FIVE
đź’ť KULSUM đź’ť
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
BY
AMINA IBRAHIM
OUM AMEER
WATTPAD@UMMU-AMEER
CHAPTER FIVE
Duk irin jan kunnen da Inna tayi min na cewa kada in wuce magrib bai shigeni ba. Domin ganin yanda wurin kamu ya ɗau haske sai abubuwan burgewa ake ban san ma cewa har takwas ta buge da minti goma sha bakwai ba. Innalilahi! kawai na shiga furtawa bayan dukkan ilahirin jikina ya ɗauki ɓari. Da gudu na je na raɗawa Amarya Hindu cewa na tafi gida dare yayi sai idan na shigo gobe.
Hannu Maimu na janyo wadda ta baje a filin DJ sai É—irkar rawa take.
Kallona tayi bayan mun fito wajen Hall É—in tace.
“Ya dai?”
Screen É—in wayata na nuna mata alamun ta duba time ina zaro ido waje nace.
“Maimu ki duba time,pass 8pm ni da Inna tace kada in wuce magrib”
Tsaki taja tace.
“To ki bari mana a ɗan ida sunce 9pm za su tashi ai....”
Da sauri na girgiza kai na nace.
“No Maimu, gaskiya ba zan iya kai tara ba. Ki duba fa nisa daga damɓa zuwa Filin jirgi gaskiya mu tafi kawai”
Numfashi ta sauke tace.
“OK! Let me call Sudais..”
A gabana ta kira shi yace yana hanya. Ganin har an kwashe kusan minti ashirin bai zo ba yasa Maimu ta kalleni tace.
“lemme say a good bye to Hindu”
Da to kawai na amsa mata. Ina nan babu abinda yake raina sai Inna da Baba. Ganin wasu mintuna biyar sun ƙara shuɗewa Maimu bata ma fito daga Hall ɗinba ballanta in yi tunanin Sudais ɗin ya zo yasa na fita kaina tsaye. Har na kai titi ko mai Keke banga ya gifta ba hakan ya ƙara ɗaga min hankali. A titin ma motoci ne kawai ke gudu duk ɗan mashin ɗinda zaka gani akwai mutum ko keke napep. Kuma ga lokaci sai ƙara tafiya yake. Hakan yasa na yanke shawarar taron lipt ba tare da tunanin mi zai biyo baya ba.
Mota kusan uku na tare ba wadda ta tsaya sai a na huÉ—u ko ita sai da mammallakinta yayi kamar ba zai tsaya ba sai kuma gashi yayi reverse ya dawo baya.
Yana zuge glass É—in motar na kutsa kaina cikin pleading tone nace.
“Lipt to Lalan please”
Muryar da ta daki massarafar jina ta sakani dasƙarewa, tamkar wutar lantarki ta jani haka naji wani zuu! Tun daga babban yatsan ƙafata har zuwa cikin massarafar tunanina. Domin murya ce wadda har na koma ga mahallici na ba zan taɓa mantawa da ita ba.
“Ke! What are you doing here by this time?”
Jikina na ƙyarma na wara ido na kalli gefen mai zaman banza. Sai yanzu na lura da shi. Muryarta na rawa kamar wadda aka turke wurin gulma nace.
“Daga wurin bikin ƙawata nike”
Cike da mamaki ya maimaita kalmar.
“ƙawa”
Tuni hawaye sun ciko idona ban san locinda na gyaÉ—a mishi kaina ba nace.
“Eh”
Bayan ya kalleni na 'yan daƙiƙu sai kuma ya kauda kai tare da yin tsaki ya kalli abokin shi yace.
“Jodan Mu tafi kawai”
Cikin tausayawa Jodan É—in ya kalle shi yace.
“But Zurmi...”
Girgiza kai yayi yace.
“No... Leave her. Mu tafi kawai”
Tun locinda muka haɗa ido sau ɗaya na soke kaina ƙasa ban sake gigin kallon sa ba, kuma nayi da na sanin wannan daren da nayi yau. Ban ankara ba naji an rufe ƙofar motar sun wuce.
Kuka na fashe da shi a raina ina tambayar kai na wannan wace irin makauniyar ƙaddara ce. Wai shi nan mutumin fa kallon 'ƴar iska yake min.
Ina cikin rera kukan rashin dalili naji horn lokaci É—aya ya karaÉ—emin dodon kunnena. Da sauri na waigo ina kallon wanene wannan.
“Shigo”
Abinda naji wanda aka kira da Jodan ya furta kenan.
Ban tsaya wani tunani ba na faɗa bayan motar tare da laɓewa bayan kujera ina mai sunne kai na ƙasa. Inna ce kawai a cikin rai na.
Bayan tafiya ta ɗan lokaci naji an tsaya hakan yasa na ɗago kaina, lokaci ɗaya idanuwanmu suka sarƙafe cikin na juna ta madubin motar.
Saurin É—auke kan shi yayi tare da faÉ—in.
“Malama sauka kije hotel ɗin da zaki je...”
Saurin katse shi nayi da faÉ—in.
“Ni gidanmu zan tafi”
“Ki nuna min gida a wannan round-about ɗin ta lalan. Malama sauka nace..”
Kamar wata gurguwa haka na mirgina na sauka daga motar ko arzikin rufe ƙofa basu samu ba.
Maganarsa ba ƙaramin ƙona mini rai tayi ba, amma na rantse da wanda rai na yake hannun sa sai yayi nadamar wannan kalmar da ya gayamin.
Ko a nan É—in sai da nayi tafiyar kusan minti goma sannan na samu mashin zuwa gida.
********
Har suka isa gida babu wanda ya yiwa wani magana.
Ganin Khaldun É—in na shirin sauka Jodan ya kalle shi yace.
“That girl...”
Wani irin kallo Khaldun É—in ya watsa masa yana faÉ—in.
“which girl are you talking about?”
Kai tsaye Jodan yace.
“The one that we drop at Lalan...”
Katse yayi da faÉ—in.
“Billah I know nothing about her. Kawai dai kasan yaran zamanin nan basu da kunya yanzu daga neman Lipt ɗin nan zata iya maƙale maka”
GyaÉ—a kai Jodan yayi alamun gamsuwa yace.
“OK! Allah ya huta gajiya. Sai mun haɗu”
“Amin. Thank you Jodan”
********
Jikina na rawa na tura ƙofar gidan tare da yin sallama a hankali... Sai dai sallamar maƙalewa tayi sanadiyyar wani wawan marin da Yah Naziru ya sauke min tare da faɗin.
“Daga gidan ubanwa kike?”
Wani irin ihu na ɓarka tare da dafe kuncena saboda ba ƙaramin ratsani marin yayi ba ina faɗin.
“Wayyo Allah Inna ta...”
Sake kai min duka yayi yana faÉ—in.
“Ke dai Allah ya shirya ki, baki jin maganar iyayenki ko makarantar ma ba za'a kai ki ba don ubanki. Daga yau na hana miki fita a cikin gidan nan kuma ko bana nan aka ce kin fita ko nan da ƙofar gida na dawo wallahi sai jikin ki ya gaya miki”
Baba da shigowar shi kenan ya kalle ni yace.
“Ummu-Kulsum abin kika zaɓawa rayuwar ki kenan ko?”
Cikin kuka nace.
“A'a Baba wallahi mashin ne ban samu ba, Dan Allah Baba kace yayi haƙuri”
Wucewar shi yayi ni kuma na ruga da gudu na shine ɗakin Innani tare da haye gadon ta mai rumfa na naɗe can ƙarshen gado ina ci gaba da rusa kuka.
Ɗakin ya shigo yana faɗin ina nike, sai dai Inna da tuni ta miƙe tana faɗin.
“Kai dai Naziru anyi mugu azzalumi, duk dukan da ka yi mata bai isheka ba sai biyo ta nan, hala jikin ƙirgi gareta...”
Ci ke da jin haushin maganar ta Yah Naziru yace.
“Ina shigowa gidan nan ko jakata ban ajiye ba kika shiga rattaba min abinda yarinyar nan take kuma shine yanzu zaki zo kina gayamin zancen banza”
“Lah! Naziru yanzu nice mai zancen banza? To ƙanen ubanka Ayuba mai kanta ka faɗawa haka....”
Tsaki Yah Naziru ya ja tare da ficewa kawai daga É—akin.
Juyowa tayi inda take jin sheshshekar kukana tace.
“Ke dai anyi shaiɗaniyar yarinya wallahi. Yarinya kamar mai bakin uwa. Allah ne shaida nice shaidar Habiba da zaki fita gidan nan amma saida kika ɓata mata rai, wallahi ki gujewa duniya tun kafin duniya tayi miki juyin masa..”
Ni dai ƙyaleta nayi ban tanka mata ba kada ta kira shi yazo yaci ubana.
Ina nan sai da shaÉ—aya na dare ta buga sannan na fito nayi alwala na wuce É—akin mu ina famar zare ido kada Yah Naziru ya rufceni.
Sai wuraren sha biyu na dare na gama duk abinda zanyi nayi shirin kwanciya wanda a lokacin Khadija ta jima da yin bacci.
Sai da na kwanta kan katifata abinda Khaldun yayi min ya shiga dawomin. Hawaye naji sun zubomin domin dana tuna kalmar nan sai naji tayi min É—aci a zuciya. Da wannan na kwanta ina Allah Allah gari ya waye ya ga mi zai biyo baya.
******
Yana shiga gida bayan ya gama duk abinda yake ya yi shirin kwanciya bacci. Ya É—auko wayar shi ya kira Meerah ringing É—aya ta É—auka.
“Yayanmu barka da warhaka”
Murmushi yayi yace.
“Yawwa Meerah. How are you?”
Meerah tace.
“Fine and Alhamdulillah”
“Good! Ina fata baki manta da maganar da mukayi ba Meerah?”
Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace.
“Yayanmu ban manta amma kasan cewa i have nobody now, bcoz ka hana ni sauraren kowa kace ba yanzu ba”
Girgiza kai yayi yace.
“But now I parmit you ai. Give them chance Sai ki zaɓi wanda ya kwanta miki”
Murmushi tayi tace.
“OK Yayanmu in sha Allah I will. Na gode”
“Yawwa good girl. To sai da safe”
OUM AMEER