16
💋ƊAN HALAK💋
MALLAKAR
UMMU MAHER(MISS GREEN)🍃
AREWA WRITER'S ASSOCIATION📚
~*Arewabooks*~
D'AN HALAK:: https://arewabooks.com/book?id=6631fffa0eeb3b80f1ef8159
~*Wattpad*~
D'AN HALAK
***
content=story_info
MAHER'S COLLECTION
***
MY CHANNEL LINKS
DOMIN SAMUN DAƊAƊAN LITTAFAINA.
***
0eYizXq3d
KEMA HAKA KI KE ZAUNE BA KIDA SANA'A? KO KUWA KINA YI SAMU NE BAKYA YI? KO KUWA KINA CIKIN MATA MASU ƘIWA?
TO KU BUƊE KUNNUWAN KU DA KYAU, SANNAN KU SANI SANA'A ITA CE JIGON RAYUWA MUSAMMAN MU MATA, UMMU MAHER TA SHIRYA TSAF WAJEN KOYA MUKU WAƊANSU SANA'O'I KAMAR
BEAD WORK🧶👚🧵
GRAPHICS✍🏻
MAGUNGUNA NA MU NA MATA🍃
RIBOMS NA YARA DANA MANYA💇🏻♀️💇🏻♀️
IDAN KIN SHIRYA KOYON DUKKANIN WAƊAN NAN SANA'O'IN KI YI MIN MAGANA TA NO ƊINA KAMAR HAKA;
***
16
HAIDAR
Wani irin ciwon kai ne ya turniƙesa, computer ɗin daya ɗauka domin yin aiki ya ajjeta can gefe, ransa amatuƙar jagule yana tunanin abubuwa da dama musamman kan wannan auren da za'a masa wanda bai shiryawa hakan ba, jin jikinsa yake tamkar ba nashi ba. ko da ya rasa yadda zai yi ya ɗauki wayarsa ya kira amininsa Hammud domin ya faɗa masa halin da yake ciki ko Allah zaisa ya samu sassauci.
Bugu ɗaya ya ɗaga yana tsokanarsa da ce wa" a'ah kaga manyan mutane kira ɗaya ninkin kuɗi k Allah dai ya.
Bai kulasa ba, daman kuma Hammud yasan ba lallai ne ya magantu ba saboda haka ya ce" kaga malam riƙe son kuɗinka agefe ba wata ƙwangila da zaka samu, wata magana ce na kira ka muyi amma inason ka bani shawarar daya kamata".
ya ɗan ja fasali, sannan ya ce" uhum ina jinka Horror".
baiyi niyyar sakin dariya ba, amma saboda kiran sunansa da yayi ahaka yasa ya ɗan dara sannan ya ce" Ammi ke son yimin auren dole, kuma wallahi ni ban shiryawa hakan ba, sai dai inason ka sani wallahi bana son wannan auren sam domin ni ayanzu haka auren ma ya fice min azuciya, gwara inyi zamana kawai domin aƙwai mutane da dama da sukayi rayuwarsu ba tare da kowa ba, kuma suka mutu cikin aminci".
sai daya gama maganarsa tsaf, sannan Hammud ya ce" banƙi ta bakinka ba Terro amma gaskiyar magana abinda Ammi tayi shi ne dai dai, haba Haidar shekararka nawa aduniya? ayanzu haka fa kana da kusan shekara 35 aduniya idan baka kai ba to kaɗanne, amma ace baxa ka yiwa kanka faɗa ba? Ammi ta sanya maka ido ne kawai, amma ganin baza kayi abinda ranta yake so ba yasa ta nema maka mafita, sannan kai da kanka kasan rashin lafiyarka aure shi ne maganinta, amma madadin ka samowa kanka mafita da maganin damuwa me ɗorewa sai kuma kayi watsi da hakan? gaskiyar magana kabi umarnin Ammi, amma idan har kace zaka bijire mata ka zauna babu mata gaskiya har abadan ba zaku taɓa shiryawa da Ammi ba".
"Hammud ba wai naƙi ta taku bane, a wannan rayuwar da muke ciki mafi yawanci mata suna aure ne saboda kuɗi, ba wai don suyi aure saboda samun aljannah ba, suna yi ne saboda muradin kansu da kuma wani ɓoyayyan sirri na son shagalin rayuwa, kuma ita kanta matar bakasan wacce iriya ba shin ƴar gidan tarbiyya ce ko akasin haka? shin me son abun duniya ce ko akasin haka? sanin gaibu sai Allah".
"haka ne, amma duk da haka ka sanya yaƙinin zakayi aure ne ba don komi ba sai don son sunnar annabi, sannan kayi domin mahaifiyarka kai yanzu awajenta kake neman aljannah ba wajen matarka ba, saboda haka ka bita sau da ƙafa azauna lafiya".
shiru ya ɗanyi alamar tunani, sannan ya ce" uhum zanyi yadda kace amma Hammud sai na dinga ganin kamar ba Ammi ce ta haifeni ba, domin tunda na taso ko jana ajiki batayi kamar yadda take jan Baby ajikinta, ko ƴan aikin gidanta tana matuƙar ɗaukarsu da muhimmanci fiye dani ma duk da nasan aƙwai wasu abubuwan da suka sanyata haka, ciki kuwa har dani na kasance ɗan fari kasancewarta Bafulatana to dole asamesu da kunya, amma abin yana shafata sosai bayan rashin uba har da rashin uba akusa dani".
Hammud ya gane me yake nufi, amma saboda bayason ya sanya abokinsa cikin damuwa sai ya ce" Ammi tana sonka Haidar, domin babu wata uwa da zata ƙi ɗan ta, saboda wani dalili hakan ma zai faru? tasha wahalar ɗaukar cikinka rani, zafi, inuwa, haka har ka girma ka mallaki hankalinka, to duk idan bata sonka wallahi baza tayi maka su ba, domin idan bakason mutum fita kake daga rayuwarsa amma ita Ammi kullum burinta ta janyo ka ajiki, shawarata gare ka kayi haƙuri komai zai zama dai dai".
ba tare daya ce komi ba ya kashe wayar, kiran Ammi ne ya shigo jikinsa amatuƙar sanyaye ya ɗaga kiran, gamida gaishe ta cike da ladabi sai dai ransa babu daɗi gamida alƙawarin da ta ɗauka na yi masa aure.
"Haidar inaso gobe kaje ku gaisa da Najma, saboda kaga abubuwa suna ƙara ƙaratowa kuma ta sanar dani cewar haryanzu bakaje gidansu ba".
jin taja wa'adin maganar sai ya ɗan ja fasali sannan ya ce" zanje in sha Allah".
daga nan bai ƙara ce wa komi ba, sanin hali yasa ta katse kiran baki ɗaya, zuciyarta duk babu daɗi akan auren da za ta yiwa ɗanta namiji tilo, sai take ganin kamar tayi masa ƙarfa ƙarfa ne ko kuma auren dole, domin sanin kanta ne Haidar mutum ne wanda bai damu da rayuwar mace ba, xata iya rantsewa da Allah tunda take bata taɓa ganin yarinyar da Haidar ya buɗe bakin ƙasaitarsa ya ce yana so ba, sai dai su suce suna sonsa wanda kusan duk macen da tayi katari dashi sai ta ƙyasa.
Ganin tayi shiru yasa Baby ma yin shirun, ta tafi duniyar tunani domin har ga Allah bataji daɗin wannan haɗin ba, domin tasan yasan wacece Najma yarinya ce wadda iyayenta suka lalatata, batasan komi ba sai shashanci da danna waya, chart da game sai kuma tiktok domin Najma tana ɗaya daga cikin ƴammatan da suke Tiktok, a ɓangaren hausawa kuwa za a iya ce mata don, domin tasan ta kan Tiktok duk inda wasu selebiriti suka kai a tiktok tasan dasu, suma kuma sunsan da ita.
Ammi ta ce" Baby bansan me yasa nayi wannan haɗin ba, saboda harga Allah wannan yarinyar ba kalar Haidar bace, yadda bai da magana da son tashin hankali na haɗasa da Najma, yarinyar da agidansu ta fitinesu idan tana gida hatta karnukan gidan nutsuwa suke, amma inaji ina gani saboda ƙawancan da muke da mahaifiyarta muka haɗa wannan haɗin, addu'ata Allah ubangiji ya basu zaman lafiya me ɗorewa".
"Ammi ni dai nasan za'a samu matsala wallahi, gata da shegen yawo da kuma ƙaryar tsiya duk da ansan mahaifinta yana da kuɗi kuma kowa yasan da hakan amma gaskiya idan kika ga rashin arxiƙin da suke aclub Allah Ammi abin ba daɗi, tamkar ba yaran musulmi ba".
Wata gauruwar ajiyar zuciya Ammi tayi sannan ta ce" to yanxu ya zanyi ne Baby? ai aikin gama ya riga daya gama, addu'ata ɗaya Allah ya daidata kansu ai mutumin banza yana komawa na gari, haka zalika mutumin ƙwarai yana komawa na banza, saboda haka ni na yarda da ƙaddara daman can Najma tana cikin allon ƙaddararsa wanda babu wanda ya isa ya goge hakan".
*******
WASHE GARI.
Shi kaɗai ya fito amotarsa ba tare da kowa ba, yasan gidansu Najma yana nan a Nasarawa G.R.A saboda haka awaje yayi fakin ɗin motarsa ya daɗe yana nazarin yadda zaiyi ya kirata, domin har ga Allah jin tsanarta yake sosai aransa tamkar dai yadda ya tsani ɓatawa mahaifiyarsa, ba don bin umarnin uwa ba da ko ahanya bata isa ya ɗaga kai ya kalle ta ba, saboda sam bata da wani tsarin matar daya yarjewa zuciyarsa wajen neman aurenta, domin manzonmu annabi Muhammad (S.A.W), ya horemu da mu auri mace don tarbiyyarta da addininta, ba don kuɗi ko kyau ko mulki ba idan ma kuɗi ne shima yana dasu kuma har yafi nasu ma, saboda haka dole ne ya samarwa kansa mafita domin ko ganin murmushinsa baza tayi ba, ballantana ma har ta ce zata faɗa masa wata magana irin tasu ta ƴan duniya ƴan tasha.
daga can nesa ya hangota cikin mota ƙirar corolla, ita da wani yana jan motar sai dariya take har tana wani ƙamesa tamkar da mijinta take hira, kana ganinsa kasan ƙwararran ɗan duniya ne wanda duniya ta gaji dasu a gidan ɗan kande, daga can gefen gidansu ya ajjeta ta fito ya yafito ya da hannunsa yana wani kashe mata idanu tamkar wanda yayi shekara ɗari rabonsa da mace.
haushi da nadamar zuwa suka ishi Haidar ƙiris ya rage zuciyarsa tsinkewa ya tafi, amma sai ya tuna umarnin da mahaifiyarsa ta basa tuno da hakan yasa ya sauke kansa ƙasa, zuciyarsa sai tsinkewa take tana wani irin luguden dakan masara.
Har ta shige gidansu bata kawo komi aranta ba.
ganin zata shiga gida kuma bata gansa ba yasa ya fito ahankali, cike da takun nan nasa mai matuƙar burge ƴam mata, daga nesa da ita ya tsaya sannan ya kira sunanta acan cikin maƙoshi.
"Najmah".
wani irin magana ɗisu ne ya kamata, tayi saurin juyowa domin tunda take arayuwarta ba'a taɓa kiran sunanta taji daɗin sunan irin na yau ba, ta amsa da sauri.
"Na'am".
Ganin Haidar yasa ta saki wata irin ajiyar zuciya gamida yin wani ƙayataccen murmushin daya gaza ɓoyuwa har sai daya fito fili ya zama kamar dariya".
wani irin baƙin ciki ne ya turniƙesa ganin murmushin da tayi, ya haɗe girar sama da ta ƙasa bai ƙara ce wa komi ba ya ɗan dafa jikin motarsa yana kallon wani waje na daban.
Cike da garaje ta ƙaraso tana yaƙe haƙora, da rashin kamun kai tamkar kurar da taga abin hararta har wani tuntuɓe take tana lilo tamkar zata faɗo kansa.
"sannu da zuwa yaya Haidar, baka faɗamin zaka zo ba ai da ban fita ba".
ya ɗan ja numfashi sannan ya ce" no ba komi".
Tasan halinsa da jin kai, da kamun kai saboda haka yasa ta ce" to mu shiga daga ciki ka gaida Hajiya ko? Dady ma yau zai dawo kaga daya dawo sai ku gaisa".
wani irin kallon ƙasa yayi mata, ta tsargu da kanta saboda haka sai ta ce" to bama sai ka shigo ba ai mun gaisa".
Sam baya son mace me shegen surutu tamkar wata aku, amma babu yadda zaiyi tunda ya ɗakko kanki da motsi........😝😝😝
na ce ba su Aisha arage surutu saboda zamuje shagalin bikin Haidar da Najma😝😝😝🤪😂 ni dai ina cikin ƙawayen masu kamun kai😂
Ina masu son shiga adashe Amma kuna fargaba🤔yar uwa ki tsarkake zuciyan ki kizo kiyi adashe cikin aminci da kwanciyan hankali insha Allah Babu rigima ko tashin hankali kwanciyan hankali zaki Yi adashen ki Kuma mu gama lfyh da yardan Allah..🥰🤝
30k weekly parking 300k
1)Haj Maryam✅
2)Ada umar/hafsat yahya✅
3)Usman
4) barrister hauwa'u
5)shafa bello/baby daura
6)
7)
8)
9)
10)
Akama slot
***
QsRmuDuL
$HAIDAR
$NAJMA
$AMMI
$BABY
$HAMMUD
MISS GRERN CE