunda ai ba suyi mishi komi ba". Tashi ya yi ya ɗibi kuɗaɗe sannan ya fita zuwa wajensu Humaira, har Hansai zata bishi ya dakatar da ita domin yasan za suje ne suyi ta kuka mata da rauni.
acan kuwa tuni Hajiya Babba ta hallara, sai Tasleem, Nasreen, duk yaranta ne sun ƙwama wani uban gilashi. Sai kallon mutane suke ɗai-ɗai tamkar suna jiran ƙiris su hau rashin mutunci, kiran wayar Hajiya Ƙarama ne ya shigo a wayar Hajiya Babba. Tana ji tana gani ta gama sauti ba ta ɗaga ba, sai a karo na biyu ne sannan ta ɗaga ba tare da ta ce komi ba.
"Duk inda kike kizo Alhaji ya dawo yana son ganinki". Tana kaiwa nan ta katse wayar ba tare da ta ƙara magana ba. Tasleem ta ce"uwar me zaki yi mata idan kin koma gidan? Uwar ƴan jin kai har tana baki comment sai kace wata uwarki"?.
Hajiya B. tayi jim ranta a matuƙar ɓace sannan ta ce"to ina zan sani ne? Kinsan Allah Lulu na kusa maganin matar nan a gidan nan, kishiyata ce fa ba uwata ba? Amma na rasa dalilin bani wannan comments ɗin da take yawan bani, ga shi kuma Alhaji baya ganin laifinta sam ni har na rasa ma me zance saboda baƙin ciki, amma a juri zuwa rafi"...
Tun kafin ta ƙarasa ta yi saurin tashi fuskarnan babu annuri, biyo bayan wasu kuɗaɗe da taga ana bawa wani sajan. Bayan shigowar wani mutumi wanda taga suna kama dasu Humairah ko da ba a faɗa mata ba tasan babansu ne.
"Uban waye wannan yake baka kuɗi? Har kake yaƙe tsinannun haƙoranka"?.
Ko ba a faɗawa kawu Jafaru ba ya tabbatar wannan ita ce matar da ta kulle yaransu, ya haɗe gabas da yamma a zuciyarshi yana ce wa Inda ba ƙasa nan ake gaddamar kokawa.
Jikin Sajan ya ɗau rawa, amma sai ya danne ya jajige domin kuwa wannan harkar ba somin taɓi bace a wajen shi, ya ce"A a Hajiya daina zagi haka shi wannan sulhu yazo ba faɗa ba, dama kuma yanzu nake son kiranki sai kuma ga shi kinzo"...
Ƙarar wayarta ita ce ta ƙara sanar mata da in har bata koma gida ba, yau ita da Marshal ne saboda dama basa shiri ya yi tafiya. Tana mugun tsoronshi shi yasa take matuƙar gudun ɓacin ranshi in har ba ta yi abin da yake so ba.
Bata samu zarafin magana ba, ta kaɗawa su Tasleem hannu suka taso jikinsu ba ƙwari domin basu san me ke faruwa a gidan ba?.
Muna hango tafiyarta Ameera ta ce"Insha Allahu mune zamu zamewa matar nan ciwom ido, wallahi tallahi tunda har ta sanya aka kulle mu ita ma bazan barta ta yi farin ciki ba". Ummi ta karɓe caraf " Faɗa ma ɓata baki ne, ai wallahi sai tasan ta taɓo mu ina dai tana da yara maza ko?". Ameera ta ce"eh yaronta ɗaya ne namiji". Ummi ta yi wani shu'umin murmushi wanda ni da kaina na kasa fassara murmushin da yaran suke yi".
Muna ganin Kawu Jafaru muka fara kuka, sosai muke yi har da riƙe hannun shi idan ka kalle mu sai mun ba ka tausayi, nan da nan muka yi baƙi duk da kasancewar mu farare. Ga yunwar da take nuƙurusarmu domin tun safe muke a cikin sel ɗin, ga wani irin zafi da huci duk da akwai raga-raga amma tamkar dai babu, ga wasu shaiɗanun mata da aka haɗa mu dasu wai an kamasu da kayan shaye- shaye, waɗanda aka kamo a gidan karuwa. Wannan takaicin ya haɗu ya yi min yawa, wai yau mune aka haɗamu da karuwai mu ba sata ba? Ba fashi ba? Ba komi ba, amma haka aka haɗamu da ƴan iska saboda mun yi faɗa da gidan Mashal?.
Kawu Jafaru ya ce" kuyi min shiru, duk ba kune kuka janyowa kanku ba? Kuna cikin rufin asirinki ku ka tonawa kanku? Uban me ya kai ku gidan waɗannan? Harda ku ka yi faɗa dasu? Yanzu kunga gashi zancan dama sajan yake wai kotu za a kaiku, akan kunje har gida kun ci musu mutunci".
Jin abin da yake cewa ya sanyani a cikin wani mummunan hali, da ƙarfi na ce"kotu kuma? Akan me zasu kaimu kotu? Sata? Ko kuma fashi?". Tuni na saki wani irin wahalallan kuka mai tafe da abin tausayi. Kallon banza karuwan nan suka shiga yi mana gami da cewa" Ke! yi mana shiru dalla, kotun uwarki ce ko ubanki? Ko kuwa cewa aka yi za a yanke miki hukuncin kisa? Da za ki ɓarewa mutane shegen ƙaramin bakinki? Shut up!".
Suka faɗa da ƙarfi, ya yinda na ƙara tsorata su Ameera suna gefe suna jan zuciya domin dama ita da Ummi suna da taurin zuciya da taurin kai rin na Babanmu, ni kuma zuciyata irin ta Umma ce. Suma haushina suke ji, saboda kukan dana ishe su da shi su kam sun ɗau aniyar indai har suka fito takan Hajiya Babba za su fara.
¢¢¢¢¢¢¢¢¢¢¢
HAIDAR
…"Haidar na ce ka yi aure, amma ka ƙi yi shin so kake na mutu banga aurenka ba? Ga shi yanzu liikita yana faɗin indai har ba ka yi aure ba spam yana taking ɗin rayuwarka zai kumbura matsirarka saboda rashin fitar shi". Sai ta fashe da kuka mai ban tausayi, Mimi ta ce"Sorry Ammi ki daina kuka ai ga shi ya samh lafiya". Ta faɗi hakan a kunya ce saboda abin da Ammi ta faɗa yanzu ya ba ta kunya duk da dama can tasan da wannan matsalar.
Hammud ya gyara zama sannan ya ce"Ammi akwai wata ƴar ƙanin Baba na tana Zaria tana karatu ana ce mata Amira, kuma yarinyar na yaba da hankalinta wallahi idan da hali a haɗa su aure mana, wallahi zai so ta domin kuwa yarinyar ta haɗa duk abin da ake so a jikin mace, ilimi, tarbiyya, addini, kyau, nasaba, arziƙi".
Ammi ta nisa sannan ta ce" to ba matsala Hammud, idan ta dawo ka yi min magana". Hammud ya ji daɗi sosai domin ya gaji da ganin abokin shi a haka, saboda haka tun yau ya kamata ya yiwa Ameera albishir domin yasan ta daɗe tana matuƙar son Haidar, tun wani zuwa Office da ta yi wajen Hammud anan ta ganshi ta hargitse ta fita a hayyacinta da ganin shi.
Duk abin da suke faɗa yana jinsu, xuciyarshi na mishi wani irin zafi da raɗaɗi wai yau shi ne ake rarraba soyayyarshi zuwa ga ƴammata, tabbas yanza cikin taskon rayuwa ba don amininshi ya yi mishi haka ba da wani ne da tuni sun daɗe da raba gari, amma hausawa sunce sawun giwa ya tadda na raƙumi duk su biyun ba zai iya ja dasu ba, Ammi da Hammud yana jinsu acan cikin ranshi saboda haka yanzu zai haƙura ya sakko, duk wacce Allah ya zaɓa mishi a matsayin mata zai karɓa sai dai inda gizo yake tsakar, shi ne sam bai da ra'ayin auren macen da baya so tabbas idan hakan ta faru zai ƙwari ko wacece ma. Domin kuwa ba za ta taɓa samun farin cikin shi ba ko annushuwa irin na mata da miji ba.
Ammi ce ta katse shirun da ce wa" ni bari na tafi gida, tunda ga Triple ɗin ka a zaune Alhaji ya dawo tun jiya, yana maka sannu ma an jima zai zo meeting ya shiga ɗazu ne a babban hall".
Bai ce ƙala ba, saboda bai san me yasa ba sam baya son mutumin ba wai don ba shi ne mahaifin shi kawai sai domin wani babban sirrin da aka rufe wanda buɗe shi tamkar ɗaukewar numfashin wasu ne, ciki kuwa har da shi Alhajin.
Tasan dama ba zai ce komi ba, saboda haka ta ajje wata rantsatstsiyar kular da suka zubo mai abinci sannan suka fice ita da Mimi. Har sun fita Mimi ta dawo da baya kaɗan, suka kashewa junansu wani irin mayen cingum ɗin kallo ita da sahibinta Hammud, sannan ta yi saurin fita tun kafin Yayanta Haidar ya gansu, A banza tuni ya ga komi a zuciyarshi yana mamakin lokacin da suka ƙulla soyayya mai ƙarfi har haka, ba tare da ya sani ko ya ji labari ba domin a iya saninshi Hammud baya ɓoye mishi komi, ciki kuwa har da sirrikan da ba kowa ne ya sani ba sai shi sai Hammud sai Allah buwayi gagari misali.
¢¢¢¢¢¢¢¢¢¢
HAJIYA BABBA
Sosai ta razana har ta kasa ɓoye damuwarta ta saki ƙara...
hum, me Hajitya b ta gani ta tsorata? Shin menene abin da ya janyo tsoron?".
MISS GREEN CE
***
CHART ONLY.📲