1&2
by @mommuhseen
SAHAAR
ADABI WRITERS ASSOCIATION
BY
MOM MUHSEN
🅿️...1&2
Tsaye nake gaban island d'in kitchen d'in dukkan jikina rawa yake yana tsuma kamar wacce aka tsamota da cikin ruwan k'ank'anra tsabar masifar da UWARGIDA HAFSA keta tsula mun,hannuna kanshi kasa sarrafa kanshi yake wajen firar Irish d'in da nakeyi,cikin wannan yana yin ne naji wuk'ar tayi wucewar mashi da hannuna,na saki wata azababbar k'ara ina sakin wuk'ar,jini kuma ya samu hanyar bulbulowa kai tsaye.
"Innalillahi,SAHAAR yankewa kikai?"
Muryar Anti Jamila naji data shigo yanzu,tana isowa da sauri ta kama hannun nawa tana tara shi ga famfon sink tana wanke mun,hawaye na zubo sosai tana ta jeramun sannu da nuna jimamin ta.
"Nasha fad'a miki ki ringa kula,ki ringa natsuwa kina aiki ina hankalin ki yake ne?"
Babu bakin magana sai kuka da nake k'asa-k'asa,inajin zafi da rad'ad'in ciwon har a raina, "muje UHAIMID ya miki dressing,wuk'ar ta same ki sosai"
Girgiza mata kaina nayi da ruwan hawaye idona nace, "UWARGIDA tace mintuna ashirin ta bani na gama aikin........Dalla wuce muje kafin na sab'a miki"
Haka ta jani zuwa upstairs dakin oga U'HAIMID,duk da yadda hannun nawa yake rad'ad'i da zogi hakan bai Hanani jin fad'uwar gaba da zullumi ba,sanyin da fitinannen kamshi ne ya buso mana bayan munyi knocking an bud'e,jinai har cikin k'ashina sanyin, kamshin kuma yana ratsa hancina har cikin kwalwata,duhu dakin ko ina rufff hasken kad'anne daga waje yake haskowa ta labulayen dakin, "Ka kunna mana haske pls bama ganin komi fa"
"I'm sleeping Baby"
Yai mgnr cikin wata lalatattar murya mai cike da shagwab'a da bacci cikin ta, murmushi tayi tana cewa "Sorry U'HAI Sahaar ne taji ciwo zaka mata dressing"
Shiru yai na wasu mintoci kamar bazai motsa ba,sai kuma haske ya bayyana ya dalle mana fuskokin mu har saida na rufe idona saboda kaifin fitulun,Toilet ya shiga ya barmu nan kafin na soma bin dakin nashi da kallo kamar dai yau na soma ganinsa,bana gajiya da kallon dakin had'ad'd'en dakine kamar a turai,minty biyar ya fito da damshin ruwa fuskar shi kamshin mouth tooth di'n daya wanke bakinsa ya iskeni har hancina , ta jani har kusa dashi na zauna a bisa sofa, "Ka gani ciwon,yanzu ta yisa da wuk'a"
Idanunsa suna wani lullumshewa yana bud'esu daker ya dora akan fuskata maimakon ciwon da take nuna masa, cikin sauri na sauke idona kasa ban yarda munyi four eyes da idaanun nashi ba, jinai ya rike hannun sosai muryar sa d'in nan mai laushi yace "wuk'ar ta shiga ciwon sosai" jinai yakara bude hannun yadda zaiga ciwon,na saki kara ina kiran "wayyo Allahna"
"Sorry"
Anti Jamila ta fad'a da tausayawa, saida ya gama gani duk hanky din dake hannuna ya jik'e da jini, baice komi ba ya tashi ya dauko fix aid box dinsa ya zauna bisa lallausan carpet din dake jikin bed d'insa kamar gashin mage, jikinsa kayan bacci ne riga da wando masu azabar laushi kalar milk, ya soma fiddo abubuwan da zai aiki dasu yana ajewa, zuciyata kamar zata fad'o k'asa saboda zullimin allura da aidin, "Ki natsu ki daure inba haka ba haka zaki ta fama dashi bazai warke da wuri ba"
Antin ta fad'a mun cikin nuna kulawa,kaina kawai na d'aga mata na sauko na zauna gabanshi ya rik'e hannun zai fara goge jinin da aidin d'in,muka had'a ido dashi kafin yawani lumshe ido yana cewa, "ba zafi ai"
Dai-dai sadda ya soma aikinsa cikin kula da kwarewa, runtse idona nai kwalla na silalomun,Anti na dafe dani kusa da jikinta tana mun sannu,d'inki aka ma hannun amma ya mun allurar kashe xafi duk da haka saida naji zafi,aka gama komi yace "Za'a anso magani anjima sai ta sha"
"Thank u U'HAI"
ya mata wani killer smile yana lumshe idanunsa,nidai ficewa nai daga dakin bazan iya tsayawa kallon iskancin su ba,basa jin kunyar kowa in suna tare da juna.
********
Aikin yamma kau saidai sauran yan aikin suka yi saboda zazzab'in daya rifeni bayan nayi wanka,ko abinci ban iya samu naci ba saboda zogin hannun,har la'asar ina kwance sai hawaye nake wata irin kewar Anna tana walagigi dani, Daker nayi sallah na dawo na kwanta kasan tayils din falon namu anan Bq din gidan, idona rufe inata sauke numfashi har bacci ya daukeni,ban farka ba sai magariba shima shigowar Humaira ta tadani jin jikin nawa da zafi rau hankalinta ya tashi, ta kamani nayi watsa ruwa ta ruga dakinta ta dauko pcm ta kawo mun, ta iske ina ta amai duk ta rikice baiwar Allah saida ta gama gyara wurin aman tace "Hadda ma yunwa Sahaar da alamun bakici komi ba,wallahi ban samu zama ba shiyasa ban shigo na dubaki ba,sai karfe biyar na gama yima UWARGIDA HAFSA dambun kifi,Ina gama wa bacci ya daukeni,bari naje na duba inga abunda zaki iyaci"
Kaina kawae na d'aga mata ban iya cewa komi, Ina kwance k'asan kawae naji kamshin turarensa kasa ma daga kaina nayi balle na kallai, durkushinsa naji gabana dai-dai shigowar Humaira tana sallama,ya ansa mata cikin sanyin muryarsa ta aje plate din tana gaida shi,
"Mike ya same ta?"
Humaira tace "Zazzabi ne ya rufe ta yanzu na iske tana amai shine naje na kawo mata abinci"
Hannunsa ya saka a goshina, "Ohh my god,na mance da magungunan"
Ya kalli abincin duk karshen tukunya ne ma ya bushe, ya mik'e yana cewa ma Humaira, "Saka mata Hijab ki kawo ta motana"
Cikin hanzari ta kamani, na fizge nace "ke ni bazan je ko ina ba"
Humaira ta dalla mun harara, "dad'ina dake wauta wallahi dilla sanya muje"
Sai hawaye suka balle mun, nace da muryar kuka "Anna ta mun iyaka dashi fa Humaira"
Bata saurareni ba ta kamani muka fito har compound d'in gidan,yana tsaye yana jiranmu front sit ya bude ta kamani na zauna, ya zaga ya shiga aka wangale tangamemen get din muka fice, wannan ne karo na biyu dana shiga motar sa tun tana sabuwa,sanyin Ac motar yasa na fara kerma ganin hakan yasa ya kashe ta duka,ya kwantar mun da kujerar na kwanta sosai Ina rufe idona,ban san inda zamu ba mun jima muna tafia kafin naji ya tsayar da motar, daker na bud'e idona na ganni Asibitinsu "Allah na rok'eka kasa kar amin allura"
Na fada cikin raina,bude kofar yai yana miko mun hannunsa,k'in kama wa nayi na yunkura na fito sannan ya rife motar bai sauraren ba ya rik'o hannuna zuwa ciki,ma'aikatan keta gaishe shi amma sai wanda yaga dama yake ansa mawa,Office dinsa muka shiga ya zaunar dani cikin three seater, hadda samun filo ya wuce bisa table d'insa yana yin waya ta landline,wlh duk yadda nake kusa dashi banji miye ya fad'a ba, yana gama wayar wayarsa tai kara ya fiddo yana dubawa, "Baby"
Kalmar da naji ya fad'a kenan,ban san ya akai naji ba na kuma sake jin yace, "Allura zan mata in tayi bacci kona one hour sai mu taho,No na sai kinzo ba"
"Ohk bye"
Lafiyayyen abinci ne da ferfesu da drinks aka kawo mun, ya sha murr yana hakimce cikin wata kujerar yana kallona,irin dan iskan kallon nan da bana so, "minty goma na baki ki cinyesu"
Na dago idanuna ina kallon shi dasu, "Kallan ni da kyau abunda kiji din haka nake nufi"
Nai kwalkwal da idanuna, "wallahi bazan iya cinye wa ba"
Na fada da muryata wacce tayi sanyi sosai, "kici iya cinki mugani"
Na fara motsa abincin ahankali amma hannuna kerma yake sosai,sai kawae ya taso ya zauna gefena ya dauki cup daya ya shiga wata kofa cikin office din, jimawa kadan ya dawo da tea mai zafi yana ta azababben k'amshi, ya kalleni yana miko mun "fara da wannan"
Ansa nayi na fara shaa yana cigaba da tsareni da mayun idanun shi, aikuwa na kware na hau tari saurin ansar cup din yai yana bubbuga bayana, na d'an matsa kadan ina cigaba da tarin, "Sorry"
Ya furta yana kallona kamar zai cinyeni, na dauki lokaci kafun ya lafa mun, raina adagule nama kasa cigaba da shan tea din,duk da yadda na soma jin yan cikina sun fara warwarwa amma bazan iya sakewa na cigaba da sha ba,idanunsa suna mun kaifi da yawa.
"In fita?"
Na masa shiru bance komi ba,sai ya tashin kuma ya fice saida ya kai kofa sannan yace, "Kafin in dawo ki tabbatar kinci saboda Allurar"
Tea din nasha rabin cup,naci cheeps din wanda laushin sa ya tafi dani ga kamshi,yayi dadi naci sosai banci naman ba nasha ruwa na kwanta,bacci ya soma d'aukana ya dawo nai saurin tashi zaune, ba zato naji ya tab'a goshina........"ka daina.......idanunsa ya zuba mun,dole na had'iye mgnr dake cikin bakin nawa, kwashe kayan yai kafin ya fara had'a ruwan allurar,dan danan gabana ya soma fad'uwa ainun, aduniya ba abunda nake masifar tsoro irin allura,shekarun baya nashata kamar me shiyasa na tsaneta......."A Ina zan miki"
Ya fada yana zama gabana bisa table din da aka dora kayan abincin dazun, numfashina keta sama da k'asa saboda tsabar tsoro, "I'm asking u"
Dago kaina nayi idona ya cika da kwalla, "Don Allah aban magani......shid'in ma ai ba sha kike ba"
"Zan sha,wallahi zan sha"
Wani gajeran murmushi ya saki yace, "Duka ba wanda za'a fasa zan miki allura kuma kisha magani"
Hawaye sharrr suka zubo ban damu na share ba, da rawar murya nace "Don Allah kar kamun da zafi"
Murmushin yake yana ta kallona, sai ya gyara zaman shi yana kallona sosai ya rage sautin muryar shi, "To ina zan miki"
Ban san sadda na mik'a masa tafin hannuna ba,abunda ya sanya shi sakin siririyar dariya zan iya cewa ban tab'a ganin yana dariya haka ba, na janye hannun ina share fuskata, "Ina kika tab'a ganin anyi allura a tafin hannu?"
Girgiza kaina nayi na kasa cewa komi, kallona kawai yake kamar ya samu tv ban san miyasa indai muna waje guda ba idanunsa basa da aiki sai kallona, "kin san yadda za'ai?"
Na girgiza kaina da sauri sai ya kalli saman cinyana, "Anan za'ai"
Na waro masa manyan idanuna masha Allah, "ba ayi a cinya, Allah ba ayi ban tab'a jin ayi ba"
Kasa rik'e dariyar sa yai ta fito,yana d'an duk'ewa yana yinta cikin wani irin class,sai kyansa ya kara fitowa sosai har yana kashe mun ido nai sakale ina kallon shi, yana tsagaita dariyar shi yace "Ki daina kallona haka, to ina kikeso na miki"
Duk naji na rud'e na marasa mizan yi, saboda bazan iya juya masa bayana ba saida yagaji sannan ya sauya fuskar shi, ya Koma U'HAIMID d'in dana sani mai miskilancin nan da izza, "jaye rigarki"
Na fara shashshekar kuka, "kina mun kuka wlh da zafi zan miki nama rantse"
Had'iye kukan nayi,na jaye rigar a hankali fatar cinyana ta bayyana fara sol sai shalki take,kamar dai ina amfani da supplement, rikicewa yai tashin farko zuciyarsa ta soma rawa ba arxiki,wani kafirin miyau ya had'iye ni kam runtse ido nai Ina jiran inji azabar karfen allurar, daker ya iya rike kanshi ya tsira har ya zare ban sani na,saida naji baya gabana da mamaki na bude idona, "An gama?"
"Aa yanzu za'ayi"
Kallon cinyana nayi naga alamum auduga hakan ya nuna cewar har ya gama, to amma ya akai banji zafi ba?
Magunguna ya b'alo ga kawo min,yana ban ruwa na fara sha da d'ai-d'ai har na gama fuskata a yatsine, filo ya samun a kujerar "oya sleep"
Zanyi magana ya d'ora yatsar sa a lips d'insa alamin baya son mgn,dole nai shiru na kwanta ina rufe idanuna.
Banyi alkawarin posting kullum ehe🧐🤓
Mom muhseen&Asad