Barrister Hibba
by @nusybee143
đź’Ą BARRISTER HIBBA đź’Ą
✍️Nusy_bee
Page 10
Hibba ta ja numfashi ta fesar,ta waiga a kaikaice ta kalli Alhaji adam yadda ya gigice,ta girgiza kai tana murmushin mugunta,sannan ta sake mayar da hankali ga Suraj tace"to Ina jin ka,zuwa yanzu nasan dalilin sace Rahama,amma menene gaskiyar maganar da tace na cewa kayi raping ɗin ta?infact ka cigaba da yi akai akai?ta ƙarashe cikin tsawa
Suraj ya sunkuyar da kanshi,cikin karaya da yanayin tausayi yace"sharrin shaidan ne,wallahi da farko banyi niyyar lalata rayuwar ta ba,sharrin zuciya ne,amma ina rokon kotu mai adalci ta rangwanta min"
"Naji wannan,akwai sojojin da suke rangadi a jejin da kuka yar da Rahama, ta bayar da number ta, sun kira ni suka sanar min,da naje na samu Rahama labour takeyi kuka jefar daita,menene dalilin hakan?"
"Na kira Alhaji adam na zayyana Masa abinda ya shiga tsakanin mu da Rahama har ta samu ciki, Yanzu haka ma labour takeyi,sai yace mu kashe ta,shine muka jefar daita,don a halin da take zata iya mutuwa,ban taɓa tunanin ganin ta a raye ba sai yanzu da na ganta"
Take kotu ta kuma ɗaukar hayaniya, ita kuma Hibba ta samu waje ta zauna saboda jirin da take gani,tana jin gunjin kukan Rahama amma bata ɗago ba,alƙali ya buga guduma akayi shiru,sannan yayi rubuce-rubuce ya kalli Barrister Nuraddeen ya tambaye shi ko yana da tambaya wa Suraj,Kai tsaye yace a'a, alƙali ya ƙara ƴan rubuce-rubucen shi sannan ya ɗago ya kalli Hibba ya tambaye ta ko akwai sauran bayani? Hibba ta miƙe cikin sanyin jiki ta fara bayani
"Ya mai Shari'a,a wani dare ina kwance ina bacci,waya ta ta tashe ni,da na farka sai naga sabuwar number,da har na share,sai akayi ta kira na babu adadi,na ɗaga sai bawan Allan nan ya gabatar da kanshi a matsayin sergeant Musa,gashi nan"ta nuna wani mutum a cikin kayan sojoji,tace "kotu na buƙatar jin bayanin yadda kuka samu Rahama,har zuwa lokacin da na amshe ta"
Sergeant Musa ya fara bayani kamar haka
"Mu kan yi zagaye a wajen lokaci zuwa lokaci,a ranar wajen ƙarfe sha ɗayan dare sai muka ga wannan baiwar Allah,da farko na zata ma ta rasu,nayi saurin kiran wani collegue ɗina wanda ya kasance health personnel ne,shine ya duba ta yace da ranta,mukayi gaggawar kai ta asibitin da ke nan kusa damu,bamu juma da zuwa ba ta farfaɗo,ka kira mu wai tace tana son magana damu,anan ta bamu number waya tace mu kira muce Rahama Ja'afar shuwaki ce
Bamu yi sanya ba muka kira a daren,anan muka gabatar da sunan da wannan mara lafiya ta saka mu,munji matar ta firgice tace mu gaya mata inda muke,mukayi mata bayani
Baayi cikakken awanni biyar ba ta iso asibitin a cikin ɓadda kama,sai dai zuwa lokacin rahama ta shiga coma,hakan yasa akayi gaggawar cire ɗan cikin ta, Barrister ta ɗauke ta ta tafi da ita,sun bar asibitin a wata tsohuwar taxi ita da drivern motar a lokacin dare ya fara yi,iyakar abinda na sani kenan"
Hibba ta gyara tsayuwa tace"na ɗauke rahama daga asibitin da su sergeant suka kai ta na mayar da ita asibitin Dr Umar,gashi nan"Muyassar yayi mamakin ganin wannan wanda ta kai dattijon da ta buge asibitin shi, Hibba ta cigaba"shine ya duba ta ya bani shawarar mika ta zuwa saint Mary's hospital acan in da nake aiki saboda tsaro,a dalilin tsaron Rahama na bar kasar england na tsawon watanni,wadda itace ƙasar da nayi karatu kuma harkoki na suka fi yawa a can,na koma Germany,kuma naƙi waiwaiyar Nigeria,sai da likitan da ke kula da ita yayi min waya ya sanar dani ta farfaɗo sannan naje manchester,gashi kuma anyi ƙatuwar Sa'a lokacin za'ayi wannan zaman kotun"
Hakika jama'a da yawa sun jinjina kuma sun yabawa wannan lawyer da ta kasance mutuniyar kirki,mai mayar da matsalar wasu a tasu,mai tsayuwar daka da jajircewa don ganin ta samar da adalci ga wanda aka zalunta,da yawan mutanen da suke jin haushin ta yanzu ƙaunar ta da sha'awar rayuwar ta suke ji,sun haɗa da Hammad da ya manta ma zaman kotun Zahraddeen ya kawo shi,da Muyassar da ya tabbatar zuwa yanzu akwai wani ɓoyayyen abu game da rayuwar wannan baiwar Allah, ba'a maganar Dr Khaleed da shine yasan komai na ayyukan Hibba,shi kam Dr Umar shine yasan wacece Hibba,don haka baiyi mamaki ba,kuma baya mamakin komai tayi
Hayaniyar da ta kaure kusan tafi ta koyaushe,alƙali ya buga guduma akayi shiru, sannan ya cigaba da rubutu,bayan ya gama ya ɗago yana kallon Barrister Nuraddeen ya tambaye shi ko yana da tambayar da zaiyiwa sergeant ko Barrister Hibba?tabbas yana da ita,amma shi fa uba ne,kuma yana da yara mata,yanzu ace ɗaya daga cikin ƴaƴan shi ta shiga wannan matsalar ai adalci zai nema mata ba tambaya zaiyi ba,don haka ya girgiza kai kawai, alƙali yayi ƴan rubuce-rubuce sannan ya ɗago, lokacin kotu tayi tsit tana sauraron hukuncin alƙali
Ya fara bayani"bisa ƙwararan hujjoji da Barrister Hibba Ibrahim Aiyo ta kawo,kotu ta yanke wa Alhaji adam doguwa hukuncin kisa ta hanyar rataya,bisa tsarin kundin Shari'a na CPC, bisa samun shi da laifin haɗa kai don aiwatar da kisan kai,da kuma garkuwa da mutum, Suraj an yanke masa hukuncin daurin shekaru goma sha huɗu a kurkuku tare da aikin wahala,bisa laifin fyade,sannan an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya,bisa samun shi dumu dumu da laifin kisan kai,sannan an yanke wa Hajiya Fatima hukuncin ɗaurin rai da rai a gidan yari tare da aiki mai tsanani saboda samun ta da laifin bada gudunmawa a aiwatar da kisa bisa kundin tsarin Shari'a na CPC"alƙali ya buga guduma,mutane suka mike suna faɗin"kooootuuu!"
Daga shari'ar rahama za'a sake zama ɗaya kafin a saurari shari'ar su Zahraddeen, Rahama ta sha kuka Hibba tana ta bata haƙuri,har harabar court ɗin Hibba ta raka ta tana ta bata shawarwari,ita ta riƙe mata jaririn nata wanda ta saka masa suna abdallah,ƴan sanda suka raka ta ta ɗauki hanyar Hadejia
A wajen dawowar ta ta haɗu da ƴan sanda suna fito da su Alhaji adam doguwa,a gaban su ta tsaya tana kallon su ɗaya bayan ɗaya a wulaƙance,daga baya ta mayar da kallon ta ga Hajiya Fatima tace"
"Abin tausayi!baki haihu ba, maimakon ki ja wadda Allah ya baki a jiki sai kika biyewa son zuciyar da a ƙarshe gashi nan ya kai ki ya baro"ta juya ta kalli Suraj tace"Kai kuma,da ace ba'a yanke maka hukuncin kisa ba, wallahi tallahi sai ka gwammaci mutuwa da rayuwa,sai na saka duniya ta zame maka masifa da bala'i,tunda kai bunsuru ne"ta kalli Alhaji adam doguwa tayi ƴar dariya tace"yaron ka ko abokin cin mushen ka, Barrister Auwal Tofa,shi ya saka min suna COBRA!saboda yadda yaga ina dakawa azzalumai gumba a hannu,kar kayi tunanin wani makircin ka na tsofaffin ƴan duniya zaiyi tasiri akaina,ni ɗin ba bagidajiya bace,da ƙwaƙwalwa nake aiki, sannan makircin da kake tunanin ka iya ni karantar shi nayi,don haka ko da Allah ya ƙaddara zaka yi wata rayuwa a gaba ka roƙi Allah ya raba ka da HIBBA AIYO!karon mu bazai taɓa daɗi ba"tana kaiwa nan ta sa kai ta wuce batare da ta sake kallon su ba ta koma wani ɓangaren court ɗin ta zauna tana ajiyar zuciya tana ɗan shafa goshin ta, hawaye na ƙoƙarin taruwa a idanun ta tana mayarwa,duk Wannan drama ɗin a kan idanun Hammad,wanda ya fito da jama'ar da suka halarci zaman Court ɗin Rahama,amma shi tsayawa yayi yana kallon Hibba da yadda take faɗa tana zazzare idanu,dama Allah ya bata wadatar su
Zuwa can ta ja ajiyar zuciya sannan ta miƙe ta koma cikin kotun,wata iska na ratsa ta,don ba ƙaramin relief ta ji ba gama wannan ƙaddararriyar shari'ar da akayi,shima Hammad bayan ta yaci batare da ta sani ba ya koma cikin audience ɗin ya zauna
Ba'a wani juma ba aka fara Shari'ar su Zahraddeen,ba ɗan ƙaramin mamaki su Hammad sukayi ba jin wai ana tuhumar Zahraddeen da yaudarar mutane a sabon clinic ɗin shi yana cire sassan jikin su,musamman ƙoda,har hanta ya ɗauke wa wani dattijo da ya rasu,banda wannan akwai abubuwa da yawa da yayi,ga shaidu da yawa, waɗanda akayi musu da wadanda akayiwa wasun su,ganin bashi da mafita ya amsa,a take kotu ta yanke masa hukuncin daurin shekaru goma a gidan yari,daga haka kotu ta tashi
Kamar yadda aka saba ƴan jarida sun so hira da Hibba,amma ko kallon su bata yi ba,ta faɗa mota,har sun kusa fita taga Hammad da Khaleed,tsayar da Muyassar tayi sannan ta sauke glass ta kalli Hammad fuskar nan a ɗinke tace"kaji waye abokin da kake yiwa mutane rashin kunya saboda shi, saboda haka idan kaima haka kake You better change don bazan ƙyale ka ba"daga haka ta zuge glass ɗin, Muyassar ya ja ya fice yana murmushi,don abin ya bashi dariya,a ƙalla Hammad zai iya zama sa'an shi ko ma ya girme shi da shekara ɗaya ko biyu,kuma shi kanshi zai iya bawa Hibba a ƙalla shekaru shida zuwa bakwai,wai amma Hammad yana mata rashin kunya!
A harabar gidan suka iske Arwa tana kukan tashin hankali,tun daga nesa da ta hango motar Hibba ta ƙaraso wajen a guje,ƴar doguwar riga ce a jikin ta mata nauyi,kanta ko ɗan kwali babu,ribbom ɗin da aka sanya masa duk yabi ya tuttuje,a ruɗe Hibba ta nufe ta tana faɗin"zainab menene?me ya faru?"
Cikin kuka take bayani"athma É—in twin ce ta tashi!"gigicewa tayi itama,har Muyassar zai wuce sai ya fasa,ya dawo ya wuce cikin gidan da sauri suka mara masa baya
Daga yadda yake duba ta kaÉ—ai ya isa shaida yana da experience a kan harkar,ya dubi Arwa yace"akwai injection É—in ta?"da sauri ta gyaÉ—a kai,yace"yi sauri ki kawo min"cikin sauri ta kawo masa,a Ć´an mintuna Marwa ta dawo daidai tana sauke numfashi a hankali tana kallon su
Da kanshi ya É—aga ta ya kwantar a kan kujera,sannan ya fice daga parlourn ko waigowa baiyi ba,har yanzu batun shari'ar nan bai sake shi ba
Dukkansu bin shi sukayi da kallo,kafin Hibba ta kalli Marwa tace"me ya tayar da ciwon nan zainab?"Arwa tace"nima ban sani ba yaya,kawai shigowa parlourn nayi na ganta tana kakari"
Hibba tace "ina mama?"
Arwa tace"tun safe aka kira ta cewa ƙanwar ta babu lafiya,ta kira wayar ki yafi sau goma don sanar miki zata je ta dawo da yamma amma bata same ki ba"Hibba bata sake wata magana ba ta haye sama don tayi wanka tayi sallar azahar da ake kira
Bayan la'asar ta fito as usual da shigar ta ta rai da rai track suit na PSG baƙaƙe,da alamu dai hibbatun mu fan ɗin PSG ce,da baƙin sneakers sai farin baby hijab, medicated glasses ɗin ta ɗore a idanun ta, Muyassar yana ganin ta ya nufe ta,ta bashi key ya fito da motar ƙirar BMW
Sai da suka harba titi sannan ta gaya masa inda zai kai ta,suna isa bakin gate É—in ta fito ta shige,shi kuma ya bita da kallo
Murmushi tayi ganin yadda Barrister Auwal yayi tsumu,matar shi a gefe tayi tagumi,tana shiga ya miƙe a firgice,matar shi tace"sannu da zuwa Barrister"murmushi tayi batare da ta kalle ta ba tace"yauwa sannun ku momy"
Waje ta samu ta zauna sannan tace"da fatan kana lafiya Barrister,Kar kaji komai,nasan kai ka saka aka ɗauke Barrister Khadijat,Ni kuma na saka aka kwashe maka yaran ka,manufar mu wata tazo ɗaya wata kuma ta saɓa,idan ka saki Barrister Ni zan saki su Aslam,akasin haka kuma"tayi murmushi da ya bayyana dimple ɗin ta "ba sai nace komai ba Barrister,ka san wacece Hibba Ibrahim aiyo"
A zabure matar shi tace"Hibba!meye ribar ki ta hakan?me yara na sukayi miki da zaki yi kidnapping É—in su?"
"Momy kar ki damu,yaran ki suna cikin kwanciyar hankali,amma komai zai iya samun su idan azzalumin mijin ki ya cutar min da ƙawa"ta waiga ta kalle shi tace"a tunanin ka ni wawiya ce da zan saki sirrin Shari'a ta kuyi min shigo shigo ba zurfi?never!da kai da Khadijat amfani nayi daku,kai don na gano waye adam,ita kuma don ta taimaka min da wasu ƙananun matsaloli
Tun daga lokacin da na fuskanci kai mayen kuɗi ne na janyo ka jiki na don nasan nan da nan za'a siye ka,sai gashi anyi, saboda kuɗi kayi ƙoƙarin kai ni ƙasa,amma kuma a ƙarshe nayi abinda na saba,wato nasara"ta miƙe tsaye,na baka nan da two hours a kawo min ƙawa ta bakin AIYO MANSION,idan ba haka ba,kar ka manta dai kai ka saka min suna COBRA!"tana kai wa nan ta fice daga parlourn tayi waje
Sai da suka hau titi sosai sannan ta umarci Muyassar ya tsaya,ya tsaya,ta fita ta buɗe gaba ta zauna tana fuskantar shi tace"ka ga dai yadda shari'ar mu ta kaya ko?"ya gyaɗa kai yana kallon ta gami da faɗin"I salute you ma'am",ta girgiza kai tace"yadda nayi a shari'ar nan haka nakeyi a rayuwa ta ta yau da kullum,bana taɓa bari ayi nasara akai na,ina fata ka fahimci me nake nufi"idanun shi cikin nata yace"sai dai kiyi min bayani"Hibba tace"to ina so ka gaya min menene mission ɗin ka na zuwa gidan mu,nasan unguwar ku gandun albasa,ƙannen ka duka mata,ɗaya tana aure a Katsina,ɗaya tana Sokoto,ƙaramar kuma a Kano tayi aure unguwar rijiyar zaki,amma wahalar uwar miji yasa suka rabu da mijin,tana da yaro ɗaya,an tabbatar min da cewa kayi karatun medicine a jami'ar Bayero,then me ya kawo ka gidanmu a matsayin driver?"
Murmushi sosai Muyassar yayi yana mayar da idanun shi ga titi, yace"ko wa kika aika yayi miki wannan binciken to daƙiki ne,tabbas dukkan bayanan gaskiya ne,amma a shekarar ƙarshe mun samu matsala da wani lecturer,na kasa jurar yadda yake yaudarar matan department ɗin mu yana don zai basu marks nayi masa gargaɗi, dalilin hakayayi min rantsuwa da Allah sai ya sanya anyi expulting ɗina,da wasu abokai ba aka haɗa kai aka saka min mal practice, tun daga nan na haƙura da karatu,nine babba kuma Ni kaɗai namiji iyaye na suka haifa, mahaifi na ya rasu shekaru kusan sha bakwai da suka wuce, mahaifiyar mu ce take ta ɗawainiya da mu har zuwa yau,ita ta ɗauki nauyin karatu na,nayi fargabar zata gamu da wani ciwon idan na gaya mata,don bata da ishashiyar lafiya,don haka har zuwa yau na bar mata cewa na gama karatu amma ban samu aiki ba,baiwar Allah kullum fatan ta na samu aiki na kula da ƙanne na,ga autar mu ita uwar mijin ma ta hana mijin nata kula da tilon ɗan shi da ke hannun mu,haka ne ya sanya bani da zaɓi da ya wuce samun wannan aikin da sunan ina aiki a wani ƙaramin asibiti ne,har yau mahaifiya ta bata san aikin driving nakeyi ba, duk a tunanin ta aikin asibiti nakeyi, musamman da ya kasance kina biya na kuɗin da babu laifi asirin mu yana rufuwa"ya juyo ya kalle ta yadda tayi sakare tana kallon shi cike da tausayi,yayi ɗan murmushi yace"for now,you are free kiyi duk kalar binciken da zakiyi,amma still Ina ƙara roƙon ki,bana son mahaifiya ta ta san cewa Ni ba ma'aikacin lafiya bane, driving nakeyi,ba damuwa ta driving ɗin ba, a'a bana son ta san cewa an kore Ni a makaranta"
Hibba ta É—auke idanun ta ta ja ajiyar zuciya tace"to in dai haka ne,meyasa baza'a binne batun ba na har abada? I mean,duk yadda za'a yi ka samu takardun ka in yaso sai na samar maka aiki a matsayin likita?"
Muyassar yace"ta yaya kenan?"gyara zaman ta tayi tace"makarantar da nayi zaka koma for a while,sai a cewa maman ka ka je ƙaro karatu, asibitin da kake aiki sun ɗauke ka scholarship,amma ya ka gani?"murmushi yayi yace"to amma wa zaiyi affording?kuma ba naji ance a waje kikayi karatu ba?meyasa bazanyi a Nigeria ba?"
"Kamar yadda nace asibitin da kake aiki,ina nufin gidan da kake aiki, dalilin da yasa na zabi waje kuma saboda acan ne har ka gama karatun ka bai zama lallai wani ya É—ago ka ba,dama special class zakayi,two years kawai zakayi,amma kai me ka gani?"ta faÉ—a tana kallon shi
A hankali ya girgiza kai yace"a matsayi na na namiji,abin kunya ne na zauna ana yi min hidima alhali da raina da lafiya ta,sai dai ki samo min daidai yadda zan iya biyan ki ko da bashi ne,na cigaba da aiki babu salary"murmushi Hibba tayi sannan tace"bani nayi maka ba, Allah yayi maka,kamar yadda wancan karon Allah ya jarabce ka,ƙin hakan kamar butulci wa Allah ne,tsawon lokacin da ka ɗauka kana driving da Allah yaso da mahaifiyar ka ta gane,bayan an kore ka daga makaranta da Allah yaso sai kaga course mates ɗin ka sun zo maka jaje basu same ka ba sun samu mahaifiyar ka sunyi mata jajen"shiru yayi cike da mamakin Hibba,bai sake magana ba,ta umarce shi ya ja motar su tafi
Suna cikin tafiya ya kasa jurewa ya kalle ta yace"akwai abubuwan da kikeyi da yawa yana bani mamaki,amma na jiya yafi tsorata ni,da farko yadda kika tsayawa yarinyar nan A'isha,bani kadai ba har sauran mutane sun yaba miki,dama last week kinyi abinda yayi matuƙar burge ni da muka je rijiyar lemo abinda kikayi wa yarinyar nan Hafsah,amma abin mamaki jiya kika buge dattijo mai shekaru da yawa sannan kika umarta a yanke masa ƙafa,na kasa gane dalilin hakan, sai kawai nayi tunanin maybe kirkin ki ga mata kike nunawa,amma yadda kika nemi taimako na yanzu ya ƙaryata tunani na,sannan yaron nan na rijiyar lemo Ameer ya tabbatar min ke kika kula dasu bayan rasuwar mahaifin su,yanzu haka ma ke kike ɗauke da nauyin karatun su, I'm sorry bana ganewa shiyasa na tambaya"
"Kar ka damu zan gaya makadalilai na,amma ba yanzu ba"ta faÉ—a idanun ta kan wayar ta
Motar ta ƙara yin shiru,zuwa can yace cikin sanyin murya"ban taɓa tsammanin zan samu takardun makaranta na ba,ko nace zan kammala karatu na,asalima bani da wannan hope ɗin yanzu,na gode sosai, Allah ya saka miki da mafificin alkhairi"ɗan murmushi kawai tayi batare da tace komai ba,haka sukayi shiru har suka ƙaraso gida
A parlour ta zauna,har zuwa lokacin Arwa tana kwance a three sitter inda Muyassar ya kwantar da ita tana bacci peacefully, Arwa kuma tana fuskantar ta ta tayi shiru,gashi har lokacin mama bata dawo daga garin su da taje ba,Hibba ta kalli Arwa tana faÉ—in"zee ya jikin nata?"Arwa ta amsa da "alhamdulillahi,bacci takeyi ne dai tunda kika fita"Hibba bata sake magana ba ta nemi waje ta zauna
Ta kai wajen mintuna talatin kafin Jabir ya kira ta a waya,cikin sauri ta ɗaga,jin abinda yace ya sa ta fice da sauri,a compound ta same su sun shigo da Barrister Khadijat da ɗanta da suke a halin suma, dai-dai lokacin Muyassar ya gama duba su yace a wuce dasu zuwa asibiti,suna buƙatar taimakon gaggawa
Su suka zuba su a mota,Hibba ta shiga gaba suka nufi asibitin Dr Umar
Dab da maghriba Khadijat ta farfaɗo,shi kuma yaron ta sai wajen tara na dare,dukan su an ƙara basu lokacin hutu saboda wahalar da suka sha
Wato Hibba ko Ni ma nace kin cancanci sunan COBRA!a ɓangare ɗaya kuma muna miki godiyar taimakon Muyassar da kikayi,kuma muna ƙage da jin dalilan ki na sauyawar halayen ki,yanzu fari anjuma baƙi
#likecommentshare
#Nusy_bee