KARAGAR MULKI

SNEAK PEEK

by @cwtsumiey19988

  KARAGAR MULKI

    By

 Cwt-sumiey
         (A historical, fictional,magical,heart touching love story, with confusion ,destiny and betrayal) 

  * SNEAK PEEK*

Ƙaddara kurma ce,ba ta ji ba ta gani tan kan bijiro a rayuwar ɗan Adam ta mabanbanta salo,wala Allah ka gaiyace ta ko kuma ba ka gaiyace ta ba,za kai maraba da ita ko kuma ba za kai ba,kai ko da zaka sa ƙafa kai farmaki da ita hakan ba zai sauya sunanta na ƙaddara ba,wani sa'in mu ne mu ke buɗe ƙofar da za mu ba ƙaddara damar shiga cikin rayuwar mu,wani lokacin ita ke bibiyarmu tamkar mayunwacin Karen da ya hangi kyanwa a cikin talatainin dare,tabbas ruhi na azabuwa idan ya kasance gangar jiki na girbar laifin da ba ita ta aikata ba,shin laifi ne dan na tsinci kaina tattare da wata jarabawar da ban san asali ko mafarinta ba,shin yin kaina ne hakan ko laifi na aikata da har Ubangiji ya jarrabe Ni da ita,na rasa gane dalilin da yasa baƙar ƙaddara irin wannan ke bibiyarta,na rayu tamkar wani asararran ɗa kuma wofinttacce wanda ba sa albarka iyaye a tare da shi,na zama tamkar bare a cikin ƴan'uwana,idan ina son in fuskanci tozarci da kuma ƙasƙanci to in tunkari wani muhalli ko majalisi na Me girma kuma mai martaba Sarki Abudullah Mahaifina ko kuma wani daga cikin Ahlina,Hmmmmm ni kaina ina tsoran ranar da hakan za ta faru,shin wai waye ni,wacce jaraba kuma baƙar ƙaddara ce ke bibiye da ni?.....

"Ummmm...ma...mam...Ummata!!!!",ya fad`a da amo ko sauti mai k`arfi tare da fusgo maganar da ga can k`asan mak`oshin shi da k`yar, kokowa sosai ya fara shi da numfashinsa da ke bugawa da sauri da sauri,hakan ya faru ne ta dalilin zuwan sak`o na bazata a cikin kwakwalwarsa,gashi shi kuma sai son ya furta wata kalma da ga bakin sa ya ke.
" Ka kwantar da hankalin ma na Yarona da gaske ni d`in ce ba fatalwa ba ce ko gizo,Ni d`in ce da kaina Giwar Masarautar BIHINAR kuma Mahaifiyar Yarima Haisam ","Dan Allah da gaske ki ke,ko dai da wasa ki ke min,idan har hakan gaskiya ne ,to ki tsaya in ji d`umin jikinki a jikina mana,na yi kewarki matuk`a na rayuwa tamkar maraya ko almajiri ko wani mara gata da galihu kullum cikin mafarki da begenki na ke,me ya sa ki ka tafi ki ka bar ni,ko dai kin dena so na ne tamkar yanda Me Martaba Sarki Abdullah ya dai na k`aunata ?,ko da ya ke ai ni ne da kaina na  shek`e ki,na za ma silar mutuwar ki,da wa'inna hannayen nawa na kashe ki,da wa'inna hannayen nawa na sa ka ki a d`akin gami da sa ka wuta a cikinsa, da wa'inna hannayen nawa na shak`e wuyan `yar'uwata Gimbiya Lailah ta mutu har lahira,da wa'inna hannayen nawa",........," Ya Isa haka ma na",ta katse shi da cikin murya mai d`auke da amon sauti da kuma amsa kuwa"Haba shalelena ta ya za ka rik`a fad`in munanan kalamai irin haka ?,ko da a tarihi da tarihi-tarihi ka ta`ba jin in da wani d`a ko da d`an gaba da fatiha ne da ya aikata kwatankwacin irin abinda ka ke fad`a ?",To idan har ke d`in zahiri ce ki tsaya inji d`uminki a jikina mana,ki tsaya in rungume ki tamkar yanda kowanne d`a ya ke rungumar mahaifiyarsa mana,ki tsaya in d`ora kaina a saman cinyarki ki tallafe ni ki lallashe ni kamar yanda ko wacce Uwa ta ke ma d`an da ta haifa",ya k`are zancensa ya na mai fashewa da kuka da murya mai k`arfi wacce ke nuna zallar halin da ya ke a ciki,ko su Jamal da suke tsaitsaye suna kallonsu kuka su ke,fuskokinku sharkaf da hawaye,"Yarona lokaci ya yi da ya kamata ka manta da Komi da ya faru a baya ka fuskacin sabuwar rayuwar da zata zo ma ka ka manta da komi",tace da shi cikin kwantar da murya gami da sanyaya lafazi domin ya yarda da kalamin ta, "Ta ya za ki ce haka Uwa mahaifiya a gare ni,ta kuma wacce fuska zan iya mantawa da duk abinda na aikata ?,bayan ni na kasance shed`an a cikin ahalinku ni d`in ba yaron albarka ba ne,yasasshe kuma wofintatce d`a ne da ba a murnar haihuwarsa ko kasantuwarsa a cikin ahali da wad`annan banzayen hannayen nawa na aikata komi da komi fa","Ni ba Kai ne ka kashe ni ba Harzan ne ya aikata ba kai ba",ta sa ke magana cikin k`araji"Harzan to waye Harzan d`in in ba ni ba,ni ne Harzan, ni ne Narshad,ni ne Azela haka zalika ni ne Azla duka gabad`ayansu ni ne tunda ba wata siffa da ake gani in sun bayya face tawa siffar", A'a Yarona kar ka ce haka domin hakan ba zahiri ba ne ba","To amma "....." To amma me?,ya Isa haka ma na Yarona,ya kamata ka dakata ka tsaya ka saurari abinda na zo da shi,ko ba ka ga `yan'uwanka ga sunan sun yi tsaye cirko-cirko su na gani da sauraron abinda ke wakana a tsakanin mu ba,ga shi Dama ba wani isasshen lokaci ne da mu ba","Lokaci kuma me hakan ke nufi ,ko dai ki na nufin za ki k`ara tafiya ki barni ne?,in cigaba da watangararriyar da rayuwata ?".
"Tabbas tafiya zan yi shalelena domin ba wai na zo ne domin in zauna ko in dauwama ba,Ni d`in na riga da na mutu  ba na da wata sauran rayuwa wacce ta wuce ta barzahu yanzu ma haka na zo ne domin in isar da wani sak`o a gare ku"....da hanzari ya katseta ya na mai girgiza ma ta kan sa,ya na cewa," A'a bai kamata ki tafi ,ba za ki tafi ki bar ni ba,ba zan bari hakan ta sa ke faruwa ba",ya na kaiwa nan ya sa ke kai mata wawura da nufin ya rik`eta,cikin yanayin zaucewa da d`imaucewa ya fara magana,"Kin gani ko,ji ba fa ki gani,guduma ki ke, ko damar da zan iya ta`ba ki bana da ita ,iya hasken surar ki da kuma sautin amon muryarki kawai na ke da damar ji,dan Allah kar ki tafi ki bar ni,ki manta da duk wani uzuri ko k`udirin da ki ka zo da shi,ki bari mu rayu a tare ko a iya haka ne ni ya wadatar min,in har zan ji muryarki in ga hasken siffar ki,ki ta`ba ni inji hakan a jikina ko da ni bazan ta`ba ki inji ba"....."A'a hakan ba za ta yiwu ba domin ni d`in ba madauwamiya ba ce,Kai bama ni ba Komi na duniyananr fararre ne kuma k`ararre ne ,ni na riga da na ci nawa zamanin ba ni da wani saura anan gaba,rayuwar barzahu ita ta fi dacewa da ni,don haka dole in tafi ko na k`i ko na so".....