Chapter 34 Book 3
KUSANCI BOOK 3
34
Haka washegari suka tattara suka wuce Ɗandume, cikin jagulewar zuciya, domin duk abinda suka sa rai zasu samo basu samo ba.
Suna kuma isa gidan Malami suka tadda abinda Haj Aseeya ta faɗa duk gaskiya ne.
Gida ya cika da ma'aikata, kowa sai kaiwa da komowa yake yi.
Alh Bello shi ma sai fita yake yana dawowa ana ƙara sauke duk wani abu da ake buƙata.Da shi da ya'yansa su Sagiru da Hamza da Anas duk ya'yan wajen Anti Amarya ne.
Baki kawai su Alh Saluhu suka saki suna kallon yadda bangaren Dada ya koma a cikin ƙanƙanin lokaci, lalle kuɗi ƙare magana.
Gaba ɗaya ɓangaren Dada ya koma wata alkaryar duniya.
Da ɓangaren Bakil da Sajeeda ne ya kwashe mafi tsokan kyawun gidan Malami amma yanzu bangaren Dada shine kat.
Domin ginin zamani akayi, komai hassadarka ƙarya ka ke ka kushe aikin da akayi.
Hakan yasa Alh Saluhu ya tattara hassadarsa ya shige sasansa, cikin ƙunan zuciya.
Babu wata tariyar kirki daya samu daga Haj Aseeya, asalima yana kallonta ya fahimci tana cikin damuwa, gashi duk fuskarta ta faɗa sai kace wacce tayi ciwo.
Alh Saluhu ya dubeta sosai yace "Ya na ganki haka duk babu walwala kamar wacce bata da lafiya".
Ta juyar da kai gefe, ita kanta tasan tana cikin damuwar da ta kasa ɓoyewa, tun daga lokacin da Mallam mai Rauhanai ya tabbatar mata da babu abinda zai iya yi akan Bakil ta shiga damuwa, ita kanta aikin da akayi mata shekara da shekaru ji take tana kuma fargabar kamar itama zata rasa dukkan damarta wata rana.
"Zazzaɓi ke dan damuna".
Yace "Allah ya baki lafiya",
Ya karkace ya zaro dubu biyar a cikin aljihunsa ya miƙa mata "Idan Murtala ya shigo sai ki bashi ya je ya samo miki magani", fara'ar fuskarta ta faɗaɗa ta karɓa tana faɗin "Yaya Nura ya yi muku kyakkyawar sallama kenan".
Ya ja tsaki yace "Ba wata sallamar da ya yi mana, ai yaya Nura bashi da niyyar taimaka mana Aseeya, baya son mu bai kuma damu damu ba, dama Bello ne, kina ganin yadda muna can a wulaƙance shi kuwa yana nan yana kwasar kuɗi yana cika asusunsa", tace "sosai kuwa, don wannan aikin na masu kuɗi ne, cikin ƙanƙanin lokaci dubi yadda aka maida sasan Dada", "Abinda ke ta bani mamaki kenan, ni kaina da nake cikin gidan ban san aikin ya yi wannan nisan ba, Dada dai haihuwa tayi mata rana, ɗan da take zaton shine masifarta yau shine ya zama sanyin idaniyarta".
Alh Saluhu ya haɗe rai yace "Mu ma ai da mune sanyin idaniyarta a lokacin da muke da shi,amma yanzu da bamu da shi mune banza a wajenta".
Haj Aseeya tace "Aini Hadeeza ce ke bani mamaki, bafa ta kulani sai wani fisgar kai take yi, har yanzu bakinta baiyi min maganar komawar Sajeeda ba". Ya saki tsaki yace "kowa dai ya je ya ci kansa, in ɗai zumuncin gidan Malami ne Allah ya raba mu da shi".
Ta taɓe baki tace "Amin dai, kowa so yake yaga bayan ɗan'uwansa, yanzu ka duba kaga irin muguwar ƙiyayyar da matan gidan nan suke yi min, daga Bintu har Hadeeza da Naja babu wanda ke shiga harkata, tun da suka je suka gaida Sajeeda a asibiti shikenan suka ɗauki muguwar gaba da ni, ga waɗannan marasa mutuncin Maryam da Harira wani irin cin kashi suka ɗauka, tunda suka dawo gidan nan wani irin raini suke yi min musamman Maryam, rannan har zagi na taso tayi, ko da yake maganganun da ta gaya min garama ta zage ni da su".
Alh Saluhu ya gyara zama rai ɓace yace"Maryam ɗin ce ta kusa zaginki? Shi Ibrahim ɗin yana ina?" Ta saki tsaki tace "Yana ko ina, duk abinda akayi ya ji ya sani duk da ba'a gabansa a kayi ba, amma yaron nan babu matakin da ya ɗauka, sai zuwa da yayi ya bani hakuri, ita da tayi laifin kuwa har yanzu bata leƙo sasan nan ta bani haƙuri ba, tunda ta samu dama, mijinta yana ɗaure mata gindi, sai abinda taga dama take yi, ya zama shanyayye abinda ta tsara masa shi yake yi".
Alh Saluhu yace "Amma kuwa Ibrahim bai ji daɗin rayuwarsa ba, Allah ya shirye shi, mu dai an jarabemu da yawa a Rayuwa, don ko da jarabawar su Ibrahim da Bashir aka barmu mun shiga uku, ace ayi ya'ya babu imani babu tausayi, basa kallon kowa sai kansu".
Haj Aseeya tace "Na rantse maka ada lamuransu bai wani damuna amma a yanzu abin na mugun damuna, bana jin daɗin komai, ina jin wani irin rashin natsuwa da rashin kwanciyar hankali kwana biyun nan". Alh Saluhu ya numfasa yace "Allah ya yi mana maganin abinda ba zamu iya ba, amma gaskiya akwai damuwa". Haj Aseeya ta dube shi tace "Nawa yaya Nura ya baku", sai da ya tsaya ya yi min inda inda sanan yace "Nawa ko ya bamu, dubu hamsin ce mu biyu wai muyi kuɗin mota". Ji tayi bata yarda da abinda da ya faɗa ba amma sai ta danne tace "To ai akwai ragowar wanda ya tura maka ko na tafiya da Sajeeda".
Ya girgiza kai yace "Na biya yan basussukan da ake bina, saboda ina son na samu kwanciyar hankali".
Ta taɓe baki tace "To koma dai menene, ka lalubo min ko dubu ashirin ne ka bani, ni ma na rage bashin da nake ci nake hidimar gidan", Alh Saluhu ya yi shuru kafin daga bisani yasa hannu a aljihunsa ya ciro dubu goma ya miƙa mata yace "kiyi haƙuri da wannan babu kuɗin duk sun ƙare".
Haka ta karɓa babu yabo ba fallasa sannan kuma babu godiya.
Lissafi kawai take yi yadda zata biya kudin kajin da ake yanka mata a kauyen mai Rauhanai.
Tasan Munzali baida kuɗin da zai ci-gaba da ranta mara ana sayen kajin, gashi mai bada kaji yace ya daina ba da bashi, ta na hango matsala fa, saboda dai bata da yadda za'ayi kullum ta dinga sayen kaza guda daya, yadda kajin nan ke tsada.
Hakika sai yanzu take hango mugun ƙoƙarin da tayi na tsawon shekarun nan da take yanka kullum.
Domin dai a yanzu zahiri tana jin ta gaza, ba zata iya ci-gaba da yin wannan yankan ba, tunda babu bashi ita kuma bata da wata hanyar samu.
Dama duk wasu yan kayanta masu daraja dalilin hakan duk ta gama ɗagawa ta sayar, tana ta adashi a bankin asara, ga mutumin da baya iya tsinana mata komai, ko abincin kirki baya iya bata, balle sutura da sauran daukar nauyinta, kawai ta ɗorawa kanta wahala da rashin kwanciyar hankali, dama duk abinda ka neme shi da asiri to da wannan asirin zaka yi ta nemansa har ka mutu, wannan wace irin masifa da taɓewa ce.
Haj Aseeya ta ƙara sakin nunfashi, ta na kallon Alh Saluhu, tana jin komai yana kwance mata, damuwa da rashin natsuwar da ke damunta kuma suna ƙara bijiro mata.
Daga bisani Alh Saluhu ya tashi yana cewa "Babu abinci ne a gidan", tayi masa wani sakaran kallo tace"Babu, ban dafa ba don banda kuɗi a hannuna".
Ya gyada kai yace "Bari naje na samo ko taliya ce sai ki dafa mana, don yinwa nake ji".
Bata tanka ba har ya fice daga ɗakin.
**********
Cikin kwanaki biyu kaɗai Sajeeda duk ta gama fita hayyacinta. Har Bakil ya gama kwanaki biyunsa ya koma gidan Jawaheer, bata bacci da daddare, ko ya ya ta rufe idanunta Mallam mai Rauhanai take gani, cikin mummunan fuska mai cike da tsoro da tashin hankali.
Ta shiga tsananin tashin hankali, ta kuma shiga tunanin hakan na nufin a duk lokacin da ta je wajen Mallam mai Rauhanai ko Haj Aseeya ta je a madadinta kenan haka zata kasance cikin cikin irin mugayen mafarkai da Wannan mummunan halin kamar yadda ta kasance a Ɗandume bayan zuwansu ƙauyen.
Gaba ɗaya duk ta firgice,a yanzu abin ya canja salo, don a duk lokacin da ta kwanta da nufin yin bacci, mallam mai Rauhanai take gani kusa da ita yana ƙoƙarin keta mata haddi, kokawa suke yi sosai wanda daga karshe idan ta farka ta kan ji gaba ɗaya kamar an cire lakar jikinta, takan ji ba ta iya magana bata iya ko da runtsa hannunta , sannan ta dinga jinta tamkar ana ɗagata sama ana saukarwa ƙasa.
Duk kwanaki biyun da Bakil baya gidanta a falo take kwana yadda kuma taga dare haka take ganin rana babu bacci.
Tsoron ka da ta sanar da Haj Aseeya halin da take ciki tayi mata faɗa ko ta ƙaryatata ko ta ɗauka cewa tsoronta ne na tsiya yasa take ganin hakan, kamar yadda tayi mata a Ɗandume, wannan dalilin ne yasa ta ja bakinta tayi shiru taƙi gaya mata.
Sai dai ita kanta tasan cewa tana cikin tsaka mai wuya.
Domin tana cikin mummunan halin da bata san inda lamarin yasa gaba ba.
Shin me yasa take ganin Mallam mai Rauhanai a cikin mafarkinta?, Mai yasa a cikin mafarkin yake son aikata alfasha da ita?, Me yasa take jin kanta kamar ya kwance?, Sannan mai yasa take gane gane masu ban tsoro a cikin mafarki?. Shin haka zata zauna bata bacci?.
Nan da nan cikin ƙanƙanin lokaci Sajeeda ta rame tayi firgai firgai.
Shi kansa Bakil har baya kaunar kwana ya zo kanta saboda yadda babu mai yin bacci a cikin su.
Nan gunta yake karewa da zaran tayi ihu ta tashi daga bacci shikenan bacci ya karewa kowa, shi zai tayi mata addu'a har ta samu kanta, duk kuma yadda zaiyi da ita akan ta dinga daurewa tana addu'a ba ihu ba kamar yadda take yi, to fa ta kasa canjawa, tunda bakinta bai saba da addu'ar ba.
Tuni Bakil ya yarda ya kuma tabbatar da cewa aljanu ne suka shafi Sajeeda.
Addu'a yake yi mata a kullum idan yana gidan tana samun sauƙi, tunda wani lokacin idan abin ya faru ya yi mata addu'a ta dawo hayyacinta tana ɗan yin bacci.
Amma idan baya gida har maganin da yake hanata bacci take sha saboda ka da tayi mafarkin mallam mai Rauhanai.
Ta rasa gane kanta, ta rasa inda zata fuskanta.
Yanzu Lokacin ma da zata samu tayi wulaƙancin a gidan bata da shi.
Tana ta kanta ne kawai a yanzu.
A kalla ta kwashe kwanaki cikin wannan masifar.Daga bisani ta fara samun sauƙi, ta daina gane ganen da take yi, ta kuma fara samun bacci, a dalilin yadda Bakil ya dage da addu'a a gidansa, sannan ya kafa mata sharaɗin ko yaushe ko yana gidan ko baya gidan kullum ta dinga sanya karatun Kur'ani a babban mp3 din da ya sayo.
Don haka dole Sajeeda ta canja wajen sanya karatun Kur'ani kullum a cikin gidan saboda ta Hakane kawai take jin sauƙin halin da take ciki.
A lokacin ne saura kwanaki uku babbar sallah, Haj Aseeya ta koma gidan Mallam mai Rauhanai bayan ya kirata a waya cewar ta zo ta karɓar ma Sajeeda taimakon da ya gama haɗa mata.
Tun da ta shiga ƙauyen yau ta ji gaba ɗaya duk wani karsashi a jikinta ta nema ta rasa.
Haka zalika yau itace rana ta farko da ta ji wani irin mugun tsoro da fargaba ya cika zuciyarta, wanda ba tasan dalili ba.
A gaban Mallam mai Rauhanai kuwa da ta zauna ji tayi kamar tana cikin wata muguwar halaka, ko ƙwaƙƙwaran motsi ta kasa yi, gabanta sai wani irin bugawa yake yi babu ƙaƙƙautawa.
Mallam mai Rauhanai ya yi mata kallon tsaf sannan ya ɗakko wani ɗan ƙaramin tulu yasa hannunsa na hagu ya fito da wata ɗaurarriyar laya da ta tsumu cikin wani irin ruwa dake cikin tulun mai warin gaske, yace
'karɓi nan"
Hannunta na wani irin rawa ta karɓa, ta kuma ƙurawa layar ido yadda take wani irin santsi da yanayin warin da take yi ya ƙara jefama Haj Aseeya tsoro a cikin zuciyarta.
Mallam mai Rauhanai ya ƙara dubanta sosai yace "Wannan layar kada kiyi wasa da ita domin babban aiki ne da Rauhanai suka ɓata lokaci wajen yin aiki a kanta, babu abinda zance akan kyan aikin nan, amma ki sani wannan layar zata canja rayuwar yarki Sajeeda, canji mafi kyau, duk wani alheri wannan layar zata kusanta Sajeeda da shi, zata samu kwanciyar hankali mai ɗorewa" .
Haj Aseeya ta gyara zama tana nazarin muhimmancin layar a tare da Sajeeda, yadda kawai ya dage yana bayani ta gane cewa shi kansa aikin yana da muhimmanci a wajensa.
Ta gyaɗa kai tace "Nagode sosai mallam Allah ya saka da alheri, menene ladan aikin, duk da dama ban zo da kuɗi ba". Ya girgiza kai yace "Bazan karɓi ko sisi ba, tunda wancan aikin ba'a samu nasara ba to wannan bawan karɓi komai ba, na bada gudunmawata a gareta".
Ta washe baki ta ci-gaba da dubansa tana yi masa addu'a da godiya mara misaltuwa.
Ya dubeta yace "wannan layar Sajeeda da kanta itace zata karɓa ta samu cikin filon da take sa kanta wanda babu mai yin amfani da shi sai ita, ta buɗe cikin filon ta sanya layar a ciki ta maida ta ɗinke, ta ci-gaba da kwanciya akai duk runtsi ta tabbatar ta tada kai da shi a lokacin da ta zo kwanciya".
Haj Aseeya tace "za'ayi hakan, wannan ai mai sauƙi ne".
Ya tura hannunsa kasan wata tsohuwar tukunyar ƙasa, ya fito da ƙwai guda uku da duk suka sha rubutu a jikinsu da Yaren ajami, tun a lokacin da Haj Aseeya tayi karatu tasan abinda aka rubuta a jikin ƙwaysyen da tashi ta gudu, amma da yake jahilci ne fal a kanta, bata fahimci komai ba, sai karɓa tayi cike da godiya tana neman karin bayani.
Ya kafeta da ido yace "wannan ƙwan a kan zallar wuta zata ɗora shi, zata ga yana konewa da kansa yana komawa baƙi idan ya gama zama baƙin ƙirin sai ta sauke ta haƙa rami ta binne su a ciki".
Ya ƙara kallonta yace "ina tabbatar miki da cewa komai zai zamo haske a rayuwarta, sauran abubuwan da zasu biyo baya ma da kanku nasan zaku neme ni".
Haj Aseeya ta shiga zuba masa godiya.
Kai kawai yake gyaɗawa yana zuba wani irin murmushi na rashin dalili.
Daga bisani ta tattara duk abinda aka bata ta tura a cikin jakar hannunta, sannan tayi sallama da shi, ta fito, da wani irin kallo ya bita.
A waje ta tadda Munzali yana zaman jiran fitowarta.
Tana fitowa ya nufota yana murmushi, "Hajjaju kin fito?".
"Na fito Munzali, zan tafi gida, ya maganar yankan kaza".
Munzali yace "Ai an kwana biyu ba'ayi yanka ba, saboda kuɗin hannuna sun ƙare kuma da gaske yake ya daina baki bashi, don babu yadda banyi da shi ba amma ya ƙi".
Haj Aseeya ta yi jugum duk ta damu tace "Gashi ni ma ba ni da kuɗi Munzali, ga bashin da ka bani, dole sai dai ayi hakuri da yankin nan na wani lokaci kafin na samu yadda zanyi". Munzali yace "To Allah ya bada yadda za'ayi, amma ni bashin da ki ke bi na ki bar sa shi a lissafin damuwarki domin na yafe miki".
Wannan karon tsayawa tayi sosai tana kallon cikin idanun Munzali, ƙoƙari take ta gano dalilin irin mutumcin da karamcin da Munzali yake yi mata a yanzu.
Sai dai babu abinda ta gane, kawai dai tana ganin hakan a matsayin karamci irin na Munzali da mahaifinsa.
Haka suka jera Munzali nayi mata rakiya kamar yadda ya saba yi mata a duk lokacin da ta zo.
Dai dai tsakiyar gidan, babu zato ba tsammani, wannan ƙatuwar matar mai hararar Haj Aseeya tun shigowarta gidan kawai tasha gaban ta.
Tana yin wani irin huci kamar macijiya, daga ita sai ɗaurin ƙirji cinyoyi duk a waje, bata da ko kyan gani.
Munzali yace "Haule menene haka?"
Ta watsa masa harara tace "Ban sani ba, ba da kai nake yi ba, sai ka saurara min ka jira har na zo kanka tukuna".
Haj Aseeya tace "To ikon Allah".
Ta matso yadda Haj Aseeya take iya jiyo mugun warin hammatar da take surmawa, har sai da ta matsa gefe, Haule ta saki tsaki tace "ke malama, kada ki ɗauka bana lura da komai, na riga na gane ki, mai niƙabin sharri, nasan dama da biyu ki ke rufe fuskarki saboda kin san da irin sharrin da ki ke shigowa gidan". Haj Aseeya tace "wane irin sharri?, Kan ki ƙalau kuwa?",
Haule tace "Ras nake, Amma ki sani zanyi miki haukar da ki ke nema don idan baki rabu da mijina ba sai na haƙa rami na binne ki da ranki".
Haj Aseeya tsoro da mamaki ya kamata,
Ta dubi Munzali da ke tsaye kamar ruwa ya ci shi.
Sannan ta dawo da kallonta ga Haule tace "waye mijinki?, Me zan ci kuma da mijinki ni da nake da aurena".
Haule ta nuna Munzali tace "Ga mijina na nan, kuma ba ni kaɗai bace mu biyu ne, kin ci Sa'a ɗayar bata nan, amma ina so ki sani wannan binbinin da ki ke yi na mijina ya ishe ki, ina ruwana da kina da aure , auren da bai hanaki bibiyar nawa mijin ba, ina lura da duk sanda zaki zo gidan nan Munzali shi ke taryarki shi ne kuma ke raka ki ki tafi, bayan ba ke kaɗai ke zuwa gidan nan gun Mallam ba, me yasa duk sauran jama'ar dake zuwa Munzali baya shigo da su kuma baya raka su sai ke shafaffiya da mai".
Wani haushi da takaici ya kama Haj Aseeya ta dubi Munzali rai ɓace tana mamakin yadda ya kasa taka ma matarsa burki, maimakon hakama sai wani mirgina katon kansa yake yi yana wani sassadda kai kasa kamar wani munafiki.
Ta dubi Haule sosai tace "ke ki ke ganin mutum anan, Munzalin me?, Me zanyi da shi, da tarin shekaruna aka, ko ba ni da miji ko maza sun ƙare nafi ƙarfin Munzali ke ba ma shi ba ko ubansa Mallam mai Rauhanai nafi ƙarfin sa nafi ƙarfin wannan ƙauyen naku, mai cike da talauci, ke ni duk wanda ke cikin wannan ƙauyen ban ɗauke shi a matsayin mutum ba, balle har na wani bibiyi Munzali".
Wannan furucin nata ba Haule ba ba Munzali ba har Mallam Mai Rauhanai da hayaniyarsu ta fito dashi daga bukkarsa sai da ya girgiza shi ya kuma tayar da hankalinsa.
Munzali ya yi saurin cewa "Haba Hajjaju ya zaki dinga yin irin Wannan maganar mara dadi? Ya zaki ce kinfi ƙarfin Mallam? Sannan ya zaki yi kice bakya kallon mu a matsayin mutane".
Haj Aseeya ta dube shi sosai rai ɓace tace "kai baka jin irin banzar maganar da matarka take gaya min, me zanyi da kai da zata dinga danganta ni da ina bibiyarka, shi yasa na gaya mata ko Mallam ɗin bai ishe ni ba, nafi ƙarfinsa balle kai, idan banda ma jaraba da rashin dogaro da Allah mai zai kawo ni wannan ƙauyen, ina jin baki san wacece ni ba?, Shashasha kawai".
Tana gama faɗin haka ta ja tsaki, ta juya ta nufi hanyar fita, a yayin da Haule ta bi bayanta tana ƙoƙarin fisgota, tana zazzaginta tana nuna haushin yadda tasa Mallam acikin maganar su.
Haj Aseeya da gudu ta ƙarasa fita daga cikin gidan saboda yadda Haule ke ƙoƙarin fisgota ta yi mata duka.
Shi ma Munzali ya kasa daga ƙafarsa ya kuma kasa yi ma Haule magana, saboda sosai abinda Haj Aseeya ta faɗa ya ɓata ransa.
Haule na juyowa tayi ido biyu da Mallam mai Rauhanai yana huci, ai da gudu ta shige bukkarta, sauran matan da duk suka fito suna kallon abinda ke faruwa suma duka suka shige bukkokinsu a tsorace.
Munzali ya juya don yaga dalilin guduwar kowa, mallam mai Rauhanai ya gani tsaye ya harɗe hannu a saman kirjinsa, idanunsa gaba ɗaya sunyi jawur, kamar yadda fuskarsa duk ta canja, nuna alamun duk abinda ya faru yanzu a gabansa ya ƙona ransa.
Munzali ya nufo shi da nufin zuwa wajensa.
Amma sai ya juya da sauri ya koma cikin bukkarsa.
Munzali ya tsaya shiru, da Haj Aseeya tasan abinda ta faɗa zai jawo mata da bata yi ba, sannan ta tafi ba tare da tasan cewa Mallam ya ji duk abinda ta faɗa ba balle ta bashi haƙuri kafin tafiyarta.
A kuma mugunta da tsarin Mallam mai Rauhanai duk abinda akayi masa ma ɓacin rai matuƙar aka kwana ba tare da mutum ya zo gabansa ya ƙaskantar da kansa ya neme shi gafara ba, to bazai taɓa yafe masa ba, kuma sai ya yi ma mutum mummunan abun da zai zama masifa a tare da shi.
Munzali sai tsuma jikinsa yake yi, yana jin gabansa na faɗuwa, lokaci ɗaya kuma yana jin tausayin Haj Aseeya.
Haka Haj Aseeya ta koma gida cikin ɓacin ran matar Munzali, da ta ɗsuketa a matsayin mahaukaciya, sannan yau shi ne karo na farko da ta ji nadamar zuwa kauyen su.
Domin tana ganin Haule ta ci mata fuska matuƙa da gaske, Munzalin da bai wuce sa'an Bashir ba ɗan cikinta, shine zatayi zaton wai tana sonsa tana kuma bibiyarsa.
Da ƙatuwar mota ta kamfani ta dibar kaya ta fara cin karo a kofar gidan malami, ana ta sauke kayan alatu na ɗaki tun daga kan gadaje har zuwa kan kujeru, firij da su talabijin, duk dai wani kaya na more rayuwa ana ta saukewa ana shiga da shi cikin gidan.
Haka Haj Aseeya ta shiga gidan cike da mamaki.
Sai da ta shiga ta fahimci duk kayan sasan Dada ake kaiwa, can ta hangi Haj Hadeeza da Haj Bintu, sai Anti Amarya ana ta shirya kayan da ake saukewa.
Wasu irin fitilu masu matukar haske da akasa a ɓangaren Dada sun haske ko'ina, waje fa ya koma kamar wata sabuwar alƙarya.
Takaici ya ƙara cika Haj Aseeya, ga ɓacin ran abinda ya faru a ƙauyen mai Rauhanai ga wannan abin da ta zo ta tadda,
Wato su Haj Hadeeza sun haɗe kai kenan sun ware ta.
Rabon da taga Anti Amarya da Haj Hadeeza a inuwa ɗaya har ta manta.
Shi ma Alh Bello malami sai kaiwa yake yana komowa cikin hidima, har zata shiga sasanta, ta hangi Ibrahim da Bashir suna fitowa daga cikin falon Dada suna goge zufa, da alama duk da su ake yin aikin, bata fita daga wannan takaicin ba ta ga Maryam da Harira da saudatu da Mariya suma duk sun fito suna kama wani ƙaton madubi zasu shiga da shi ciki.
Tana nan tsaye idanu jajir kamar ta fasa kuka, Hafiz da Abba suma suka shigo da barguna da zannuwan gado, ba su ko ganta ba saboda idanunsu basa kanta, suka wuce.
Wato dai yau ɗaya duk gidan Malami sun haɗe kai akan aikin Alh Nuraddeen canji, su kaɗai aka ware ita da mijinta da Alh Nasiru, shin wai mai ta tarewa gidan Malami ne?, Wace irin tsana suke yi mata a yanzu?, Me yasa babu mai shiga harkarta.
Cikin tsananin tashin hankali da ɓacin rai, ta buga kofar sasanta ta shiga ta maida ƙofar ta rufe.
Ko daki ta kasa shiga nan bakin ƙofa ta zauna tana shaƙar iskar takaici.
Dai dai lokacin Murtala ya turo ƙofa zai shigo, langa langar kofar ya ja rigarsa, har sai da ta yage, ya juyo cikin ɓacin rai yana cewa "wannan masifa da yawa, kullum zan shigo sasan nan sai kofar nan ta yaga min riga, wai kofa shekara kusan biyu amma an kasa gyarata, sai asara take ta jawoma mutane".
A fusace Haj Aseeya tace "Anƙi a gyara, kai uban me ya hana ka gyara tunda tana ja maka asara, marasa amfani kawai". Murtala ya haɗe rai ya ƙarasa shigowa yana faɗin "Au, na manta shi fa sasan nan ba'a faɗan gaskiya, bari nayi shuru Umma".
"Kada Allah yasa kayi shurun ma ka ci-gaba"
Murtala ya tsaya yana kallonta yace "Ya na ganki haka?, Duk rai a ɓace, na shigo ɗazu na tadda bakya nan, shine naje nasa hannu a aikin sasan Dada, anan na samu na rana, Baba Bello wata arniyar shinkafa yasa Anti Amarya ta dafama duka ma'aikatan muka ci muka koshi harda nama a ciki, ɗazu kuma da na gaji da aikin zan fita, Baba Bello dubu biyu ya ɗauka ya bani kyauta".
Ta watsa masa harara tace "Kyauta ko ladan aikin wulakanta kan da kayi masa,ku dai ba ku da zuciya, shashasha mara kan gado, na ɗauka kai kana da hankali zaka fi sauran tunani ashe duk ƙanwar ja ce".
Murtala ya dubeta sosai yace "Yanzu don na taimaka a aikin da akeyi ma Dada shine ki ke ganin rashin kyautawata, haba umma wai wane irin tunani ki ke da shi ne?, Me ke sa ki ke irin wannan halayen marasa kyau, idanunki na lura kullum a rufe suke da hassada da rashin son ganin cigaban kowa, kinfi son komai yakasance ke kaɗai zaki amfana da shi".
Tsananin mamakin maganganun Murtala yasa Haj Aseeya ta buɗe baki,
"Ni kake gaya ma haka Murtala?".
Ya jinjina kai yace "Gaskiya ce da bakya so umma, ko yanzu ai kema Yakamata ko da bakya nan da ki ka dawo ko ba ki taya su aikin komai ba, kema ki leƙa kiga yadda aikin ke tafiya ki ga guri kisa albarka, amma kunnena na ji ana gulmarki a wajen cewa tunda aka fara aikin sasan Dada baki taɓa takowa kinga wajen ba.......".
"Au gulmata suke yi, makirai marasa mutunci, idan sun isa su zo suyi a gabana, naƙi naje na gani ɗin ina ruwana, ko an kasa da ni ne balle na ɗauka, sannan har kaji ana gulmata amma ka kasa yin komai ka ji kawai ka wuce".
Murtala ya gyara tsaiwarsa yace "To me zance musu umma, bayan nasan gaskiya duk suka faɗa, gaskiya Yakamata ki canja umma lokaci dai baya jira" .
"Fita ka bani waje".
Cikin tsawa da karaji Haj Aseeya ta faɗa, nan da nan Murtala ya gigice domin bai taɓa ganin mahaifiyarsa a cikin irin wannan mummunan yanayin ba....................
Yar Gidan Imam✍️✍️