ALWASHI

14

by @rufaidaumar

ALWASHI

14

***

***

***

***

Daren nan shi ne mafi ɗaci a wurinsu, Mama da kanta ta ɗorawa Sameera ruwa, haka ta tabbatar ta gasa mata jiki bayan ganin irin ta'asar da aka yi mata, kowannensu na sharar hawaye. Sameera kuwa tunda ta yi ɗif babu abinda take kokari ta ga ta tuna face yadda abubuwa suka wakana sai dai ba ta iya tuno komai ba illa fitowarta daga gidan Haj Salma da ma shaƙa mata abu da aka yi wanda tun daga shi ba ta ƙara sanin inda kanta yake ba sai a yanzun da ta gama dawowa daidai. Mama koda ta duba ta ga an yi wa ɗiyarta rauni amma kuma ta sani ko giyar wake ta sha ba za ta iya fitar da ita zuwa asibiti don a ɗinke ta ba saboda yin hakan tamkar tonawa kai asiri ne. Daƙyar ta lallaɓa Sameera yin wankan tsarki kafin su kai ga shigewa ɗaki sai dai babu wanda ya runtsa a cikinsu. Sameera sai sumbatu take tana basu labarin ita dai ta san cewa ta kammala kitso kuma da za ta fito ne aka shaƙa mata abu a hanci a cikin gidan ba wai a waje ba. Kuma sai a sannan ne ta ba su labarin Zaks da yan duniyan abokansa, takaici kamar ya kashe Laila. Ta dinga magana cikin muryar kuka wai Sameera don me za ta ɓoye musu, wai kwadayin abin duniya ne ya sa ta kasa bayyana musu halin da take ciki a gidan kitson saboda kada ta daina samu. Haka Laila ta rufe idanu ta dinga zazzagawa Sameera baƙaƙen maganganu kafin ta ƙara rushewa da kuka ta ce

"Shikenan, ai ga shi nan kin jawo mana baƙin fentin da ba zai taɓa kankaruwa ba. Don lalacewar rayuwarki tamkar tamu ce. Garin neman gira kin rasa ido, akan abin duniyar da bai taka kara ya..."

Tsawa Mama ta dakawa Laila tana fadin,

"Da wanne ki ke so mu ji ne?! Za ki yimin shiru ko sai na buge bakin ya yi jini?! Ke kin fi kowa sanin halayyar yar uwarki, ba za ki iya yi mata uzuri ba? Ashe ba ki san mece ce ƙaddara ba Laila? Ba za ki tausayawa halin da take ciki ba za ki ƙara mata zafi kan zafi?"

Dole Laila ta kama bakinta amma zuciyarta ƙuna take, ita ke tausayin Sameera kuwa domin ita kaɗai ji take inama a kanta abin ya faru ba Sameerar ba.

Washegari kuwa Mama ta riga su farkawa sakamakon baccin da ya kwashe su dab da asuba wanda ba su yi zaton ma za su yi ba. Tashinsu ta yi suka yi sallah, ba ta koma bacci ba tana dakon garin ya ƙarasa wayewa ta ɗunguma zuwa gidan kitson tare da Sameera don ta rantse sai ta bi ba'asin wannan cin zarafin da aka yi wa ɗiyarta. 

   Aikuwa gari na haske ta miƙe da gyara zaman hijabin da ba ta ko cire sa ba dama, Laila ta so bin su amma Mama ta dakatar da ita, ganin yadda ran Maman yake a ɓace yasa ba musu ta haƙura ta zauna.

  A hanya Sameera da Mama babu mai magana kowaccensu saƙe-saƙen zuci ya mamaye ta har suka ƙaraso ƙaton ƙyauren gidan.

Mama ta sauke wani dogon numfashi jin da ta yi Sameera ta ce nan ne gidan, jikinta gaba ɗaya sai ya yi wani mugun sanyi. Duk yadda Sameerar ke koɗa musu gidan tana yabo ba ta zaci girmansa da tsarinsa ya kai har haka a fili ba. Ji ta yi bugun zuciyarta ya karu sai ta daure ta cigaba da jan ƙaramin casbahar dake hannunta wanda take tasbihi. Maigadin ganin Sameera kuma da safiyar Allah haka yasa shi buɗe musu ƙofar bayan sun gaisa sai dai ya kula fuskar Sameerar a kumbure kamar wacce ta ci kuka.

   Kai tsaye sashin Haj Salma suka nufa. Sun iske kofar a rufe gam ga dukkan alamu basu tashi ba, nan Sameera ta kwankwasa ya kai sau biyar jifa jifa, can dai aka yi sa'a aka buɗemusu, Balaraba ta gani ɗaya daga cikin masu aikin Haj Salma. Suka gaisa da ita, da mamaki cike a fuskarta take duban Sameera,

"Sameera, lafiya kuwa?"

Sameera ta yi mata murmushin yaƙe amma ba ta ce uffan ba, ganin haka itama ta ba su hanya gami da fadin

"Ku shigo ku jira don ba su tashi daga bacci ba amma nasan suna dab da tashin."

Da toh Mama ta amsa, Sameera kuwa kai ta ɗan jinjina tana mai ɗan kai duba ga ƙaton agogon bangon falon wanda ke nuni da ƙarfe takwas da kwata na safe.

Sun ci kusan mintuna talatin kafin su tsinto muryar Mami na magana daga kicin ɗinta, can kuma ta ƙaraso falon. Ganinsu ya sanya ta ɗan haɗe fuska kaɗan. Sameera ba ta kawo komai ba tunda ta san wasu lokutan matar sam ba ta da wata fara'a ballantana kuma da ya kasance yanzun safiya ce, ƙila kawai yanayinta ne babu daɗi.

  Bayan ta zauna ta dubi Mama kafin ta maida duba ga Sameera tana ɗan yarfa hannu ba ta damu da amsa gaisuwar da suke kwararowa ba ta ce.

"Lafiya Sameera na ganki wata iri? Wani abu ya faru ne?"

Sameera kawai sai ta fashe da kuka don ba ma za ta iya cewa komai ba, ita kuwa Mama wani ajiyar zuciya ta sauke don ita kaɗai ta san ya take jin yanayin zafin ƙirjinta ta ce

"Abu kam babba ne ya faru Hajiya. Ni ɗin mahaifiya ce ga Sameera, sunana Kubra."

Mami ba ta ce uffan ba, Mama ta dubi Sameera ta ba ta iznin yi mata bayanin komai. Nan Sameera ta danne kukan, tiryan-tiryan ta korawa Mamin duk abin da ta san ya faru da ita a jiyan da za ta fito daga gidan. Mama ta ɗora da labartamata yadda wani bawan Allah ya tsinci Smaeerar ya kawomusu ita gida. Mamaki ƙarara da kuma wani kallo da ya fi kama da na raini Haj Salma ke watsa musu.

"Kina nufin a compound din gidan nan abin ya faru wai?"

Sameera ta gyaɗa kai.

"To ya aka yi kuma aka tsinceki a wajen gidan alhalin a cikin gidan abin ya faru? Yau ni Salma na ga wata sabuwa."

Sameera ta kalli Mama da ke kula da Haj Salma sosai, ta fahimci sam ba ta yarda da abin da suke faɗi ba, ta fi ɗaukar abin matsayin tatsuniyar gizo kawai don haka ta gyara zama ta soma magana wanda ya katse ƴar dariyar da Haj Salma ke ɗan yi dake nuni da kamar an raina wayonta.

"Ki yi hakuri Hajiya, an sani ba ka shaidar ɗan yau, sai dai ni Kubra zan iya bugun ƙirji na shaidi yarana a kan yin maganar da ba haka ba, tunda nake da Sameera ba ta taɓa kawo min abin da bai faru ba tace ya faru, kuma ba wannan ne gidan kitso na farko da ta fara zuwa ba, amma duk..."

"Kinga Malama don Allah yi shiru ki bar ɓata bakinki, ƴarki dai a wannan karon ta kawo maki batun da ba hakayake ba. Ta yaya za'a ce a gida babba irin wannan hakan ta faru amma babu gilmawar kowa har maigadi? Haba don Allah, ita dai ɗiyarki ita ta san inda ta je har wannan ƙaddara ta afku a kanta. Kuma ni idan da ace ba ku zo da wannan sharrin ba to ni mai rungumar Sameera ce na tausayamata har ma na baku taimakon da ya dace don a gani na an zama ɗaya, sai dai kuma dama ance ɗan adam butulu ne. To tun wuri ku tattara ku fice min daga gida, koda wasa kar ku ƙara gigin zuwar min da batun banza da wofi. Giyar wake nake sha da kuke tunanin za ku zo da wannan ruɓaɓɓen zancen na ɗauka? Toh wane ne ma a gidan nan da aka taɓa kamawa da halin akuyanci wanda zai sanya ni yarda da batunku?"

Sameera ta yi ƙasaƙe tana kallon Mami bakinta a buɗe, kamar ba ita ce da bakinta ta taɓa ji tana labarta irin munanan ɗabi'un su Zaks ba na neman mata da shaye-shaye, kamar ba ita ce ke cewa yaranta su kiyaye kar su sake su bari wani abu ya haɗa su da abokan su Zaks ba, amma duka ta mance waɗannan hirarrakin da suka yi a gabanta har ma yanzu take ikrarin babu wani mai halayyar akuyanci a gidan? Ke dai ki je ki ƙara tuhumar ɗiyarki don ba ka shaidar ɗan yau."

Mama kuwa kallon tsanaki take bin Mamin da shi, ba ta fiye son tana hada idanu da su ba asalima zufa take yi duk da sanyi mai ratsa jiki dake busowa ta ƙofar falon da yake a buɗe. Ta kai duba ga yatsunta na dama da ta ajiye a saman kujera wadanda suke rawa sai kawai ta yi murmushi ta share hawayen da ba ta san sun taho ba. Ta miƙe tsaye tana riƙo hannun Sameera da jikinta ya yi nauyi ta ma kasa tashin.

"Hajiya Salma kenan, to Alhamdulillah, kamar yadda kika ce na je na tuhumi ɗiyata, ba sai an kai ga haka ba saboda na san kalar tarbiyyar da na ba su. Kuma ki sani komai daren daɗewa ƙarya fure take ba ta ƴaƴa. Watarana ko waye ya aikata wannan mugun aikin ga Sameera, na tabbata alhakinta sai ya tarar da shi a duk inda yake rayuwa."

Jin haka ya sa Haj Salma miƙewa tana mai dakamata wata tsawa.

"Ke kar ki faɗawa mutane magana mana! Aikim banza! An ce maki mu jahilai ne? Ta yaya abu har haka zai faru a babban gida irin wannan kuma babu idon kowa a wuri? Wato kin yi zaton za ki faɗi mu yarda ko? To duk wani mugun baki zai ƙare ne a kanku ke da ita. Mu dai kam na gaba ya yi gaba! Ku fice min a falo!"

Yadda Haj Salma ke maganar da ɗaga murya ya sa su Afrah fitowa, su dai shiru suka yi, Afrah ce ma ke tambayar ko lafiya? Nan Haj Salma ta dube su ta ce su koma ba ta saka da su a lamarin ba, haka suka juya suka koma ɗakunansu. Mama a fusace kuma cikin hawayen baƙin ciki ta ja hannun Sameera dake kuka kashirɓan suka fice daga gidan gaba ɗaya.

***

Koda suka komo gida sun tarar Laila da wata Amarya wacce suka yi alƙawarin ta dawo yau za ta mata ƙunshi suna rikici, Amaryar har da su kuka wai ita don me Lailar za ta mata haka alhalin ta saka rai a yau za ta samu kuma ga shi lokaci ya kure a ranar za'a soma biki. Laila tun tana ba ta hakuri da nuna mata ba ta jin dadin jikinta har ta fusata ta ba banza ajiyarta. Shi ne Amaryar mai rawar kai har da su Allah ya isa. Ƙala Laila ba ta ce mata ba, a haka su Maman suka shigo. Nan ta nemi sanin abin da ke faruwa, Amaryar da idanunta har sun yi ja a gefe kuma ƙawarta ce wacce nata ran ke a ɓace ta dage akan ta zo su fice kar su ɓata lokaci su nemi wata mai ƙunshin amma ta ƙi tafiya. Ita ce ta yi wa Maman bayani, haƙuri ta bata. Ta lallaɓa ta suka bar gidan, Laila da tun shigowarsu hankalinta kacokam ya koma garesu cikin kaguwa na son jin meke faruwa. Suna shiga ɗaki, ta ga dai babu mai niyyar cewa uffan kowannensu cike da jimami, ta kasa hakuri ta tambaya. Mama tace abar zancen saboda kirjinta na zafi. Dole haka Laila ta bari ta bi umarnin Mama wajen dora abinci ba don dukkansu suna ji zasu iya ci ba.

***

Sai da aka shafe wata ɗaya curr sannan suka samu abin ya lafa musu a zuƙata ban da Sameera da duk wanda ya santa da fara'a zai fahimci sauyinta lokaci guda. Duk sadda aka zo kitso sai dai Laila tace su tafi Sameera ba ta jin dadi. Hatta gidan su Zakiyya sun aiko amma dayake Laila ta fi jin zafinsu akan kowa don a ganinta da ace tun farko Sameera ba ta san su ba, to da yau ba su haɗu da wannan baƙin cikin ba. Kuma yadda abin ya ɗaurewa Mama da Laila kai, har Haj Nabeela mamansu Zakiyyar ta zo duba jikin Sameera amma ba su ga alama koda wasa ta san wani abu da ya faru ba koda daga bakin ƙawarta Haj Maimuna wacce silarta ne Sameera ta san Hajiyar Barhim.

A hankali kuma sauyi sosai ya fara bayyana a jikin Sameera, farko ba ta kula da cewa wata ya ci ya cinye ba ta ga hailarta ba, sai da ta fara amai da kananun ciwo hankalin Mama ya tashi. Ta dube ta a hargitse don a lokacin su biyu ne kacal a tsakar gidan, Laila ta shiga banɗaki.

"Kinga al'adarki na watan da ya wuce?"

Mama ta tambaya cike da rawar baki, Sameera da ta ji wani rass kamar ƙirjinta zai fito. Daƙyar ta ɗago kanta ta kalli Mama da idanuwanta wadanda ƙiris ya rage ta bar gani saboda wani irin luuu da take ji a tsakar kanta. Mama ta riƙo ta sosai.

"Ban gani ba."

"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Allah kai ne gatana ni Kubra, Allah na godemaka da dukkan jarrabawarka a gare ni da yarana." Kawai sai Mama ta fashe da kuka. Laila da basu ma ji fitowarta ba, amma kunnuwanta sun zuƙo mata komai, ba ta san sadda ta ƙara sunkutar buta ba ta koma banɗakin saboda cikinta da ya kaɗa. Mama ba ta fahimci suma Sameera ta yi a jikinta ba sai da ta ɗan muskuta ta ji ta tafi gaba daya za ta faɗa kan aman da ba ta kai ga korawa ruwa ba. Butar kawai ta ɗauka ta yayyafa mata ruwan a fuska ta ci sa'a ta farfaɗo.

Ranar ita ce rana mafi baƙin ciki a tattare da su.

Washegari Mama ba tare da shawarar kowannensu ba ta shirya ta kuma tunkarar gidan Haj Salma, ta dai ce musu tana zuwa amma ba su san ina za ta ba.

Ta iske ba ta ɓangarenta wai tana ɓangaren Maigidan, Alhaji Sada.

Afrah ce ta je har can ta iske Alhajin tare da Haj Salma ta sanarmata zuwan Mahaifiyar Sameera, jin sunan yasa Alh Sada kallon Mamin cikin tamke fuska. Mami gaba daya ta ɗan ruɗe ta cewa Afrah ta je tace mata ta fice ba ta buƙatar ganinta. Har Afrah ta kama hanya ne Alh Sada ya dakatar da ita.

"Je ki yi mata iso ta zo nan mu ji da me ta zo."

Da sauri Mami ta dube shi, Afrah kuwa tuni ta fice ta yiwa Mama jagoranci har falon sannan ya bata umarnin ta tafi ta rufe ƙofar.

Mama ba ta ko tsaya ƙarewa dukiyar dake shimfiɗe a falon kallo ba ta gaida Alhajin cike da nutsuwa. Ya amsa mata shi ma kafin ya ce.

"Lafiya dai ko?"

Yin da ya yi kamar bai san komai ba ya sa Mama kallon Haj Salma wacce ke harararta. Ta ga dama ce wacce ƙila hakan zai sanya su samu adalci a zancen tunda tunanin namiji ya sha bamban da na mace. Tiryan-tiryan ta koromasa duk irin ta'asar da aka yi wanda suke da tabbacin daga gidan abin ya faru. Har zuwa batun cikin da ya tabbata Sameerar na da shi a yanzu.

Kofin dake hannun Alh Sada wanda yake kurɓar shayi sai da ya kusan faɗuwa, Mami kuwa a gigice ta miƙe tsaye ƙirjinta na wani irin bugu da karfi. Mama tana lura da su, ta ga sun shiga kiɗima kwatankwacin wanda suka shiga.

"Ƙarya kike yi! Wallahi kin yi kaɗan ki tozarta mu a garin nan!"

Cewar Mami tana nuna ta da yatsa lokaci guda hawaye na cicciko mataa kurmin idanu. Mama ta yi murmushin yaƙe.

"Tozarta ku kuma? Ashe kenan kun san komai ko kuwa yaya?"

Alh Sada nan da nan ya dubi Mami.

"Salma wuce ki ban wuri zan yi magana da ita tunda ke ba ki iya ki kama bakinki ba."

"Amma kuma..."

"Wuce nace!"

A dole saboda tsawar da ya yi mata ta sa kai ta fice zuwa ɗakinsa ta bar falon. Mama ta dube shi ta sadda kai tana jira ta ji me zai fito a bakinsa.

"Hajiya abin da nake so da ke, ko nawa kike da buƙata zan baki amma abu ɗaya nake nema."

Wannan karon da tsantsar mamaki take dubansa, ashe sun sani? Sun san komai? Raina mata hankali aka yi a farko? Ta ma kasa magana ta dai yi zugum kawai tana jiran ta ji me zai ce. Shi kuwa ya ɗora zancensa bayan ya haɗe girar sama da ta ƙasa tamkar bai san wani abu wai shi dariya ba.

"Kuskure aka samu akan ita yarinyarki. Yaron ma na hukuntashi yanzu haka ba ya ƙasar gaba ɗaya. Bana son duk wani abu da zai ɓata min sunana ko na zuri'ata, don haka ina so maganar nan a bar ta a matsayin tsautsayi ne. Sannan..."

Ya janyo wani ɗan akwati dake gefensa ya buɗe ya fiddo wasu rafar dubu-dubu har guda uku ya cillawa Mama,

"Ku je a cire cikin kuma magana ta mutu gaba ɗaya. Idan da halin barin garin ina so ku nesanta da mu. Hakan zai fi maku kyau domin na rantse maki duk wani abu da ya wuce wannan ya kuma ɓullo daga baya, to ki sani cewa don na ɓatar da ku a doron ƙasa ba ƙaramin aiki ne a wurina ba koda kuwa ba kashe ku na yi ba. Ke duk ma abin da zai faru ku yi kuka da kanku!"

Mama ta kasa magana gaba daya, hawayen ma sun ƙi fita gaba ɗaya sun bushe, kirjinta ke wani irin tafasa sai dai har ya kai aya ta kasa cewa uffan. Bai mata iznin miƙewa ba, da kanta kawai ta miƙe ba ta ko kalli kuɗaɗen da aka yi mata wurgi da su ba, har za ta fice sai ta juyo ta dube shi dakyau.

"Kana da karfin iko saboda kana taƙamar kai din mai dukiya ne. Sai dai kuma ka sani Allahn da ya azurtaka, yana sane da mu da haƙƙinmu da kuka ɗauka na wannan baƙin zaluncin. Abin da duk ku ka yi a kanmu na zalunci za ku ga sakamakonku tun a nan duniya kafin a kai ga zuwa lahira. Bamu da kuɗi da ƙarfin ikon yaƙarku a duniya, amma muna da babban makamin da ya fi kuɗi da mulki da komai, wato addu'a. Zamu kai ƙararku ga Allah."

Tana kai wa nan ta fice ba ta damu da ruwan ashariyar da ke fitowa a bakin Alh Sada ba kai kace wani tsohon ɗan tasha ne.

***

Koda ta koma gidan ba ta iya sanar da yaran komai ba, har zuwa dare.

"Ƙarshen zamanmu a garin nan na Katsina ya zo, dole mu tattara mu sauya jaha. Ita ce hanyar da zan tseratar da ku daga zagi ko aibatawar al'umma."

Furucin da ta yi musu kenan cikin daren tana mai dafa kan yaran nata biyu wadanda kowaccensu ta ɗora kanta a saman cinyar Maman suna fidda hawayen da suka fi borkono raɗaɗi.

***

KANO...

©Rufaida Umar

WOMEN OF WORDS WRITERS ASS.