Page 3&4
*🌹TUNANIN ƘARSHE 🌹*
A taste of the final thoughts before the storm begins…
Fateyzahraah
__________________________
*Arewabooks*
I just published "Page 1&2" of my story "TUNANIN ƘARSHE" :: https://www.arewabooks.com/chapter?id=685712185aac0a5a758c596e. Check it out!
*WhatsApp Channel*
***
***
*WhatsApp Group*
***
*Comments Section*
***
*Facebook Page*
***
__________
***
*Domin karfafa mana qiwwa ku yi following tare da liking shafinmu na Facebook 🤙🏼*
–––––––––––––––––––––––––
Copy is not Allowed!
©2025 Fateyzahraah
–––––––––––––––––––––––––
The Writer Of:
SILAR WAYA
HOORIYAH
SUNE SILAR ƘADDARA TA
MURADINA
BAN AIKATA BA
ƘWAI A BAKA
*❖ AND NOW❖*
*TUNANIN KARSHE*
Young Talented Writers Ass..(YOTA/020)
Season 1, Chapter 3&4.
بسم الله الرحمن الرحيم
_____________
A ƙofar gidan ta tsaya ba ta da takamaiman inda za ta nufa, amma zuciyarta cike take da ƙunci da jin haushin rayuwarta. Sai iska ta dinga kaɗawa a kumatunta yayin da ta ke takawa cikin layin, tana tafiya da kakkausar murya tana rerawa kanta waƙa mai ɗan nau’in baƙin ciki.
Wurin da zuciyarta ta ja ta zuwa shi ne gidan ƙawarta Safwah, wadda ke zaune a unguwar Gama. Safwah ce ta fi kusa da ita a cikin duniya. Ita ce ƙawar ta kwalli ɗaya jal da ba ta da kamar ta sun san sirrin juna fiye da ko wane mutum, yau ba ta cikin yanayi mai kyau. Koda yake ta saba zuwa gidan a haka. Ranta cike yake da rashin jin daɗi, zuciyarta tana shan wahala a cikin kwanakinnan.
Ta ci gaba da takawa a hankali, tana jin cewa akwai buƙatar ta sake zuba wani fata a cikin zuciyarta, A haka ta ƙarasa bakin titi ta hau napep.
A ƙofar gidan ta tsaya, tana latsa wayarta tare da kara ta a kunne tare da cewa "Gani a waje, zoki buɗe min" tace tana katse kiran. Ba a jima ba, ƙofar ta buɗu, sanye da doguwar riga fara wadda bata kai ƙasa ba, kyakkyawa ce fara tass fuskar ta cike da mamaki da tambaya ta ce "Ke lafiya? Na ji shiru sai kace wata ‘yar gudun hijira" tana kama hannunta.
murmushi tayi irin wanda yake ɓoye kuka, sannan tace
"Meye zaki ce in gidan ya zama karen dare? Ina jin kamar na ƙone masa ƙofa na fita."
Safwah ce ta kalleta cike da tausayi tana riƙe da hannunta suka shiga ɗaki. Zubewa tayi a gado, hannayenta a goshi. Ba ta buƙatar ciyarwa ko tambaya a wannan lokaci, zuciyarta tana buƙatar fitar da jiki daga matsi da ƙuncin gidan da ba ta jin daɗin zama a ciki, ba tare da ta farga ba hawaye suka zubo a kan kuncin ta. Da sauri Safwah ta sa hannu ta share mata su tana cewa "*Manee*" sunan da take kiranta da shi, "kiyi haƙuri ki daina kukan nan, babu abinda zai ƙara miki sai baƙin ciki" kallon ta tayi idanun ta cike da kwalla ta ce "Safwah mutanen nan sun tsane ni, zuciyata zafi take min kamar ta fashe" tace tana tashi zaune, bata ce mata komai ba ta fita Safwah babu jimawa ta dawo hannun ta riƙe da cup miƙa mata tayi, a hankali ta saka hannu ta karɓa tare da sha tana miƙa mata cup ɗin ajiyar zuciya ta fara sauke wa ajere. "*Manee*" Safwah ta kira ta "Hakuri zaki yi da Rayuwar nan, ki fitar da komai a ranki" shiru tayi sai ta cigaba da cewa "Ki more kuruciyarki, ki amincewa Fa'oz zaki ji daɗi ki manta da damuwar gidanku, kalleni misali ce a gare ki ba wanda ya isa ya nuna min yatsa kaf ƴan uwana, shiyasa na zaɓi zama ba tare da su ba" ta ƙara sa faɗa tana sakin wata siririyar dariya
"Mtwssss, Safwah ni kwata-kwata Fa'oz bai min ba ya fiya takura ga gadarar tsiya sai kace wani basarake" ta faɗa tana ɓata fuska buɗe baki Safwah tayi zata yi magana Manee tayi saurin katsewa da cewa
"Kinga ni kawo min abinci yunwa nake ji"
Murmushi mai faɗi Safwah tayi tana faɗin "Ba dai ƙya so in faɗa abinda ke raina ne na gaskiya kike wani waske wa" ta faɗa tana tashi ta fice. Gyara kwanciyar ta tayi tana rufe idon ta ruff tare da faɗa wa duniyar tunani...
💦💦💦💦💦
*GAYA LOCAL GOVERNMENT KANO STATE*
Gida ne mai kyau da tsari kato irin gidan da ya sha fenti, babban tsakar gida ne da ya sha gyara tass da shi babu datti.
Babbar mace ce a tsaye gefen ta matshiyar budurwa ce kusa da ita tana wasa da ƴan yatsunta
"Ɗauka ki kai mata ɗaki, ki ɗauko kwanukan da suke ciki" tace da ita idanunta a kanta
"Umma wallahi tsoro nake ji kar ta dake ni kamar yadda ta ke yi wa Hafiz" ta faɗa muryarta tana rawa
Wani irin kallo ta watsa mata tare da haɗe rai "Ni kike so na ɗauka na kai mata Sabrah?, Ko Uban naku kike so ya kai mata?" Da sauri ta hau girgiza mata kai "Ba haka nake nufi ba, zan k kai, Allah ya huci zuciyar ki"
"Ke kika sani kuka, in kin ga dama ki kai mata in baki ga dama ba ki barshi, in Shehun ya dawo ya kai mata tunda ƴar uwarsa ce, mara tunani kawai" tace tana wuce wa ɗaki.
Jiki a sanyaye Sabrah ta sunkuya ta ɗauki langar zuciyarta bugawa take da sauri ta nufi kofar dake can ƙarshen gidan, makulli ta ɗauka akan taga tare da ajiye langar a ƙasa ta buɗe ƙofar ɗakin, bakin ta ɗauke da sallama ta shiga ciki palour da ƙofofi guda biyu a ciki babu komai a cikin palour sai tabarma dake malale a ƙasa, babu kowa a ciki nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tare da wucewa gurin ɗaya daga cikin ƙofar.
Ƙaton bedroom ne me yalwa,wanda ya wadatu da kayan gado da suka kasance cikamakin ado da kyawun ɗakin, duk da ba na zamani bane, ya yi kyau ga kuma haske sosai tarwai. Abinda zai baka mamaki shine, duk da irin kayan ado da bedroom din ya mallaka, kusan komai na dakin a hargitse yake, hatta da farin bedsheet din da dake shimfiɗe akan gadon a yamutse yake guri guda, uwa uba kuma ya ɓaci da wasu abubuwa da bazaka iya tantance meye a jiki ba, illa dai ka ragewa kanka wahala ka kirasu da datti kai tsaye.
Daga can tsakiyar gadon kuwa, kayan sa wa ne zube, gefen su mace ce zaune sannan a cure waje daya, tamkar wadda ke shirin saka kanta cikin gangar jikinta ta koma abu guda, ta rungume gwiwoyinta sosai a ƙirjinta. Baka iya hangen fuskarta, amma kana iya hangen gashinta me tsaho da santsi daya cukurkude, kwatankwacin yadda zare yake cakudewa guri guda, tsahon sumar ya sanyata barbazuwa har saman bayanta, jikin ta sai rawa yake. Doguwar riga ce ta atamfa a jikin ta, kallo daya zakayi mata kasan me tsada ce, sai dai duk ta yage ta canza yanayi tayi wani irin azababben squeezing.
Idan ka kasa kunne da kyau zaka iya jin sautin kukanta, sautin da bashi da wani qarfi ko karsashi a cikinsa ko misƙala zarratan, saboda rashin wadatacciyar garkuwar jiki da zata bata wannan damar, uwa uba kuma tayi kukan tayi kukan har batasan adadi ba, ta zubda hawayen da har sai data daina sanin lokacin tahowarsu, har sai da idanunta suka fara gani dishi dishi, ta yanke tsammani daga samun dukkan dauki, ta kuma gama sallamawa ƙaddara rayuwarta. Ɗago kai tayi tana kallon mai shigowar bata motsa ba amma ta zuba mata idanunta, wani irin bugawa zuciyar Sabrah ta shiga yi ganin yadda fuskarta tayi kaca-kaca da tabo ga jini duk ya ɓata ta. Gaba ɗaya dauda ta mamaye ta baka iya shaida kamaninta "Hajiya ga abinci, Umma tace na ɗaukar mata waɗancan kwanukan" shiru bata yi magana ba, itama bata ƙara ce wa komai ba dan tasan ba lallai ta tanka mata ba ta taka zuwa gurin da kwanukan suke ajiye
Kamar kiftawar ido ta ganta a gabanta, batayi wata-wata ba ta tsinka mata mari, idanu ta waro waje wata irin azaba na ratsa sassan jikinta lokaci guda, Kafin ta yi yunƙurin ceton ranta ta shaƙo wuyan ta, wahallaliyar ƙara ta saki jikinta na rawa dan shaƙar bata wasa bace, balle shekarun ba ɗaya ba. Buga kanta ta shiga yi da bangon ɗakin, ƙara ta saki wadda tafi ta farkon tana cewa "Umma kizo ki ceceni Hajiya zata kashe ni" tana sakin kuka....
____________
💭 #TunaninƘarshe 💔🌒
Comments,✨React🙃 & Share🙌😊 mutanen amana*
*Kamar ko yaushe ƙofar ƙorafi, gyara ko shawara a buɗe take a ko da yaushe🥰🤍*
~07077791941~
*Fateyzahraah🖋️🌌**