Matar Khalees

Matar Khalees

by @nusybee143

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 13

A hargitse umaima ta shiga ɗakin Nadiya tana faɗin"ƙawa!ashe wannan shegiyar likitar tana nan?tsinanniya masifaffiya"

Nadiya tace"rabu da ita,ai dole ta tafi tunda dai ba gidan ubanta bane"

Mima bata juma ba ta wuce gida,tana fita Deeja tayi saurin datse ɗakin ta da makulli,kamar ta sani kuwa,motar Mima na barin gidan su umaima suka zo suka fara buga mata ƙofa,cikin sauri ta ɗauko airpiece ta kunna Suratu Yusuf a wayar ta ta toshe kunnen ta, a haka bacci yayi awon gaba da ita

Washe gari a kitchen ta Samu amarya da ango,cikin shauƙin soyayya suke sarrafa abinda zasu ci,ta sha mamakin ganin Khalees ko kallon ta baiyi ba,amma ta dake tace

"Yallaɓai ina kwana"

Ya waigo yana kallon ta kamar mai yin mamaki,sannan yace"lafiya,bazaki gaida amarya ba?"

Wani watsatstsen kallo tabi amaryar dashi kafin tace"amarya ina gajiya?"

Cikin salon kissa Nadiya tace"gajiya kam babu ita bata da muhalli, saboda na mallaki gwarzon namiji Ni kaɗai,ya zama nawa"

Wani malalacin murmushi Deeja tayi,sannan ta ɗaga babban ɗan yatsan hannun ta alamar jinjina tace

"Ina taya ki murna,kuma na sara miki babbar mace"tana gama faɗin hakan ta ɗauki abin da ya kawo ta tayi hanzarin barin kitchen ɗin

Abin yazowa nadiya a bazata,don tayi tsammanin zata ƙuntata ran Deejan amma sai taga akasin haka,don haka ta bi ta da ido zuciyar ta cike da ƙunci

Duk da hakan ya ɓata wa Deeja rai amma sai tayi ƙoƙarin dannewa,ta shirya ta karya sannan ta fice zuwa office

Daga office gidan barrister zee ta wuce,zee ta rinƙa tausar ta,tare da ƙara jaddada mata ta riƙi addu'a,kuma sam kada ta daina bawa mijin ta kulawa,anan ta yini har bayan la'asar sannan ta koma gida

A falo ta iske su, Nadiya ta kwanta a jikin shi tana ta zuba masa shagwaɓa,shi kuwa duk yabi ya ruɗe,ta shigo da sallama,amma babu wanda ya amsa,itama sai ta ɗauke kanta da nufin faɗa wa ɗakin ta

"Ke dakata!"a cewar Khalees

Cak ta tsaya batare da ta juyo ba,bai damu ba yace"daga ina kike?"

"Daga office,da na taso sai naga ya kamata na bawa amarya da ango waje su sake,don haka nima nayi nawa wuri"ta bashi amsa

"Tabbas kinyi tunani mai kyau"a cewar Nadiya

Deeja ta kalle ta sannan tace"ai ni koyaushe tunani na mai kyau ne,bana abu mara kyau,ba kamar sauran gama garin mutane nake ba,ina fatan kin gane"bata jira amsar ta ba ta shige ɗakin ta

Nadiya tana mamakin Deeja,amma idan ta san wata ai bata san wata ba,dole a haɗa da asiri da tuggu don ganin bayan ta,don haka ta ɗaga kai ta kalli Khalees cikin kissa tana faɗin

"Love da alama gidan ka yafi ƙarfin ka ko?"ya kalle ta cikin kulawa tare da faɗin"me kika gani?"

"Ace kamar ka da kuɗin ka da martabar ka amma ace matar ka tana fita aiki?me za'ayi tunani kenan?baka bata abinci kenan fa,wannan ai sai ya zubar maka da mutunci"ta tsare shi da idanu don ganin yanayin shi

Shiru yayi kafin daga bisani ya gyaɗa kai yana faɗin"zancen ki gaskiya ne love,dole nayiwa tufkar hanci"

Wani sanyin daɗi ya ratsa Nadiya,ta sake gyara kwanciyar ta tana faɗin"Weldone my love,lallai ka cika jarumin maza"yayi wani murmushin nuna jin daɗi yana kallon ta

A ɗaki ya samu Deeja tana danne-danne a laptop ɗin ta,ganin yadda ya shigo mata fuska babu rahama ya sanya itama ta dake ta sha mur, tun daga amsa sallamar shi bata sake duban inda yake ba,shima bai damu ba ya dube ta yana faɗin

"Ban amince miki ki qara fita aiki a gidan nan ba, saboda ba zaman kanki kikeyi ba,da fatan kin gane"yana gama faɗin"hakan ya juya ya fice daga ɗakin

Ta ɗan bi shi da kallo,kafin tayi ɗan murmushi,ta sani sarai aikin Nadiya ne,ai kuwa zata basu mamaki

Washegari ta fito cikin shirin riga da zani na lace,ta ɗora ƙaton mayafin ta a kanta, hannun ta rataye da jakar ta

Yau ma kamar kullum a falo ta tarar dasu suna ciyar da junan su abinci,ko kallon banza basu ishe ta ba tayi hanyar fita

"Ke dakata!"taji Muryar Khalees a fusace

Ta juyo fuskar ta babu alamar damuwa,ta zuba masa ido tana jiran mei zai ce

"Ina zakije?"ya tambaye ta

"Idon ta fes cikin nashi ta amsa"in da na saba zuwa,wato wajen aiki"

"To ban bada izini ba"

Ai dama ba kai ka bani izini na fara aikin ba

"To sai ki zaɓi ɗaya,auren ki ko aikin ki?

Maganar ta dake ta sannan ta qara jinjina wa kaidin Nadiya,Amma da yake jaruma ce idanun ta fes cikin nashi kanta tsaye ta amsa"na zaɓi aiki na"

Ba Khalees ba,hatta Nadiya ta tsorata da jin furucin Deeja, Deeja bata kula ba ta juya ta fice daga falon

Da shirin ta ta dawo daga wajen aiki,a nufin ta duk abinda Khalees zai yi mata ta tanadi abinda zata mayar masa,sai dai ko da ya dawo ko kallon sashen ɗakin Deejan bai yi ba

A haka rayuwa ta kasance musu har zuwa tsawon sati biyu, Nadiya da umaima babu irin asiri da tuggu da basuyiwa Deeja ba amma a banza,duk da anyi nasarar raba ta da mijin ta, tsakanin ta dashi sai kallo daga nesa,amma Allah ya cire mata damuwar hakan

Da farko su Farida suna kawo mata ziyara suna ɗebe mata kewa,amma sai da Nadiya tayi tuggun da Khalees ya hana su zuwa,hakan bai dame ta ba don sau tari ta kan je gidan hajiyan suyi hira,hajiyar tayi ta mata nasihohi da ƙarfafa mata gwiwa

#Nusy_bee