CHAPTER 3
by @deejasmah
JIRWAYE.......
Khadeejah Bint Ismail (Deejasmah)
Young talented writers association (YOTAWA)
CHAPTER 3
Kamar yanda suka yi shirin tafiya kamun a ranar ta Alhamis suna dawowa daga classes ɗin su na ranar suka fara shiri inda da taimakon Mufee Adeeyah ta shirya cikin Buobou gown na lace baƙi da adon milk wanda Amah ce ta siyan musu same color da Ateeyah sai dai ita an mata riga da skirt kamar yanda ta fi ƙwarewa a sakawa ita kuma tayi Buobou don ba ta son kayan da zai matse ta ko kaɗan.
Sosai kayan ya fito da kalarta da take ji fair haka don ba fara ba ce tas amma ba ruwan tarwaɗa ba ne tana dai tsaka tsakiya, a kamammin fuska duk da tana kama da TeeTeen amma ta fita kyau ainun musamman ma da ya zama ba ta lalata skin colorn ta ba tana nan a yanda take ba ta shafa kowani kalar mai sai Nivea da Stella shower gel ɗin da take wanka kuma na Oriflame ne mara sa haske. A ƙyale-ƙyale na rayuwa kuma babu wani abinda yake burge ta a jikinta ma babu wani abun da zai iya burge kowa duk da tana da dirin da ko makaho ya shafa zai iya tabbatar da hakan amma kalar suturar ta kan ɓoye hakan. A komai na rayuwa she's exactly the opposite of TeeTee wata sa'ilin ma in zaka haɗu da su daban ma ba lallai ka lura cewa suna yanayi ba, don ita gashin da TeeTeen ta ƙara saboda DeeDeen ta fita ne amma ita kuma locking nata gashin tayi tun tana secondary school. Sai dai in ya mata tsufa a warware a sake wani duk bayan 2 weeks kuma take zuwa a wanke a gyara mata shi amma ko kusa ba ta kitso har ji ma take yi wani lokacin kamar a yanke mata shi.
Amma yau Bouboun da ta sanya ya mata kyau ainun musamman da Mufeen ta zauna ta yi waxing gaban gashin ya kwanta sosai, sannan ta mata ɗauri simple amma ya ɗan bayyana gaban gashin sai gyalen Chantilly da ya hau da kayan sosai. Sai dai a duk kyan da tayi da magiyar da Mufeen tayi akan ta saka wasu ƴan wedges nata ƙi tayi don tace ta barta da crocs ɗin ta su zata saka, babu yanda ta iya haka ta ƙyaleta jakar ma don ta dame ta ne ta riƙeta zama tayi a bunk tana jirar Mufee ta kammala sai ga kiran Rhidwan cikeda yatsine ta ɗaga don duk da tana son shi ta tsani nacin kira da zuwa.
Yanzun ma abinda ba ta son ya sanar mata wai yana cikin school ya kusa hostel ɗin su, cikeda tura baki tace masa ai za su fita ne ai ko yace in sun shirya sai ya sauke su a wajen bikin. Ji tayi kamar ta ce ya koma ba sai ya ƙaraso ba , dama ce masa tayi sun riga da sun tafi amma yanzu ba dama tunda yana hanya.
Mufee da ke ɗaura ɗankwali ne ta dubeta tana cewa '' what?".
''Rhid ne zai zo wai'' ta amsa not able to hide her annoyance.
Dariya ta saki tana cewa '' Ni fa ina son wannan soyayyar taku as, one time sweet and lovey dovey but another time kuma you'd be acting as if he's forcing himself on you bayan it's so obvious that he loves you ''.
''Na ji Malama ki yi ki shirya, he'd be here any moment''.
Uhmm ta furta yanzu kam ta ƙoƙarta ainun wurin haɗiye dariyarta tana jinjina kai tabbas Deeyah and Teeyah have quite something in common.
Cigaba da ɗaurinta tayi har sanda ya iso Deeyahn ce ta fita tana shaida mata yana waje waiting for them. Fita tayi ita kuma ta ƙarasa ta rufo musu ɗakin tana binta a baya.
Tun da ta fito yayi tsaye cur da idanun shi yana kallonta kai kace wacce aka canjawa halitta, she looks as exactly kamar ran da ya fara ganinta kyakkyawa da kyawawan takunta da ke kuma haskaka yanayin ta zai iya cewa tundaga ranar bai kuma ganinta irin haka ba but be just doesn't care not because bai son ganinta a hakan but because bai son ya nuna mata kamar kwalliyan ta ya kawo shi yanda yake kallon nata kuwa ya kuma sakawa ta na jinta very self-conscious karon farko a rayuwarta she isn't someone that gives a damn about how she looks amma a yau ta ji kamar ta tsaya ta tambayi mutanen da suke a gefen ta '' how does she looks?".
Inda Allah ya taimake ta bata kai ga tambayar ba ya ba ta amsa da '' Ya Ilahiy,Bae you look so gorgeous ''.
Ɗan duƙar da kai tayi tana sakin ajiyar zuciya all the weirdness da take ji yana sauka a hankali, murmushin da ba ta san yana ƙara mata kyau ba tayi tana ɗan juya masa idanu ba tare da ta sani ba. Wani shegen murmushi ya saki yana ciro wayar shi yana ɗaukarta hoto, ji tayi kamar ana wani ma ya ɗauketa amma ta rasa ta ina mai ɗaukar yake waige ta fara yi sai dai babu kowa a gefen nata. Dawo da kallonta tayi kan shi tana jin duk excitement ɗin ta na guduwa don a duniya ta tsani ta jita somehow watched, sosai canjin nata ya ba shi mamaki sai dai kafin ya kai ga faɗin wani abu Mufee ta fito sai kawai ta saki ajiyar zuciya tana nufar ƙofar motar bin ta yayi ya buɗe mata ta shiga ta zauna daidai da isowarta wajen jin suna gaisawa ya sanya ta tuna ' wai ashe fa ba su gaisa ba'.
Sai da ya tada motar kafin ta iya gaishe shin ya amsa a ƙasan maƙoshi yana tambayar ta inda suka nufa, Ahmadu Doka ta amsa masa a hankali.
''Ta wurin MTN office?".
''Yeah ta nan''.
''Ta singer za mu fita kenan'' ya furta yana jan motar zuwa gate, hira suke yi ƙasa-ƙasa inda ba ta wani ja da nisa ba ta sake saboda tabbas Rhid gwanin iya kawar da damuwa ne da ɓacin rai without even trying hard to do that.
Ficewar su daga harabar hostel ɗin ya sanya shi fitowa daga maɓoyar shi dake nan tsakanin Royal Tropicanan da kuma PG yana sakin ajiyar zuciya, kallon gefen shi yayi ya tabbatar babu wanda yake wucewa gyara p-cap ɗin shi yayi yana sakin wani makirin murmushi a hankali yace '' Su kuma dukan su mayun maza ne kenan? But what's the relationship between her and this guy and who even is he?".
Wannan tambayar kan shi yayi mawa amma kuma sai ya ji kamar wani assignment ne ya ƙaru a kan wanda aka ba shin, wani machine da ke parke na dispatch riders ya nufa ya haye yana mai lissafi a kan shi. Bai bi su ba don bai cikin aikin shi for that day don task ɗin da aka ba shi kawai ya nemo wacece twin ɗin Teeyah Hussein Shamaki ne nothing more nothing less, a yau kuma ya samu duka information ɗin da yake nema a kan ta har ma da ƙari tabbas tips ɗin shi na ranar sai ya fi na kullum. Jan machine ɗin shi yayi zuwa ɗayan assignment ɗin don an tabbatar masa da yau TeeTeen zata fita kuma har location ɗin inda zata jen an tura masa.
Seems like we too have a stalker😶.
Around 4:30 suka iso venuen kamun inda ake yi a cikin gidan su amaryan, wurin ya haɗu ainun musamman yanda aka yi decorating wajen ga ƴan mata sun ci ankon adire sai kaiwa suke da komowa. Su na zuwa Aunty Mami ce ta musu iso cikeda jin daɗin zuwan nasu don akwai ta da son mutane sosai kuma bikin ƙanwar mijinta ake yi ga shi ba ta da ƴanuwa da yawa a Kadunan duk sauran suna can Zaria wainda suke garin duk sun zo mata bikin don haka cikin su suka shige suna kallon tsarin kamun.
Shelar shigowar amarya da ƙawayenta aka yi wanda ya sa tayi focusing tana duban su, ai ko sai ga su nan sun shigo da wata kalar step dance da alamun sun tanade shi don yau kuma an daɗe ana rehearsal inda aka saka musu waƙar Ali Jita na sadaki. Karaf idanunta ya faɗa kan TeeTeen da ke kusa da amarya tana mata liƙi MC ko sai mata kirari yake yi '' Ɗawisu sarkin ado, fara mai farar aniya aminiyar ƙwarai ga amarya, yanda kike fara haka zuciyarki ma take fara. Ƴar gidan Shamaki kun yi gadon Alkhairi, ka ga cinyar sa maganin mai haɗama''.
Sosai kirarin yake shigar ta don ko sai sake ɓalle mint take yi tana liƙi, fuskar nan da ɗan murmushin da kallo ɗaya DeeDee ta mata ta san cewa she's faking it don ita ko kusa ba gwanar murmushi ba ce. An ci ɗinkin nan fitted gown da ya kama ta tsam a duk curves ɗin ta, yau ɗin ma ko arziƙin gyale ba a samu ba ɗankwalin kan nata ma wani kalar ɗauri aka mata da ya fito da gashin nan da aka kama in ponytail ya zubo har gadon bayanta. Makeup ɗin da aka mata ko ya ɓoye kamanninta ta yanda ba lallai mutanen wajen su gan shi a fuskar poor Adeeyah ba. Don ko kusa babu haɗi ita dai ko a jikinta sai ma cewa Mufee tayi '' da alamu Tee tana da kusanci da amaryan can sosai''.
''That's what I've been saying I thought kin ce bata da friends mata sai maza''.
''Sure, shiyasa abun ya bani mamaki ko ita amaryan ƴar Greenfield ce?".
Wata mata daga gefensu tayi karaf tace '' ai ko can take ita ma wannan mai liƙin ai an ce a can suka haɗu''.
''Allah sarki'' ta amsa tana kuma kallon filin rawar imagining yanda amaryan tayi convincing TeeTeen har tazo mata biki talkless of yanda tayi uwa tayi makarɓiya a bikin knowing quite well itama hates weddings fiyeda tunani, sai kuma ta taɓe baƙi a ranta tana jin daɗin yanda ta fara ƙawance da mata in aka ci sa'a zata iya yanke alaƙarta da wainnan mazan.
We hope so.
Ita ba ma ta san da suna wurin bikin ba sai da aka tashi kamun ta nufi wurin motar ta da niyyar barin wajen DeeDee ta mara mata baya tana kiranta da sunan da ita kaɗai ke kira wato ''TeeTee, Tee''. Da sauri ta waiga tana kallon mai bin ta a bayan tun daga sama har ƙasa, expressions ɗin fuskarta so disgusted kamar ta ga abun ƙyamar nan. Tana isowa ko ta tarbeta da cewa '' Really? DeeDee Shamaki? I thought 'we' hate weddings '' stressing the word we.
''Is that what you tell your twin sister you haven't met for 2 weeks?".
Taɓe bakinta tayi tana jifarta da wani kalar kallo kamar irin ta ga ƴar maulan nan tace '' ina tambayarki me kike yi a nan? Ke me yasa ba ki son zama inda Allah ya ajiye ki? How could you just barge in here to disgrace me?".
''I'm not here for you''.
''Then what are you here for? Looking like this?" Cikeda wulaƙanci kamar ba abokiyar haihuwarta ba.
Iska ta fesar tana kallonta bakinta kamar an ɗaure ta rasa mai ma zata faɗi in da Allah ya taimake ta ma a hankali take maganar don inda tayi da ƙarfi sai kaf mutanen bikin sun san me suke ciki don TeeTee akwai murya.
Baki ta buɗe da niyyar ba ta amsa ta katse ta da cewa '' Never mind, but stop disgracing yourself by trying hard to fit into any circle because you just can't. Take this as an advice from someone you know, it'll help you''.
Tana faɗin haka ta faɗa motar ta tana mai jan numfashi, sai dai ta ƙasa driving kan ta ta bar wurin da ƙyar ta samu ta fita daga gidan tana ko fita ta yi parking tana mai dafe zuciyarta. She just can't deny the fact that DeeDee ta yi kyau wanda shi ne abinda yake tsikarinta a rai ba komai ba, ta tsani ta ganta ta saka kaya masu kyau shiyasa take jin daɗi in ta ganta da kimonos ɗin ta ko baggy trousers. Ta tsani jama'a su san ta har suyi acknowledging ɗin ta as ɗiyar Hussein Shamaki, ta fi son har ƙarshen rayuwa ta zama ita ce kaɗai wacce duniya ta sani da wannan sunan wanda ba zai taɓa yiwuwa ba indai har zata dinga shiga cikin mutane. Hannu ta kai ta buga steering wheel ɗin tana jin kamar ta koma ciki ta janye ta ta ƙarfi da yaji amma hakan won't help the matter don kowa sai ya san me take ciki, zai kuma yi affecting that image da ta sha wahala wajen building a wajen mutane. She's a model wacce ba ta taɓa shiga scandals ko wani kala ba na social media ya zata yi idan har duniya ta ɗauki cewa tana wulaƙanta twin sistern nata? May be it'll be the end for her, kwantar da kanta kawai tayi tana jin komai ya ƙwace mata.
Ka ji masifa sai kace wacce ta haɗu da maƙiyiyarta ba ƴar uwarta ba, hassada ce take damunta ba komai ba fa.
But hassadar har da ƴaruwarka?.
Tana zaune a cikin motar ta ga fitowar su a motar Rhid, tsaki ta ja a bayyane ta furta '' wahalallu haka zaku ƙare ai'' ta ƙarashe tana tada motar ta mara musu baya.
DeeDee dai abun ya dake ta duk da ba yau ne karon farko da ta wulaƙanta ta ba amma na yau ɗin sosai yake damunta, ba ƙaramin ƙoƙari tayi wajen dannewa ba har murmushi take yi tana biyewa Rhid da hirar shi yayinda a can ƙasan ran ta take maimaita innalillahi ta ko samu salama a rai da zuciyarta sai kawai ta ji komai ya wanye kamar ma ba a yi ba.
As expected inuwarsu dai ya naɗi duk abinda ya faru har da videos da yayi musu ba da sanin su ba yana turawa wajen wanda ya saka shi aikin.
Somewhere in Nigeria.
''Bro you just can't believe it, yarinyar can ƴar akuya ce fa she's beefing her real twin for crying out loud'' ya furta yana zama a kan couch har lokacin da wani kalar dariya. Magana aka yi daga can sashen wanda ya sanya shi kuma sakin dariya yace '' Wallahi fa but It's making it more interesting zan tura maka videon ka gani''.
''Alright Bro, zan tura masa ai yayi ƙoƙari sosai yaushe zaka shigo ne?".
''They won't be patience enough to wait for you, ka san dai kana shirin ƙure su ko? They are doing all these because........''
Ding yaji an katse wayar ta ɗayan end ɗin, numfashi ya sauke yana jinjina halin ɗan uwan shi shi dai bai son a gaya masa gaskiya akan zuwa gida. Wanda shi ne babbar matsalar da ke damun matasan mu da sun ƙetara sun bar gida sai an yi fama da su kafin su juyo gida, ɗaiɗaiku ne kaɗai suke tunanin gida har ma kan zo su ga iyaye su koma bakin aikin su.
Toh Allah ya shirya su da mu ya kawo sauƙin lamarin.
Ameen.............
Deejasmah.