Barrister Hibba
by @nusybee143
💥 BARRISTER HIBBA 💥
✍️Nusy bee
Page 12
Washegari da safe ya emergency call daga asibitin shi,dole ya shirya ya bi jirgin ƙarfe tara,Ummi da ƴan biyun shi ne suka raka shi,surutun Mifra har hawa masa kai yakeyi,don har yanzu baya cikin nutsuwa
AIYO MANSION, ALI MUHAMMAD KABO AREA, RAILWAY ESTATE, KANO STATE
Washegari da safe Hibba ta fito don zuwa dubiyar ammi,daga nan zata wuce wajen Khadijat da za'ayi discharging yau,yau ba track suit,abaya ce sky blue a jikin ta,sai Arwa da zata raka ta sanye da tata abayar blue black,Marwa ta bi su da kallo, Arwa sai murna take don tun da ta dawo daga karatu babu inda suka taɓa zuwa,tunda suka fito zasu tafi shopping ta hana su basu sake attempting fitar ba ma, Marwa tace"ina zaku je?"
"Yaya ce tace zamu je dubiya,ke baki da lafiya"
Da sauri ta miƙe tana faɗin"don Allah yaya nima zan je, Please"
"Ba fa zamu je da ke ba,don dubiya zamu je ba jinya ba,ki zauna ki taya mama hira"a cewar Arwa tana karkaɗa ƴar jakar hannun ta tana murmushi
"Dalla malama da ke nake?idan kika sake saka min baki a magana ta sai kin gane kuren ki"
"Dubiya ce dai bazaki je ba,kuma sai an saka ɗin"a cewar Arwa tana murguɗe-murguɗen fuska
Marwa ta yunƙuro a fusace zata bada amsa Hibba da ta gama gyara mayafin ta ta kalle su fuska a ɗaure tace"duk wadda ta sake magana bazan tafi daku ba"suka yi shiru, Marwa da taga da gaske tafiya zasuyi su bar ta tayi ƙwal ƙwal da idanu tana faɗin"Please yaya!"
Sai da tayi ɗan jimm sannan tace"to shirya,but don't forget to come with your inhaler" cikin sauri ta faɗa ɗakin ta batare da ta gama jin abinda yayar take faɗa ba,mintuna kaɗan sai ga ta ta fito da irin shigar Arwa,dama tayi wanka ta sanya kayan shan iska,suka wuce zuwa mota,Arwa riƙe da basket,sai halin nata takeyi,wato surutu
Muyassar yana zaune a motar,har ya fito da ita,don Allah Allah yakeyi ya koma asibitin shima,don zeenat ta kira shi da sassafe take gaya masa cigaban da aka samu cikin farin ciki,suna zuwa suka gaisa, sukayi masa ya mai jiki?Hibba da Marwa suka zauna a baya,Arwa ta zauna a gaba,ta fara basu labarai iri-iri,dama ita bakin ta baya shiru,sai da hibba ta gaji tace"Arwa can you shut your mouth off please?"
Shiru tayi, Muyassar yayi ɗan murmushi yace"for me I'm enjoying,Amma idan yaya tace ayi shiru mu ma sai mu zaɓi shirun"ƴar dariya sukayi su duka, daga nan sukayi shiru har suka isa
Sun samu ammi zaune tana sallar walaha,sai da ƙwalla ta ciko idanun Hibba don tuna tata mahaifiyar,bata taɓa wasa da sallar walaha,har ma da sauran nafilfili,ƴan biyu suka gaida zeenat da ke zaune tana danna waya,ta amsa tana murmushi tana kallon su,tana ƙaunar ƴan biyu sosai,kuma Wadannan ma daga ganin su ƴan biyu ne,suka sake gaisawa da Hibba,suka tambaye ta ya mai jiki?ta amsa mai jiki alhamdulillah
Zeenat ta kasa daurewa tana kallon su tace"amma ƴan biyu ne ko?"suka amsa da"eh"zeenat tayi murmushi tace"I see!gashi har yayar taku ma kamar ku ɗaya sak kamar ƴan uku,haske kawai kuka ɗan fi ta,amma kanku ɗaya"Arwa uwar surutu ta kama baki tace"wai!kanmu ɗaya?a yanzu amma ko?ta girme mu sosai to,itace uwar tamu ma,itace ta raine mu ma"da sauri Muyassar ya kalli Arwa da mamaki, Hibba ma kallon ta tayi cike da jin haushi,ta san surutun Arwa shiyasa bata cika son tafiya wani wajen daita ba,amma saboda nacin ta da son yawo take fita da ita
Hira suka cigaba da yi da Arwa har ammi ta idar,da girmamawa suka gaishe ta,suka tambaye ta jiki,ta amsa musu da sauƙi
Da murmushi ammi tace"mun gode sosai,mun gode Allah ya saka da alkhairi, Allah yaji ƙan iyaye"
Wannan addu'a ta ƙarshe da ammi tayi mata sai ta ƙara wata ƙima a idanun ta ta musamman,ƙwalla ta ɗan kwanta a idanun ta,ta sunkuyar da kai tana ƙoƙarin mayar da ita,duka Muyassar yana ankare da ita,sau tari yana mamakin dalilin yawan son kuka da Hibba takeyi,amma kuma sai ta hana hakan faruwa, zeenat da Arwa kam sai hira akeyi, khaleel ɗan zeenat kuwa yana wajen Marwa
Muyassar ya kalli ammi yana murmushi yace"itace shugabar wajen aiki na ammi,waɗannan ƙannen ta ne"ya nuna su Marwa
"Masha Allah! Allah ya sawa rayuwa albarka"suka amsa da ameen suna ɗan taɓa hira
Kiran da Maryam tayi a wayar mama tana kuka wai sun tafi sun bar ta ya sa Hibba ta miƙe tana faɗin"to ammi zamu tafi,na bar yarinya tana bacci,yanzu ta tashi,bari mu koma,daga nan zamu wuce wata dubiyar ma"
Zeenat tace"amma ku bar min ƙawa ta Please and please,anjuma zan rako ta da kaina"Arwa tayi karaf tace"Please yaya!"Hibba bata sake magana ba tayi gaba tana kara yi musu sallama,ganin Marwa ma bata da niyyar tashi ta fice daga ward din, Muyassar ya biyo bayan ta
A hanya suka haɗu da Dr Umar, murmushi yayi suka gaisa,sannan ya kalli Hibba yana murmushi yace"ina mutuniyar tawa?"
Hibba tayi murmushi tace"tana ciki"sai da gaban Muyassar ya faɗi,bai san sanda ya tsaya yana kallon su ba, Hibba ta cigaba"da ƴar uwar tace zata zauna shine itama taƙi biyo ni,kasan haɗe min kai sukeyi"Dr Umar yayi dariya yace"to ke a wa zaki shiga tsakanin ƴan biyun yaya?"Hibba ta girgiza kai tana murmushi tace"nima dama ban ɗora a ka ba,anyi discharging khadija ne?"
"A'a,sai zuwa anjuma gaskiya,don mijin ta ma yazo tun a jiya,ashe all this while ma bai san abinda ya faru ba sai jiya da dare"
Hibba ta gyara tsayuwa tace"yeah Ina sani naƙi bari ya sani,abu Ni ya shafa Ni zan magance shi,a jiyan ma ban so ya sani ba,bari na ƙarasa wajen ta"tayi gaba Muyassar ya cigaba da bin bayan ta
Sun samu Barrister Khadijat cikin ƙoshin lafiya,ga ta gwanar surutu ta juya Yaren su Igbo sai labari take bawa mijin ta,mijin nata yana ganin su Hibba yayi murmushi,suka gaisa,da harshen turanci yakeyi musu godiya,don shi kam bai iya Hausa ba,itama Khadijat albarkacin tashin Kano da tayi ne,sai da tayi shekaru ashirin da uku a Kano aure ya mayar da ita Lagos,yanzu shekarun ta huɗu da aure,ɗan ta Mukhlis kam bai san wani yare ba banda Igbo
Yana ganin Muyassar ya gane shi,yana ta daga masa hannu yana yare,shi dai Muyassar ya ɗauke shi yana murmushi suka fita,shima mijin Khadijat fita yayi ya bar ƙawayen suna ta hira
Sun kai wajen rabin awa kafin Hibba ta fito, Muyassar ne ya mayar da ita gida,a balcony ta hango Maryam,tana hango su ta taho da gudu,amma sai Hibba ta juya yare zuwa German ta fara mata faɗa,ganin yadda ta firgita tana ja da baya ya sa Muyassar ya fuskanci faɗa takeyi mata,ya janyo ta yana bawa Hibba haƙuri,ita kam ta shige bayan Muyassar,Hibba bata sake bi ta kansu ba ta shige cikin gidan
Ma'aikatan gidan fa sun samu abin gulma,dama tun farko Muyassar baya hira a cikin su,shi dai bar shi danne dannen waya ko ya ware kanshi can gefe,gulmace gulmacen da akeyi sau tari ba wai son su yakeyi ba,kuma baya taɓa saka musu baki,shiyasa suke masa kallon mutum mai girman kai,tunda wani lokacin sallama ma ba safai yake musu ba idan zai tafi gida, Jabir shine abokin shi dama,a silar shi yazo gidan aiki,abokin shi ne tun a secondary,shi Jabir ma yayi aure har da ƴar shi ɗaya
Hibba bata daɗe da komawa gida ba Nafi'u ɗan wan mahaifin ta ya kira ta yace ya iso,saukowa tayi sanye da rigar Jersey na PSG da straight skirt baƙi,a parlour ta ganshi a zaune,ta ɗan saki fuska,ya gaishe ta har da durƙusawa, murmushin takaici tayi ta amsa sannan tace"tuntuni nace kazo,why sai yanzu?"
Nafi'u ya sunkuyar da kai cikin ladabi yana faɗin"na koma makaranta ne"
Ta samu waje ta zauna tana faɗin"okay Allah ya taimaka,bani account number dinka"da zumuɗi ya karanto mata,ta saka masa 200k sannan ta miƙe batare da ta sake ko da kallon shi ba ta haye sama,sai da ta kusa shiga ɗakin ta sannan ta leƙo tana faɗin"ka gaishe su"ta shige batare da ta saurari godiyar shi ba
A da tana tunanin tsakanin ta da mutane kuɗi ne kawai,idan kana dashi kawai zasu girmama ka,basa soyayya don Allah,idan baka da kudi baka da amfani,mai kuɗi kuma shine mutum,amma Muyassar ya ƙaryata tunanin ta,duk da kasancewar tana samun girmamawa amma babu wanda ya damu da menene damuwar ta?yaya take gudanar da rayuwar ta?me takeyi daidai da ba daidai ba?sai Muyassar,don haka jin shi take kamar ɗan uwan ta na jini fiye da su Nafi'u,taji har ranta ta yarda zata iya gaya masa damuwar ta,ko Allah zai sa taji sauƙin ƙunci da baƙin cikin da ke danƙare a zuciyar ta shekaru kusan sha biyar
A yau mahaifiyar Muyassar tayi mata nasiha da kalaman da rabon da taji su tun mahaifiyar ta na raye,ta goge hawayen ta tana yiwa iyayen ta addu'ar samun rahamar Allah
Ƴan biyu basu dawo ba sai daf da azahar Muyassar ya dawo dasu,su kansu sun kasance cikin farin ciki,basu da abokan hira,basa shiga cikin mutane,ko a hostel ɗin su a cosmopolitan University da suke attending su kaɗai ne a ɗakin su,a gida daga su sai mama sai yayar su,karo na farko da suka shiga mutane suka sake sukayi hira,don bayan tahowar Hibba an samu ƴan dubiya sosai,da yawan su ƴan uwan su Muyassar ɗin ne,haka suka yi ta hira da Arwa don bata da wahalar sabo,itama Marwa duk da bata cika saka baki ba sai da ta sake,kuma anan ma sai da sukayi abinda suka saba,wato faɗa,faɗan ma akan khaleel ɗan zeenat, Muyassar da ya koma bayan ya sauke Hibba ne ya raba faɗan,don zance na Allah faɗan ƴan biyun dariya yake bashi,Arwa tsokanar tsiya, Marwa kuma ba haƙuri,ga bala'in son girma, zeenat kam burge ta sukeyi sosai
Ammin su Muyassar ta kula da abubuwa da yawa daga twins,abin ka da babba,mai nazari,ta gane kamar basu tashi da uwa ba,ko kuma sun tashi a sakalce, musamman Arwa,don ita Marwa miskilanci yana ɓoye wasu ɗabiun nata,ta dai ƙudurce zata tambayi Muyassar
Kwanan ammi uku aka sallame ta,jikin ta yayi kyau sosai,don ta samu kulawa yadda ya kamata kasancewar asibitin Umar asibiti ne mai kyau sosai, washegarin da aka sallame ta Arwa ta roƙi Hibba ta bar su su je su ƙara ganin jikin ta,bata ja ba ta bar su,sunyi murna sosai,tun wajen goma Muyassar ya tafi dasu gidan su,itama Hibba ficewa tayi harkokin gaban ta,har ta dawo wajen ƙarfe uku basu dawo ba,sai da ta gaji ta kira su a waya,bayan ƙarfe biyar na yamma sannan suka dawo
Ko ba'a faɗa ba taga farin ciki a fuskokin su,yadda basu gaya mata me ya saka su farin cikin ba itama bata tambaya ba,amma taji daɗi sosai yadda yaran ta suka samu farin ciki a gidan su Muyassar sosai ko da bata nuna musu ba ko a fuska,amma a rayuwar ta bata da abin da take ƙauna kamar murmushin waɗannan bayin Allah,babu abinda ta tsana kamar kukan su,suma kuma haka,yayar su itace komai nasu,itace farin cikin su itace walwalar su
Sati biyu tsakani Hibba da Muyassar suka je immigration office akayiwa Muyassar ɗin international passport,don a lokacin shirye shiryen makarantar shi ya fara nisa,a hanya yayi ta mata godiya,sannan yayi mata tambayar da ta girgiza ta
"Ma'am I'm sorry,zan sake shishshigin da na saba,tun daga lokacin da twins suka je dubiyar ammi na a asibiti sun ce wai kece uwar su,kuma nima naga alamu kamar kece kowa nasu, Please idan bazaki damu ba ina son jin brief daga labarin ki,zuwan da ƴan biyu gidan mu ban san me suka gayawa ammi na ba tace tana tausayin rayuwar su,a yanzu kullum basu da magana ita da zeenat sai maganar ƴan biyu, I'm sorry idan tambayar tawa ta ɓata miki rai"
Ajiyar zuciya ta sauke,cikin sanyin murya tace"muje gida,zan baka labarin rayuwar mu yau in Sha Allah, wataƙila kaima ka iya taimakar mu"
"Ni kuma na taimake ku?da me kenan"
Ta buɗe idanu tana kallon shi tace"kai ma kana cikin waɗanda suke ganin dukiya itace komai ko?"
Murmushi yayi yace"a'a!me ya kawo wannan maganar kuma?nine nake ganin kamar babu ta inda zan iya taimakon ku"
Hibba tayi ɗan murmushi tace"akwai yadda zaka iya taimakon mu mana,na farko kaine Mutum na farko da ka fara ƙaryata tunani na na cewa ana girmama mutum ne kawai don abin hannun shi,kayi min faɗa kaga nayi ba daidai ba,rabon da ayi min faɗa irin haka tun mahaifiya ta tana raye"
"I thought mama ce ta haife ku?"ya faɗa yana ɗan kallon ta,kafin ya mayar da hankalin shi kan driving
"Iyayen mu sun rasu,autan mu ma ya rasu"ta faɗa cikin sanyin murya,ƙwalla tana cika idanun ta
Shiru yayi cikin tausayin su,kafin shima cikin sanyin murya yace"Allah yaji ƙan su yayi musu rahama"ita dai bata sake magana ba
Kamar daga sama taji ya sake jefo mata wata tambayar"menene alaƙar ki da Maryam?"
Ɗagowa tayi ta kalle shi,shima ya ɗan kalle ta sannan ya cigaba da driving,ta sauke ajiyar zuciya tace"ƴa ta ce"
"Na sani,amma menene alaƙar ki da ita?ina nufin ina kika same ta? su waye iyayen ta?ya akayi take hannun ki?"
Kallon shi kawai takeyi babu ko ƙiftawa,shi kam hankalin shi na ga driving ɗin shi,a hankali ta furta"nice mahaifiyar ta"
Still bai kalle ta ba yace"yaushe kika auri mahaifin ta?"
Hibba ta ɗauke kai tace"ban taɓa aure ba"
"Nasan da haka, shiyasa na tambaye ki iyayen Maryam"
"Ai ba dole sai nayi aure zan haihu ba ko?"ta faɗa tana ɗauke kanta ta mayar da idanun ta window
Kamar daga sama taji yace"baki taɓa haihuwa babu aure ba,kuma baki fara akan Maryam ba,baki da alaƙa da ita banda kasancewar ki poster mother a gare ta,ba wai don wani abu na faɗa ba shine iyakar abinda na gani, Hibba a yadda kike da ace Maryam ƴar ki ce bazaki taɓa nuna ta ga duniya ba, beside,ke ba irin waɗanda suke zubar da mutuncin su a titi bane"
Ga mamakin shi sai shashsheƙar kukan ta yaji,ya kalle ta da sauri,ta saka gaban baby hijab ɗin ta ta rufe fuskar ta,da yake yau ma kayan gadon ta saka, track suit na PSG lemon green,da sauri yace"I'm very sorry idan tambaya ta ta ɓata miki rai"Hibba ta janye hijabin ta daga fuskar ta tana goge hawayen fuskar ta tace"Muyassar na gode da kulawar ka,da damuwar ka da komai akan abinda ya shafi rayuwa ta,babu wanda ya taɓa yi min haka tun bayan rasuwar mahaifiya ta,Maryam ba ƴa ta bace, mahaifiyar ta ta rasu,amma mahaifin ta yana nan a raye,ta dawo hannu na ne ma dalilin rasuwar mahaifiyar ta,Ni kuma na rike ta Ni kaɗai ne saboda ahalin ta ba musulmai bane,Ni kuma ina so ta rayu a matsayin musulma"ya jinjina kai batare da ya iya cewa komai ba,itama bata sake magana ba ta kwantar da kanta a jikin kujerar da take zaune ta lumshe idanu, lokaci lokaci Muyassar yake kallon ta cike da tausayin ta,don ba sai an faɗa masa ba,akwai abinda yake damun ta
Har suka je gida babu wanda ya sake magana,ita kaɗai ta shiga,bata samu mama a gidan ba,dama ta san zasuyi yafiya ƙauyen su ita da Maryam,a can ma zasu kwana,ƴar ƙanwar ta ta haihu sun je suna,ƴan biyu kam sun koma makaranta shekaranjiya,kama stairs ɗin tayi ta wuce sama, bata sauko ba sai bayan kusan mintuna arba'in,still wasu track suit ne a jikin ta farare,ta ɗora babu hijab ɗin ta na ƙa'ida
Sai da ta zauna sannan ta kira Muyassar ya shigo parlourn,sai dai ya zauna cikin sanyin murya tace
"Zan baka labarin mu,ni da ƴan biyu na da silar da yasa muke rayuwa a hagunce, Ni kaina nasan rayuwar mu da gyara amma ban san yadda zanyi na gyara ba,da ina da yadda zanyi da na chanja mana rayuwa, mutane da yawa suna mana kallon mutanen banza,kuma kowa da yadda yake aibata mu,babu yadda zanyi ne amma babu wanda zai so a rinƙa yi masa kallon banza,babu wata uwa da ta fara nuna mana ita uwa ce a wajen mu bayan tafiyar tamu uwar daga mama sai mahaifiyar ka,shiyasa lokacin da ƴan biyu suka ce zasu je ban hana su ba,bana son su shiga mutane don matsalar da zasu shiga ta wuce wadda suke ciki yanzu
To fa! wacece Hibba? menene ya tsaya mata a rai ya hana ta walwala haka?yaya akayi ta zamo uwa ga ƴan biyu bayan ga mama? tukunna ma dai,ba mama bace mahaifiyar su kenan?sai naga ra'ayoyin ku a comment section
Yau ma nayi post biyu ba sabon ba🙈
#likecommentshare
#Nusy_bee