Barrister Hibba
by @nusybee143
đź’Ą BARRISTER HIBBA đź’Ą
✍️Nusy bee
Page 9
Ba kowa bace face wadda ta kai wa ziyara asibitin saint Mary's hospital a manchester, yanzun ma rungume take da babyn ta, fuskar ta wasai babu alamun damuwa, iya firgita da tashin hankali Hajiya Fatima, Suraj da Alhaji adam doguwa sun shige shi,sai kallon ta sukeyi cike da tashin hankali,ta wuce wajen da aka tanada don shaida ta tsaya,da dakewar murya ta furta
"Suna na rahama Ja'afar shuwaki!nice na shigar da ƙara akan matar mahaifi na,don ina kyautata zaton itace ta sa a kashe min mahaifi"
Hibba ta gyara tsayuwa tana kallon ta tace"Malama Rahama duk mun san da wannan,sai dai abin mamaki kwana biyu ya rage a sake zama na huɗu a kotun nan aka neme ki aka rasa,bayan kin tabbatar a zama na gaba zaki kawo hujja mai ƙarfi da zata tabbatar da cewa abinda kike zargi akan matar mahaifin ki gaskiya ne, kotu tana bukatar jin dalili"
Rahama ta ja numfashi idanun ta suka kawo ruwa,da ido Hibba tayi mata nuni na ƙwarin gwiwa, Rahama ta jinjina kai sannan ta fara bayani
"Kamar yadda na faɗa da farko,tun farkon auren su ina ganin yadda take maltreating ɗin shi idan ya hana ta kuɗi,tun anan na fara dasa ayar tambaya akanta,daga baya kuma sai ta fara masa satar maƙudan kuɗaɗen da suka wuce kima,da na gano hakan nayi mata magana,amma sai tace na fita a sabgar shi ko ta sa a kau dani,sam ban ɗauki gargaɗin ta a bakin komai ba,amma bayan nansau biyu ana farmaka ta don kashe ni, Allah yana kare Ni
Lokacin da aka kashe mahaifi na bana nan,naje garin mahaifiya ta haɗejia,amma maganar an tsinci mahaifi na a gefen hanya da asuba a mace,wai har anacewa bugun zuciya ne ya same shi a hanya ban ɗauka ba sam,tabbas mahaifi na yana da matsalar zuciya,wannan shine dalilin da yasa duk wata hanya da zata ɗaga ciwon shi ma baya bin ta,sannan mahaifi na indai ba wani dalili ba baya wuce Isha'i a waje saboda girma,amma a ce har asubar washegari matar baba na bata nemi mahaifi na ba sai da aka kawo mata shi,wannan abu ya bani tsoro,da haka nayi ta bibiyar ta, sai kuma naji tana waya da ƙanin ta tana faɗar yanzu gashi Allah yayi sun kawar da wannan tsinannen tsohon amma abin haushi kusan 75% na dukiyar shi duk sunan wannan shegiyar yarinyar ne, kasancewar a hans free ta saka wayar naji ƙanin nata na faɗin"to yaya fati aka kada Giwa ma ballantana Zomo,kawai mu kada ta"
Naji tsoro sosai,kuma na kasa yarda da kowa akan wannan case,sai naga dacewar tuntuɓar wata matashiyar lawyer da ke zuwa tana mana lecture once in a while, barrister Hibba Ibrahim Aiyo,kuma cikin hukuncin Allah ta karbi magana ta,har ma ta bani shawarar shigar da ƙara tunda akwai hujjoji akansu,ita zata tsaya min
Da haka muka shigar da ƙara,aka fara shari'a,lantana mai aikin mu ta turo min wani video ta WhatsApp inda Suraj da Hajiya Fatima suke hayaniya akan cewa tace zata bashi 50m,amma ta bashi 30m,ɓaro ɓaro naga Suraj yana faɗin"Aunty fati kinsan wahalar da na sha kafin na kashe wancan bushashshen tsohon ne? har da zaki ce wai 30m?"ita kuma Hajiya Fatima tace"kai banza ne,ba sai yarinyar ta gusa ba tukuna zaka samu dukiyar mai yawa?bashi da iyaye fa,itace za'a bawa rabi,Ni da ƙannen shi rabi"iya nan video ɗin ya tsaya,tayo min voice ta WhatsApp tana faɗin na gudu,ita ta turo min ne don na gudu,Ni kuma nayi forwarding wa Malama ta kuma lawyer ta
Abin mamaki,kwanaki biyu kafin ayi zaman Shari'a na gaba ina ɗaki na ina bacci sai farkawa nayi na ganni a wani jeji mai duhuwa, yadda akayi naje can sam ban sani ba,Suraj ne yazo ya gaggaya min magana sannan yace min tabbas su suka kashe abbana,kuma nima sai sun kashe Ni,sun gana min azaba mai yawa,a ƙarshe Suraj yayi raping ɗi na"daga haka rahama ta fashe da kuka mai tsuma rai,da yawan mahalartar kotun ma suka fashe da kuka,ciki har da Hibba
Muyassar, Hammad, Khaleed,da da yawan mazauna kotun kallon Hibba suka koma yi,ba wai kukan tausayi take ba, a'a kuka take mai bayyanar da tsantsar ciwo da baƙin ciki
Rahama ta cigaba"daga lokacin ya daina azabtar dani sosai,amma ya mayar dani kamar matar shi, lokaci lokaci har ciki ya bayyana a jiki na,yayi min dukan da sai da nayi tsammanin cikin zai fita,amma bai fita ba
Sai da ciki na ya isa haihuwa na fara naƙuda sannan suka ɗauke Ni suka jefar dani a cikin daji,na kai kusan awanni uku a wannan halin ban ma san na suma ba wai har an kaini asibiti,a sannan naji wasu mutane suna magana akai na, Allah ya bani ikon basu number ɗin Barrister ta, kasancewar na haddace ta a kaina saboda irin makamanciyar wannan matsalar,nace su kira number ɗin su ce Rahama jaafar shuwaki ce ta basu,ƴan mintuna bayan haka ban sake sanin abinda nakeyi ba, sai a kwanakin nan ko sati ba'a yi ba na farka na ganni a garin manchester a wani asibiti saint Mary's hospital,anan likitan da yake kula dani Dr Leonardo yayi min bayanin cewa Barrister Hibba ce ta kawo ni, ban taɓa tsammanin karamcin ta ya kai hakan ba,abin baƙin ciki ga jariri na haifa,kuma an bamu kulawa sosai Ni dashi, shekaranjiya ta saka aka ɗauko ni daga manchester aka dawo dani Nigeria,amma sai aka sauke Ni a Abuja,ban dawo Kano ba sai yau da safe,don ina sauka akayo nan dani,batun video kuma"ta nuna Barrister Hibba tace"nasan baza'a rasa a wajen ta ba"
Kotun ta ɗauki hayaniya,masu kuka nayi,masu tsinuwa nayi,masu jajantawa nayi,sai da alƙali ya buga guduma sannan akayi shiru, alƙali ya tambayi Barrister Nuraddeen ko yana da tambayar da zaiyiwa Rahama,jiki a sanyaye ya girgiza kai,alƙali ya kalli Hibba yace"kotu tana buƙatar ganin video ɗin da lantana ta turawa rahama"babu musu ta goge hawayen ta ta dauko laptop din ta tayi playing video ɗin ta miƙawa alƙali
Da yawan mutane suna jin me ake cewa duk da dai basa gani, Suraj ya fashe da kuka yana faɗin"zanyi magana alƙali, wallahi zanyi bayanin komai"
Wani banzan kallo Hibba ta watsa masa ta ɗauke kai,alƙali ya bashi dama,yazo ya tsaya a kusurwar shaida,cikin rawar murya ya fara magana
"Wallahi yaya ta Hajiya Fatima ce da aminin mahaifin Rahama Alhaji adam doguwa ne suka sanya Ni na kashe Alhaji Ja'afar shuwaki,ina da hujja ma"jikin shi na rawa ya ciro wayar shi ya kunna voice É—in su cikin farin ciki suna tsara yadda zasu kashe bawan Allah su gaje dukiyar da ya wahala ya tara, sannan idan ya mutu komai ya lafa,sai Alhaji adam doguwa ya auri Hajiya Fatima
Kotu ta ɗauki hayaniya sama da koyaushe,don bayyanar sunan Alhaji adam doguwa ya bawa mutane mamaki sosai,a duniya Alhaji Ja'afar bashi da amini irin Alhaji adam,tare suke harkar kasuwancin su,ya ɗauki rahama kamar su Na'ima ƴaƴan shi,har gidan take zuwa tayi kwanaki,har aka sace ta bata taɓa sanin Alhaji adam amanar mahaifin ta yake ci ba,a gigice ta miƙe daga wajen zaman ta ta kurma ihu,a guje Hibba ta ƙarasa wajen zaman nata ta riƙe tana mata magana har ta nutsu tana shashsheƙar kuka, Hibba ta zaunar da ita ta amshe yaron hannun ta ta miƙawa maman Ameera dake zaune a wajen,maman Ameera ta amsa tana kallon yaron da tausayawa
Hibba ce ta koma inda take tana kallon Suraj tace"kenan kaine ka kashe shi?"
Kanshi a ƙasa ya jinjina kai
Murmushi mai ciwo tayi tace "ikon Allah!to kenan da gaske baka fita ba bayan shigar ka gidan?"
"Alhaji adam doguwa na samu a gidan a lokacin da nazo,shi ya tsara min yadda zanyi,bayan mun gama shi ya nuna min wata kofa da ake controlling da remote ta bayan gidan,ita kanta Aunty fati bata san da ƙofar ba,don kawai ganin shi tayi ya shigo,kuma tare dashi muka fita"
"To ta yaya kuka kashe shi?"
"Rufe fuska ta nayi da mask na É—ora masa pillow akan fuskar shi na tsawon mintuna goma,ban wuce mintuna biyar da gamawa ba na fice na bar gidan"
"An ce an ga Alhaji Ja'afar shuwaki a yashe a bakin titi, kenan kawo shi wajen akayi?"
"Eh, bayan na fita, Alhaji adam ya kira yaran shi suka fitar da shi ta wannan ɓarauniyar hanyar cikin dare,bayan ya ɓatar na duk wata hujja,shine ya saka nayi kidnapping rahama,ya saka yaron shi ya kashe lantana da mota,kuma still Ina zargin shi da ɓacewar Barrister Khadijat onyeakachi,don yayi kokarin ganin bayan Barrister Hibba ko ta Ina,amma unfortunately,wayon ta da dabarun ta sun wuce shekarun ta na aiki,duk wata hanyar hakan ta toshe, shiyasa ya ɗora idanun shi akan Barrister Khadijat,don barrister Auwal yayi joining su Barrister Hibba ne don Alhaji adam ya saka shi,kuma ya fara samun yadda yake so,don shi ne ya ɓatar da video na farko da Rahama ta turawa Hibba,amma daga baya Hibba ta sake samu,ya san da cewa muddin sunan mu ya fito nashi ma sai ya fito, shiyasa ya toshe dukkan wata kafa da asirin mu zai tonu"
TabÉ—ijam! Rahama kinga rayuwa! Alhaji adam doguwa!!!ko da yake cin amana abu ne da yake common a cikin al'ummar mu, Hibba kam nima na yarda wayon ki da fikirar ki sun wuce shekarun ki na aiki, salute To You ma'am!!!!
#likecommentshare
#Nusy_bee