ALWASHI

15

by @rufaidaumar

ALWASHI

15

Sanadiyyar dawowar Kubra da ƴan biyunta birnin Kano kenan. Suka yada zango a wata unguwa da ake kira Miltara. Gidan mai unguwa suka fara tunkara inda ta nemi alfarma wurinsa akan ita baƙuwa ce kuma mijinta ya rasu sai ko marayun yaranta, suna buƙatar a nema musu gidan haya da zasu zauna.

  Bayan dai tambayoyin da suka sha sannan mai unguwa ya gamsu, nan yace su cigaba da zama tare da iyalinsa kafin a nema musu gida.

   Sai da suka shafe sati kafin daƙyar a nemo musu wani ƙaramin gida amma kuma a can Kwanar Ungoggo. Ciki da falo ɗaya ne sai falle ɗaya sai ko ƙaramin kicin da banɗaki a tsakar gidan. Shi ma tsakar gidan ba wani fili ba ne an dai lailaye shi da sumunti, kafin ka shigo gidan kuma akwai zaure mai ɗan faɗi kaɗan sai wata ƙofar da za ta kawo ka tsakar gidan kai tsaye. Ma'ana dai ƙofofi biyu ne kafin ka tadda tsakar gidan.

   Dayake ba daɗi ne ya taso da su daga Katsina ba, sai duka rayuwar ta yi musu ƙunci da wani irin duhu. Wuri guda suke kwana. Mama da Laila ne suka fara ƙoƙarin nuna jarumta a gaban Sameera gudun kar hakan ya haddasa mata wani ciwo na daban.

Mama ke yawan yi wa Laila nasiha amma fa hatta da lalle ba ta yi ko marmarin gwadawa ba tun zuwansu unguwar.

Watarana suna zaune da yammaci, lokacin ba su fi sati da zuwa unguwar ba, aka yi sallama suka amsa. Sameera na daki ta samu bacci wanda daren jiyan kwata-kwata ba ta samu yin sa ba sakamakon kukan da ta ci sai kuma rashin ƙarfin jiki sanadin amai da ta kwana yi da har ya galabaitar da ita. Daga Mama sai Laila dake tunanin sana'ar da zasu fara yi don ba zai yiwu su zauna haka ba a cinye ɗan abinda aka tara. Laila ta kafe ita har abada ta daina ƙunshi, Mama ba ta takura mata ba don ta san ɗimuwa ce ta sanya ta wannan kafiyar amma zuwa gaba za ta cigaba da tausarta.

Daidai nan matar da suka amsawa sallama ta shigo, babbar mace mai kamala tun daga shigarta har saman fuskarta. Tana riƙe da hannun wani yaro da zai kai shekaru uku a duniya. Cikin ɗan yaƙe na rashin sanin wace ce Mama ta gyara mata wurin zama tana fadin,

"Bismillah, ƙaraso. Sannu da zuwa."

Matar ta ƙarasa ta nemi wuri ta zauna, ƙamshin turarukanta gaba ɗaya ya mamaye ƙofofin hancinsu. Laila ta gaishe ta fuskarta ba yabo ba fallasa, ta amsa tana maida duba ga Mama. Bayan an gaggaisa ta ce.

"Suna na Zubaida Rabi'u, shekaranjiya muka tare a unguwar nan ni da Maigidana Alh Abdullahi. Yarana shida, amma wannan ne ƙarami sunansa Saifullahi. Dama cewa na yi bari na shigo mu gaggaisa da makwaftana. Ina fatan zumunci zai ɗore."

Mama ta saki fuska sosai.

"Allah Sarki, sannun da zuwa, mu kanmu ai sati kenan da tariyarmu. Kinga ba mu yi kyan kan shiga ko'ina ba ma. Ni sunana Kubra, sai kuma yarana ƴan biyu. Laila da Sameera."

Laila ta dubi Mama, kamar ba ta so wannan dogon bayani ba, to idan kuma aka gane Sameera na da ciki fa? Amma kuma sai ta tuna ashe fa sun ma sauya gari, ko me zasu ce anan, in sha Allahu hakan ba zai zama tonuwar asirinsu ba. Ta sauke ajiyar zuciya itama ta ɗan saki fuska kaɗan ga Maman Saif.

Maman Saif kuwa jin Mama ta ce ƴan biyu ne ta hau fara'a da hirar ai itama ta taɓa yin ɓarin ƴan biyu, tana son ƴan biyua rayuwarta amma Allah bai ba ta rayayyu ba.

"Kuma tubarakAllah kyakyawa da su, ina ƴar uwarta?"

Mama ta murmusa.

"Bacci ta samu ta yi dayake jikin ba daɗi. Mijinta bai jima da rasuwa ba, fama take da ƙaramin ciki."

Ta ƙarashe tana jin zancen cikin na yi mata suka a zuciyarta. Laila ta dan runtse idanu, ba ta san dalilin mahaifiyarta na yin wannan batun ba domin ita dai ba ta hango wano ɗaurewar zumunta tsakaninsu da matar da ta kira kanta Zubaida ba.

"Allah Sarki, Allah ya gafarta masa. Ita kuma ya sauke ta lafiya."

Mama ta amsa da amin, ba jimawa ta yi musu sallama, Mama ta taka mata har zaure kafin ta dawo ta zauna.

"Meyasa ki ka ce haka Mama?" Tambayar da Laila ta fara yi kenan.

Ɗan murmushi ta yi.

"Zamu dauwama ne zaune a gida ba tare da unguwa sun san da zaman cikin Sameera ba? Hakan da muka faɗi a gidan mai unguwa da ma nan din, shi zai sa mu rayu cikin kwanciyar hankali ba tare da kallom zargi ko zunɗe daga makwaftanmu ba. Kar fa ki manta sana'a ce zamu fara, kuma dole a dinga zagayen shige da fice a gidan nan. Don haka tun yanzu idan muka yi wa lamarin tufka komai zai zo ya wuce."

Laila ta jinjina kai tana kauda ƙwallar da ta cicciko mata ba tare da ta bari sun kai da zuba a saman fuskarta ba. Wai yau ƙaddarar ciki ce ta afkawa ƴar uwarta ɗaya tilo, Sameera? Kaico wannan rayuwa, bawa bai isa ya tsallake ƙaddararsa ba.

***

A sannu-sannu Mama ta fara sana'ar siyar da dafaffiyar taliya ƴar murji da manja da yaji sai ko ɗanwake, a hankali aka fara saninsu. Maza haka za su yi ta aiko yara suna zuwa da kwano su siya haka matan gida ma. Laila sosai take taya ta hidima musamman ganin Sameera ta ɗan dawo da ƴar walwalarta duk da sun sani na ƙarfin hali ne don ƙarfafa gwuiwarsu.

  A ganinta zumunci ba zai ɗaure da Maman Saif ba, sai kuma a hankali ta kula matar ta ma fi yawan shigowa akan sauran makwafta ga uwa uba aiken abinci da ma wani abin kwalam ɗin zuwa ga Sameera don ba laifi suna da rufin asiri fiye da su, mijinta ƙaramin ma'aikacin gwamnati ne sannan itama tana siyar da magungunan mata wannan yasa asirinsu yake a rufe daidai gwargwado. Sosai take jin su a ranta, haka yasa Mama da Laila suka ɗan saki jiki da ita, Saif kuwa kusan shi ya zamewa Sameera abokin hira, haka zai zauna ya yi ta mata hirarsa ta ƙuruciya da yarinta musamman ranakun alhamis da juma'a. Yadda yaron ke sanya Sameera nishadi da dariya, sai ya shiga ran Mama da Laila su ma domin a duniya yanzu ba su da burin da ya wuce garin ran Sameera a sake babu ɗigon damuwa. 

  Haka suka cigaba da tafiyar da rayuwar har cikin Sameera ya shiga watanni takwas, zuwa lokacin Waec da Neco ya jima da fitowa, babu yadda Sameera ba ta yi da Laila akan ta daure ta nemi jami'a ba kamar yadda ta ke da buri amma Laila ta ce ita sam ta gama karatun matuƙar ba tare za su yi ba.

"Kar ki fasa rayuwa babu ni Laila, kar ki ce saboda ni za ki kashe rayuwarki, don Allah don Annabi (s.a.w) kar ki ƙara saka ni jin na tsani kaina da rayuwata. Ki yi kin alfarma ki cika daɗaɗɗan burinki koda a yau babu ni don ban san me gaba za ta haifar a kanmu ba."

Fadin haka suka haɗu suka yi sha kukansu, a ƙarshe Laila ta yi mata alƙawarin in sha Allahu wata shekarar za ta nemi jami'a, tare kuma zasu je. Murmushi kawai Sameera ta yi wanda Laila ba ta gano manufarsa ba a sannan.

Cikin na da wata takwas ta tashi da wani irin ciwon mara, hankalinsu ya tashi. Dole a daren Mama ta nemi taimakon Maman Saif, nan suka wuce asibiti mafi kusa a motar mijinta. Aka tabbatar musu ba haihuwa ba ne kawai juyi ne. Sai zuwa safiya suka dawo gida don dama can Maman Saif suka bar su, washegari kuwa ita da kanta ta kawo musu abin kari har gida don tana shirin zuwa asibitin Laila ta yi mata waya da sabon layin da ta sauya kan cewa an sallamo su sun dawo gida.

Kusan wannan shi ne musabbabin da ya sa Laila sakar jiki da ƴan gidan su Maman Saif. A duniya idan da abin da take so a yanzu shi ne ta ga an damu da Sameera, kuma an taya su kula da ita. Dole a wannan karon ta zubar da makaman yaƙin ƙin mutane domin ta kula Maman Saif ta bambanta da irin waɗanda take tsoron za su haifar musu da matsala wannan ne ya ƙarfafa mata gwuiwa kuma ya sa ta shiga ranta take mata kallo kamar wata Uwa don bai fi su yi sa'anni da Mama, ba wata babba ba ce sosai itama.

Cikin Sameera ya shiga wata tara cif, zuwa lokacin Mama ta siya duk abin buƙata na kayan jariri, Laila ko kallonsu ba ta son yi. Abin mamaki kuwa Sameera a wannan lokacin ta yi sanyi matuƙa ta kuma ƙara yarda da cewa wannan cikin ƙaddararta ce. Ta na ji a ranta ko me za ta haifa, da yardar Allah za ta ƙaunace shi. Ba za ta ƙi shi ba.

Ranar da za ta fara naƙuda tun yamma hadari ya soma haɗuwa garin ya yi duhu, Mama na gefe tana lazimi. Sameera da ta ƙurawa sararin samaniya ta windo idanu sai ta sauke ajiyar zuciya ta kai duba ga Laila da ke gefenta, kamar yadda take kallon waje, hakan itama Laila ke kallonta. Ɗan murmushi ta yi ta kauda fuskarta tana ƙokarin danne ciwon marar da take jinsa kaɗan-kaɗan tun safe yana ɗan murɗa mata.

"Kallon na mene ne haka Lailatu Adamu Kibiya?"

Laila ta sauke ajiyar zuciya gami da ɗna harararta. Ta san dama idan ta so tsokanarta haka take jan sunanta da na baban ta yi ta mita ita kuwa tana mata dariya.

"Kin fara ko?" Cewar Laila.

Ɗan murmushi Sameera ta yi gami da riƙo hannun Laila ta dora saman cikinta da zuwa lokacin ya rage juye juye a cikin saboda rashin wadataccen wuri kamar a watannin baya. Da sauri Laila ta dube ta zuciyarnan na zafi, za ta janye hannun Sameera ta riƙe gam. Murya a raunane kuma idanu cike da ƙwalla ta ce.

"Ki yi haƙuri Laila, na sani ko me zan haifa ba zamu sauya sunansa daga shegen da aka haifa ba ta sunnar Ma'aiki (s.a.w) ba. Amma ki saka a ranki wannan jinin Sameera ne, ƙaddararta ce kuma ƙaddararki kema. Ina sonki fiye da komai a duniyata bayan Mahaifiyarmu, bana son damuwarnan da na jefa ku ciki. Sanadina kin bar sana'arki ta ƙunshi wanda nake ɗorawa kaina laifi har gobe, nake kuma ji na tsani kaina da kaina da na zama sanadiyyar rushewar mafarkinki."

Laila tuni itama tata fuskar ta jiƙu da ruwan hawaye, Mama dake saman darduma ta ƙuramusu idanunta da suka kaɗa kawai ba tare da ta katse laziminta ba. Amma kuma duk abin da Sameera ke faɗi tana jinta.

Sameera ta ɗora da faɗin,

"Ban sani ba ko rayuwata za ta yi tsawo Laila, amma ina roƙonki koda ace ban cigaba da wanzuwa a doron ƙasa ba, ki yi haƙuri ki taya ni son abinda ke cikina, ba shi da laifi. Da ace son ransa ne, ba zai taɓa bari ya fito a shege ba. Kowa yana son a kira shi ɗa nagari wanda aka haifa ta hanyar aure. Ki yi haƙuri Laila, ki so abin da ke cikina. Don Allah kar ki kashe burikanki saboda rashina, ki janye alƙawarin da kike yawan furtawa cewa za ki rama min abin da aka min. Babu ramuwar da ta fi kamar bar wa Allah komai, ina jiyemaki tsoron abin da zai iya faruwa a sanadin ramuwar. Bana son ki haɗu da ƙaddarar da ta fi tawa, Laila sun fi mu kuɗi da komai na rayuwa, ki share su ki gina rayuwarki da ta Mama da kuma abin da zan..."

Ta ɗan dakata tana cije leɓɓanta sakamakon ciwon da ya taso mata, ga wata irin iska da ke kaɗawa har kayan shanyarsu da ke saman igiya a tsakar gida suna faɗowa. A gigice Laila ta riƙo ta, Mama ma ta zabura ta miƙe.

"Ko haihuwar ce?"

Jin muryar Mama sai Sameera ta girgiza kai tana sheshsheƙar kuka. Ta miƙawa Mama hannu, itama ta karaso ta rungumota jikinta. Ta umarci Laila da fita ta kwaso kayansu, a dole ta miƙe don gaba ɗaya ji take idan ta bar wurin koda da ƙiftawar idanu ne to fa za ta rasa Sameera na har abada don jikinta har rawa yake da irin waɗannan maganganun da Sameera ke yi.

Sameera kuwa rungume cikin Mahaifiyarta ta yi tana faɗin.

"Mamana ki yafe min, koda ban rayu ba don Allah kar ku juyawa abinda zan haifa baya. Mama ina sonku sosai."

Mama da itama tuni ta kasa riƙe hawayenta ta dafa kan Sameera.

"Da yardar Allah ba za ki mutu ba, za ki rayu kamar kowa ke da abin da ke cikinki. Sameera idan ki ka mutu wane hali za ki bar mu ni da ƴar uwarki. Laila yi maza ki saka hijabi ki nemo mana abin hawa."

Laila tuni ta yi jifa da kayan hannunta a saman ledar ɗakin ta ja hijab ta fita, ga iska na ɗaga mata hijab amma hakanan take tafiya tana share hawaye. Maman Saif ba ta gida sun je gidan biki can cikin gari a lokacin. Haka ta karasa bakin titin don ma dai Allah ya taimaka ba su da nisa sosai. Nan ta taro tasi suka dawo tare, ta shiga daidai lokacin ciwo sosai ya tasarwa Sameera, haka Mama ta sanya mata hijab ta kama hannunta gami da ba Laila umarnin taho da yar jakar da ta haɗa na haihuwa.

Suka rufe gidan bayan Laila ta zura wayarta da muƙullin gidan cikin aljihun doguwar rigarta na atamfa suka fice zuwa asibitin gwamnati mafi kusa da su.

Fitar da Sameera ba ta ƙara dawowa gidan da ƙafafunta ba kenan, sai gawarta, sai ko jaririnta Aliyu Haidar da ta tafi ta bar shi rungume a kafaɗar Laila...

WANNAN KENAN.

***

©Rufaida Umar