FOUR
💝 KULSUM 💝
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
BY
AMINA IBRAHIM
OUM AMEER
CHAPTER FOUR
Zaune yake a ƙasa ya tanƙwashe ƙafufunsa kan shi a ƙasa yayin da Hajiyarsa ta ke kan cushion. Cike da girmamawa ya gaida ta ta amsa sannan ya yi shiru yana sauraren jin dalilin kiran sa da ta ke.
Cikin ruwan sanyi ta fara mi shi magana.
“Khaldun kullum dai tatsuniyar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi. Shekara arba'in da biyu ba wasan yara ba, ka mayar da ni kakar ka game da zancen auren nan naka. Ga Sa'adu shi kansa yana so yayi auren nan amma ka ƙi ba shi dama”
Ƙara tausasa murya yayi cikin nutsuwa yace.
“Hajiya ni ban hana Sa'ad aure ba, daman wan can lokacin da yazo min da zancen cewa nayi ya dakata ya bari har ya samu ko shekara uku ne a office, kafin sannan ya ƙara sanin ciwon kansa. To amma kuma tun daga lokacin ni bai sake tuntuɓata da maganar ba”
“Oh haka kukayi da shi dama?”
Khaldun yace.
“Eh Hajiya”
Tace.
“To kuwa Sa'adu zai zo ya sameni. Batun Aure kuma sai ka fara yin aure kafin Sa'adu yayi saboda haka ina sauraren ka na baka wata ɗaya ka samo yarinya, Ko Ayusha na gaya maka tun satin can suka aiko a sanya musu rana still itama har yanzu baka ce min komai ba”
“Hajiya batun Ayusha munyi magana da Baba Mu'azu ta waya ɗazu, nace a saka nan da wata ɗaya kawai, kuma ko Meerah jiya na yi magana da ita nace kuna dawowa daga wannan tafiyar da zakuyi ta fitar da mijin aure”
Cikin tsantsar mamaki take kallon ɗan nata. Tun shekara uku da suka gabata ta so a yiwa Ayusha aure kamar me ya kawo ƙabli da ba'adi ya gaya mata wai dududu nawa Ayusha take da za'a ce a yi mata aure ta yi ƙarama a jira dai ta ƙara, kuma a lokacin tana da shekaru ashirin da ɗaya. Ballanta Ameerah da take da shekaru sha tara zai ce ta fito da miji.
“Auren na Ayusha ne nan da wata ɗaya Khaldun? Itama Ameerar ce zata fito da miji? Karatun nata fa?”
Ƙara risinawa yayi yace.
“Eh Hajiya haka nike so in sha Allah, karatu ta ida a ɗakin mijin ta, aure baya hana karatu”
Ajiyar zuciya ta sauke tace.
“Tau shi kenan ! Nasan cewa kana da dalilinka na yanke wannan hukuncin. Miyasa?”
“Tabbas Hajiya ina da babban dalili na amma na barwa zuciyata, in dai hakan yayi miki shi kenan”
Gyaɗa kanta tayi tace.
“Na san ba zaka yanke wannan hukuncin ba ba tare da dalili mai ƙarfi ba, saboda haka na amince. Allah yasa shine mafi alheri. Allah yayi muku albarka ya ƙara shiryar da ku yasa kuma ku gama da duniya lafiya”
“Ameen Ameen Hajiya, Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana mai albarka. Allah yasa a tashi lafiya. Zan fita gobe in sha Allah zanyi wata tafiya zuwa China amma ba zan wuce kwana biyar ba”
Miƙewa tayi ta nufi kitchen tana faɗin.
“Allah ya tsare ya bada sa'ar abinda aka je nema”
“Ameen”
Tashi yayi shima ya nufa ƙofar fita yana mai neman layin Sa'adu.
Yana ɗagawa Sa'ad ɗin yace.
“Good Evening Yayanmu...”
“Evening. Where are you now?”
“Ina Kaduna. And I told you Yayanmu Ko ka manta ne?”
Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace.
“I forgot. Idan ka dawo zamuyi magana”
Sa'ad yace.
“OK! thank you”
*****
Yau kwana biyar rabona da Maimu, bata nemeni ba nima kuma ban nemeta ba. Tun ranar kuma ban sake leƙa ko ƙofar gida ba. Ina nan abin duniya duk ya ishe ni, Inna tayi juyin duniyar nan tana tambaya ta mi ke damuna ganin yanda kwana biyu duk na shige gashi,na ce mata ba komai ba na jin daɗi ne.
Wallahi Allah yaga zuciyata ta kamu da matuƙar son Khaldun,domin duk irin mazan da nike haɗuwa da su kala-kala ban taɓa ganin wanda ya yanke ni ba kamar sa. Amma na riga da nasan na bar baya da ƙura domin Khaldun yayi min nisan da ba zan taɓa cimmasa ba. A haka Maimu take nema ta ƙara tunkuɗani ƙarshen rami ta kai ni can ta baro.
Ƙarfe biyar na yamma na fito shirye cikin wani tsadadden lace da Maimu ta sa na cinnawa Inna wuta sai da ta sayamin shi domin ita ma saurayinta ya saya mata irin shi zamu saka a wurin kamun ƙawarmu Hindu da za tayi aure. Dubu arba'in da bakwai haka Inna ta bani su cas. Yah Naziru sai mita yake kamar zai dukeni kullum cewa yake tafi sona fiye da su, duk kuɗinta yanzu gareni suke ƙarewa.
Ita kuma ganin na zauna ina rusa kuka yasa ta ɗauko asusunta ta buge ta ƙirge su ta bani sannan kuma ta bani dubu biyar na ɗinki.
Jakata na saƙale a hammata ta wayata kuma na riƙe a hannuna na fito. Gun murhu na taradda Inna da Khadija suna girki Innani kuma na gefe tana gyara alaiyahunda za'a saka a miya. Muryar tausayi na yi domin in samu dama gun Inna nace.
“Innata na fito”
Kallona Inna tayi daga sama har ƙasa tace.
“Ina zaki je haka”
Nima kallon kaina na sake yi amma ban hango wani aibu ba, domin Abuja bubu ce aka yimin yayi masifar kyau sannan kuma ya amsheni ba kaɗan ba, ni kaina na san cewa ba ƙaramin kyau nayi ba.
Murmushi nayi tare da marairaicewa nace.
“Haba Inna! Kin san fa da bikin Hindu har gidan nan tazo satin can ta kawo katin gayyata, yau ake kamu gobe Juma'a walima sai yinin biki Inna..”
Wata uwar harara Innani ta makamin tana faɗin.
“Shegiyar yarinya mai mugun kwaɗayin abin duniya, duk wanda yazo mutumin kirki tace bata so, ta fi so kullum tana gararambar yawon biki, to mu dai duk wani abun sharri ya faru dake wallahi Allah ya isa bamu yafe miki ba, tunda Allah ya gani mu dai munyi iya yinmu,ah to ko dai bawan Allah nan Naziru kuma bisa ga gayamiki gaskiya yake, shi kuma sulmanu idan ya sa ƙafa ya fice baya dawowa sai goma na dare to ina zai san sharrin da kike ƙullawa..”
Wani irin haushin Innani ne naji ya turnuƙeni tuni na hau banbami ina faɗin.
“Ni dai Innani kin dai ga duk kwanakin nan babu ruwana da ke ko?ki fita a harka ta kamar yadda na fita harkarki to yayi...”
Harara Inna ta makamin tana faɗin.
“Yi mata rashin kunya tunda yanzu gani kike ke kin girma...”
Ƙara marairaicewa nayi kamar zanyi kuka nace.
“Inna dan Allah mana..., kiyi haƙuri kinji, Allah ba zan wuce bakwai ba”
Gyaɗa kanta tayi tace.
“Kada ki wuce Magriba Kulsum dan Allah, Allah ya tsare”
Murmushi nayi nace.
“Na gode Inna, in sha Allah ba zan wuce ba...”
Kallon Innani nayi ina dariya na nufi ƙofa nace.
“ƙawata na fita sai na dawo”
Hararata tayi tace.
“'ƴar iska munafuka, kin yi da ubanki Shu' aibu mai saida gwanjo....”
Sai kuma ta juya ta kalli Khadija tare da miƙa mata ƙaramar wayar ta ƙirar Itel tace.
“Ungo Hadiza kamomin Lombar Shegen yaron nan da na ba kuɗi na ya siyomin akuya 'ƴar ƙasa yau kusan sati biyu babu Akuya babu labari, matsalar baƙauye kenan”
Dariya Khadija tayi tace.
“Ke Innani ke fa kika je har gidan su kika kai masa kuɗin nan kika roƙeshi....”
“Ke rabani er iska, ai duk ƙila ma bakin ku ɗaya”
Kamo mata Khadija tayi ta miƙa mata ta tashi tana faɗin zata je tayi sallah.
******
Wajen mai make-up ɗinmu na cimma Maimu saboda ina fitowa na kira ta tace tana can.
Kallo na tayi da murmushi tace.
“Kulsum is that you? Ko muna faɗa ne? Kin bari shaiɗan yayi tasiri a zuciyar ki game dani”
Girgiza kaina nayi nace.
“A'a, kawai dai na ɗan ba kaina hutu ne”
Sake kallona tayi tace.
“Wow! Kinga kyawunda kikayi kuwa Kulsum, wallahi da na ganki sai na ji duk na raina kaina a lace ɗin nan”
Nidai ban sake ce mata ci kanki ba haka ma mai make-up ɗin har ta gama mata. Na riga na gama fahimtarta ta a wannan fannin duk abinda mukayi sai ta yi ta mita tana faɗin nawa yafi nata tun ina damuwa har na zo na gane kalar rayuwar ta kenan.
Ana gama mata tace ayimin nace a'a na gode 'ƴar light make-up ɗinda nayi ta ishe ni.
Wani saurayinta ta kira yazo ya ɗaukemu zuwa Damɓa don can ne ake bikin. A motar ta ke tambaya ta wai ya maganar da mukayi. Nace mata ta bari zamuyi magana.
Muna zuwa muka haɗe da sauran ƙawayenmu su Kubra. Duk yanda suke son hulɗa dani Maimu bata so sai ta ce ai ajinmu ba ɗaya ba kuma kafin ma in santa su na fara sani, don bana manta haɗuwarmu ta farko da Maimu shekara uku da suka wuce wurin bikin wata ƙawata muka haɗu. Duk zatonta daga gidan wasu hamshaƙan masu kudi nike sai daga baya ta gane ai ni ɗin er gidan Malam shehu ce suma ɗin dai haka suke kamar mu amma ita gidan su mamanta su huɗu suke su kuma 'ya' yan gidan sun kai su talatin. Tunda muka haɗu ta shige jikina ta hana ko wace ƙawa ta raɓeni biki in ya kai bangon duniya sai munje anko ma ba'a magana domin komai tsadar sa sai mun saya. Ko kuma kawai mu sayi sababbin kaya na kece raini muyi ta ɗinkawa muna fafa. Ita daga secondary bata ƙara gaba ba ni kuma tunda na gama Yah Naziru ya cewa babanmu a nemamin FCET na dinga kuka wiwiwi na kafe nace bana sonta sai University, Kuma sai nayi Jamb har sau biyu ban ci ba shi ne Yaya Naziru yace a nemamin in fara diploma a A.B.U Zaria saboda can yake degree ɗinsa wanda a yanzu yake final year.
Gefe ta jani tana faɗin.
“Kulsum wai mi kika yanke, da zafi zafi fa akan bugi Ƙarfe”
Girgiza kaina nayi nace.
“Gaskiya A'a ni dai Maimu. Na gama hangawa ba zan iya ba. Ko fa hannuna bai riƙa ba taya zan mishi wannan sharrin...”
Cikin fushi tace.
“Relax baby! Bakya fahimtar zance ne wai? Wurin Mahaifiyarsa zamu. Daga nan magana ta ƙare sai zancen auren ku kuma. Haba dan Allah! Ko nice Nike son mutumin nan iyakar abinda zanyi kenan”
Ajiyar zuciya na sauke nace.
“To shi kenan, mu bari gobe....”
Cike da farin ciki tace.
“Allah ya kai mu. Daga gobe zan fara ƙirgen date ɗin bikin ƙawata”
Daga nan muka wuce muka shiga harakar bikin da ya kawo mu.
OUM AMEER