Barrister Hibba
by @nusybee143
đź’Ą BARRISTER HIBBA đź’Ą
✍️Nusy bee
Page 6
Jabir ya zaro idanu a tsorace yace"kai Muyassar!a wane dalilin?har akwai wani iko da ta nuna maka wanda baka nuna mata ba a matsayin ta na boss ɗin ka?kuma Ni banga abin zafi anan ba,ya kamata ace ka bi komai a sannu, rayuwar ma gaba ɗaya nawa take?kuma dukkan wani aiki da kake gani a duniya da kalar ƙalubalen shi,ita fa wannan matar indai ka bi dokokin ta wallahi lafiya ƙalau zaku zauna,duk wasu maganganu da su mas'udu suke faɗa akan ta ƙarya sukeyi,ko nace shaci faɗi,just try her zaka bani labari"ya ƙarasa maganar yana bubbuga kafaɗun shi
Ajiyar zuciya Muyassar ya sauke sannan ya wuce wajen zaman shi ya zauna yana tunanin yadda zai zauna da Hibba lafiya su rabu lafiya
Wajen ƙarfe uku na yamma Hibba ta fito,kamar dai yadda ta saba sanye da track suit ash colour na PSG,da baby hijab ɗin ta,sai ƴar ƙaramar jaka da ta saka wayar ta da ƙananun abubuwan buƙatun ta, idanun ta sanye da medicated glasses da bata rabo dashi,a harabar gidan ta ga Muyassar a zaune,batare da tace masa uffan ba ta jefa masa makullin motar ta,bin makullin da ya faɗi ƙasa da kallo yayi, girgiza kai yayi ya ɗauki makullin ya danna,motar ƙirar GMC tayi ƙara ya ƙarasa ya fito da motar,shine ya buɗe mata motar,bayan ta shiga ya mayar ya rufe,sannan ya shiga mazaunin driver,ya tayar suka bar gidan
Sai da suka hau titi sannan tace "unguwar rijiyar lemo zaka kai ni"batare da yace uffan ba ya gyaÉ—a mata kai
Sai da suka kusa isa inda zasu je,daidai wani gida dake ɗan ciki da titi taga taron mutane yara da manya maza da mata har da matasa,yaran sai ihu suke suna kiran "ɓarauniya ɓarauniya!!", wata budurwa ta hango wasu gardawa sun cacumi wuyan hijabin ta,sai kuka takeyi cike da tashin hankali da rashin sanin madafa,take ta ji kanta ya sara,wani moment da bazai taɓa gogewa a memory ɗin ta bane ya haska,da sauri tace"tsaya,tsaya!!"shima dai zai so yasan abinda ke faruwa, shiyasa bai wani ɓata lokaci ba ya tsaya
Ya fito don buɗe mata ƙofa ina!tuni har ta fice daga motar ta ƙarasa inda matasan da suke rirriƙe yarinyar take tana faɗin"me yake faruwa ne? laifin me tayi haka?"
Wani saurayi da bai wuce shekara sha takwas ba cikin yanayin rashin kunya yace"ɓarauniya ce,sata tayi mana"
"Me ta É—auka muku?"
"KuÉ—i ta sace mana,har dubu bakwai"take wajen ya É—auki sallallami
Hibba ta girgiza kanta cike da takaici sannan tace
"To kunga,ku sake ta zamuyi magana,zan biya Abinda ta sata,ke yaya sunan ki?"
"Yarinyar tana share hawaye tace"Hafsah"
"Malama Hafsah me ya kai ki É—aukar musu kuÉ—i har kika janyo sukayi miki irin wannan tereren?"
Cikin gunjin kuka tace"Aunty jarrabawa nake son zanawa ta WAEC,shekaru uku kenan,na kasa haÉ—a kuÉ—in sai wannan shekarar na samu na haÉ—a,sai da na kai akace akwai dubu goma da zan biya,shine na É—aukar musu kuÉ—i,amma wallahi ba hali na bane,na rasa yadda zanyi ne"shiru Hibba tayi tana kallon yarinyar,sai kuka takeyi,sauran mutane sai surutu sukeyi a cewar su WAEC É—in dole ce,cikin sanyin murya Hibba tace"ina iyayen ki?"
"Mahaifi na ya rasu,sai mahaifiya ta,ita kuma tana da larurar ciwon ƙafa,sauran duk ƙanne na ne su huɗu,sai na yi suyar awara da wankau sannan muke samun abinda zamu ci"
Shiru Hibba tayi tana jan numfashi da kyar,batare da ta kuma magana ba ta buɗe seat ɓangaren mai zaman banza ta dauko wasu envelope guda uku,ɗaya ta miƙawa matasan tana faɗin"ga kuɗin ku, Allah ya huci zuciyar ku"sauran biyun kuma ta miƙa wa Hafsah tana faɗin"ki biya har da NECO,ki rubuta JAMB, Allah ya taimaka"ta ciro complementary card ɗin ta ta miƙawa Hafsah tace "wannan kati na ne,ki samu waya ki kira ni"daga haka ta faɗa mota batare da tabi ta kan godiyar da Hafsah ke jera mata ba
Muyassar ƙam ya kame yana tsananin mamakin wannan mata,idan yace karamcin da tayiwa Hafsah bai burge shi ba yayi ƙarya,to menene gaskiya a halin ta, wulaƙanci da I don't care attitude,ko damuwa da damuwar mutane,bai ƙara nutsewa a kogin mamaki ba sai da yaji shashsheƙar kukan ta,ya duba ta madubi,tabbas kuka takeyi,kuka kuma mai bayyanar da ciwon da zuciya take ji,to menene dalili?indai Hafsah ce shi a ganin shi ai ta magance matsalar ta ko?to menene abin kuka kuma?shi dai ya cigaba da driving ɗin shi ba tare da yayi Magana ba don yasan tsaf sai ta yarfa shi
Kafin su ƙarasa gidan Hibba ta goge hawayen fuskar ta,suna ƙarasawa wajen gidan ta umarce shi ya tsaya,yana tsayawa wani matashin saurayi da zai kai sa'an su Marwa ko ya girme musu da shekara ɗaya ko biyu ya taso da fara'a ya nufo motar ya buɗe baya yana murmushi yake faɗin"yaya!yaushe kika dawo?"
ĆŠan murmushi tayi tace "umma tana nan?"
"Eh tana nan,yaya wannan karon Germany ta riƙe mana ke da yawa,ke da bakya wuce 2-3 months"
Fitowa tayi tana faÉ—in"Ameer ayyuka na a wannan karon sun fi yawa fiye da lokutan baya,mu je cikin gidan dai"tayi gaba ya biyo bayan ta, Muyassar ya bi su da kallo, zuciyar shi fal mamakin su waye waÉ—annan da suka samu irin wannan daraja a wajen Hibba
Hibba kuwa a rumfar ƙofar ɗakin umma ta samu umman,ita kanta umma cikin matsanancin mamaki take duban Hibba, Hibba ta ƙarasa tana murmushi ta rungume umma tana faɗin"nayi missing ɗin ku baki ɗaya"
"Lallai ma Hibbatu,wato sai yau ake ganin ki ko?"Hibba ta ja baya tana murmushi take faÉ—in"ayyuka umma"daga nan suka zauna suna gaisawa
Sun daɗe suna hira,har da Ameer kafin ya fita,da ameera da ta dawo daga tahfeez kuma tayi joining ɗin su bayan ta gama ihun murnar dawowar yaya,su kaɗai kawai ta gayawa dalilin daɗewar ta,suka jajanta sosai,don ameera har kuka tayi,tace"Allah ya tsare gaban ki da bayan ki yaya, Allah ya kare ki daga sharrin dukkan mai sharri"murmushi Hibba tayi tana faɗin"ameen autar mu,umma yau me kuka dafa ne?Ni fa nayi kewar traditional dishes ɗin ki"umma tayi murmushi tace"sanin dokar ki ta ƙin magana sai an gama cin abinci yasa banmiki magana ba sai mun gama hira,dambun tsaki ne da zogale nayi yau har gyaɗa na saka,Ameera zubo mata"Hibba tayi wani sassanyan murmushi ta mayar da kanta jikin bango ta kwantar tana tuna baya,yadda suke shan drama ita da su Arwa akan abinci,a hankali ƙwalla ta fara taruwa a kwarmin idanun ta,tayi dabara ta goge
Hibba bata tafi ba sai bayan ƙarfe biyar,shi dai Muyassar ba bakin magana,ga lokacin tafiyar shi gida ya wuce,daga nan ma wani mall na kayan wasan yara ta saka shi ya kai ta
Shima sun ɓata kusan mintuna ashirin da biyar,daidai wajen parking lot tana daf da shiga motar ta,kamar ance ɗaga kai ta hango wannan likitan da ta taɓa mari a asibitin su Dr Khaleed
Shima wani kallon banza yake watsa mata, bata ƙara kallon shi ba ta faɗa mota suka wuce gida
Bayan ta fito daga motar zata wuce gida ta zaro dubu ashirin ta miƙa masa batare da tayi magana ba,ganin bashi da niyyar karɓa sai ta ɗora akan motar ta wuce cikin gidan,ya bi ta da kallo
Jabir ne ya ƙaraso da sauri yana faɗin"wannan kuɗin overtime ɗin ka ne fa ta biya ka"
"Okay bata da bakin bayani sai dai ta wani ajiye min wasu kuÉ—in ta kamar wani dabba da za'a ciyar?"
"Nace don Allah kayi haƙuri,haka yanayin ta yake,mitar bata da amfani"ya saka hannu ya ɗauki kuɗin ya damƙa shi a hannun Muyassar yana faɗin"take it easy please Brother,komai mai wucewa ne, watarana mu ma duk Bama nan"
Muyassar ya amshi kuÉ—in ya yi masa sallama ya nufi hanyar fita
Yana shiga cikin gidan su ya jiyo kukan zeenat,amma yana sallama tayi hanzarin goge hawayen ta tana amsa sallamar shi,sai da ya zauna sannan ya kalle ta yace"me ya ke damun ki?"
Shiru tayi da farko,kafin daga bisani tace"yaya kan ciwon khaleel ne,sai yunƙurin tashi yake"jikin shi a sanyaye ya ciro kuɗin da Hibba ta bashi ya kirga dubu goma ya bata yana faɗin"ki kai shi peadiatric a duba shi sosai,idan da buƙatar ƙarin kuɗi kiyi min magana"da mamaki zeenat ta kalle shi tace"yaya wata fa yayi tsakiya, Allah yasa ba bashi ka karɓo ba"Muyassar yace "ko bashi na karɓo ai maganar lafiya akeyi zeenat, ballantana ma ba bashi na karɓo ba,na aiki ne"yana gama faɗa ya wuce ya fara alwala
Zeenat cikin sanyin murya tace"na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi ya ƙara buɗi"ta share hawayen ta,tace"yaya ya kamata ka ƙara yiwa baban shi magana,bai kamata....."
"Hold it please zeenat!na gaji da yiwa mukhtar magana,yayi duk abinda zai yi, Allah bazai hana mu yadda zamu kula da khaleel ba in Sha Allah,don haka ki kwantar da hankalin ki kawai"yana gama magana ya cigaba da alwalar shi
MIAMI BEACH, FLORIDA,USA
"Kana bani mamaki Auwal,yanzu wannan yarinyar da a haihuwar kaji ka haife ta,wadda tun kafin tazo duniya kake aikin lawyer amma ka kasa gano shirin ta, gaskiya ina jin babu amfanin saka ka wannan aikin"cikin faÉ—a mutumin yake magana
Daga can ɓangaren Barrister Auwal cikin kwantar da murya yace"I'm sorry alhaji, wallahi yarinyar nan ta shirya,har Lagos fa naje don na lallaɓa wannan ƙawar tata ta gaya min wani abu,amma abin mamaki ban samu komai ba,da alamu ko dai bata faɗa mata ba ko kuma tayi mata warning"
Babu ɓata lokaci Alhaji adam doguwa yace"sai a kamo ƙawar tata ko ɗan ta,zata magantu ta faɗi abinda suke ɓoyewa ita da tsinanniyar ƙawar tata"
Babu ɓata lokaci Barrister Auwal yace"Barrister Khadijat bata sani ba, definitely da ta sani ko hint ne zan samu"
Cikin jin haushi Alhaji adam doguwa yace"amma ka manta ne itama Khadijat lawyer ce?"
"Na sani alhaji, shiyasa na zo mata da dabaru,amma wallahi yarinyar nan babu abinda ta faÉ—a mata"
"To yanzu meye abinyi?kasan ya kamata fa muyi duk mai yiyuwa kafin ranar zaman kotun nan,don ma sauƙin ta an kawar da Rahama da suke taƙamar itace shaidar"
"Alhaji ka kwantar da hankalin ka,na san ƙwarewa irin ta Barrister Nuraddeen,wacece wata Hibba kuma?"
"A'a fa Auwal!kar ka fara raina iyawar yarinyar nan,da ƙwaƙwalwa take tunani,ka duba fa ƙannen ta tun a Abuja muke bibiyar su har zuwa nan Kano amma mun kasa kama su"
Auwal ya jinjina kai yace"tabbas three days back sun fito har na saka yara na sun fara bibiyar min su kawai sukayi reverse suka koma,amma ka kwantar da hankalin ka Alhaji,zanyi ƙoƙarin ganin na kifar da yarinyar nan a gaban ka"
"To Auwal, Please try your best"
"Okay sir"
To pa!na fara ruɗewa akan Barristers ɗin nan guda biyu, Awwal da Hibba 🙆
#Nusy_bee