4
by @nkds
❉্᭄͜͡𝘚O 𝘿𝔸𝑵☆ R̲A̳Yᑌᗯᗩ ♥️
☆♥︎L⋆o⋆v⋆e⋆ ᖴOᖇ 𐐛օv𝖊♥︎☆
𝗕Ⲩ 𝔸mmⅈ𝖊ყ ℓαуℓєян & ɴᴀɪɴᴀʀ kd♡
Page 4
Sai washegarin ranar Esherh take sanin Maah a gida ta kwana domin koda Maah ɗin ta dawo dare ya yi kuma tuni Esherh ta yi bacci shi ya sa bata tashe ta ba sai da Safiya ta yi misalin takwas lokacin Esherh ta fito cikin shirinta tsaf na fita aiki ta sakko ƙasa. Versace woman suit ne jikinta launin pink da ta yi matuƙar dacewa da ita riga da wando ta riƙe coat ɗin a hannu ƙafafunta cikin wasu arnun ankle strap heels, sai ƙamshin perfume na Le Labo Kawai take fitarwa gashinta da ya sha gyara in upsweep style kuwa naɗe cikin veil na Louis Vuitton da ta yi rolling kanta da shi a hankali take taku ɗaiɗai daga kan stairs ɗin har ta ƙari sa sakkowa zaraf idanunta ya shiga na Maah dake zaune a Dining area da alama breakfast ta kammala jerawa shi ne ta zauna zaman jiran sakkowar Esherh'n.
“Laa Maah Tah wai kece da gaske?”
Esherh ta faɗa cike da zumuɗi tana ƙari sawa har da ɗan gudu-gudunta Dining Room ta a je mini bag nata Pink color a kan Kujerar Dining ɗin tare da ɗafalewa Maah ɗin ta rungumota tana dariya.
Dariya Maah ta yi tana shafa kanta ta ce.
“Wato dai ke har a kullum bakya girma ko? Yanzu Fisabilillah so kike ki karyani?”
Turo Lips ɗin ta dake ɗauke da Fenty Beauty Lip gloss ta yi jin abin da Maah ɗin ta ce cike da shagwaɓa irin yadda ta saba ma ta ta ce.
“Waassh MaahMaah kinji ki da wani batu fa yanzu ni ɗin har wani ƙiba gareni da zan karya ki?”
Maah tana murmushi ta ce.
“Sosai kuwa dan na lura kwana biyun tashen cin abinci da yawa kike fama da shi.”
Dariyar da ya bayyana haƙoranta farare tar da su Esherh ta saki jin kalaman Maah tasan da biyu ta yi dan ta tsaya taci abinci.
Sai lokacin suka gaisa cike da ƙauna irin na uwa da ‘ya kuma cike da raha sannan Maah ta ƙara da faɗin.
“Zauna muyi breakfast ɗin kafin ki tafi dan nasan ba ƙaramin abu ba ne a wurinki ki iya fita Company ba tare da kinci komai ba”
Maah ta faɗa tana ɗan kafe ta da ido har da wani ɗaure fuska wai dan ma kar Esherh ɗin ta ga fuska har ta ce a ƙoshe take.
Ba musu kuwa Esherh ta zauna suka ci abincin suna yi suna fira bata ci da yawa ba ta tashi ta yi ma Maah sallama sannan ta baro Ɓangaren nasu bayan Maah ta haɗa ta da wani abincin a flask da shima musamman ta yi ma ta kamar yadda ta saba na Lunch sai da Esherh ta biya ta gaishe da kakan nata wato Mahaifin Maah ɗin ta cikin raha kamar yadda suka saba sannan ta yi masa sallama ta bar ɓangaren nasa daga nan ta ƙari sa wurin Security na musamman da Granny da kansa ya ware domin bata tsaro zuwa aiki kasancewar Ranar Monday ne tushen aiki wata farar JAGUAR XJL sabuwa fil ɗaya daga cikin security ɗin ya buɗe ma ta ta shiga sannan ya rufe kana motocin guda uku a jere suka ƙari sa harabar Babban Gate na Estate ɗin tare da fita daga ciki a nutse har suka hau titi kasancewar ta ba mai son gudu da mota ba shi ya sa motocin suke a jere kuma a hankali suke tafiyar.
Ethereal Kreations Joint EKJ
Shahararre ne kuma lamba cikin Company da a ke ji da su ta hanyar samar da kayayyaki na sakawa na mata da ma sauran kayan ado irinsu sarƙa abin hannu jaka da sauransu, ainihin Companyn mallakar Maah ne sai dai sakamakon abubuwa da suka yi ma ta yawa ya saka shekaru biyu ke nan da ta damƙa akalar Companyn gaba ɗaya a hannun ɗiyarta Esherh domin Fashion Designer ta karanta kuma cikin ikon Allah a ƴan waɗan nan shekarun ba ƙaramin ɗaukaka da nasarori Companyn ya ƙara samu ba shi ya sa a koda yaushe Maah take alfahari da ɗiyar nata dama kuma tun farko da sunan Esherh ɗin ta buɗe Companyn ma'anar EKJ ɗin shi ne ESHERH KALTHOM JEDDY's sai dai ta ɓoye hakan a ranta ta kuma saka wa sunan wani ma'anar daban saboda wani manufa nata shi ya sa Esherh tana kammala karatu ta yi gaggawar damƙa ma ta ragamar Companyn yanzu Matsayin CEO Esherh keda a Companyn kuma tana iya kar bakin ƙoƙarin ta wurin ganin a kullum Companyn ya ci gaba da samun nasarori da ɗaukaka domin ta wannan hanyar ne kaɗai zata tabbatar wa da Maah ɗin ta cewar lallai jaruma ce ɗiyar nata kuma mai ƙaunar farin cikinta.
♡♡♡
Esherh zaune take cikin hamshaƙin katafaren Office nata dake hawa na ƙarshe kuma ya wadatu da komai na alfarma cike wasu takardu take before su shiga meeting da zasuyi da wani Companyn na fashion design daban a kan wata ƴar saɓani da ta shiga tsakaninsu na design ɗin sabuwar sarƙa da za su fitar sai kuma wancan Company ɗin suka ɗauka suka danƙarawa nasu design ɗin suka kuma riga su fitarwa.
Knocking ɗin ƙofar Office ɗin a ka yi kusan sau uku a tare haɗe kuma da danna doorbell dake wurin duka lokaci guda.
Ba tare da ta ɗago daga abin da take yi ba kuma bata nuna damuwa a kan wannan abu da a yi ba dan ta bari ta ga wani mahaluki ne hakan ya sa ta bada umarnin shiga ta hanyar furta.
“Come on in.”
Kafin ta rufe baki sai ga Basma ta bayyana cikin office ɗin kai da gani kasan a wani irin fusace take sai dai ganin yadda ko arziƙin Esherh ɗin ta ɗa go ta kalle ta bata samu ba bare ta sama gwarin gwiwar zubar mata sa buhu-buhu da wando na rashin mutunci da kuma warning da ta zo ta yi ma ta a kan mijinta hakan kuma da Esherh'n ta yi ba ƙaramin ƙara fusa ta ta yi ba.
A fusace ta ƙari sa tare da buga desk ɗin gaban Esherh da hakan ya sa wasu daga cikin takardun dake wurin suka yi sama wasu kuma suka zube.
A hankali ta ɗa go manyan fararen idanunta tare da ware su saman fuskar Basma dake uban huci sannan cikin nutsuwa ba tare da wani reaction ba ta sake lumshe idon nata sannan ta ware su a kan Sakatariyar ta da ta biyo bayan Basman a ruɗe cikin son fidda kai tun kafin Esherh ta furta komai Sakatariyar ta riga ta da faɗin.
“Am so sorry ma'am nayi duk iya ƙoƙarina a kan hanata shigowa amma taƙi har sai da ta riba ce ni sannan ta shigo....”
“Okay You can wait outside.”
Esherh ta katse da faɗin hakan tana mayar da hankali wurin ɗaukar takardun da suka barbaje a ƙasa, godiya Sakatariyar ta yi ma ta sannan ta fita taja musu ƙofa.
Ci gaba Esherh ta yi da abin da take yi kamar ba zata kula Basma da ta gama kai wa iya wuya ba sai dai ta kasa taɓuka komai tun daga duban farko da Esherh'n ta yi ma ta.
“Zaki iya zama naji dalilin zuwanki idan kina buƙatar hakan a ka sin hakan kuma nan ba filin shirme da shiririta ba ne zaki iya jira a waje har zuwa lokacin da kika shirya faɗan abin da ya kawoki.”
Esherh ta fara maganar ba tare da kalla inda Basma ɗin take ba ta kuma ƙare tana mai ɗagowa tare yi mata wani duba tana jingina bayanta jikin Kujerar da take kai.
“Ke Esherh ba roƙon ki nazo ba da har zakiyimin wannan kalamai zuwa nayi domin yi miki kashedi da babbar murya a kan ki rabu da mijina ko fita a harkarsa inda kuma ba haka ba hhhh to fa duk abin da ya biyo baya ki kuka da kanki!”
Basma ta faɗa a tsawace tare da fizge handbag ɗinta da ta aje ta juya da nufin barin Office ɗin.
“Who are you and your fucking husband?”
Tambayar rainin hankalin da Esherh ta yi ma ta shi ya sa ta tsayawa cak! Sai kuma a wani irin fusace ta juya domin bata amsa daidai da tambayarta sai dai ganin Esherh tsaye dab da ita da batasan lokacin da hakan ya faru ba shi ne ya sa ba shiri gabanta ya yi mummunar bugawa sai ta kasa faɗin abin da ta yi niyya.
“Daga mijin naki har ke idiot dake ban ɗauke ku a bakin komai ba kuma wannan ya zama karo na farko kuma na ƙarshe da zaki ƙara zuwarmin office da shashanci irin wannan domin na rantse kika ƙara to fa shafawa idanuna toka zan yi sannan na haɗa ki da security su lallasa min ke idiot!”
Esherh ta ƙare maganar tana fidda hannuwanta dake zube cikin trouser pocket nata sannan ta ƙari sa gaban madaidaicin Fridge zake office ɗin ta buɗe tare da ciro Holandiya sannan ta koma saman Sofa na office ɗin ta zauna ƙafa ɗaya kan ɗaya sannan ta fara kurɓar abin ta hankali kwance.
“Zaki iya tafiya idan baki da sauran abin faɗa.”
Esherh ta katse Basma da ta shiga Duniyar mamaki da kuma tsoro da faɗin hakan bayan ta sauke bottle ɗin a bakinta.
Jiki a sanyaye kuma da ɗan gudu-gudu Basma ta bar Office ɗin cike da takaicin wannan cin mutunci da Esherh ta yi ma ta.
Bayan fitar Basm girgiza kai kurum Esherh ta yi tana mamakin rashin haƙuri da kuma kishin hauka na wasu matan, ita Allah ya gani ma Omer ɗin ma baya gabanta sam sai dai wannan zuwan da Basma ta yi dama tsokiburutsunta sun saka taji wasan ya fara yi ma ta armashi zata so wasan ya ci gaba domin ganin yadda Basma zata yi.
Mintuna kaɗan da faruwar hakan suka shiga meeting ɗin ainihin lamarin shi ne ma'aikaciyar wancan Kamfanin ta kasance tsohuwar ma'aikaciya ce a kamfanin su Esherh ɗin kuma tana daga cikin waɗan da suka fitar da wannan design sai dai an koreta daga kamfanin ne sakamakon kamata hannu bibbiyu da a ka yi da karya dokar kamfani ta hanyar bada sirrinsu ga wani kamfanin daban shi ya sa a ka koreta ita kuma da ta tashi sai ta shiga wancan Kamfanin da ta sama dama shi ne ta basu design na kamfanin su Esherh a matsayin ita ta ƙirƙira su kuma da basu san ainihin gaskiya ba sai suka fitar da sabuwar sarƙa da irin wannan design ɗin.
Shiru Esherh ta yi lokacin da suka kawo nan kowa ya san gaskiyar da ma'aikaciyar da kanta ta faɗa ganin asirinta ya tonu.
Miƙe wa shugabar ɗayan kamfanin da a ka yi meeting ɗin da su tayi cike da takaici tare bawa ma'aikaciyar wasu kyawawan tagwayen maruka biyu sannan ta ƙara da tabbatar ma ta da korarta a aiki da suka yi dalilin wannan abu da ta yi kana ta juya tana duban Esherh da ta juya tana shirin barin Ɗakin taron.
“Bakiji ba?”
Juyowa Esherh ta ɗan yi domin taji mai zata ce.
Cikin sanyin murya Matashiyar ta furta.
“Zamu iya magana a keɓe Please?!”
Shiru Esherh ta yi tana yi ma ta kallon nazari sai kuma ta jinjina kanta.
_____
“Ga wannan”
Matashiyar ta faɗa tana a je ma Esherh Maltina a kusa da ita sannan ita ma ta zauna zaune suke cikin wurin hutawa da kuma cin abinci dake Companyn.
“Na gode.”
Esherh ta faɗa sai kuma suka yi shiru ita Matashiyar ta ƙanƙame bottle na fiji water dake hannunta yayin da Esherh ta yi shiru tana jira taji ta inda zata fara da dalilin son sun keɓance ɗin.
“Am sorry again about what happened earlier Wallahi nima ban san haka abin yake ba.”
Matashiyar ta faɗa tana ɗa gowa suka haɗa ido da Esherh sai Esherh taga ashe ma har hawaye take yi.
“Karki damu ba wani abu komai ya wuce kuma ba laifin Kamfanin ku ba ne amma duk da haka ku dinga kula.”
Esherh ta faɗa tana duba Tiffany & Co wristwatch dake ɗauke a tsintsiyar hannunta.
Cike da murmushi Matashiyar ta yi ma ta sallama sannan ta ƙari sa wurin motocinta dake jiranta suka bar Companyn.
Sai yamma liƙis Esherh ta koma gida shima badan lokacin barinta Company ya yi ba sai dan jikinta da yake yi ma ta ba daɗi.