Barrister Hibba

Barrister Hibba

by @nusybee143

💥 BARRISTER HIBBA 💥

✍️Nusy bee

Page 11

Washegari da misalin karfe bakwai da rabi na safe Muyassar ya iso, Arwa ce tayi masa jagora har cikin gidan don yaga jikin Marwa,sai surutu take zuba masa,na cewa jiya fa yaya cikin farin ciki ta kwana,don dama shari'ar nan ta hana ta walwala,dama ita Arwa akwai surutu ba kamar Hibba da Marwa ba, murmushi kawai yakeyi,zuwa yanzu ya gane ƴan matan ba wai girman kai gare su ko wulaƙanci ba, tsoron shiga mutane ne kawai, wataƙila akwai abinda akayi musu,ko kuma yanayin su ne a haka, Allah masani

Da sallama suka shiga,Marwa tana zaune a kujera,mama kuma tana zaune kusa da ita tana bata tea,yayi murmushi ya gaida mama cikin girmamawa,ta amsa da fara'a,Marwa ma ta gaishe shi cikin sanyin murya,ya amsa yana murmushi yace"how are you feeling?"

Tace"alhamdulillah!"yayi mata ƴan tambayoyi,jin duka babu matsala ya ja baya yana kallon Arwa yace"kiyi min magana da Yaya,tace zamu koma asibiti"

"Good morning Uncle"waigawa yayi ya kalli ƴar babyn da tun ranar da Hibba ta dawo bai ƙara ganin ta ba,yanzun ma sanye take da doguwar riga iyakar ta ƙauri milk colour,gashin ta brown colour an raba shi biyu an kitse shi jelolin sun sauka gefe da gefen ta wajen kafaɗa, fuskar nan a washe ƴan haƙoran nan a waje,ta burge shi sosai,ya kamo hannun ta shima yana ta murmushi yace"morning sweetheart!how was your night?"ta waro idanu tana murmushi tace"it was awesome uncle!mama na tana ta farin ciki nima nayi farin ciki"shock ya shiga jin Hausa a bakin ta,a ɗaya bangaren ya cika da mamaki don tabbas ya ganta tare da Hibba amma ko da wasa bai kawo ita ta haife ta ba, musamman da ya kasance kallo ɗaya za'a yi wa yarinyar a samu amsar baturiya ce saboda yanayin halittar ta,amma ya danne ya shiga yi mata hira,wadda ta danganci karatun ta, yarinyar ta bashi mamaki kuma ta burge shi,jin yadda tayi karatun addini sosai,haddar izu biyu da rabi da tayi ta zauna sosai akan ta, adduoi kuwa kusan babu wadda ba'a taɓo mata ba,tuni yarinyar ta shiga ranshi musamman da yaji sunan ta Maryam,sunan mahaifiyar shi

Ya shagala yana ta hira da Maryam har Hibba ta sauko,sosai taji daɗin yadda Muyassar yake damuwa da duk abinda ya shafe ta,mama da ƴan biyu sai kallon su sukeyi suna murmushi, ballantana ma Arwa da tun daga kular mata da sister ɗin ta ita fa kawai taji ta samu babban yaya namiji

Hibba ce tayi gyaran murya tana faɗin"Uncle zamu tafi, it's getting late"murmushi yayi ya juyo yana faɗin"good morning Yaya!"murmushi tayi tana gyara zaman baby hijab ɗin ta,yau ma dai kayan gadon ne,track suit blue black ta PSG, sai sneakers shima blue black,ta ƙarasa saukowa daga jikin staircase da ta tsaya tana faɗin"ka san meyasa bana amsa gaisuwar ma'aikata na?"

Yace "a'a sai kin faɗa"yana kallon ta

Tace "saboda bana amsawa wanda ya girme ni gaisuwa,kuma a da haushin mutane nake ji"

"Ko me yasa?"ya tambaya yana kallon ta, murmushi tayi tayi gaba shima ya bi bayan ta

Sun samu Barrister Khadijat ta ji sauƙi tana rungume da yaron ta da ya tada rigima akai shi wajen Uwar shi,tana ganin su tayi murmushi tana faɗin"Barrister Aiyo! congrats!! gaskiya You deserve the name Cobra!kinyi ƙoƙari sosai, congratulations once again dear"murmushi Hibba tayi ta zauna gefen ta, Muyassar cikin sakin fuska ya gaishe ta da jiki,ta amsa a mutunce tana masa godiya,ya ɗagawa Mukhlis hannu yana murmushi,duk da rashin yardar shi shima ya daga masa nashi hannun,hannu ya miƙa masa,ba musu ya tafi,ya ɗauke shi suka fice daga ɗakin

Hibba ta kalli Khadijat da daɗi kamar ya kashe ta ganin Mukhlis ya yarda har an fita dashi tace"me ya faru ne khadija?munyi waya kin hawo taxi sai na jiki shiru?"

Murmushi Khadijat tayi tana kallon Hibba tace"bari ke dai Aiyo,kinsan wai Barrister Auwal ya saka aka sace ni?mutumin kawai,gashi dattijo amma na banza? Hibba tace "na sani ai, shiyasa nima nace a ɗauke masa yaran shi da yake so kamar ranshi, don yaji idan da daɗi,sai da Umar ya kira ni jiya yace kin farfaɗo sannan nace a mayar dasu gida"Khadijat ta ƙyalkyale da dariya tace"to da ban farfaɗo ba ya zakiyi masa? Hibba tace"wallahi bazan saki yaran ba sai ya gayawa duniya abinda yayi miki"Khadijat tayi murmushi ta fara bayani

"Bayan shiga ta taxi ban san bacci ya ɗauke ni ba sai farkawa nayi na ganni a wani waje mai duhu,sai da nayi a ƙalla awa shida sannan wani ƙaton mutum baƙi ya shigo,da Igbo yayi min magana cewa idan nayi taurin kai sai sun kashe ni,nace ina yaro na?ya daka min tsawa yace nayi masa shiru,daga nan yake tambaya na wai hujjojin da Barrister Hibba ta bani,nayi musu bayanin cewa ba komai a hannu na,suka fara min allurai,daga baya dai Barrister Auwal yazo yana min bayanin har dashi a shirya komai,har ya ƙara da cewa da yace ma bazai kama ni ba,amma yanzu yaga hakan zai fi zama mafita,nace ko me zasuyi min suyi min,amma bansan wata hujja ba,shine suka yi min wasu allurai still,suka fita,Ni dai daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba sai anan"

Hibba ta ja ajiyar zuciya tace" aikin mu akwai haɗari Khadijah,sai dai kariyar Allah"

"Mhmmm! ba wannan ke bani tsoro ba ma Hibba,sai yadda ake haɗa baki da Mutanen mu ake cin amanar aikin mu, Barrister Auwal ya bani mamaki,haka fa yayi ta bibiya ta lokacin da kikayi tafiyar nan baki dawo ba, imagine har Lagos ya bini yake tambaya na wai ya ake ciki?munafukin har yana cewa shi damuwar shi kar a sake shiga kotu batare da Rahama"Hibba ta girgiza kai tana jinjina makirci irin na Barrister Auwal sannan tace"ba don komai naƙi dawowa ba sai don Rahama da take manchester,kuma naƙi zama a manchester ɗin don kar su gano wani abu, tuntuni na gano da saka hannun adam doguwa a komai, shiyasa na sake taka tsantsan sannan kuma na saka a bibiyar min shi,abin mamaki sai gashi suna communicating da Auwal, imagine Wai Auwal,dama kuma ina zargin Auwal zai iya yin komai akan kuɗi shiyasa na nemi taimakon shi akan shari'ar nan,suna min kallon biri ina musu kallon ayaba"Khadijat ta fara tafa hannayen ta tana murmushi tana faɗin"Weldone Barrister!gaskiya babu lawyer da take bawa azzalumai wuta irin Cobra! Allah ya cigaba da kare ki da mu baki ɗaya"Hibba ta miƙe tana murmushi tana faɗin"ameen inyamura"Khadijat ta ta galla mata harara,don da gaske ta tsani sunan,ita kuma Hibba indai ta so tsokana sai ta rinƙa kiran ta da sunan

Basu wani juma sosai ba Muyassar ya mayar da Mukhlis bayan ya siya masa chaculate da ice cream, Khadijat sai murna takeyi ganin yadda Muyassar yake son yaron ta da ko Hausa baya ji kwata kwata,suka fice zuwa gida

A hanya zeenat ta kira shi tana kuka,bayan ya ɗaga yake tambayar ta abinda ya faru,cikin kuka take faɗin"yaya  jikin ammi ne ya motsa,wani irin numfashi takeyi"ya sauke ajiyar zuciyar damuwa yace"okay relax zeenat!am on my way,bani mintuna talatin kawai"ya kashe wayar ya kalli Hibba yace "I'm sorry mamana babu lafiya,zan iya sauka anan?tana bukatar proper treatment"idanun ta na kan wayar ta tace "mu wuce gidan naku kawai"yayi ɗan murmushi yace"thanks"sannan ya ɗauki hanyar gidan su

A cikin motar ya bar ta ya shiga gidan,jin shiru ya sa ta bi shi gidan batare da shakkar komai ba,sai kawai sallamar ta yaji,kafin ya gama tantance wa yaji zeenat tana amsawa,yana ɗagowa yayi ido huɗu daita tana kokarin cire sneakers din ƙafar ta

Sai da ta ƙara sallama sannan ta shigo parlourn,ganin yanayin maman tace da zeenat ta kama mata su kai ta mota sai Muyassar ya kai su asibiti,da farko zeenat ta tsaya tana kallon ta irin kallon ban sanki ba ɗin nan,sai da Hibba tayi murmushi tace"kar ki damu ni abokiyar aikin yayan ku ce"ganin Muyassar bai ce komai ba ya sa suka kama mama da ke numfarfashi zuwa mota,ya bi su jiki babu laka zuwa ƙofar gidan

Shine ya ja motar suka nufi asibitin Umar

Matsalar ciwon zuciya da hawan jini ne,an bata proper treatment sosai,suna tare a asibitin har bayan Isha'i,daga kan mama zuwa twins babu wanda bai kira ta ba,amsa ɗaya take ba su cewa tana lafiya,sai bayan Isha'i ta saka Muyassar yayi dropping ɗin ta a gida,tayiwa zeenat sallama don lokacin ammi bacci takeyi

Har suka isa gida danna wayar ta kawai takeyi,suna yin parking ta fito,don yunwa take ji,duk hankalin su ba'a kwance yake ba babu wanda ya tuna da abinci,sai da ta sauka sannan ta kalle shi tace"bari na baka abinci ka kaiwa zeenat,kaga tun ɗazu bata saka komai a cikin ta ba"yayi murmushi"thanks very much Yaya abokiyar aiki, Allah ya saka da alkhairi"tayi murmushi ta wuce cikin gidan,babu jumawa Arwa ta fito tana murmushi hannun ta riƙe da basket mai dauke da manyan warmers tana tambayar shi mai jiki,ya bata amsa alhamdulillah,ya tambayi tasu mai jikin,tace" wannan ai bata da kirki,ɗazu ma sai da mukayi faɗa da ita,ta cika rainin hankali"yayi murmushi yace"ke kuma kina mata rashin kunya ai"tace"Ni fa wallahi ban yarda ta girme ni ba,tare fa aka haife mu,kawai ana cewa ta girme ni duk ta raina ni"yayi murmushi yana kallon yadda take faɗa tana zazzare idanu, exactly yayar ta,abin Allah bambancin ta da ƙannen nata hasken fata da suka fita ne kawai,sai kuma yanayi a fuska da ke nuna itace gaba dasu


Bai sake magana ba,ya amshi basket din yayi mata sallama ya shiga motar ya tayar ya fice  don kai wa su zeenat abinci

LAMIƊO CRESCENT, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA

Ina labarin Dr Hammad ne? 

Murmushi sosai yayi bayan Hibba ta bar shi a inda ya kada masa warning,ya kalli Dr Khaleed da yake ta dariya yana faɗin"seriously this girl is so funny"

"Ko kuma both of you are so funny ba"a cewar Dr Khaleed yana dariya

Hammad ya kalle shi yana faɗin"what do you mean Khaleed?"

Khaleed yayi dariya yace"nothing,kawai dai fitar ka ta ɗazu na tuna da dawowar ka"

Murmushi kawai Dr Hammad yayi, Dr Khaleed ya cigaba"there is something behind,ina fata Allah yasa ayi damu"Hammad ya girgiza kai yana murmushi ya wuce motar shi ya fice daga Kotun

Ranar haka ya wuni sukuku, Ummi tayi tambayar har ta gaji,ƙarshe yace mata stress ɗin aiki ne,yana bukatar ya huta,hakan yasa bayan sallar Isha'i ya shige ɗakin shi

Tunani ya rinƙa yi akan Hibba,akwai halaye da suka haɗa da Namra, waɗanda babu mai fuskantar na Hibba sai wanda ya zauna da ita,ita ɗin selfless ce,tana sanya dukkan ƙarfin ta don kawar da damuwar wani,amma bata ɗaukar raini ko wulaƙanci, sosai take burge shi,amma abinda yake bashi tsoro ya san zuwa yanzu yana ɗaya daga cikin waɗanda ta tsana a rayuwar ta,tuna haka ya sanya jin wani iri a ranshi

Tashi yayi zaune ya jingina da gadon ya lumshe idanun shi,don shari'ar su Zahraddeen yaje,amma shari'ar su rahama ta ɗauki hankalin shi sosai,ya yaba kuma ya jinjina wa Hibba,tayi matuƙar kokari kuma tayi basira da wayo,da ace ana samun lauyoyi irin su Hibba ai da ɓarna ta ragu a ƙasar mu,ya daɗe yana ƙoƙarin gano yadda zai shawo kanta,kafin dabara ta fado masa,yayi murmushi ya kwanta a kan gadon shi yana jan bargo ya lumshe idanu yana tuna Barrister Hibba

Gaskiya ne malam Hammad 😅ai sai ka dage,don Barrister Hibba tamu da alamu fa akwai ta da taurin kai,kuma dai kaima ka faɗa kana ɗaya daga cikin waɗanda ta tsana,amma dai ka jarraba sa'ar ka😁

#likecommentshare

#Nusy_bee