Page 16
by @sanazty
WUTAR ƘAIƘAYI
Wattpad@SaNazdeeyah_
_Arewabooks@sanazty
Facebook@SaNaz Deeyah
Youtube: ***
KARAMCI WRITERS ASSOCIATION
[karamci tushen mu'amula ta gari]
Saura Pages 4 free pages sun ƙare, har na gama da group 1 grouo 2 yana jiran wanda basu biya ba, ku hanzarta a karanta tare daku
Book 1
```🆓Page 16```
Kallon Affan ta yi ta ga ya haɗe rai, ta mayar da kallonta ga Yazid daya ke tunkarosu tare da Lukman abokinsa, sai dai tun kafin su ƙarasa Faruq ya tare su, Sadiya ta lumshe ido ta yi dan ta san zuwan Faruq ba zai haifar da ɗa mai ido ba.
"Malam lafiya kuwa? Na yi tunanin babu abinda ya yi saura, mene ya kawo ka gidanmu?"
Murmushi Yazid ya yi tare da faɗin "Akwai kuwa, idan ka manta zan tuna maka, akwai Najma da Ihsan kuma sune suka kawo ni gidan nan"
"Su ma a yanzu baka da cikakken iko dasu, dan haka ka fice ka bar mana gida"
"Kodai har yanzu baka warke daga ciwon son ba? To ka sani Sadiya ta maka zarra kuma tafi ƙarfinka, koda a mafarki kuwa" Jin haka ya saka Faruq cikin ɓacin rai ya ɗaga zai wanke Yazid da mari. "Faruq...." Sadiya tayi saurin furtawa, hakan ya saka shi tsayawa cikin ɓacin rai ya juya ya kalleta. Da sassarfa ta ƙaraso inda suke. "Baka da hankali ne? Abban su Najma ne fa"
"Koma waye?" Ya furta cikin tsawa.
Jin hayaniya ya saka Saddiqa da Surayya fitowa daga cikin gidan.
"Yazid kuma a gidan nan" Saddiqa ta faɗa tana ƙarasawa.
"Lafiya kuwa? Mene ke faruwa?" Ta furta lokacin data ƙarasa gabansu.
"Kana kallo wannan zai aureta, saboda tafi ƙarfinka har abada." Ya nuna Affan da hannu.
Hannu Sadiya ta saka ta dafe kai, ganin Yazid na neman tona sirrin da babu wanda ya sani.
"Wai mene ke faruwa ne? Yazid dan Allah kar ka biyewa Faruq ku yi ta sa'in sa"
Kallonsa Faruq ya yi sannan ya ce "To bari ka ji muna nan da kai zaka ji labarin aurena da Sadiya kai ni da kaina sai na kawo maka katin ɗaurin aure"
Surayya baki ta saki, yayinda Saddiqa ta ɗauki maganar Faruq a matsayin shirme. "Faruq idan na isa to kar na kuma jin kayi magana"
"Aunty Saddiqa ki ƙyaleni da shi yana kallona a matsayin wanda ba zai iya ba"
"To ina iyawar bayan har kayi jinya ka tashi bata so ka ba, idan da zata so ka ai da tun kana jinya ta tausaya maka, ko ka ɗauka ban san komai ba, Sadiya ba matar yara bace"
Sai lokacin Sadiya ta fashe da kuka, kawai ta durƙushe a ƙasa. "Faruq ka koma cikin gida ko na kira Mameey"
"Babu inda zan koma sai dai idan tare da ita dan ba zan barta da wannan azzalumin ba"
"Sadiya tashi ki koma ciki" Saddiqa ta faɗa tana kama hannunta.
"To mene ya kawo shi, ya koma inda ya fito"
"Ina ruwanka kai dai ka tafi kawai" Ta faɗa rai ɓace.
Tana miƙewa ta janye hannunta daga na Faruq ta ƙarasa gurin Affan da sauri.
"Affan dan Allah ina so ka turo magabatanka tare da sadaki a satin nan"
"Am....Sadiya am very sorry ni ban san mene zan faɗa ba am speechless because shi wannan ɗan uwanki ne, wannan kuma tsohon mijinki kuma akwai yara tsakani"
"Karka damu, ka tafi kawai zamuyi waya" Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "But dan Allah kar ki ɗaga hankalinki" Kai ta gyaɗa tana murmushin yaƙe.
Suna zaune a falo kowa ya yi shiru, har lokacin Sadiya ta kan goge hawaye, shi kuwa Faruq ransa a ɓace yake sosai ganin Mameey ta bawa Yazid damar shigowa.
"Dama nazo ne na karɓi yarana ne dan ina so riƙonsu ya dawo hannuna" Cikin tashin hankali Sadiya ta ɗago kai tare da faɗin "Wallahi baka isa ba, ba zan taɓa yarda in bayar da ƙananan yarana ba"
"Kar na ƙara jin kinyi magana" Mameey ta faɗa rai ɓace "Dama ko bai zo ba na yi niyyar mayar masa, dan bana so ya riƙa mana sintiri gida, na fi so a yi rabuwa ta har abada" Da sauri ya ɗago ya kalli Mameey sai kuma ya sake sauke kai ƙasa. Faruq kuwa daɗi ya ji sai dai bai so Mameey tayi furucin zata mayar da su Najma ba.
"Mameey gaskiya nima ban bayar da goyon bayan a ba shi yaran ba, saboda mata ne kuma baya da aure." Saddiqa ta furta rai ɓace.
"Amma ai ina da iyaye, kuma ina da ƙanne mata"
"To hakan me zai amfanar? Yazid wallahi ba zan iya baka yarana ba, sai dai duk abinda zakayi ka yi, saboda ban san wane hali za su shiga ba idan bana tare dasu"
"Idan kuma mutuwa kika yi fa? Ba dole a wani wurin za su rayu ba, ni kuma wallahi sai kin ba shi yaransa, sai mu ga idan rantsuwarki tafi tawa."
"Mameey a gaskiya nima ban bayar da goyon bayan a bawa wannan azzalumin yaran ba" Faruq ya furta yana haɗe rai.
"Azzalumin ai ubansu ne idan ya ga dama ya kashe su ai jininsa ne"
Da sauri ta miƙe cikin tashin hankali tayi bedroom ɗinta, Yazid da ido kawai ya bita yana jin zafi a ransa.
"Surayya tashi ki haɗa sauran kayan yaran dama yanzu suka dawo ai, ya ɗauka ya tafi."
"Mameey dan Allah kar ki raba Aunty Sady da yaranta"
"Kiyi abin da na ce ko kuma ranki ya ɓaci"
Da sauri itama ta miƙe ta bar parlourn.
Bayan Wasu Mintuna
Jin kukan Najma ya saka ta miƙe daga kan gadon, idanuwanta jajir ga kanta da yake sara mata haka ta fita falo taga Yazid ya ɗauki Najma sai zullo take, Ihsan ce bata ma yi kuka ba, za ta ƙarasa gurinsu Saddiqa ta riƙo hannunta, ta kalleta cikin tashin hankali sai ta ga ta girgiza mata kai saboda lokacin Mameey na tsaye.
"Ba su ƙaunata wallahi na san ba za su riƙe min yarana ba, dan Allah kar ku rabani dasu" Kuka sosai take kuma a fili, Faruq ya ƙaraso gurin tare da kallonta "Ki bari su tafi amma na miki alƙawarin za su dawo"
"Sai dai idan bayan raina" Mameey ta yi maganar da ɓacin, da sauri Yazid da Lukman suka bar parlourn, ita kuma Sadiya ta ƙarasa gaban Mameey "Mameey nice baki so? Idan har baki son su Najma saboda Yazid to nima baki sona, saboda idan da jinin Yazid a jikinsu nima akwai nawa, nina haifesu Mameey yadda kike jin son mu nima haka nake jin son yarana ak....." Bata ƙarasa ba taji saukar mari, ta riƙe kumatun sannan ta kalli Mameey "Ki dawo cikin hankalinki, da ina sonki ai kin ƙunsa min baƙin ciki kin auri wanda ba zaɓina ba, ƙasƙantattun mutane masu baƙar zuciya, to baƙin cikin da kika ƙunsa min rabinsa baki ji ba a yanzu" Doguwar ajiyar zuciya ta sauke sai kuma ta ɗiba da gudu kamar mahaukaciya ta fita, Faruq ya rufa mata baya.
A gabansu Yazid ta ja tunga lokacin suna gab da get.
"Yazid dan Allah ka mayar da aurenmu ko dan yarana, na san za su sha wahala idan ba su tare dani"
"Kiyi haƙuri Sadiya, na miki alƙawarin yaran nan za su zauna ne kamar kina tare dasu"
"Yazid wane zunubin na aikata maka da kake son rabani da rayuwata, ina son yarana dan Allah ka tausaya min" Ta furta tana kai gwiwoyinta ƙasa, Lukman wucewa kawai ya yi dan ji ya yi kamar zai zubar mata da hawaye.
Faruq na ƙarasowa ya fuzgi hannunta har sai da ta miƙe tsaye, ta kalleshi rai a ɓace ta ce "Ka cika ni"
"Ba zan cika ki ba, bai kai matsayin da zaki durƙusa masa ba saboda babu laifin da kika masa"
Ɗayan hannu ta saka tana ƙoƙari fuzge hannunta daga riƙon da Faruq ya mata amma ta kasa. "Kiyi haƙuri Sadiya" Shi ne abinda Yazid ya furta sannan ya wuce. Hannu ta saka ta riƙe wuyanta saboda jin wani abu daya tokareta, bata san lokacin data ɗora kanta a ƙafaɗar Faruq ta fashe da kuka, shi kuma a lokacin ya ji wani abu ya tsikareshi tun daga babban yatsa har ƙwaƙwalwa, sai dai ba zai iya janyeta ba, kawai ya sauke ajiyar zuciya ne.
*Dare*
Yana zama ya kallesu. "Ya naga fav bata fito ba?"
"Waye kuma fav ɗinka?"
"Ai kin san waye baya anan?" Ya mayarwa da Surayya amsa. Dan a yanzu da yake jin zai iya zama da ita a matsayin mata, ba zai iya kiranta da Aunty ba sannan ba zai iya faɗin sunanta gatse-gatse a gaban wasu, amma a gabanta yana iya faɗa.
"Sau biyu ina zuwa amma taƙi fitowa kuka kawai take, ga Aunty Saddiqa ta tafi."
Miƙewa ya yi Mameey ta kalleshi "Faruq ka zauna ka ci abinci kar ka biye mata, idan yunwar cikinta ta dameta za ta fito ta nema ai"
"Ba zan iya ci ba idan har bata ci ba."
Ya ɗebi abinci mai yawa a plate sannan ya ɗauki gorar ruwa ya wuce.
Yana shiga ya ganta a kwance kan gado ko ɗankwali babu ta baza gashin kanta da yake a tsefe yake, bata ɗago ba duk da ta san an shigo, a gefen gadon ya zauna sannan ya ɗauki ɗankwalinta dake gefe.
"Sady!"
Jin muryar Faruq ya saka ta yi saurin ɗagowa ta kalleshi, miƙa mata ɗankwalin ya yi ta karɓa tare da ɗaure kanta sai dai gashin ya fito ta ƙasa kasancewar tana da yalwar gashi. Kallonta yake sai yake ganin kamar ta koma masa wata sabuwa fil a leda, ya ƙare mata kallo tun daga sama har ƙasa zuciyarshi na jin kamar ya janyota jikinshi ya rarrasheta. Ajiyar zuciya ta sauke ya dawo daga duniyar tunani daya faɗa, ba shi take kallo ba idanuwanta na kallon gefe.
"Abinci na kawo mu ci, dan na ce idan baki ci ba nima ba zan ci ba"
"Na ƙoshi"
"Ni na san kina jin yunwa, dan Allah karki azabtar da kanki da yunwa."
Kuka ta saki a fili ta kalleshi "Yaro me su Najma suka yiwa Mameey ta tsanesu, ko zata tsanesu saboda Yazid nima ya kamata ta sosu saboda ni, amma tun kafin na samu matsala da Yazid dama Mameey bata ƙaunar yarana"
"Wallahi Mameey na ƙaunarsu, kawai dai Yazid ne take jin haushi"
"Na san an rabani da yarana ne saboda a ƙuntata min"
"Na miki alqawarin yaranki za su dawo gareko ko ba yanzu ba"
"Idan har ba su dawo gareni a yanzu ba na san ba za su dawo ba, saboda bani da yadda zan yi"
"Akwai"
Kallonshi tayi da rinannun idanuwanta ta ce "Ta wace hanya?"
Plate ɗin ya ajiye a side drawer sannan ya kalleta. "Idan kika aureni ni ne zan riƙe yaranki tamkar mahai...."
"Ya isa Faruq" Ta furta sannan ta dafe kai.
"Ka riƙa faɗin abin da zai yuwu"
"Kina ganin kamar ba zai yuwu bane?"
"E, saboda ni yayarka ce, kuma bazawara"
"A hakan nake sonki"
Murmushi takaici tayi tare da faɗin "Idan har ba so kake zuciyata ta buga ba to ka tashi ka fita ka bar min ɗaki"
"Sadiya..."
"Ka fita Faruq" Ta furta cikin tsawa.
Miƙewa ya yi ya ce "Zan iya fita daga cikin ɗakinki amma ba zan iya fita daga rayuwarki ba, ina sonki kuma a wannan karon zan yi yaƙi ne har sai naga na mallakeki, kuma zan sanarwa da kowa cewar ke nake so ciki kuwa har da Baffa Umaru."
"Idan kai mahaukaci ne ai su ba mahaukata bane."
"Na haukace kam indai akan sonki ne ai na daɗe ina hauka" Yana gama faɗa ya fice.
Ranar shima bai ci abinci ba haka ya kwanta ya kuma kasa bacci, yana ta tunanin ta ina zai ɓullowa lamarin, haka ɓangaren Sadiya kwana tayi tana kuka, idan ta gaji zata huta sai kuma ta ɗora daga inda ta tsaya. Tun asuba Mameey ta jiyo kakarin amai, dan haka da sauri ta nufi ɗakin nasu.
Surayya ta riƙeta a toilet ita kuma sai amai take babu komai a aman face ruwa. Hannu biyu ta saka ta riƙe kanta saboda juya mata da taji yana yi.
"Kin ga maza je ki kira Faruq"
"Mameey gani, yanzu na dawo daga masallaci, waye ba lafiya?" Ya faɗa yana shigowa dan shima kakarin ne ya saka shi shigowa ɗakin.
"Sadiya ce babu lafiya ka ɗauki key a ɗakina kan mirrow ka fito da mota mu kaita asibiti"
Da sauri ya juya ya fita.
***** *****
Ba su katse mata magana ba har sai da ta gama tare da jaddada masu cewar suna son tsayar da ranar biki nan da wata uku.
Ayda ta yi murmushi tare da faɗin "Kuma ni Affan bai sanar dani ba, amma Anni kece kika yanke hukunci ko kuma wa?"
Kallonta Anni ta yi kafin ta ce "Ya miki yawa ne a rage?"
"A'a Farhan batayi magana ba sai ni"
"To ai na ga kece mara kunyar tunda maganar bikinki ake kike tsoma baki"
Jin haka ya saka duk yanayin su ya canja, "Anni bikina ko dai na Farhan?"
"Bikinki da Affan dan cewa ya yi kece zaɓinsa" Bata san lokacin da ta miƙe tsaye ba, Farhan kuwa ji tayi gabanta na bugu.
"Anni hala kin manta ina tare da Nasir? Kuma ko da Affan yazo mun yi deciding Farhan, itama har ta aminta da shi"
"Wane aminci ita da ko number juna basu, ta riƙa shan ƙamshi tana miskilanci na iskanci, to ai kuwa idan ma hange take ta daina, saboda ke ya zaɓa kuma babu abinda zai hana aurenku"
Farhan da gudu ta yi ɗakinta, ita kuma Ayda ta dafe kai. "Anni dan Allah ki ƙara magana dasu wallahi ina son Nasir."
"Kina son Nasir amma ƙaddara Affan ta zaɓa miki, Ayda shi fa Nasir ɗin nan bai shirya aure ba, saboda sau biyu ana cewa ya fito amma yaƙi, to mene amfanin soyayya da gaibu?"
Duk yadda taso Anni ta fahimta amma ta ƙi, sai kawai ta juya ta yi bedroom, tana shiga Farhan ta ɗago ta kalleta. "Wallah ban ga wanda ya isa ya hanani auren Affan koda kuwa kece"
Cike da mamaki take kallon Farhan, sai kuma ta goge hawaye tana murmushi. "Wai kina yiwa Affan wannan son amma kika kasa tsayawa ku fahimci juna?"
"Ke Ayda ki shiga hankalinki, ni ba sa'arki bace"
Murmushin yaƙe tayi sannan ta ce "Tun zuwansa ni ban ɗora raina a kan shi ba, saboda ina son Nasir kuma da shi nake son rayuwa."
"Idan har haka ne meyasa Affan ya zaɓeki?"
"Saboda shimfiɗar fuska tafi ta tabarma, zan faɗa miki gaskiya wannan jan ajin da kike yi babu abinda samari ke kallon shi face wulaƙanci, ko shi Affan tun ranar daya zo abinda kika riƙa yi naga bai ji daɗi ba kuma fuskarshi ta nuna, sai dai shi mutum ne mai zurfin ciki shiyasa ma bai taɓa faɗa min ba, kuma idan kin lura bai kuma dawowa ba. Sai dai ya faɗa min cewa zafin kishin matarsa ta farko shi ne abinda ya jawo mata baƙin jini a gurin family sannan kuma ya fara tunanin ƙara auren wannan yarinyar da aka kashe gab da bikinsu."
Zama Farhan ta yi tare da faɗin "Nima da wasa nake, kin san bani da wannan kishin"
"A yanzu ba zan gane ba, amma a shawarce ko kina da shi to ki rage.
"Ayda wallahi na ji ina son shi, ta ina kike tunanin zan ɓullowa lamarin?"
"Dole mu zauna mu nutsu sannan mu yi tunanin mafita."
Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting.
VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:
Guda 1: ₦500
Guda 2: ₦900
Guda 3: ₦1400
Guda 4: ₦ 1800
Za'a turo kuɗin ta wannan account.
Acct no: 6370370016
Acct name: Halima Salahu Adamu
Bank name: Fidelity Bank
Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number ***
Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number ***.
Shaidar biya ta wannan wannan number ***
lLITTAFAN SUNE:
1-WUTAR ƘAIƘAYI
2-WA'ADI.
3-A CIKIN IDO..
4-TAZARAR SO
#FITATTUHUƊU2025
#WUTARƘAIƘAYI
#SaNaz_deeyah