Barrister Hibba

Barrister Hibba

by @nusybee143

💥 BARRISTER HIBBA 💥

✍️Nusy bee

Page 8

Fitowa tayi daga ward ɗin ta nufo reception inda tayi tonon sililin ta,anan ta iske Muyassar da su Dr Khaleed,kai tsaye wajen Dr Khaleed ta ƙarasa,ko kallon Dr Hammad batayi ba,tana ɗan murmushi tace"don Allah a bata proper treatment Dr,ka haɗa Bill ka tura min ta WhatsApp idan akwai abinda ya rage,a gayawa Aliyu na gode sosai da wannan ƙoƙarin da yayiwa wannan baiwar Allah,kuma in Sha Allah bazan bashi kunya ba zan inganta rayuwar ta,Ni yanzu ina da wasu ayyuka,sai anjuma Dr"Dr Khaleed yana murmushi yace"Allah ya biya ki da aljanna Barrister,kin ceci rayuka da dama,kin kuɓutar da wasu, Allah ya kula miki da bayan ki"murmushi kawai tayi tace"see you later Dr"har tayi gaba tayo baya tana kallon Dr Hammad a fuska a bala'in ɗaure tace"gobe ina gayyatar ka zaman court don ganin hukuncin da za'a yanke wa wanda kazo kana min ihu saboda shi,bayan kaji laifin da ya aikata sai ka ɗauki matakin da yayi maka,for now dai bani da lokacin ka"ta sa kai ta wuce, Muyassar ya bi bayan ta cike da mamakin halayen ta

Har suka hau titi babu wanda yace komai as usual,sai kalle kalle take a maimakon danna waya da ta fi yi,babu zato yaji tace"samu waje kayi parking,sannan ka koma ɗayan seat ɗin"juyawa yayi yana kallon ta bayan ya tsayar da motar,bata sake sauraren shi ba ta fito ta buɗe motar,ya fito da mamaki ya koma gefe,ta shige motar ta tayar ta ja ta da gudun tsiya tana shan U-turn

Mamaki ya kama shi ganin tayi kan wani mutumi dattijo abin tausayi,gashi da gani ma mabuƙaci ne,babu tausayi ta ɗauke shi da motar ta cillar gefe cikin jini,juyawa tayi tana kallon shi bayan ta kashe motar, murmushi mai kyau a kwance kan fuskar ta, Muyassar ya kasa jurewa yace"Madam lafiya zaki bige innocent person kamar haka?don wallahi da gayya kikayi,sannan kuma sai murmushi kike,meye hakan?"ko kallon shi batayi ba ta fito daga motar, lokacin mutane sun fara taruwa

Ƴan sanda ne suka raka su,bata shiga cikin asibitin ba ta kira babban likitan wanda ya kasance matashin saurayi,don bai fi sa'an ta ba,ko ya bata shekara ɗaya,tana ganin shi tayi murmushi,shima murmushi yayi yace "ya dai Barrister?akwai magana ne?"

"Yeah akwai ƙarin bayani Dr"ta bashi kudi kimanin 200k tace "a duba shi ko ya samu wata larurar,idan da bukata sai ka kira ni,wannan kuma",ta sake bada 500k tace"ƙafar shi da ta karye,bana so ya sake taka ta,so nake a yanke ta,so nake daga rana irin ta yau,ya zamo nakasashshe"Muyassar ya kalli Hibba da sauri,zuwa yanzu ya fara tantamar anya kan Hibba ƙalau yake?likitan da ya kasance likitan ta,kuma abokin aikin ta yayi murmushi ya karɓi kuɗin yana faɗin"an gama ranki ya daɗe"bata sake magana ba ta miƙawa Muyassar makulli,ya amsa yana kallon ta,bata damu da irin kallon da yake mata bata juya ta wuce mota,shima ya bi bayan ta

Har suka ƙarasa gida Hibba gwada kiran Barrister Khadijat takeyi Amma bata shiga,ta ja tsaki yafi a ƙirga, shi dai Muyassar sai kallon ta yakeyi cike da mamakin yadda ɗabiun ta suke,yanzu wannan kalar anjuma wata kalar

Suna tsayawa a parking lot ta fito ta wuce cikin gidan ko kallon shi bata sakeyi ba tana ta cigaba da kiran Barrister Khadijat, shi kam bin ta yake da kallo ganin ko makullin motar ta ma bata amsa ba ta shige ciki

Zama tayi a parlour tayi shiru tana tunani,sunyi waya da Barrister Khadijat dab da tashin su daga Lagos,sannan ta kira ta ta sanar mata cewar ta sauka,har ma tace mata gata a taxi ta nufo railway estate,amma daga baya kuma sai ta ji ta shiru,tun daga lokacin kuma bata sake samun wayar ta ba,har Dr Khaleed ya kira ta kan case ɗin A'isha,daga nan ne ta sha'afa yanzu kuma ta dawo hayyacinta

Barrister Khadijat bata kashe wayar ta,ita kaɗai ce Tata wadda bata ɗorawa idon mikiya ba,wata ƴar dariya tayi,a fili tace"idan junan ku sammako,to Hibbatu a hanya ta kwana,mu je zuwa"daga nan ta ɗaga waya tayi kira wata number,maganar mintuna biyar tayi ta kashe wayar ta tana wani irin murmushi

Washegari tunda ta tashi sallar asuba bata koma ba,dama ba wani baccin kirki tayi ba,daren tayi sallah tayi tasbihi ta roƙi Allah nasara a wannan Shari'a mai sarƙaƙiya,ƙarfe takwas ta fito harabar gidan inda Muyassar yake jiran ta da wajen mintuna goma,sai da ya sake kallon ta don bai taɓa ganin ta da wata shiga ba sai track suit,Amma yau suit ce ta lawyers a jikin ta sai ƙatuwar rigar Lawyers a hannun ta,kanta sanye da waya baƙar hula mara nauyi,yau ko baby hijab ɗin ma Babu

Kamar koyaushe ma yau bata amsa gaisuwar da masu aikin suke mata ba ta faɗa mota, Muyassar ya ja  suka nufi court

A can ta iske Dr Khaleed, Dr Hammad da sauran collegues ɗin Dr zahraddeen,,da fara'a suka gaisa da Dr Khaleed, Dr Umar,ɗaya daga cikin ma'aikatan asibitin Khaleed sai shishshige mata yakeyi amma ko kallon banza bai samu ba,shi fa Wannan lawyer ɗin tayi masa hundred percent,Amma Sam baya gaban ta, Hibba ta ɗora da faɗin

"Dr Ni kam kayi waya da Barrister Khadijat onyeakachi kuwa?tun jiya na kasa reaching wayar ta"

"Wallahi Barrister Ni kaina rabon da na same ta tun shekaranjiya da mukayi waya da ita a wayar mijinta take cewa jiya zata zo,kuma daga baya bana samun ta"

Barrister Hibba tace"in Sha Allah ba komai, she is safe,but definitely akwai abinda yake faruwa,amma in Sha Allah ko menene ma zan yi maganin shi"daga haka ta juya ta wuce cikin harabar court ɗin, Hammad kam sai bin ta da kallo yakeyi,zuwa yanzu ta daina bashi haushi,burge shi ma takeyi

Ƙarfe tara aka fara sauraren ƙarar Rahama jaafar shuwaki da ta shigar akan matar mahaifin ta,kan zargin ta kashe mata mahaifi,ita da ƙanin ta Suraj Yusuf Dala

Hibba ta miƙe ta gabatar da kanta a matsayin lauyar Rahama,shi kuma Barrister Nuraddeen ya miƙe ya gabatar da kanshi a matsayin lauyan Fatima Yusuf Dala

An gabatar da inda zaman kotu na ƙarshe ya tsaya,cewar Hajiya Fatima Yusuf ta kira ƙanin ta Suraj a Daren da aka kashe Alhaji Ja'afar shuwaki,tabbas masu gadin gidan sun ga shigar Suraj Amma basu ga fitar shi ba,kuma an tabbatar da cewa Alhaji Ja'afar ya shigo gidan amma ƙarshe sai aka ga gawar shi a yashe a hanya,sannan kuma dama kwana biyu ana ganin Hajiya Fatima tana alamun rashin gaskiya wadanda akayi bayani a zaman da ya gabata,an gabatar da shaidu kamar su masu gadin gidan,mai aikin gidan ma tace ta san wani abu,amma unfortunately daga fita cefane ta gamu da haɗarin mota ta rasu, Rahama tace akwai hujjar daa ta riƙe zata kawo a zama na gaba,sai dai kuma abin tashin hankalin an wayi gari babu rahama babu dalilin ta,da wannan shari'ar tayi ta yin tafiyar hawainiya, Barrister Hibba da Khadijah onyeakachi da Barrister Auwal Nuhu tofa ne suke jan ragamar shari'ar,amma a yau iya Barrister Hibba kaɗai ta halacci zaman,kuma still an ce ba'a ga Barrister Khadijat onyeakachi ba,kuma wani ƙarin tashin hankalin Barrister Auwal ya kira wayar Dr Khaleed cikin tashin hankali yake sanar musu da cewa an sace masa yaran shi guda biyu a hanyar su ta dawowa daga makaranta, Aslam da inaaya. Yau dai zaman kotun sam babu daɗin ji,kowa a firgice yake,banda Barrister Hibba da take aikin ta cikin nutsuwa

Hutun rabin lokaci aka bayar,wanda ana dawowa Barrister Hibba zata gabatar da shaidun ta na ƙarshe da tace tana dasu,shi dai Muyassar yana zaune kamar an dasa shi,gaba ɗaya duniyar ma tsoro take bashi,jin irin wannan Rashin iymani akai akai,haba! shiyasa takeyiwa ƴan biyu kulle,wani lokacin kuma take abubuwa wasu iri,to dai Allah ya bata nasara

Bayan an dawo zaman kotu alƙali ya buƙaci Hibba ta kawo shaidun ta,da farko ta fara da mai gadin gidan da tambayoyi kamar haka

"Malam salahu,kace kaga sanda Suraj ya shiga,da kamar ƙarfe nawa ne?"

"Da kamar karfe tara da rabi na dare ne"

"Kace baka ga fitar shi ba ko?"

"Gaskiya ne ranki ya daɗe,tabbas malam surajo ya shiga cikin gidan amma banga lokacin da ya fita ba"

"Ya saba shiga gidan ya daɗe ne,ko ma nace ya kwana?"

"Gaskiya bai saba daɗewa ba,don duk sanda yazo baya wuce awa guda ko awa biyu"

"To kai malam salahu baka ganin ya fice lokacin kana banɗaki ko wani abu da yayi kama da haka?"

"Gaskiya babu yadda za'ayi wani ya fita ba tare da sani na ba, saboda a kowanne lokaci gidan a kulle yake,sai anyi min magana nake amfani da makulli na buɗe"

"To malam salahu mun gode"ta koma ta zauna

Alƙali ya tambayi Barrister Nuraddeen ko yana da tambaya,ya amsa da eh sannan ya miƙe yana kallon malam salahu yace

"Lokacin da Suraj ya shigo gidan kaga alamu na tsoro ko wani rashin gaskiya a tare dashi?"

Malam salahu ya girgiza kai yana faɗin"a'a"

Barrister Nuraddeen ya ƙara tambayar shi"

"To baka ganin cewa shi Suraj tunda gidan ƴar uwar shi ne zai iya samun spare key saboda zirga-zirga wani lokacin?"

Ɗan jimm malam salahu yayi sannan yace"bani da tabbas akan hakan ko akasin hakan,amma tabbas kafin ranar Ni nake buɗe masa ƙofa a duk zuwan da zaiyi"

Barrister Nuraddeen ya girgiza kai ya kalli alƙali yana faɗin"ya mai Shari'a Barrister Hibba aiyo tana son ta ɗora laifin akan Suraj ne kawai,amma dai babu wata hujja da take nuna cewa su suka kashe Alhaji Ja'afar shuwaki shi da yayar shi"

"Ba haka bane ya mai Shari'a,idan har suna da gaskiya meyasa hujjoji suke ɓacewa ɗaya bayan ɗaya? Yanzu haka ma Barrister Khadijat onyeakachi da Barrister Auwal Nuhu tofa duk basu halarci wannan shari'ar ba, saboda sun shiga matsala"

Barrister Nuraddeen yace"ya mai Shari'a Barrister aiyo tana ta kawo uzururruka marasa amfani don kawai tayi ta jan Shari'ar nan bisa son zuciyar ta,banda haka babu dama ƙaddara ta samu mutum sai a ratayawa sharia?"

Alkali ya dubi Hibba yace"ki kawo tsayayyun hujjoji da zasu gamsar da kotu,idan ba haka ba zan na kori ƙarar nan"

Hibba ta jinjina kai,duk jama'ar kotun kallon Hibba sukeyi,don dai kowa yasan iya ƙoƙari anyi don binne gaskiya,amma iya sanin mu ai ita gaskiya bata mutuwa,komai tsayin lokacin da ta ɗauka a binne sai ta fito

Hibba ce ta waiga wani ɓangaren tana faɗin"shaida ta ta gaba itace RAHAMA JA'AFAR SHUWAKI!!"

Kowa waige waige yakeyi don ganin Rahama,sai ga  wata matashiyar mace ta fito daga wata kofa sanye da dogon hijabi har ƙasa


Wacce Rahamar 🙆wadda ta ɓata?ko wadda su Alhaji adam doguwa suke batun sun kashe ta?ko dai wata rahamar dabam?amma fa rahama Ja'afar shuwaki guda ɗaya ce,itace dai ta ɓata,kuma itace wadda aka kashe,to yaya akayi yanzu ta shigo a raye?kai! wannan Barrister Hibba din ma fa ta fara zama abar tsoro,za dai muji komai a next post

#likecommentshare

#Nusy_bee