WUTAR ƘAIƘAYI

Page 13

by @sanazty

WUTAR ƘAIƘAYI

Wattpad@SaNazdeeyah_

_Arewabooks@sanazty

Facebook@SaNaz Deeyah

Youtube: ***

Facebook Page: ***

KARAMCI WRITERS ASSOCIATION

[karamci tushen mu'amula ta gari]

Book 1

```🆓Page 13```

Da yatsa ya nuna ta tare da cewa "Ki shiga hankalinki, rashin mutuncin na ki ya tsaya iya ni kada ki yarda ki sako mahaifiyata a ciki." Kallonsa take sai kuma cikin ɓacin rai ta fuzgi Fu'ad ta yi gaba.

Tsawon sati ɗaya sam basu kula juna, har ya saba da cin abinci a waje kafin ya dawo gida, da dare kuma sai dai yaje side ɗin Mommy ya yi dinner dasu ko kuma ya saka Lawisa tayi masa abinda yake so, dan baya son cin abincin masu aiki. Yau bayan sun gama cin abinci Mommy ta dakatar da shi, "Affan lafiya dai?"

"Mommy lafiya ƙalau" "A'a Affan karka ɓoye min, ni fa mahaifiyarka ce, naga kwana biyu anan kake dinner at times har da breakfast, sannan kuma ita kanta Badriyya ina kula da ita yau kwana biyu bata zo ta gaishe dani ba, hakan ya nuna bata ɗaukeni a matsayin uwa ba."

Shiru ya ɗan biyo baya kafin ya ce, "Mommy kiyi haƙuri, kin san na fara bincike akan kisan yaron da aka yi, so ni kaina ba a nutse nake ba, ko baccin kirki bana yi, amma ban san cewa Badriyya bata shigowa ba, Mommy tun ranar dana sanar mata an saka ranar bikina da Nashwa ta fara wannan gabar dani, ni kuma aikin da nake ne ya saka ban biye mata ba."

"Matar ka ba mace bace Affan, sam baka yi sa'ar mata ba, sai dai fatan Allah yasa wannan auren da zakayi ya zama alheri ya sa matarka ta so ka ta kuma kula da kai" Shiru ya yi bai iya cewa komai ba. "Ka je kawai, da safe kafin ka wuce kazo zamu ƙarasa magana"

"To Mommy" Sallama ya yi musu sannan ya wuce.

Yana kwance a gado ta banko ƙofar har sai daya furgita dan lokacin bacci ya fara ɗaukarsa. "Lafiya kuwa?"

"Ba lafiya ba, Affan wallahi indai ina da rai ba zaka ƙara aure ba" Ƙafafuwan shi ya zuro ƙasa lokacin da take faɗin "Sai dai bayan ranka ko nawa ran." "Badriyya ko dai kin sha wani abin?"

"Babu abin da na sha amma wallahi ba zan taɓa bari na haɗa miji da wata banza ba, saboda kar ka kusanci wata macen na rabu da duk ƙawayena, duk wata mace da na san ba muharramarka bace bana yarda tazo gidana, sai kuma kawai yanzu kace zaka ƙara aure to wallahi sai dai ayi mutuwar kasko, ni da ita mu rasa gabaɗaya" Sai lokacin ta ɗago hannunta ya ga wuƙa, dan bai lura da ita a hannunta ba.

"Me kike ƙoƙarin aikatawa ne?"

"Kisa, zan kasheka in kuma kashe kaina" Ta furta tare da fashewa da kuka kuma ta nufo shi da wuƙar a hannu, cikin zafin nama ya riƙo hannun suka fara kokawa har sai da ta yankeshi a hannun hagu da ƙyar ya samu ya ƙwace wuƙar daga hannunta tare da kifa mata mari. A gurin ta zube tana kuka, shi kuma da sauri ya fita saboda yadda hannun ke zubar jini da alamu a jijiya ta yanke shi, a haka ya ƙarasa side ɗin Mommy har sun kulle ya yi ta bugawa.

A parlour Mommy da Lawisa suka yi kiciɓus, "Mommy waye haka a daren nan?"

"Ina zan sani ni har na fara bacci bugun ƙofar ne ya tayar dani." "Mommy jira anan bari na ji ko waye"

"Kar dai ki buɗe sai kin tabbatar da mai bugun ƙofar" Kai ta gyaɗa sannan ta ƙarasa jikin ƙofar. "Waye"

"Affan ne buɗe Lawisa." Jin haka ya saka ta buɗe da sauri, kasancewar barandar da haske ya saka ta ga jinin a ƙasa yana ɗiga kafin taga hannunsa daya riƙe gam "Subhanalillahi" Ta furta tana zaro ido, lokacin kuma Mommy ta ƙaraso.

"Yaya Affan lafiya? Mene haka"

"Me kika tsaya tambaya kina gani yana zubar da jini, maza ɗauko box kiyi masa dressing" Mommy ta janyoshi ciki sannan ta mayar da ƙofar ta yi mata key.

Lawisa na gama yi masa dressing ya jingina bayansa da kujera tare da lumshe ido. "Affan!" Mommy ta kira sunansa, a hankali ya buɗe ido ya kalleta. "Waye ya maka wannan? Gidan dai babu alamun 'yan fashi sun shigo"

"Mommy ku kwanta kawai da safe sai mu yi maganar, ni zan kwana anan kan kujera"

"Duk ɗakunan gidan nan ace ka kwana a kujera, ko babu extra room ai ka kwana a ɗakina bare ma akwai. Kuma ka san ba zan iya bacci ko kuma sa mun nutsuwa ba tare da ka faɗa min abinda ya faru ba."

Bai ɓoye komai ba ya faɗa musu, Mommy ta hasala sosai ta kuma ce lallai sai taje part ɗinsu a daren, da ƙyar Lawisa ta hanata saboda time ɗin ɗaya har da mintuna shidda, ta ce mata dan Allah koma mene a barwa safiya. Ranar Mommy bata samu bacci ba, sai dai shi Affan ya yi bacci saboda allura da Lawisa ta masa, Mommy kuwa tausayinsa kawai take, a ɗakinta ya kwana, ta kuma kwana tana nafila tare da yiwa Affan fatan samun mace ta gari.

06:30am

Kamar a mafarki ta riƙa jiyo bugu, a hankali ta buɗe ido, ganinta ta yi anan kwance dandan ƙasa, tunda Affan ya mareta ya fita tasha kuka, ta kuma raba dare tana kuka bata farka ba sai wannan bugun ƙofar ne ya tasheta, in da Allah ya taimaka ma tana cikin jinin al'ada da ta makara sallar asuba. Jiki babu ƙwari haka ta ƙarasa jikin ƙofar a buɗe ma take kawai dai an tura ne, tana buɗewa ta ji saukar mari har biyu a kumatu guda, aikuwa har sai da hawayen dole ya zubo saboda azabar marin, ji tayi an fuzgi hannunta an fita da ita sai lokacin ta ga Mommy ce, hankalinta ya tashi sosai. Mommy kuwa bata sake ta ba sai a ɗakinta inda Affan yake kwance. "Gashi nan ki kashe shi" Jin haka ya saka ta fashe da kuka mara sauti, ta saka hannu ta rufe baki lokacin da hawaye suke ambaliya a fuskarta.

"Kin san kisa ko? Za ki iya kisa saboda za a miki kishiya ko? To ki sani Affan aurensa babu fashi in ya so ga shi nan ki kashe sa, idan baki iya zama ki tafi mana ko an miki dole ne?" Kan ta a ƙasa ta kasa cewa komai sai hawaye kawai. "Tun da Affan ya aureki bai huta ba, dubi yadda kika mayar min da ɗa, duk kin bi ki zabura shi, wannan wace irin masifa ce ya ɗauko mana, kara nake miki amma ba wai dan ban san abubuwan dake faruwa ba, ana aure dan a jidaɗi amma shi Affan yana aurenki jindaɗi ya yanke masa" Mommy faɗa kawai take ta in da take shiga ba ta nan take fita ba, sai da ta gama tas sannan ta ce,"Ki tashi ki ɓace min da gani, kuma ki kira wani a cikin masu aiki a goge duk inda jini ya ɗiga." Da sauri ta tashi ta fice "Shashasha."

Tana haɗa kaya tana kuka a haka Lawisa ta sa me ta. "Wannan ba mafita bane Aunty Badriyya." Ɗagowa ta yi idanunta a jiƙe da hawaye ta ce, "Lawisa wallahi idan na zauna komai zai iya faruwa"

"E ki dai zauna ɗin, amma kin san tafiyarki za ta iya ƙara tunzura Mommy tunda har yanzu cikin fushi take" Zama ta yi gefen gadon ta saka hannu ta rufe fuskarta, Lawisa a hankali ta ƙarasa gabanta tare da dafa kafaɗarta. "Aunty wallahi Yaya har yanzu yana ƙaunarki you're his favorite, koda Mommy ta saka ya auri Nashwa kawai tausayin maraicin ta ya saka ta yi haka ba wai dan ba ta sonki ba, dan Allah karki yi abinda za ki ja Mommy ta tsaneki"

"Idan har Affan yana so na meyasa ya karɓi tayin auren Nashwa?"

"Saboda ya farantawa Mommy, ita kanta Mommy ba dan ta ƙuntata miki ta yi hakan ba." Haka dai Lawisa ta yi ya rarrashi har Badriyya ta janye maganar zuwa gida, Lawisa da kanta ta mayar mata kayan cikin wardrobe.

*11:00am*

Yana shigowa ta kafe shi da ido, ko amsa sallamarsa bata yi ba bare ya samu damar da zata kula shi, ya ƙarasa kujerar da take ya zauna a gefenta sai ta yi sauri ta miƙe tare da canja kujera. Murmushi ya yi sannan ya ce, "Ina so na yi magana da ke." Ba ta ba shi amsa ba, ya cigaba da cewa, "Badriyya ina sonki, wallahi da gaske ina son ki, kuma har yanzu ina son ki" Baki kawai ta taɓe tana jin ɓacin rai na ƙaruwa. "Na san kuma kema kina sona tun da har baki son kowa ya raɓeni, ki sani wallahi a abubuwan da kike min in wani ne da tuni ya ƙara aure ko kuma ya rabu dake, sai dai ni ina duba ƙaunar da kike min da ita nake miki uzuri. Badriyya, Nashwa ba ta da matsala ni na tabbatar zuwanta gidan nan ba....."

"Hold on da Allah, ka ga Affan idan maganar waccan yarinyar za ka yi zan tashi ne in tafi karka sake yi min maganarta saboda na tsaneta kuma kome zaka faɗa ba zan taɓa ƙaunarta ba koda na second ɗaya ne." "Amma ki sani wannan abubuwan da kike yi jahilci ne."

"Ka faɗa kanka tsaye Affan, ka ce ni jahila ce ba sai ka tsaya kana kwaskwarima ba." "Hmmm! Ban san haka kike ba, gabaɗaya gani nake kamar canjo min ke aka yi"

"Ai fiye da haka ma zaka gani muddin baka janye maganar auren nan ba to wallahi kisa ne ƙarshen ta sai dai a shigo da gawarta gidan nan." Tana gama faɗa ya yi daidai da shigowar Mommy da Lawisa wanda a kunnensu suka ji furucinta na ƙarshe.

"Gawa kuwa wataƙila taki za a fitar a nan gidan, ki sani zan ajiye surukuntaka in kashe ki a duk ranar dana shigo na iske kin kashe min ɗa, ba zan bari hukuma ta ɗauki mataki ba saboda na san za a barki ne ki cigaba da shaƙar iskar duniya saboda yanzu ba a kashe wanda ya kashe, to ni kuma a lokacin za a bugani a jarida da sunan na kashe matar ɗana."

"Mommy..."

"Ka rufa min baki Affan, ba zan zuba ido ana wannan shashancin a gabana ba, shiyasa tun jiya na ce ka sawwaƙe mata amma shegen baƙin na ci ya hanaka, to wallahi ba zan lamunta ba." Tana gama faɗa ta wuce, Lawisa da ido kawai take bin Badriyya da kallo, kenan duk irin nasihar da ta yi mata bata ratsata ba.

****** ******

Kallon ciwon ta yi wanda har ya warke. "Yaya ko dai zamu haƙura da juna?" Murmushi ya yi sannan ya ce "Saboda wannan ɗan ciwon?"

"A'a ba dan shi ba, ka san nima Aunty Badriyya tana kirana tana kuma min gargaɗi a kanka"

"Oh wai bata daina ba?" "E, amma ban faɗa ba dan ka mata faɗa dan Allah"

"Ina ɗaga mata ƙafa ne kawai saboda wannan aikin da nake."

Kallon takardun tayi sannan ta ɗauka. "Habu Labbo Bala" Ta furta a fili tare da zaro ido. "Wannan ba ɗan takarar senator bane?"

"Shi ne"

"To me ya yi?" Gyara zama ya yi sannan ya ce "Wata biyu da suka wuce akwai wani yaro ɗan tiktok da ya fito ya yi magana akan 'yan siyasa har ya ce zai tona asirin 'yan siyasa guda biyar ya kuma lissafo sunayensu, kwana biyu da yin abin aka nemi yaron aka rasa kuma har yau babu labarinsa, jami'an tsaro sun yi burus da lamarin kasancewar ɗan talaka ne ya yi ɓatan dabo, to mu kuma 'yan jarida mun ƙi mu haƙura shi ne muka shiga rigar 'yan sanda"

"To amma meyasa sai Labbo Bala kaɗai?"

"Ba fa abinda ya kamata ki sani bane, ki bari idan komai ya bayyana za ki ji, amma maganar gaskiya dukkansu mun yi bincike akai sai dai zarginmu yafi karkata a kan sa, yanzu ma da na saukeki a gida zan je in cigaba da aikin bincike ne."

"Yaya yamma ta yi fa, ya kamata kaje gida ka huta"

"Hutu ba nawa bane a yanzu Nashwa, yawwa ina son inji nawa zan baki na event ɗin?" Ya faɗa dan ya kawar da waccan maganar.

"E to! Hall already an kama kuma ka bayar da kuɗin komai, sai na lalle da gyaran gashi"

"Okay zan tura miki ta account"

"Zuwa next week zan wuce kano, yaushe zaku shigo?"

"E to ina tunanin ranar dinner"

"Yanzu har sai na kai wannan lokacin ban gan ka ba?"

"Kwantar da hankalinki, keda zan ɗauko ki na kawoki gidana ki riƙa gani na kullum" Hannu ta saka ta rufe fuska, ya yi murmushi tare da faɗin "Nashwa akwai kunya" Ɗan lumshe ido ta yi tare da janye hannun.

"Yaya duk ranar dana haihu ace wannan ɗana ne, kuma wanda muka haifa ni da kai, to gaskiya ban san irin farin cikin da zan yi ba. Ji zan yi duk duniya na fi kowa sa'a da ina ganin kamar ranar ba zata zo ba"

"Kamar yau ne Nashwa, insha Allah za ki ga yaranki"

"Allah yasa"

"Amin." A gida ya sauketa, sai dai yana wuce wa Allah ya kawo mata empty napep ta tara ta ce yabi bayan Affan amma karya bari ya sani.

Ganin sun nufi bayan gari abin ya bata mamaki, ta fito da wayarta tana ɗaukar guraren da suke wucewa, sai da suka shiga wata doguwar hanyar da babu titi sannan taga ya parker mota, ta yi saurin fita ta ɗauki 10k ta miƙawa ɗan napep ta ce ya juya da sauri dan ta san Affan zai iya cewa a juya da ita, yana juyawa Affan ya juyo a tsorace, ganin Nashwa abin ya matuƙar ba shi mamaki" Da sauri ya ƙarasa gabanta "Meyasa kika biyoni?" "Saboda ba zan iya barinka a halin nan ba" "Wane hali? Zuwanki nan akwai risk, shiga mota muje"

"Muje ina? Kawai mu ƙarasa zan iya tayaka aikin."

"Su waye nan" Jin magana da ƙarfi ya saka suka ɗaga ido, han go bodyguards ɗin Labbo Bala suka yi, sun saito bindiga. "Na shiga uku" Nashwa ta faɗa tare da fashewa da kuka. "Ki shiga mota" Ya furta lokacin da bodyguards ɗin suka yo kansu su huɗu. "Bindiga ce Affan kawai mu miƙa kai." Ganin za ta ɓata masa lokaci ya saka ya fuzgeta yana buɗa motar aka harba bindiga.

Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting.

VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:

Guda 1: ₦500

Guda 2: ₦900

Guda 3: ₦1400

Guda 4: ₦ 1800

Za'a turo kuɗin ta wannan account.

Acct no: 6370370016

Acct name: Halima Salahu Adamu

Bank name: Fidelity Bank

Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number ***

Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number ***.

Shaidar biya ta wannan wannan number ***

lLITTAFAN SUNE:

1-WUTAR ƘAIƘAYI

2-WA'ADI.

3-A CIKIN IDO..

4-TAZARAR SO

#FITATTUHUƊU2025

#WUTARƘAIƘAYI

#SaNaz_deeyah