SIX
💝 KULSUM 💝
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
BY
AMINA IBRAHIM
OUM AMEER
CHAPTER SIX
Wata irin muguwar zabura nayi na miƙe zaune tamkar wadda tayi mummunan mafarki sanadiyyar wani mugun duka da naji an ɗanamin a cinya.
Ɗaga kaina nayi inga wane maga'isan ne wannan. Saurin miƙewa nayi Ina zare ido ganin Inna ce.
Harara ta maka min tace.
“Wuce kije ki hura wuta ki ɗora min tukunyar kunu kuma ki zazafa tuwon nan sannan ki mayar da ruwan wanka. Idan kin gama ki wuce duk niƙar da aka kawo da safen nan ke zaki yi ta, muntuniyar banza”
Tana ficewa na ɗauko wayata na duba agogo. Ƙarfe shidda da minti ashirin. Ko ƙwaƙwƙwaran minti talatin banyi da kwanciya ba bayan na kambala sallar asuba. Hawaye naji sun silalomin akan kumatuna domin yau nasan wahala ce zata mayemin. Muddin Inna tayimin irin wannan to tabbas ranar sai na ɗanɗana kuɗata domin duk wunin ranar duk aikin da yake gidan ni zan yi shi ko mutuwa zanyi Inna ba zata ɗagamin ƙafa ba.
Sai da na gama shan kukana sannan na ɗaura zanina akan kayan baccina na fita waje. Still ina hawaye Ina haɗa wutar gawayin. Ina tsugune na hango duhun Yah Naziru ya shigo gidan, domin gari ba gama haske ba, da alama daga masallaci yake.
Sharen hawayen Ido na nayi ganin ya nufo in nake. Kafe shi nayi da ido duk da bana ganin shi ƙirjina kuma sai duka yake ina ta addu'a a raina kada ya dukeni. Jiki na mazari nace.
“Yah Naziru Good morning...”
Shiru yayi bai amsa ba. Nima ɗin sai na yi shiru na kasa motsawa.
Zaunawa yayi kan kujerar tsakar gida a hankali ya furta sunana tamkar yau ya fara sanina.
“Ummu-kulsum...”
Nima jiki a sanyaye nace.
“Na'am Yah Naziru”
“Kulsum duniya wanda bai zo ba ma jiran shi take ballantana wanda yake cikinta. A lokacinda kika goga bariki kika tsufa aka daina yayin ki ko kika mutu a lokacin sabbin 'ƴan bariki za su fara tashe. Wallahi ki kiyayi kanki ki kiyayi ƙawayen banza. Don ina sonki ne nike faɗa miki gaskiya kada a kai ranar danasani wanda ba zai amfane ki a wannan lokacin. Na bincika FCET sai nan da wata biyu za su fara admission can zan nema miki, kina zuwa kina dawowa gida. Don na gama nazari idan aka kai Zaria it would be worst domin babu wanda zai riƙa tsawatar ki. Kuma mungama magana da kowa a gidan nan kada ma Kice zaki fara wata hauka wallahi mganinki zanyi”
Daga haka ya miƙe ya wuce bai jira na amsa masa ba. Wasu sabbin hawayen naji sun zubomin ga wani irin tuƙuƙi da zuciyata ta ɗauka tamkar an ɗora ta akan tuƙubar tsire. Ina ganin ya shige ɗakin shi na fashe da wani irin kuka a raina ina faɗin wallahi ko za'a mutu ba zan je FCET ba, Sai dai idan ta tafasa ta ƙone. Wani irin sabon tsanar Yah Naziru ce naji ta dirar min a zuciyata domin duk wata hanyarda zanyi farin ciki sai ya nemi ya toshe ta.
*******
Shirye yake cikin shadda Sky blue ga tarkacensa a hannun sa. Agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannun sa ya duba yaga har takwas ta gota da mintuna talatin. Ɗan ƙara hanzartawa yayi domin he's late, yasan yanzu akwai mutane da yawa suna can suna jiran sa a office.
Kusan cin karo suka kusa yi da Sa'ad wanda yake ƙoƙarin buɗe ƙofar ɗakin nasa. Kallon Sa'ad ɗin yayi yace.
“Tun ranar da na nemeka sai yanzu ka dawo?”
Da sauri ya soke kansa ƙasa yana murmushi yace.
“Yayanmu I'm sorry. Wallahi nasan na yi maka laifi shiyasa na kasa zuwa in da kake...”
Gyaɗa kansa yayi yace.
“Ok yanzu kuma da ka zo laifin ya wuce kenan?”
Da sauri ya girgiza kansa yace.
“A'a Yayanmu Ina ko laifin ya wuce. Kafin dai in faɗi wata magana ina mai baka haƙuri...”
Kaɗa kai kawai Khaldun yayi ya nufi hanyar waje yace.
“OK...”
Bin bayan sa Sa'ad ɗin yayi ganin ya shige mota shima ya faɗa motar yana faɗin.
“Kayi haƙuri Yayanmu wallahi dalilin da yasa naje gun Hajiya Ina tsoro kada in sake yi maka magana a karo na biyu kace a'a shiyasa na je gunta nasan dole zata nemeka”
Numfashi ya sauke sannan yace.
“ To naji, yanzu a ina yarinyar take? su wanene iyayenta?”
Cike da farin ciki Sa'ad yace.
“Tudun wada suke Yayanmu, Babanta kuma lecturer ne a nan ZaCas”
Gyaɗa kansa yayi alamar gamsuwa yace.
“OK, zamu yi magana da Baba Mu'azu sai muje in sha Allah”
“Yayanmu Na gode Na gode, ubangiji ya ƙara girma da ɗaukaka ya ƙara rufa asiri”
Har ya juya zai buɗe motar ya kira sunan sa yace.
“Sa'adu..”
Waigowa yayi yace.
“Na'am yayanmu”
Kallon sa yayi cikin ido yace.
“Sa'ad kadai yarda da mutuncin ta da kuma tarbiyyarta?”
Gyaɗa kansa yayi yace.
“Sosai Yayanmu, in sha Allah ina da confidence akanta kashi saba'in cikin ɗari”
Yace.
“OK, I'm glad to hear that. Allah ya Sanya alheri”
Sa'ad yace.
“Amin Yayanmu....”
Cikin tsoro tsoro ya sake cewa.
“To amma Yayanmu what about you?”
Kallon sa yayi na ɗan lokaci sannan cikin mamaki yace.
“What about me as how?”
A daburce yace.
“Eh to... Ina nufin kaifa batun auren...”
Kallon sa yayi kamar mai nazarin wani abu sannan ya ce.
“Get out of my car..”
“But Yayanmu....”
“I said get out..”
Daga haka ya sauka daga motar yana mai faɗin Allah ya baka haƙuri.
*******
Ƙarfe uku na rana na sulale na fito daga gida bayan uban wunin da na kwashe ina gabzar aiki tamkar anyi hayata. Duk wani aiki da ke gidan yinin yau ni nayi shi Khadija ko kauda kare bata yi ba. Innani sai zagina take tana yaɓamin maganganu. Ni kuma tuna abinda na ɗaukarwa rai na akan Khaldun yasa sai da nayi duk yanda zanyi na fito daga gidan. Tuwon dare na kan wuta na bar shi na fito abina. Nafi son idan na koma in yanka ni Yah Naziru zai yi ya yanka ni.
Layin Maimu na shiga nema ba ƙaƙƙautawa tazo ta kai ni dai gidan su Khaldun wurin mahaifiyarsa........
OUM AMEER