KULSOOM

THREE

by @oumameer2671

               💝 KULSUM 💝

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

             BY

AMINA IBRAHIM

     OUM AMEER

 

CHAPTER THREE

    Washe gari sai wuraren ƙarfe tara na safe na iya  rama sallolinda ake bina na Magrib da Isha sannan na gabatar da sallar Subhi, sakamakon dogon daren da na shafe ban samu na runtsa ba ina karanta wasiƙar jaki.

  Bayan na kambala na jingina jikina ga bangon ɗakinmu still ina  kan sallaya zaune ina lazumi hawaye kuma a hankali suna saukomin lokaci lokaci.

  Kallona Khadija tayi cike da tuhuma tace.

“Anty Kulsum baki da lafiya ne?”

Ɗan game fuska nayi nace.

“A'a lafiya lau nike..”

Tace.

“If so what happen to your eyes? Naga sun kumbura kuma sunyi Ja kamar kinyi kuka”

Cike da masifa nace.

“ I said I'm fine, kada ki dameni please”

Ficewarta tayi ta barni tana mai ɗaga shoulder ɗinta alamar ba ruwanta. ni kuma sai bin ta nake da uwar harara ina jin kamar naje na rufe ta da duka saboda kowa na gidan ji nike yana bani haushi.

  Sai kusan sha ɗaya na safe na fito,Madafa na nufa na ɗebo ruwan zafi na nufi toilet na murzo wanka na na fito. Kan hanyar toilet ɗin na haɗu da Innani kasancewar duk faɗin gidan toilet ɗaya ke gare mu.

Kauda kaina na sake yi ina sauraron inji ta sauke min kwandon jidalinta sai dai itama ko kallon inda nake bata sake yi ba sai ma raɓaninda tayi ta wuce abinta tana mai jan tsaki, hakan kuwa da tayi min ba ƙaramin daɗi yayi min ba, domin da zamu shekara haka to ba ƙaramin farantamin za tayi ba.

  Mayukana na jiki na ɗauko na zauna ina shafawa. Innata itace abin alfaharina ni da Khadija da kuma yayanmu Naziru, babu wani abinda zamu ce muna so in dai bai fi ƙarfinta ba face tayi mana shi daidai da matsayinmu. Domin cewa take kada ka bari in dai abu bai fi ƙarfinka ba ɗanka ya gani ga wani. Babanmu ya kasance mai sayar da kayan hatsi a kasuwa itama Inna kayan hatsin take sayarwa a cikin gida tana bawa mata idan sati ya zagayo su kawo mata kuɗi, ga kayan tarkacen yin  girki komai tana sayarwa ga injin niƙa ga gawayi da itace. Kuma sai Allah ya sanya albarka a kasuwancin nata don ba ƙaramar riba take samu ba haka ma Babanmu. Dalilin hakan ne yasa tun daga primary har zuwa secondary na kuɗi mukayi daidai da matsayinmu ni da Khadija. Haka kayan sawa kayan kwalliya komai muke so saya mana take. A yanzu da naga na taka wani matsayi na cikakkar budurwa kuma haɗuwata da Maimu ta ƙara wayar min da kai yanda zan iya karkarowa kaina mutunci a duk inda nike, hakan yasa komai na manyan babes na ke yi. Kayan organic skin care  ɗinnan na zamani su inna take sayamin yanzu,hakan yasa fata ta kullum take luwui tana ƙyalli da sheƙi, Farina ya daɗa ƙara kyau da walwali. Hakan yasa kullum ƙofar gidanmu bata rabo da masu yimin sallama mutanen kirki masu sona da aure tsakani da Allah, amma ni sam ba sune a gabana ba, hangen abinda yafi ƙarfina shi nasa a gaba, domin da zan zauna in yi  nazari na masu hankali to tabbas zan gane cewa wutsiyar Raƙumi tayi nesa da ƙasa.

Ina cikin zura kayana najiyo sallamar Maimu a tsakar gidanmu. Muryar Innani na tsinkaya tana faɗin.

  “Wace mayyar ce da sanyin safiyar nan?”

Ɗan risinawa Maimu tayi tace.

“Innani Ina kwana?”

Wani irin kallon wulaƙanci ta jefa mata tare da taɓe baki tace.

“Sai wani fama kike da dogon wuya kamar jumina, wallahi ni dai Allah ya gani bana ƙaunarki a cikin raina, ah to ita gaskiya ɗaya ce a faɗeta komai ɗacin. Tunda kika shigo rayuwar Kursume tarbiyyarda Sulmanu da Habiba suka yi mata ta taɓarɓare, kullum sai shegen yawo kamar kunci ƙafar kare, ah to ita dai gaskiya ɗaya ce ƙarewa da duniya lafiya yafi komai daɗi...”

Leƙowa nayi na ƙarewa tsakar gidan kallo ganin Inna bata wurin rai ɓace nace.

“Maimu come in..” 

Daƙuwa Innani ta jefamin tana faɗin.

“Jar bayan gidanku! Jar bayan gidanku nace! Yo naji figaggiyar yarinya fitsararriya, to wallahi ni dai ba ruwana duk abinda kuka ɗauko ya ƙare bisa kanku”

Ciki na koma abina ina  turo baki ina gunguni domin Innani ba ƙaramin kofsamin take ba. Itama Maimu ta biyo bayana tana jin haushin irin cin kashinda Innani ke mata duk sanda ta shigo gidanmu. Haka ma ga Innata duk sanda ta ƙyalla ido taga Maimu ta shigo gidanmu shikenan fara'arta ta ɓace.

  Kallonta nayi nace.

  “Share ta Maimu kin san halinta ai”

Murmushin dole ta ƙirƙiro ta ɗora shi akan fuskarta tace.

“Lah! Ba fa komai Kulsum, waye bai san tsoho ba, whats up? Wallahi duk kin ɗaga min hankali tun 7am na fita kuma ba don kowa ba sai don saboda ke”

Zaunawa nayi ina mai ƙara lowering voice ɗina nace.

“I didn't get you, what do you mean by saboda ni kika fita tun 7am?”

“Eh to area ɗin su khaldun naje...”

Gyara zamana nayi ina mai ƙwalo ido waje nace.

“Doing what a area ɗin su khaldun?”

Murmushi Maimu tayi tace.

“You are joking with me Kulsum. Naje area  ɗin ne yin bincike Allah ya taimakeni akwai gidan su wata ƙawata kusa ga gidan su khaldun ɗin. Shine naje tare da addu'ar Allah yasa tana ƙasar domin suma gidan su wasu shegu ne in gaya miki,sai ko naci sa'a tana nan. Bayan mun gaisa a siyasance na shiga tambayarta khaldun. Do you know what Kulsum”

Ƙureta nayi da fitilun ganina kamar zata ɓace min jikina ya fara mazari tamkar wadda ake yiwa kiɗan gangi nace.

“Sai kin faɗa Maimu”

“Da ƙyar da suɗin goshi na samu ta ɗan furzarmin da wani zance game da shi. Babban abun farin ciki shine mun gano weakness ɗinsa wanda tilas zai mana abinda muke so... ”

  Muryata na rawa nace.

“And what is that?”

“Mahaifinsa ya rasu shekara bakwai da suka wuce, yana da ƙannenshi guda uku, akwai Sa'ad shine  mai binsa, akwai Ayusha sannan Meerah. Mahaifiyarsa bai haɗata da komai ba, yana yi mata biyayya fiye da zato, duk abinda ta umurcesa ko na daɗi ko akasinsa muddin bai saɓawa addini ba to  zai  aikata shi babu ɓata lokaci. Saboda haka yanzu dole ki san ta yanda zaki kitsawa Inna cewa you are 4weeks pregnant kuma kinsan wanda yayi, saboda haka kawai aje gidan su. Muna zuwa da wannan zancen na san dole zata ce sai ya aure ki kinga kuma bai isa ya gardama ba, shi kenan mun samu abinda muke so”

  

Yadda zancenta ke shiga ta wannan kunnen haka yake fita ta wannan domin wannan maganar banza ce maganar wofi. Sai da ta dire na girgiza kaina a ruɗe nace.

“Allah ya tsare ni Maimu, Haba! Cikin Shege fa? Mi Inna da Baba suka yimin da zan saka masu da wannan kalmar...”

Tsaki ta ja tace.

“That's your problem ke kullum a baibai kike ɗaukar zance shiyasa ba ki da fahimta. Bafa cikin gaske ba, kawai wata dama ce damar kuma ta ƙarshe wadda daga ta wuceki  shikenan..”

“A'a Maimu jikina fa in duk kunne ne ba zan yarda da wannan gurguwar shawararba, da muguwar rawa aka ce gwamma ƙin tashi, nayi kunya ɗaya ba zan sake ta biyu ba. Beside Innata firgitattar kurwa ce da ita, ina zuwa mata da wannan zancen lokaci ɗaya zata birkice min ƙila sai tayi suma goma, daga nan sai zawo sai asibiti. Ga Innani ga Babanmu ga Yah Naziru, kai ina! Gaskiya a'a”

Girgiza kai tayi a ranta tana addu'ar Allah yasa in amince sannan tace.

“Kulsum ina so kafin ki yanke hukunci ki fahimceni da kunnen basira. Mahaifiyar Khaldun tana so yayi aure amma ko budurwa bai da ita a yanzu, wannan itace damar ki ta ƙarshe ta samun khaldun. Bafa kaina nake yiwa fighting ba ke ce, duk alherin nan da nike binki da shi sai nike ganin kamar baki yabawa”

Ajiyar zuciya na sauke tare da Kallonta nace.

“Maimu, I will think about it, gaskiya abin ne da wuya. Cikin Shege fa. Hmm! Ai fata ta gari lamiri.”

Miƙewa tayi tare da saƙala Jakarta tace.

“OK! Sai naji  daga gare ki, ki zauna kiyi tunani, dama ce da ta suɓuce miki shikenan”

Tana fita na koma ruwa da sabon tunani, kwata-kwata yunwa tundaga daren jiya na nemeta na rasa. Anya na shirya ma aikata wannan katoɓarar kuwa ni Kulsum?

   

            OUM AMEER