KUDIRAR ALLAH

2

by @nazeefanashe

K’UDIRAR ALLAH

P2.

NAZEEFAH SABO NASHE✍🏽

Wattpad Nazeefah381

ArewaBooks’s @Nazeefah

***.

Bin motar Haidar ya yi da kallo kafin ya saki sassauk’ar ajiyar zuciya yana lumshe idonsa wani irin zafi da turiri yake jin zuciyar sa take yi, duk da k’ok’arin danne b’acin ran da yake yi hakan bai hana bayyanuwar b’acin ran akan kyakykyawar fuskarsa ba. Tausayin kansa ya sake mama ye shi kafin ya d’au hanyar da zata sada shi da ainahin cikin Gidan direct.

Faffad’ar haraba ce mai girman gaske fiye da ta wajen da ake ajiye motoci. Bakomai a harabar sai manyan bishiyu da suka yiwa tsakargidan ado da inuwa mai k’ayatuwa a idanun mai kallo. Yanayin damuna da ake ciki ya sake k’awata wajen baka sha’kar komai sai k’amshin tarin bishiyun da suke cikin harabar lemon tsami guava mango da sauran dangoginsu. Ya sake mai da hankalinsa kan k’ofar da zata kai shi sashen da Umma take marik’iyarsa inda anan aka warewa tasa mahaifiyar nata d’akin mai d’auke da parlour da toilet aka kuma saka mata duk wani abin more rayuwa duk da zamantowarta mara hankali bai hanata tsaftace d’akin ba idan ka shiga zata zaka yi mai cikakken hankali ce mamallakin sashen.

Umma da take zaune a babban parlourn da ya raba sashenta da na Mahaifiyar Jaheed d’in ta bi shi da kallo murmushin kan fuskarta na sake yalwata ta ce “Ka dawo kenan Mujaheed?” Shi d’in ma murmushin da kai tsaye za’a kira na k’arfin hali ya saki yana d’aga mata kai kafin ya rusuna ya gaisheta. Ta amsa masa cike da kulawa saboda yarda take jin Jaheed d’in kamar ita ta durk’usa ta haifesa bata banbance soyayyar sa da ta nata y’ay’an data tsuguna ta haifesu abu d’aya ta sani Ba ita ta yi nak’udarsa da shayar da shi amma duk wata hidima da Uwa take wa d’anta ita ta yiwa Jaheed, shayarwa ce dai a hakan a haukar Uwarsa ita ta shayar da shi, abin mamaki yarda take ba shi kulawa ba zaka ce k’wak’walwarta da motsi ba duk da akwai wani keb’antaccen sirri da ita ka’dai ce ta sani.

Jaheed ya dubi Najwa yana fa’din “Najee samo min ruwa.” Da sauri ta mik’e don a rayuwarta tana girmama lamarin Jaheed da kuma duk wata hidima data danganceshi, yarda take son sa bata jin tana son nata jinin haka. Ruwan mai sanyi ta d’auko a fridge d’in da yake dinning area d’in Umma. Ta kawo masa a k’aramin tray. Bai bi ta kan cup d’in da take mik’a masa ba ya b’alle murfin ruwan ya fara kwankwa’da. Sai da ya shanye tas kamar ruwan ne zai tafi da bak’in cikin da ya masa dafifi a zuciyarsa sannan ya ajiye robar yana sakin huci a hankali. Umma murmushi ta saki ganin yarda yake wayancewa wajen son kawar da b’acin ran da ya kasa b’oyuwa a fuskarsa ba duk da k’ok’arin danne shi da yake. Ta fi kowa sanin Jaheed da halayensa kaf idan yana cikin farin ciki ta sani kamar yarda idan yana cikin b’acin rai duk k’ok’arin sa da son danne b’acin ransa hakan baya b’oyuwa gareta a k’wayar idanunsa take banbance halin da yake ciki, don haka cikin raunin murya ta dubeshi tana furta “Sun ce ka turo ko?” Da sauri Jaheed ya d’ago yana kallonta cikin mamakin jin abinda ta ce, ya yi mamaki k’warai da gaske da har ta gano abinda yake ciki, kamar ya ce mata ya aka yi kika gane sai dai ya ja bakinsa ya tsuke yana duban T.V ha’de da ‘d’aga kai a hankali muryarsa ta kasa b’oye b’acin ran da yake ciki saboda yarda ta raunana ya ce “Sun ce Umma.” Sakin ajiyar zuciya ta yi tana furta “Kada ka damu wannan karan za’a dace In sha Allah, abin buk’ata ka dage da addu’a.” Shiru ya yi yana jin sauk’in nauyin da k’irjinsa ya yi, kalamin Ummansa ya sauk’ak’a masa fargabar sa da b’acin ransa. Umma ta dubi Najwa ta ce “Je ki zubo masa abinci daga ganin wannan idon kana jin yunwa.” Murmushi ya saki a hankali yana jin dad’in kulawar da Umma take ba shi har yanzu ganinsa take kamar yaro, ko don bai yi aure bane oho, ko kuma tausayawa irin rayuwar da ya taso a ciki take shine bai sani ba. “Ka ci abinci ka je ka samu Nene ka gaya mata.” Ya

D’aya kai kawai yana mamakin duk sanda irin wannan zata faru sai Umman ta umarceshi da ya gayawa mahaifiyarsa ta kan ce “Ko kallonka ta yi bata maka addu’a ba zai da’da’da maka balle idan ka furta addu’ar itama zata maimaita Allah kuma Zai amsa In sha Allah.” Jaheed murmushi kawai ya saki yana amsar Abincin da Najwa ta zubo masa a plate ganin favorite food d’insa ne Alkubus da miyar taushe yasa ya saki murmushi gefe guda kuma kunun aya ne. Zamewa ya yi ya zauna a kan carpet don yafi ganewa ya ci abinci k’afar sa a tank’washe kuma yafi cin abinci da hannu idan ba’a bak’on waje ba shi yasa sau tari yafi ganewa cin abinci a falon Umma inda zai bararraje ya tsoma hannunsa ya ci son ransa. Ya wanke hannun A wash hand basin da yake dinning area d’in sannan ya dawo ya fara cin abincin yana fa’din “Madalla da Umman mu mai da’din tuwo.” Murmushi Umma ta yi ta ce “Ka hango Alkhbus ba dole Ai ka fara

santi, dama sai kacewa Khairin ta dage ta iya Alkubus mayensa zata aura.” Murmushi ya saki a zuciyarsa yana fatan Allah ya amsa addu’ar Umma yau ya gan shi ga shi ga Khairi a gida d’aya matsayin ma’aurata da yafi kowa murna a duniya don ya tabbata a ranar ba na biyunsa wajen farin ciki, bai san kuma irin godiyar da zai wa Allah ba gani yake ko kwana ya yi yana sallah godiyar ta yi ka’dan. Sai da ya cinye abincin tas ya kuma taune tantak’washin sannan ya yi Hamdala yana duban Najwa da take kallonsa k’asa k’asa, haka kawai Jaheed yake burgeta duk wani abu da ya yi burgeta yake yi, sau tari tana hasasho Mijin da zata aura ya zama mai halaye kamanni da komai irin na Jaheed, tun kan ta san ba d’an uwanta bane da suke ciki d’aya balle yanzu data fara girma sai take auna Jaheed d’in a matsayin Mijin aurenta tun bayan data san ba maharraminta bane. Jaheed ya dubeta yana furta “Zo ki kwashe kwanukan nan, kullum

Baki da aiki sai kallo ya kamata Umma ta fara saka ki aiki Wallahi kada ki tashi baki iya komai ba.” D’an mitsitsin bakinta ta turo kafin cikin shagwab’a ta ce “Kai Ya Jaheed Wallahi ina aiki yau fa ni na yi alkubus d’in nan.” Wani irin waro ido ya yi yana kallonta ba Najwa ba hatta Umma sai da ya sata dariya yana furta “Lie Lie ya mik’e kafin ya kai mata rank’washi a kai ya ce “Mai k’arya dai d’an wuta.” Ta dubi Umma tana furta “Umma gaya masa don Allah ba ni na yi ba?” Umma tana murmushi ta ce “Gobe ya tsaya ki yi a gabansa sai ya tabbatar.” Girgiza kai ya yi yana fa’din “Ah to kin dace tunda kin gado hannun Umma.” Ya fad’a yana tura k’ofar da zata kai shi Inda parlorn Nenensa yake. Najwa zata bi shi Umma ta saka baki ta kirata sau tari ita take hanata binsa musamman a irin wannan lokacin da yake matuk’ar buk’atar d’umin mahaifiyarsa ko dai bata magantu ba idan ya gaya mata damuwarsa Zai ji sauk’i cikin k’irjinsa, don haka ta hanata bin sa Najwan ta dawo tana turo bakinta gaba na jin haushin rashin binsa duk da sonta da hakan don tana son kullum ta dinga ganin Nenen musamman idan suna tare da Jaheed sai ta dinga jin wani irin farin ciki data kan rasa dalili.

A zaune ya tarar da ita tsaf da ita cikin shigar doguwar rigar atamfa jikinta sanye da hijab kamar kullum. Ba abinda zai da ka gane tana hauka sai idanunta idan ta zazzaro maka su sai kuma yanayin yarda take mayar maka da maganar da duk ka furta sai ta maimaita maka kamar mai karatu. Tana ganinsa ta d’ago a fisge tana kallonsa fuskarta na d’an sakin murmushi ka’dan mai bayyana matsayin ta na mahaukaciya. Jaheed murmushi ya saki ya zauna a gefenta kamar yarda ya saba yana kama hannuwanta ya matsa su ka’dan ya ce “Yau Nene ba kya kallo?” Sake maimaita masa abinda ya ce ta yi. Jaheed ya saki ajiyar zuciya yana fatan ranar da Ummansa zata samu waraka ko Zata fa’di inda asalinta da danginta suke ko da wannan ya tsira zai gode wa Allah idan ma bai samu dangin mahaifin nasa ba, fiye da yanzu da bai san kowa nasa ba yake watagangaririya a rayuwa. Idanu ya sauke cikin na Nenen data kafa masa nata idon kamar mai son gano wani abu a cikin idon nasa. Shiru zuwa wani lokaci suna kallon kallo kafin Jaheed ya sauke nasa idon yana furta “Ki yi min addu’a Nene sun ce na turo.” Ta sake maimaita abinda ya ce Jaheed ya d’ago yana kallonta yana mamakin yanayin damuwa da ya gani tattare da ita kamar yarda ta saba a duk sanda zai zo mata da makamanciyar magana irin wannan mamakin hakan yake sosai tunda ya san bata da hankalin da Zata dinga feeling farin ciki ko bak’in ciki a cikin ranta, bai san me yake janyo mata wannan yanayin ba mai bayyana zallar damuwar da take ciki. Idan ba idanunsa ne ya gaya masa ba har tarin k’walla ya gano kwance cikin k’wayar idanunta. Bai ji komai a ransa ba tunda ya san Nenen ba abinda ta sani irin maimaita magana na ta salon haukan kenan da tun tashinsa a haka ya santa. “Allah ya baka abinda kake so Jaheed Allah yasa su baka aurenta Jaheed.” Hakan kuwa da yake so ta furta hakan ta maimaita masa ya saki murmushi har lotsawar hab’arsa tana sake k’aruwa, itama murmushin ta saki tata lotsawar hab’ar na sake bayyyana wanda wannan ne kawai abinda suke kamanceceniya da shi banda haka ba ta inda Jaheed yake kama da ita komansu mabanbanci ne. Kwanciya ya yi a cinyarta yana sakin ajiyar zuciya a hankali kafin ya d’au hannun Nenen ya saka a kansa a duk sanda yake cikin damuwa wannan d’in yana dag cikin abinda yake kawar masa da Rabin damuwarsa. Nenen ta shiga yamutsa masa Sumar kansa tsawon lokaci kafin ya d’ago yana mayar da k’wallar idanunsa da suke zuba ba shiri, a gaban Nene kawai yake iya sakar k’wallarsa ta zuba bai damu ba banda haka ba wanda zai ce ya san k’wallarsa tun bayan girmansa sai Nenne da yake iya bayyana rauninsa kai tsaye a wajenta. Bai juyo ya kalleta ba da itama zai ga tata k’wallar da take zuba ba k’akkautawa saka kansa kawai ya yi ya fice daga d’akin. Sai da ya tsaya a corridor ya kawar da duk wata fuska ta damuwa sannan ya saka glass d’in idanunsa bak’i wuluk don bata son Umma taga idanun da suka canja sannan ya fice da sauri ya ji da’di sosai da bai samu Umman da Najee a babban parlourn ba.

Yana fita Nene ta kifa kanta tana wani irin kuka mai tsuma zuciya, kukan tausayin Jaheed yake da yarda da sanin ta ta b’oye masa waye shi? Sannan ta d’auki haukan k’arya ta d’orawa kanta duk don gudun kada a tambayeta asalinta da na Jaheed d’in. Tana tausayin d’anta kamar yarda sau tari zuciyarta take son ta bayyana masa asalinsa sai dai tsoron bala’in da sanin asalin nasa zai haifar yana togaceta daga aikata hakan, zamanta a matsayin mahaukaciya da rashin sanin asalin Jaheed shi ya fiye musu alheri daga ita har Jaheed d’in fiye da bayyanar gaskiyar lamarin, tabbas abinda ta b’oye shine alheri garesu gaba d’aya daga ita har duk wani masoyin ta. Da sauri ta mik’e tana dannawa k’ofar d’akin mukulli kafin ta juyo ta fa’da toilet da azama ta d’auro alwala. Tana fitowa sallaya ta shimfi’da ta fuskanci alk’ibla cikin nutsuwa ta tada sallah. Rako’i da yawa ta yi kafin cikin sujjadar k’arshe ta fashe da kuka tana furta “Ya Allah ka zama gatanmu ni da Jaheed a rayuwa, Allah ka bashi mata ta gari ka gajarta masa wahalar rayuwar neman aure.

Zaku iya samun book ‘din nan a arewa book @Nazeefah ko ku saka sunan book ‘din kawai.

JIKAR NASHE CE✍🏽