Page 5&6
*🌹TUNANIN ƘARSHE 🌹*
A taste of the final thoughts before the storm begins…
Fateyzahraah
__________________________
*Arewabooks*
I just published "Page 1&2" of my story "TUNANIN ƘARSHE" :: https://www.arewabooks.com/chapter?id=685712185aac0a5a758c596e. Check it out!
*WhatsApp Channel*
***
***
*WhatsApp Group*
***
*Facebook Page*
***
__________
***
*Domin karfafa mana qiwwa ku yi following tare da liking shafinmu na Facebook 🤙🏼*
_______________________
Copy is not Allowed!
©2025 Fateyzahraah
_______________________
The Writer Of:
SILAR WAYA
HOORIYAH
SUNE SILAR ƘADDARA TA
MURADINA
BAN AIKATA BA
ƘWAI A BAKA
*❖ AND NOW❖*
*TUNANIN KARSHE*
Young Talented Writers Ass..(YOTA/020)
Season 1, Chapter 5&6.
بسم الله الرحمن الرحيم
____________
☆🌚Waiwaye🌚☆
Ƴarinya ce ƙarama wadda ba zata gaza shekaru sha biyu ba, sanye take Uniform riga da wando onion purple and black tafe a cikin layin shiru babu hayaniya, dai-dai wani gida ta tsaya tana tura ƙofar tare da kwasa a guje zuwa ciki, tura ƙofar palour'n gidan tayi tana kwala kiran "Ummiee" babu kowa a cikin palour.
Yalwataccen palour ne da ya sha carpet da ado cikin purple colour light and dark, sai kujeru ɗaya nau'in kalar light, ɗaya kuma kalar dark, sai stairs tana kallon ƙofar, ya cika dukkan sharuddan zama ƙawataccen falo na alfarma dake nuni da zallar dukiya da kuma wadatar da ahalin suke ciki.
Kana sanya qafarka abu biyu zaiyi maka maraba, sassanyan ƙamshin turaren da burner ke bayarwa da kuma ƙamshin girkin dake fita a kitchen din gidan dake manne da falon qarqashin stairs din. "Ummiee" ta ƙara faɗa muryarta na rauni kamar ana ja da ita. Idanunta suka cika da ƙwalla, zuciyarta na ambaton kewar da ta jima tana ɗauke da ita, wadda yanzu ta kai ƙololuwar da ba zata iya ɓoyewa ba.
Tun jiya aka ce mata Ummiee zata dawo, kuma tun jiya zuciyarta ta kasa sukuni. Sai yanzu ta tabbata babu wanda zai iya maye gurbin Ummiee a rayuwarta.
Dattijuwar mata ce ta fito daga cikin kitchen tana faɗin "Har kin taso?" juyawa tayi inda taji maganar bata fuska tayi tare da ɗaga mata kai hawaye na gangaro wa daga idanunta "uhmm-uhmm Aamanee" "Karki ɓata ranki Ummiee tana ɗaki, ta dawo ɗazu"
Da ƙyar ta sakar da ɗan murmushi, ta goge hawayen da suka jiƙa gefen kyakkyawar fuskarta "Hajjaa barka da gida" tace tana wucewa da sauri. Girgiza kai kawai Hajjaa tayi tare da cewa "Allah ya shirya ki Aamanee" tana komawa kitchen ɗin.
Tsararrren corridor wanda ya ƙawatu da wasu gold leaf picture frames, fentinsa olive green ne, kalar da ta dace da wajen sosai daya ƙawatu da fitilu masu haske tarwai, sai flowers a maƙale a kowacce corner daga jikin bango, wanda suke bada qamshi na musamman da kuma samun kyakkyawar iska fiye da iskar da na'urar AC dake kafe a wajen zata bayar.
Ƙofofin dakunan bacci ne guda biyu a wajen, kowacce da ɗan taƙi kaɗan daga qofar dake kusa da ita, ƙofar dake hannun dama ta murɗa sallama ɗauke a bakin ta.
Matshiyar mace ce da ba zata haura shekaru talatin da biyar ba zaune akan sallaya da charbi a hannunta tana ja, kaɗan ta waiwayo tana kallonta tare da sakar mata ƙaramin murmushi haɗi da amsa sallamar "Baby kin dawo?, Ya karatun?"
"Ummiee" Aamanee ta nufi gareta da gudu, ta faɗa jikinta kamar zata nitse, tana ƙara sakin hawayenta da bata samu damar fitarwa ba tun jiya.
Ummiee ta rungume ta gam, hannayenta biyu na bubbuga bayanta cikin salon rarrashi, tamkar ana ƙoƙarin kwantar da zuciyar jaririya da ke kuka bayan ta faɗi. Tana jin yadda numfashin Aamanee ke fita da huci-huci kamar wacce aka ɗaure da kewar shekara.
"Shhh Baby, Ummiee'n ki na nan. Na dawo kin ji? Kiyi hakuri da kewar da kika sha."
Aamanee ba ta ce komai ba, sai ƙara shigewa jikinta da tayi, kamar tana son ta huce da kansa cikin ƙirjin mahaifiyarta.
“Na kira ki, na kira ki sau ba adadi Ummiee amma ba ki amsa ba” ta faɗa muryar ta a karye.
Ɗago fuskarta Ummiee tayi tana share mata hawayen dake kwance da yatsanta, ta share mata hawaye, tana kallonta idanu da suka cika da tausayin zuciyar ‘yarta. “Aamanee, Ummiee ba ta da niyyar barinki da damuwa haka. Garin babu network ko kaɗan”
“Na sani” ta ce, tana gyara zaman kanta a gefen kafaɗar mahaifiyarta. “Amma ban taɓa jin gidan nan ya zama haka ba, kamar babu rai cikinsa, sai da kika dawo nake jin iska tana ƙamshi.”
Murmushi Ummiee tayi amma murmushin da ya zo ne da tauna zuciya. Ta san cewa ‘yarta ta fara girma, ta fara fahimtar banbanci tsakanin zama tare da uwa da kuma rashin hakan. Ta bubbuga kanta kaɗan, sannan ta ce "Wannan shine gidan mu Aamanee, kuma in har kina ciki, to ina jin kamar bana rabuwa da shi ko kadan. Sai dai idan ba da ke ba. Ki fahimci cewa komai nake yi ko tafiya ce, ko dawowa ce duka don ke ne. Don gaba ki zauna cikin nutsuwa, karki ji kamar duniya ta cuce ki."
Aamanee ta ɗago kai, idanunta sun yi jajir, amma zuciyarta ta fara samun sauƙi. "Ummiee, zaki kara tafiya ne?"
Shiru ta ɗan yi, tana kallon ƴarta, sannan ta ce da taushi, "Zan dinga tafiya, amma ba zan bar ki cikin duhu ba. Zaki dinga ji kaman ina tare da ke, ko da ba ki ganina ba. Zan bar miki rubuce-rubuce da sakonni, zan kira ki fiye da da."
Shiru tayi bata ƙara cewa komai ba, can Ummiee ta kara ce "Aamanee tashi ki cire Uniform ɗin nan, kiyi wanka da Sallah" bata ce komai ba ta miƙe ta shige toilet dake cikin ɗakin bata jima ba fito ɗaure da towel da sauri-sauri ta shiya tayi salla, kusa da Ummiee ta dawo suka cigaba da hira...
◆◇◆◇◆◇◆◇
◆◇◆◇◆◇◆◇
◆◇◆◇◆◇◆◇
Zaune suke ita da Aamanee a palour Assignment da aka bata suke yi hankali kwance
"Salamu alaikum" yace fuskar sa na ɗauke da alamun gajiya.
Muryar tasa ta katse masu karatu, ɗago kai tayi ta kalle shi, idonta ya hango wani abu daban "Wa’alaikumus salam, Sannu da dawowa Allah yasa lafiya dai?” Ta tambaya, tana kokarin fahimtar natsuwarsa. Zama yayi ba tare da ya kalli idonta ba a kujerar dake facing nasu, sannan ya janyo numfashi kamar mai shirin zayyano hukunci. Bata ƙara ce masa komai ba ta miƙe ta shiga kitchen, ba jimawa ta fito hannun ta ɗauke da tray yana ɗauke da ruwa da kofi a kai tana ajiye masa .
"Abby sannu da dawowa" Aamanee tace tana miƙe wa "Yauwa Sweetheart, aiki ake yi?" Kai ta jinjina masa ba tare da tace da shi komai ba ta ruga stairs a guje.
Zama Ummiee tayi daga gefen sa, yana wasa da car key da ke hannunsa.
"Amina ashe kin dawo" "Eh tun safe, na kira wayar ka baya tafiya, nayi zaton zaka dawo da wuri ma" ta faɗa tana kallon ƙwayar idanunsa
"Aiki ne yayi min yawa, ya kin samo?"
Shiru tayi tana tunanin yadda zata sanar da shi abinda ta tarar tasan ba lallai ya fahimce ta ba wani irin bahagon mutum ne abu kaɗan ne yake fusata shi "kinyi shiru ina ta magana baki ce komai ba" muryar Abby ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi "Alhaji ba'a dace ba, na tarar su Kawu Lurwanu sun ari kuɗin an zuba a gona"
"Ku***mar Uban can, da izin wa suka juya kuɗin naki?" Ya faɗa a zafafe.
A matuƙar ruɗani ta kalle shi jin furucin da yayi, ƙasa tayi da muryarta tana cewa "Alhaji dani da duk abinda na mallaka duk ƙarƙashin ikon su suke, suna da hakki a kai na tunda su suka riƙe ni tun ban san kai na ba, kuma..."
"Ya ishe ki haka Amina" ya faɗa a tsawace yana miƙewa "To ki sani har yanzu sharaɗina na da yana nan, in har baki karɓo min kuɗi nan ba zamu bar gidan nan" "bari in sanar da ke na siyar da gidan nan”
Shiru ɗakin ya ɗauka, Idan aka ce ana jin nauyin iska, yau ta tabbata. Ummiee ta kasa fahimtar kalmar da ya furta. Kamar ba Hausa ba ce.
"K… kace me Alhaji?" Ta faɗa da wata murya da ba ita ta saba ba, murya mai cike da rikicewa.
"Na siyar da gidan. Za mu tashi nan da mako guda, masu gida na buƙata tunda baki karɓo kuɗin ba"
Zuciyarta ce ta fara rawar jiki. Tamkar an saukar mata da dutse mai zafi a ƙirji.
“Na san baki ji daɗin ba, amma ba zan iya ci gaba da riƙe shi ba. Kuɗin gidan yana da amfani. Daga baya sai mu…”
Da sauri ta katsa shi tana cewa “A'a! Don Allah ka tsaya anan. Gidan nan? Gidan da na kafu da shi? Gidan da nake ganin shi tamkar mafaka ce gare ni da Aamanee? Gidan da ke da tarihi masu yawa?”
Hawayen da suka daɗe suna ɓoyuwa suka fara silala, sun fi ƙarfin da idanu za su iya riƙewa. Ta miƙe tsaye kamar wacce aka tsayar da zuciyarta cak. Da ƙyar ta iya haɗo kalmomi tare da cewa “Ka yi min haka? Ka yi mana haka? Me muka yi maka?”
Idonta ya bushe da hawaye, amma zuciyarta ta ƙone. Ƙahon tashin hankali ne ya hango ƙofar zuciyarta. Ta tsaya gaban shi tana numfashi sama-sama, kamar wacce ta tsinci kanta a ƙasan da ba ta san mafita ba.
“Ina zamu? Me zamu ce wa Aamanee? Wane gida za mu kai ta da ita zata ji kamar nata ne?”
Abby kuwa kamar dutse ne a kansa, ya kasa ɗagowa, Ya sunkuyar da kai kamar wanda ya rasa mafita, yana jin kalmomin ta kamar ƙugiya ne a kunnensa.
Aamanee daga sama tana leƙen bene. Ba ta gane komai ba, amma muryar Ummiee ta faɗi da kuka da shigewar mahaifinta cikin shiru ya isa ya gaya mata wani abu na faruwa, zuciyar ta na sanar mata "Tabbas Rayuwa zata sauya."
____________
💭 #TunaninƘarshe 💔🌒
*Zuciyar mace na iya jure ɓacin rai, amma idan aka tsinke tushen ta, me ya rage?*
Comments,✨React🙃 & Share🙌😊 mutanen amana*
*Kamar ko yaushe ƙofar ƙorafi, gyara ko shawara a buɗe take a ko da yaushe🥰🤍*
~0707779141~
*Fateyzahraah✍️*