CHAPTER 2
by @deejasmah
JIRWAYE
Khadeejah Bint Ismail (Deejasmah)
CHAPTER 2.
Wani azababben gudu take yi akan titin tana yi tana sakin tsaki, ji take kamar tayi aman wuta saboda masifar dake cinta a rai da zuciyarta. Haushin nata ya kuma dad'uwa a daidai sanda ta kusa isa stadium roundabout sakamakon uban holdup d'in da yake wajen, dole ta rage gudu ta shiga jerin wainda suke jere suna jiran chance d'in su ya zo su wuce. She just hate the fact that she's going through this again, wayarta ne yayi k'ara da sauri ta d'ago wanda inda a normal mood take ba zata yi saurin d'aga kiran ba sai ta kusa katsewa ma kafin ta d'aga but because tana neman wanda zata saukewa kwandon masifar dake ranta ta d'ago wayar ''Deedee Shamaki'' shi ne sunan da yake yawo kan screen d'in d'agawa ba tare da tayi magana ba ta jiyo muryar twin d'in nata mai sanyi sosai wanda duk da kusan suna kusan kama da na juna amma nata yafi na Dee zak'i sosai ita kuma sanyi ne da kuma shak'ewa kamar tayi kuka tana cewa '' Hey Twinnie ya kike?".
Wani kalar tsaki ta ja tana cewa '' miye ruwanki da yanda nake? Yaushe muka fara tambayar juna yanda muke? When did that started?".
''Twinnie......''
''I told you time without number that I'm not your twin, you are also not mine but a mistake in the family but because you are dumb you don't always get it''.
Shiru Deedeen tayi tana mai jin wani kalar d'aci yana ziyartar k'irjinta hakan ya bata damar cigabawa '' You better stay off me, ya fiye miki kwanciyar hankali you get it? Or no you won't because you are really stupid mtswwww''.
Tana gama fad'in hakan ta yanke wayar tana jifa da ita kan seat, yayinda ta gefen Deedeen ta tsaya kasak'e rik'e da wayar a kunnenta damuwarta yana kuma hauhawa not because of maganganun da ta fad'i mata but because of how she sounded. She's pretty sure tana cikin damuwa daga tone d'in ta, da sauri ta cire wayar daga kunnenta tana kunna system d'in ta location d'in Ateeyahn ta fara nema within seconds ta gano inda take wato stadium roundabout a tsaye kuma take cak bata motsi alamun tana cikin holdup, locations d'in ta ta hau dubawa for the past 2 hours nan ta gano tana café 1 har da seat number sai da ta gani a take ta yi concluding cewa tabbas a can aka b'ata mata rai wanda ta tabbatar ba clients bane but wancan circle d'in da take tare da su. Duba calls d'in ta tayi nan taga numbers d'in friends d'in ta maza da su kawai tayi waya a ranar sai Affansu da suka yi waya fin sau goma a ranar. Wasu 'yan binciken ta kuma yi sannan ta fita daga wurin, kashe system d'in tayi tana mai lumshe idanu. Kana ta bud'e glasses d'in idonta ta gyara tana kallon cikin class d'in da take, tun magrib ta baro room d'in su ta dawo SLT 3 don a nan take zama tayi 'yan karatun ta da rubutun ta at most times kuma aiki ko yanzu d'in ma wani code take warwarewa wanda aikin DIA ne da ta kan musu aiki time to time and it is something that needs privacy shiyasa take zuwa class ta tafi can last seat ta zauna tana kallon d'aid'aikun students dake shigowa wasu su yi karatu wasu kuma 'yar soyayyar su suke tsinka sai kusan 11 take komawa d'aki. Komawa tayi page d'in da take before nan ta ga har Ateeyahn ta bar wajen ta nufi hanyar off-campus d'in da take zama wanda kusa yake da Greenfield University inda take karatu, sai da ta tabbatar da shigar ta room kafin ta samu sukuni. Fita tayi ta koma kan aikinta wanda ya d'auketa lokaci mai tsayi sai kusan 10 kafin ta iya warwarewa mail ta tura musu kana ta kashe system d'in ta gaji ainun, wayarta ta d'auka wacce take cikin DND nan ta tarar da misscalls rututu na Ridhwan Audi kamar yanda tayi saving number. Tura baki tayi tana folding wayar a k'asan mak'oshi ta furta '' sai dai kuma gobe Mr.''
Daga haka ta kwashe kayakin ta da suke kan desk ko ta kan sauran drink d'in da ta ajiye bata bi ba ta rataya backpack d'in ta ta wuce room, sanda ta je samu tayi Mufee tana kwance dirshan tana kallo a system d'in ta. Hi kawai tace mata ta wuce toilet wanka tayi ta kimtsa jikinta gadgets d'inta tayi plugging a charge ta kwanta ba ta ko dad'e ba bacci ya d'auketa kallonta Mufee tayi tana mai murmushi a duniya tana fatan inama ace ita ce ke da saurin bacci kamar Deeyah don ita dai sai tafi hour tana juyi kafin bacci ya d'auketa while ita ko da ta kwanta ba ta shige 5 minutes take bacci.
Me too I dey envy those sets of people oo, daga sun kwanta sai bacci while we will be struggling and overthinking for more than an hour kafin baccin ya d'auke mu muna yi kuma muna farkawa. God Abeg.
The following day da wuri ta farka timetable d'in Mufee ta duba nan ta ga bata da class sai 10 da yake kowa yana da timetable d'in shi a wurin bunk d'in shi da kuma study table d'in su. Kai ta gyad'a kawai don ita tana da 9-11, yam d'in da Mufeen ta fere probably da asuba ta wanke ta zuba a tukunya ta tafasa ta musu golden yam. Wanka ta shiga tayi ta fito cikin usual kayanta cargo pants blue-black sai farar baggy shirt ta Nike sleeves bakake ta saka sai ash ɗin jersey veil da ta yi clipping ya rufe gashin kanta da aka yi locking, haka nan tayi ma kanta kyau duk da colors ɗin sun yi yawa amma kuma ba wainda ba su yi matching ba ne. Tote bag ɗin ta ta ɗauko ita kuma pink ce ta " she-code Africa" su system din ta ta saka a ciki sai note da pen, water bottle ɗin ta ta cika da ginger tea sannan ta iya yin breakfast tana kallon wall clock ɗin su 8:09. Wayarta ta ɗauko ba tare da ta bi ta kan misscalls ɗin Rhid ba, number Affah ta kira kamar yanda ta saba a duk safiya. Bai ɗaga ba instantly sai da ya kusa katsewa ya amsa yana cewa '' Assalamu alaikum Adeeyah''.
''Waalaikas Salam Affah, Barka da safiya''.
''Yawwa Barka kun tashi lafiya? Ya makarantar?".
''Alhamdulillah, ya aiki ya su Amah?".
''Kowa lafiya, ba dai matsala makarantar ko?".
Kai ta girgiza tana mai jin zuciyarta na yin mata nauyi tace '' Babu komai''.
''Toh Masha Allah, ku cigaba da maida hankali okay?".
Kafin ta kai ga amsa masa ya katse wayar ji tayi hawaye yana cika mata idanu, sai dai ta daure tana hana kanta yin kukan faɗi take tana maimaitawa '' It's okay Adeeyah Shamaki you can do this'' sai da ta ɗan ɗauki lokaci kafin ta iya haɗiye yanayin da ta ke jin kana ta juya akalar kiran nata ga Amah, ita kam ringing biyu ta ɗaga tana cewa ''my baby''.
Murmushi ta saki tana jin sauƙi yana saukan mata tace ''Amah na, good morning ''.
''Good morning Sweetheart''.
''Ya gidan ya aiki?".
''Alhamdulillah, ya school ya Mufee fa?".
''She's fine Amah, bacci ma take yi''.
''That's great to know, you coming home this weekend?".
''No Amah may be next weekend I'm kinda occupied this weekend ''.
''Alright Sweetheart but be taking things easy for yourself okay?".
''In shaa Allah Amah, I love you ''.
''I love you more Baby''.
''I'm off to class''.
''Alright Allah ya miki albarka''.
''Ameen Amahna'' ta yanke wayar cikeda nishaɗi ran ta fes, kiran TeeTee ta yi sai dai har ta katse ba ta ɗaga ba. Ba ta sake kira ba don ta san may be ko ba ta tashi daga bacci ba ne or ba ta kusa da wayar, she knows who TeeTee is and no matter ba ta ƙin ɗaga wayarta sai dai ta jera mata maganganu marasa daɗi ta yanke kiran.
Ajiyar zuciya ta saki tana kwashi kayakinta ta bubbuga pillown da Mufee take kwance, idanu ta buɗe cikeda bacci tana cewa " what?".
''I'm off".
''Ba dai har 9 ɗin ta yi ba?".
Kai ta girgiza tana cewa '' zan tsaya PG ne''.
Ohh okay ta amsa tana miƙewa, ƙofa suka nufa ita ta fita tana ce mata bye ita kuma ta datse ƙofar.
Turus ta ja tsaya sakamakon ganin wata mota a bakin hostel ɗin na su, sai kuma ta basar ta hanyar fara duba cikin bag ɗin ta kamar irin ta yi mantuwar nan. Cigaba da tafiyar tayi har ta zo gaban motar, wanda yayi dai-dai da fitowar mai ita.
Matashin saurayi ne wanda ya tara duk wani suffar maza a tattare da shi, baƙi ne irin mai ƙyallin nan wanda hutu ya sake fiddo da kyan jikin na shi. Sanye yake da hoodie da wando kalar blue sai crocs baƙi yana sakin mata murmushi. Ɗan tura baki tayi tana cewa '' really? Rhid?".
''Toh ya kike son in yi Bae? Jiya how many calls na miki wayarki na DND ba kuma ki kirani back ba ya kike so in yi in ba in zo ba?" Ya amsa a mugun shagwaɓe kamar wani yaro, lumshe idanu ta yi tana buɗewa tace '' but in da ban fito ba fa?".
''Then I'd wait har sai sanda kika fito or Mufee, it wasn't like na san lecture hall ɗin ku da sai in je can''.
''You really are impossible'' ta amsa tana ɗan sakin murmushi, shi ma murmushin ya saki yana cewa '' ba ki yarda zan iya binki lecture halls ɗin ku ba ko?".
''Not even that, but how could you wait for me all day? Work fa?".
''i'm off today'' ya amsa yana lumshe idanu.
''Off?".
''Yeah, call fa zan yi yau and I'll have to rest da rana''.
''Oh okay, ni kuma ina da class by 9''.
''And it is almost 9, oya hop in lemme drop you off at the venue''.
''Nan kusa ne fa, and zan tsaya PG hostel in amshi power bank ɗina''.
Kai ya girgiza yana cewa '' okay lemme walk you''. Hannu ta kai tana dafe goshinta cikeda jinjina nacin shi ta murguɗa masa baki juyawa tayi ta ɗayan hannun ta shiga cikin motar, murmushi yayi ya shiga driver's seat ya tada motar suna tafe suna hira kaɗan-kaɗan PGn dai da bata je ba kenan don NB ne venue ɗin a nan ya ajiyeta ba shi ya tafi ba sai kusan 15 mins after 9 shima don ta matsa ne. Shi ma sai da ya kafa sharaɗin she should call him da rana kafin, buɗe motar ta yi da gaggawa ta fita don ta ga shigar lecturern na su kusan 10 minutes kenan.
Sallama tayi masa ta fita tana jin shi yana mata tsiya wai tana tsoron lecturern kar ya hanata shiga class, ita dai bata tanka ba don burinta ya tafi. Ƙofar hall ɗin ta nufa ai ko kamar yanda tayi expecting a tsattsaye ta ga students ɗin da ya hana shiga class don dama policyn shi in dai har ya shiga babu wanda zai shiga bayan shi. Wa'inda ke tsaye ko suna ganinta suka fara kiran sunanta '' ASH''
''Witchie''.
Tsayawa tayi tana duban Sakaɗaɗi da ke gefenta yana dariya yana cewa '' be like say im go let us enter''.
''You think so?".
''Yes, ke zaki shige mu biyoki a baya''.
Taɓe baki tayi tana cewa '' or rather in juya hostel kawai ba, You know say I no like wahala''.
''We know, let's give it a try'' ya furta da sauri sauran da ke gefenta suma suka haɗa baki wurin cewa '' Please''.
Idanu ta rintse ta buɗe kana ta wuce gaba tana ɗan tura ƙofar da aka rufe ɗin sai dai ba ta shiga ba sai kanta ta tura, da sauri duka students da lecturern suka zubo mata idanu. Idanu ya ɗan buɗe yana kallonta ya kuma kalli front seat da ta saba zama bata nan. Nan ko yace '' That's why the class seems a bit off, ashe ASH was not in class what happened? Why are you late?".
''It was.....''
Bai jira ta gama magana ba yace '' never mind, you can enter and the others too'' da sauri ta furta thank you sir, cikeda sakin ajiyar zuciya don ya taimake ta inda ya barta sai ta ƙarasa ma bata san me zata ce ba. Shiga ciki suka yi da sauran ƴan wajen suma suna ta faɗin thanks sir wanda yake annoying lecturern, bayan sun zazzauna ne ya koma podium ɗin shi yana cewa '' y'all know why I did let them enter right? It's because she's never late in my class always punctual and attentive'' students da yawa taɓa baki suka yi duk da sun san gaskiya ya faɗi amma ai hakan bai shafe su ba, ganin ba su bawa hirar muhimmanci ba ne ya sanya shi ajiye ta yana cigaba da lectures ɗin da ya fara mostly yana tsayawa asking questions which he's directing it to Adeeyah and as usual tana ba shi amsa har ma tayi explanation fiye da yanda yake yi ma.
Ta fito daga class ɗin ta na ƙarshe by 3pm ne ta tarda 2 misscalls daga Amah, murmushi ta saki da mamakin kiran nata sai ta bayar da hakan da cewa ko wani abun zata gaya mata da ta manta. Kiran ta mayar tana tafiya towards PG hostel ɗin da ta so zuwa tun safe amma zuwan Rhid ya hana ta. A daidai lokacin ne kuma Amahn ta amsa kiran, gaishe da ita tayi ta amsa itama tana tambayarta class ɗin ta na ranar Alhamdulillah ta amsa tana sauraron maganar Amah dake cewa '' You have to come home this weekend, your Affah Insists ''.
''But Amah...''
''No Buts Love just do as you are told''.
''Okay Amah but sai Saturday zan samu damar zuwa in shaa Allah sai in dawo Monday early morning ''.
''I'd tell him so, bye bye then'' tana faɗin hakan ta yanke wayar, numfashi ta ajiye haka nan take jin fargabar haɗuwarsu da Affahn nasu musamman da ba ta san dalilin shi na kafewa akan sai ta zo gida ba.
Power bank ɗin nata ta amsa ta wuce hostel ɗin su, kamar jiya yau ma Mufee ba ta dawo ba. Sai dai bata kwanta ba couscous ta dafa ta ci nata kafin ta jawo system ɗin ta tana aiki rabi kuma tana waya da Rhidwan da ya sata gaba da kiraye-kirayen wayar shi, ba ta da yanda ta iya dole ta ɗaga tana amsawa lazily wanda hakan da take yi ba ƙaramin kashe shi yake yi ba.
Viaducts Apartments, Auckland New Zealand.
Ɗunɗin ɗakin yake ba ka ganin haske sai hayaƙin da ya kaure ɗakin wanda yake fitowa daga sigarin da ake sha, yayinda karan shi ma yake bada ɗan haske. Zuƙa ɗaya aka yi wa sigarin ya ƙare akan ash tray ya ajiye sauran karan babu komai, lightern da ya kuma kunnawa ya ƙara lighting wani tabar hakan ne ya ɗan haska fuskar shi da ba lallai ka gane kalar shi ba.
Kira ne ya shigo wayar shi dogon tsaki ya saki yana kallon gefen shi, sunan Snake ne yake yawo kan screen ɗin. Hannu ya kai ya ɗaga rejecting yayi yana maida kiran, wanda babu ɓata lokaci wancan ɗin ya ɗaga ba tare da yayi magana ba yace ''Uhmm?".
Wata magana da aka faɗa daga can gefen ne ya sanya shi cewa'' what the heck Sna?!''.
Ƙara bayani aka masa ta can hannun yayi shiru yana sauraren abinda ake cewa sai da ya kammala bayanin ne ya iya cewa '' that means that you didn't do your work well, and it was your fault''.
''I don't care Sna you know quite well I don't accept failure, so you have to make up for that''.
''It's just that we were squared we never expect anything like that''.
''Who the hell he is?''.
''It's not a he Scor but a she,mace ce ''.
''What the fuck?!" Ya furta yana zabura cikeda takaicin jin wai mace ce ta ɓata masa aikin da ya yiwa mugun tanadi, duk yanda Snake ɗin ya so masa bayani Scorpion ɗin bai ko saurare shi ba saboda masifar da yake cin shi abu ɗaya ne kawai ya iya faɗa masa '' Find her!!!".
Yana faɗin haka ya yanke wayar yana sakin wani kalar haki a jiggace yayi jifa da wayar a bayyane ya furta '' how dare she?! How dare someone decode what I encode?!" Ya ƙarashe da ƙaraji kamar mai shirin fasa ɗakin...........
Shi kuma wannan bawan Allahn min aina? Who he is?
Deejasmah