FreeArewaPen original
ALWASHI
- 1views
- 25chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · 1
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.Ina godiya ga Allah ya ban damar fara littafina mai suna ALWASHI, Allah ya sa ya amfanar ya kuma nishaɗantar da al'umma. Ameen. Free novel ne. Ƙofa a buɗe take don gyara ko shawara ba da cin zarafi ba. Na gode. Sadaukarwa ga Uwa a gare ni, Marigayi Haj Sa'adatu (Mamma). Ina roƙamata addu'a daga bakunanku. Allah ya jaddada rahma gareta. Ameen.*** ALWASHI 01Na 'yar daƙiƙa kaɗan, sai da ta ji tamkar wani abu makamancin rai, ba ya tattare da gangar jikinta sakamakon daukewar da numfashinta ya yi, shiru ne ya ziyarci rumfar da take ciki tare da wasu da ta kasa tuna ko akwai wata alaƙa tsakaninsu ko babu. Walƙiya mai ƙarfi da aka yi, ta haska mata fuskar Nos din da hasken fitilar wajen bai sa ta bi ta da kallon tsaf ba sanadin ruwan da ake shararawa kamar da bakin ƙwarya. A hankali kuma ta girgiza kai ta shiga ja da baya cike da tashin hankali daidai sadda wata dattijuwa da ke gefenta tana salati ta riƙe ta tamau. Saukar ɗumin hawayen da ta ji na matar ya ba ta damar juyowa da sauri ta dube ta bayan ta farfaɗo daga suman tsayen da ta yi a farko. "A'a Mama, ban ji da kyau ba. Ki bar zubda hawayenki. Ba ta mutu ba, walla..."Da sauri Mama ta sanya hannu ta rufe mata baki. "Ki yi hakuri Laila, mu rungumi wannan ƙaddarar. Amma fa wannan ita ce gaski..""Ni ban yarda ba! Ban ji a jikina ba! Mama tare fa muka zo duniya da Samira, kin ce ba mu wuce mintuna talatin tsakaninmu ba! To ta ya ya za ta mutu amma na kasa jin cewar za ta bar duniyar a gangar jikina?""Ya isa Laila! Kar ruɗani ya sanya ki aikata saɓo mana! Ki gaggauta jan istigfari. Allah kaɗai ne masanin gaibu, kuma shi ke da ikon rayawa da kashewa. Ta rasu, a gabana Samira ta cika da kalmar shahada! Idan su ba ki yarda da su ba, ni da na yi naƙudarta ai za ki gasƙata ni ko?"Mama ta yi furucin ta na jijjiga ta. A hankali ta zame jikinta daga riƙon da ta yi mata kawai ta juya ta shiga tafiya a cikin ruwan da ke kwarara ba'a hayyaci ba. Tana jin Mama na kwala mata kira, kiran na ƙara kusanto ta, tana ƙara ƙaimi da sauri wurin ganin ta fice daga asibitin, ba iyaka asibitin kawai ba, ta rantse da Allah da ace akwai wata duniyar da za ta tafi ta manta da komai da ya faru a rayuwarsu, toh za ta yi bayan ta aikata abu guda ɗaya tilo a doron ƙasa. Fisgo ta da aka yi da karfi ya sa ta juyo ba tare da ta shiryawa hakan ba. Mama ce. Cikin tsawa ta ke girgiza ta gami da fadin."Ina za ki je?! Laila guduwa za ki yi ki bar ni bayan kin san cewa yanzu ke kaɗai ce duniyata?"Kallonta kawai take tana kyafta idanu a dole sanadin ruwan da ke sauka a...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.