Page 1&2
*🌹TUNANIN ƘARSHE🌹*
A taste of the final thoughts before the storm begins…
By
Fateyzahraah
Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin kai, Alhamdulillah! Godiya ta tabbata ga Allah SWT, wanda ya bani ikon fara rubuta wannan littafin Allah yasa yadda na fara rubuta wa lafiya na gama lafiya, Ameen!.
Ƙirƙiraren labari ne ban yi shi ɗan cin zarafin wani ko wata ba, idan wani abu yayi kamanceceniya da rayuwar wani ko wata to Arashi ne, kuma idan har kun ga wani abu na ƙaddara cikin wannan labari, to wannan hanya ce ta bayyana yadda ɗan adam zai fuskanci gwagwarmaya.
Labarin na nuni da yadda wasu lokutan cikin rayuwa suke zama marasa fata, duk da cewa mutum yana cikin gata da soyayya. Rayuwa ba ta zo da sauƙi ko shahararrun hanyoyi kawai, yana da alama za a fuskanci ƙaddara mai cike da ƙalubale. Wannan labari yana ƙunshe da wahala da juriya, wanda zai taɓa zuciyar ku, yana neman ku duba a cikin zuciyar ku kuma ku yi tunanin abin da zai faru na gaba.
Bari mu fara wannan tafiya, wani tafiya ne na fuskantar ƙaddara mai tsanani, soyayya mai wahala, da kuma ɗaukar nauyin zama cikakken mutum a duniya mai cike da sauye-sauye.
__________________________
*Arewabooks*
*WhatsApp Channel*
***
*WhatsApp Group*
***
*Comments Section*
***
*Facebook Page*
***
__________
***
*Domin karfafa mana qiwwa ku yi following tare da liking shafinmu na Facebook 🤙🏼*
–––––––––––––––––––––––––
Copy is not Allowed!
©2025 Fateyzahraah
–––––––––––––––––––––––––
The Writer Of:
SILAR WAYA
HOORIYAH
SUNE SILAR ƘADDARA TA
MURADINA
BAN AIKATA BA
ƘWAI A BAKA
*❖ AND NOW❖*
*TUNANIN ƘARSHE*
Young Talented Writers Ass..(YOTA/020)
Season 1, Chapter 1&2.
بسم الله الرحمن الرحيم
__Shimfiɗa__
Rayuwar gidan mu tamkar gidan haya take babu nutsuwa, bashi da bambanci da gidan ƴan dambe ne da ko wane lokaci ake iya fasa kai. Na tashi cikin gata da ƙaunar iyayena, ƙauna wadda ta zarce duk wata kyauta da zan iya tambaya daga rayuwa. Sun ɗauke ni tamkar ƙwai a kwarya, tamkar ƙaramin zinariya a akwatin ƙima. Kwatsam, ƙaddara ta fantsama garwashi a tsakiyar farin cikinmu. Duk irin soyayya da gata da nake ciki, lokaci guda komai ya dusashe. Rayuwa ta sauya fuska, duniya ta juya min baya. Na wayi gari cikin kunci da kaɗaici, babu mai kula da ni, balle har ya nuna min ƙauna a cikin halin da nake ciki.....
🌺𝑴𝒂𝒇𝒂𝒓𝒊🌺
_UNGUWAR MARIRI, KANO STATE_
8:00 AM
Safiyar Litinin safiya ce da duk wani Ma'aikaci Hankalinsa yana kan Aikinsa, haka zalika yara masu himma Su na makaranta wasu su na shirin tafiya, masu aiki sun tafi wasu kuma suna shirin kasuwa, Unguwar ta kaure da rayuwa, kowa na gabatar da tasa hanya da nufin dogaro da kai.
Amma a gidanmu, abin ba haka yake ba...
Tun daga farkon layin gidan Malam Aminu Ka ke jiyo hayaniya da ke ratsa kunne. Idan ka matso kusa, sai ka ji karar murya daban-daban na kai komo cikin gardama. Kana shiga gidan hayaniya na ƙaruwa, kamar kasuwar dabbobi ce. Babu wanda ke sauraron wani, kowa na ta faman zazzare zance cikin ɗaga murya. Cece-kuce, gurnani da takaddama sun mamaye sararin gidan, tamkar wani za a yanka. Tun a farkon shigowarka zaka iya fahimtar gidan na zaman mace huɗu ne. Yaran dake kai kawo a tsakar gidan a ƙalla zasu iya kaiwa goma koma fiye da haka, wasu sanye da uniform wasu nacin abinci wasu kuma na ɗan kai kawo, Cece-kucen da mutanen gidan suke yi cikin ɗaga murya ne, ya haifar tashin hayaniyar da ba ka iya gane abin da suke cewa.
Manyan mata ne guda biyu suke cacar baki, gefe ga yara matasa da yara kowa yana ziga Uwarsa, Ba za ka iya gane takamaiman abinda ya haddasa faɗan nasu ba kowa sai saka baki yake, wasu suna tsaye cirko-cirko Su na kallo.
Daga can gefe, Matashiyar budurwa ce da ba zata haura shekara ashirin da biyu zuwa da biyar ba. Sanye take da kayan bacci wanda da kaɗan suka haura gwiwar ta, kanta a buɗe babu ko ɗankwali tsaye take daga bakin kofar ɗaki tana kallon kowa ɗaya bayan ɗaya. Wani irin tsaki taja, wanda yaja yawancin hankulan jama'ar da ke wajen wanda yasa suka lura da fitowar ta, lokaci guda gidan yayi tsittt sai ajiyar zuciyar masu faɗa ke tashi, magana ta fara da faɗa-faɗa da muryarta mai daɗin amo da Sauraro "Wane irin iskanci ne wannan?, da sanyin safiya kuna ta yi wa mutane ihhu a cikin gida sai kace karnuka? Wai ba zaku barmu mu huta ba da safen ma?, Ka fita waje kayi hayaniya da mutane gidan ma in ka dawo ko lokacin hutawa baka da shi?" Ta faɗa tana hararar su.
Ɗaya daga cikin matan gidan da take cacar baki ce ta fara cewa "Sannu rasa kunya ɓerar tanka, har kin fito za ki fara faɗa mana magana?, Ko ce miki aka yi akwai sa'an ki a cikin mu?"
Wani kallon kin raina wa kan ki hankali ta mata sannan tace "Ina ni ina sa'a da ku?, Mutanen da baku san ciwon kanku ba, baku da aiki sai faɗa kun maida gida sai kace na ƴan gala ko gidan dambe kullum cikin hayaniya da sanyin safiya" shiru tayi can ta cigaba da cewa "kun dai ji kunya kun girma baku san kun girma ba, a gaban ƴaƴan ku wooohho" tace tana fashewa da dariya tare da juyawa ta koma cikin ɗakin, cikin wani taku tana rangwaɗa, tsittt tsakar gidan ya ƙara yi kowa yana sake-sake a zuciyarsa, can wadda ta bata amsa taja tsaki tare da cewa "Lallai yarinyar nan ta raina mu da yawa, har mu zata faɗa wa magana, a gaban ƴaƴan mu sannan ta wuce ta barmu?, Lallai wankin hula na son kaimu dare Hadiza" tace tana waiwayo wa ta kalli Hadiza sannan ta cigaba da cewa "Ya kamata mu tashi mu fara gyara ɓarakar da ke son ɓullo wa tun kafin ta girma" ta faɗa tana dafa kafaɗar wadda ta kira da Hadiza (Matar da suka gama cacar baki) jinjina kai Hadiza tayi sannan ta ce "Abinda yake min yawo a zuciya kenan Hindu tun ba'a yi nisa ba yarinyar nan mai kama da aljanu ta fara irin haka in aka yi nisa me kike tunanin zai faru?" "Ku kuma mene kuka tsaya mana akai kuna kallon mu?" Cewar Hindu tana watsawa yaran kallo mai kama da gargaɗi sum sum yaran suka fara wucewa wasu Na yinbɗakin iyayensu wasu na yin ɗakin yaran gidan wasu kuma fita ma suke daga gidan baki ɗaya gefe Hindu ta ja Hadiza suka zauna a bakin wata ƙofa da nake kyautata zaton kitchen ne tana cewa "Yanzu to mene abin yi?"...
🌼🌼🌼
Daga cikin ɗaki kuwa tana shiga ta sauke ajiyar zuciya toilet dake cikin ɗakin ta nufa babu jimawa ta fito ɗaure da towel alamun wanka tayi gaban madubi ta tsaya tayi simple make-up kana ta buɗe wardrobe dake cikin ɗakin kaya ta ɗauko ta zira riga ce iya gwaiwa sai dagon wando skin tight Wanda ya kama jikin ta sosai har shatin pant nata ana gani mayafi tayi rolling iya wuya tare da ɗaukar wata jaka wayarta ta saka a ciki ƙirar Iphone 16 plus cikin takun ta na yanga da kwarkwasa ta fito rufe ɗakin tayi tana yin hanyar fita kamar daga sama taji suna cewa
"Mtwssss a haka dai zaki ƙare, ƴar iska mai yawon banza" cewar Hadiza ko ci kanku ba tace da su ba tayi ficewar ta daga gidan.....✍️
🌘✨Shin wacece wannan budurwar mai faɗa da manyan gidan? Shin ƙarfin zuciyarta ne ko rashin tarbiyya?
🌘✨Wannan irin kallo da budurwar ke yi wa rayuwa, shin zai kai ta ga nasara ne ko halaka?
🌘✨Za ta iya tsallake wannan hayaniya ta rayuwa kuwa? Ko wannan shi ne Tunanin Ƙarshe?
*“Idan kai ne, me za ka yi da irin wannan rayuwa?”*
*“Shin wannan budurwa tana tafiya ne kan hanyar canji ko halaka?”*
*Fada mana ra’ayinki a comment, kada ki manta da share domin a bar kowa ya ji daɗi!*
*Next post yana hannunku — yadda kuka karɓi wannan zai ƙayyade yawan posting.*
💭 #TunaninƘarshe 💔🌒
*Somin taɓi ne ba'a fara komai ba😜yanayin yadda kuka karɓe shi, shi zai bani damar posting kullum😊👌. Comments,✨React🙃 & Share🙌😊 mutanen amana*
*Kamar ko yaushe ƙofar ƙorafi, gyara ko shawara a buɗe take ko da yaushe🥰🤍*
~07077791941~
*Fateyzahraah🖋️🌌*