FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample Β· 1&2
SAHAARADABI WRITERS ASSOCIATION BYMOM MUHSENπ ΏοΈ...1&2Tsaye nake gaban island d'in kitchen d'in dukkan jikina rawa yake yana tsuma kamar wacce aka tsamota da cikin ruwan k'ank'anra tsabar masifar da UWARGIDA HAFSA keta tsula mun,hannuna kanshi kasa sarrafa kanshi yake wajen firar Irish d'in da nakeyi,cikin wannan yana yin ne naji wuk'ar tayi wucewar mashi da hannuna,na saki wata azababbar k'ara ina sakin wuk'ar,jini kuma ya samu hanyar bulbulowa kai tsaye."Innalillahi,SAHAAR yankewa kikai?"Muryar Anti Jamila naji data shigo yanzu,tana isowa da sauri ta kama hannun nawa tana tara shi ga famfon sink tana wanke mun,hawaye na zubo sosai tana ta jeramun sannu da nuna jimamin ta."Nasha fad'a miki ki ringa kula,ki ringa natsuwa kina aiki ina hankalin ki yake ne?"Babu bakin magana sai kuka da nake k'asa-k'asa,inajin zafi da rad'ad'in ciwon har a raina, "muje UHAIMID ya miki dressin...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.