13&14
by @mommuhseen
SAHAAR
ADABI WRITER'S ASSOCIATION.
BY
MOM MUHSEEN
🅿️...13&14
Babu wanda na sanar ma da cewar na koma Hostel har sadda Anna zata dawo sai Humaira,saboda aganina ba buk'atar hakan kuma ma duk wanda zan sanar mawa d'in bai wuce Oga Fauzan ba,shi kuma yanxu ya zamar mun wani mutum na daban ban san miye a ranshi ba amma alakarmu tana sauyawa,ada d'ari d'ari muke da juna yanzu kuma yana yawan shigemun sosai,bana son kusancinmu ko kusa shiyasa na rage d'aukar wayarsa idan naga ya kikkira da yawa sai in bishi da text din ban hkr cewar ina karatu ne,har rannan tura takai bango ya iskoni har makaranta.
Yammacin alhamis ne ranar ma nida Feedo azumi mukai ita na ramuwa ni kuma na litinin da alhamis, inajin azumin sosai nai kwance a katifa kamar ruwa,itace take ta hada-hada had'a mana abun bud'a bakin, wayata na jikin caji tayi kara amma ban motsa ba balle in d'aukota, "Sahaar wayarki fa kinaji kuma"
Na lumshe idona nace "Kyaleta bazan iya wata doguwar mgn ba sai nasha ruwa"
Zuwa tai ta lek'a wayar tana cewa, "Anya kuwa zaki iya?sbd naga wannan Ogan naki yau da gaske yake yi"
Ta aje mun wayar gefena,naita kallon kiran zuciyata ta doka sosai kwana na uku kenan ban dauki wayarsa ba,Oga Uhaimid kuwa sau d'aya ya kirani ina class lokacin ban dauka ba,bai kuma kira ba.
"Feedo ya zanyi?"
Na fada kamar xan kuka sosai, dariya tai tace "Ya zaki fa Sahaar,ki dauka kawae kiji miye xaice"
Kira na uku na dauki wayar gabana yana fad'uwa nasan ban kyauta ba, "Assalamu alaikum Oga Fauz.........kimun shiru Zainab"
Aiko na turo baki kamar yana ganina, "watau kin rainani ko?ni kike ignoring har haka ko?"
"Don Allah Oga.......nace kimun shiru anan, I give u five minute to meet me out of get"
Daga haka ya sauke wayarsa ya barni da ita rik'e ga hannu, "wayyo na shiga ukuna,"
Na fad'i ina bubbuga kafafuna bisa katifa,kwalla ta cika idona nace "Feedo wai yana wajen get,kuma minty biyar yaban in samai"
Dariya take tace "maganinki kenan ai"
"Haka ma zakice ko?"
Hade hannuwanta tai tana ban hkr, "Afuwan Qawata daure kije inma yaga yadda kika galabaita nasan zai sallameki"
"To ni mizan masa?wlh Ya cika takurawa na rasa miye yake mawa ni wlh"
Feedo na kunshe dariyarta tace "kisa plat din takalma karkije ki fadi......ban sakawa dilla ke kuma"
Feedo ta bushee da dariya tana rugawa toilet karta isketa,naja k'uta kawae na fito riga da wando ne na Pakistan da jidda ta dauko mun cikin siyayyar da muka tab'a zuwa da Oga Fauzan, aikuwa yana cikin motarsa haka na isa kamar iska zata kayar dani,lokacin ma ana daf da kiran sallah magriba, na bud'e sit din gaba na shiga da sallama naji wata ni'ima tana baibayeni tare da sassanyen kamshi mai ratsa zuciya,ba irin na Oga Uhaimid ba mai hawa kai.
"Ina wuni Oga fauzan........tada motar kawae naga yayi yaja, a rud'e nace "Innalillahi, Oga fauzan ina zamu don Allah ka tsayar da motar wlh azumi nake kuma ana ta kiran sallah"
Banza dani yai inata masa magiya har muryata ta dishe karfina da miyan bakina suka k'are,na koma cikin kujerar nai lakasss, tafiyar minti ashirin da biyar mukai ya tsaya restaurant ba irin wanda mukaje rannan ba,budewa nai zan fito ya watso mun kallo dole na koma, ransa bace yake dani naga alama kuma zan iya cewa ban tab'a ganinsa cikin bacin rai haka ba,tabbas ban kyauta ba ina laifin wanda ya damu dakai?yadda yake kula dani da damuwa dani ba kamar oga Uhaimid ba,shi ya cika fad'in rai da masifa.
Take away na hangoshi dashi ya taho babbar leda guda biyu, ya bude ya aje gabana ya rufe ya zagayo ya zauna, muka fita da restaurant d'in.
Har muka iso k'ofar wani tamfatsetsen gida kamar a billa,wannan ko billa albarka gini ne na masu dashi gini ne irin na yan boko wanda suka jik'u cikin naira,kai kana kallon shi kasan naira tace wayyo Allah a wurin, kada na tunzura shi da yawa shiyasa bance uffan ba amma cikin raina tashin hankaline sosai, wallahi idan ka shigo falon tsakiyar gidan zaka dauka ba a kaduna kake ba, kitchen ya wuce ta wata hanya mai k'ofar slider ta glass, sai gashi ya fito da plates da cups da spoon, da kanshi ya ciro komi ya juye har sannan ba fara'a ko kad'an fuskar tashi,saida ya gama sannan ya kalleni "ga hanya can kibita zaka kaiki daki kiyi salla ki fito kiyi bud'a bakin"
Ya mik'e yana ficewa daga falon gaba d'aya, saida na dad'e kafin na iya tashi nabi hanyar daya nuna mun d'in,wallahi saida na raina kaina dana shiga dakin kuttt wannan kyau haka, daker na iya sarrafa kayan toilet d'in saboda ban saba ganin kalarsu ba.
Kafun ya dawo na cika cikina dai-dai misali har saida nabar saura,yana shigowa ya zauna yaci abincin sama-sama yasha ruwa ya mike yana yin gaba, "muje na maidaki"
Biyosa nai muka fito har duhun dare ya mamaye gari amma fitilun dake compound d'in komiye ka yar zaka iya ganinsa duk kankantarsa saboda hasken wurin tamkar tsakiyar rana.
Bayan mun dauki hanya ne cikin raunin murya nace masa, "Don Allah Oga Fauzan ka........idan ba zaki kirani Hamma yadda jidda ke kirana ba pls ba dole saikin ambaci sunana ba"
Ya katseni da fad'in hakan,na sauke kaina k'asa ina jujjuya hannuna, kafun na sake cewa "kayi hkr Hamma don Allah"
Baice uffan ba tukinsa yake hankali kwance,shagon Rufaida muka tsaya ya fita da kanshi yaje ya kwaso kayayyaci cike da leda,ya aje gabana ya rufe daga nan bamu tsaya ko ina ba har muka iso cikin makaranta bakin get d'inmu na hostel, kasa fita nayi na jiyo ina kallon shi sosai kamar zan kuka nace "Don Allah Hamma Fauxan"
"Ka yakuri"
Bude idanunsa yai yana kallona dasu sun d'an canxa kalarsu yace cikin yanayi marar dad'i, "Kin dauki kulawar da nake baki matsayin takurawa ko.......wallahi ba haka bane,na rantse maka ba haka nake nufi ba don Allah kayakuri"
Girgiza kanshi yai yace "Zan baki space.........Hamma"
Tsareni da idanu yai har saida naji sunmun girma na sadda kaina kasa, "zan tafi kuma bazan sake zuwa ba,ko gida kika dawo karki zo inda nake.......Hamma nace fa na tuba,don Allah kayakuri"
"Hakurin da zanyi kenan ai kije kawae abunki"
Ya maida kanshi jikin kujera ya rufe idonsa,naji na damu sosai na kuma kasa fitar,na sake jiyowa idona yai kwalkwal Zan kuka "Hamma don Allah fa,inata baka hkr pls kaji"
"Miyasa bakya son daukar kirana?"
Hawayena ne suka zubo sharrrr,na kasa rik'esu saboda bansan mizance masa ba,bazan iya cewa inajin tsoron alakarmu ba bazan iya cewa bana son in zurma da yawa ba,sai na zab'i kawae na masa kuka kila ya huce ya kuma fahimci ba da son raina nai hakan ba........Ya salam,Ni bance kimun kuka ba zainab"
"Ka daina kirana zainab bana son sa"
Na fada da muryar kuka inata shashsheka,matsowa yai yana sassauta muryarsa, "To dago kiga"
Na ciro fuskata ahankali,sai ya ban hanky dinsa girgiza kaina nayi, "Aa,ai baka ce ka hakura ba"
Murmushi ya subuce masa, yana cikin kujerar kasala na rufeshi yace, "To na hakura goge hawayen"
Na ansa ina gogewa kamshinsa mai dadi yana ratsa hancina, "To kace ka janye mgnrka"
"Ni bazan janye ba inhar ina kiranki kina shareni"
"Nayi alkawari ko exam nake rubutawa ka kirani Hamma Zan dauka insha Allahu"
Ya sauke ajiyar zuciya yana ta kallona, cikin sanyin murya yace "Mun shirya KO?"
Na daga kaina sannan yace "Yaushe zaki dawo gida to?"
"In Anna ta dawo insha Allahu"
"Allah ya kaimu,kije dare yayi"
Haka mika rabu zuciyata tana ta mun sak'e sak'e da yawa,na isa daki da ledar daya bani kayan lashe lashe ne ciki dasu shawarma da pizza da sauransu, Feedo tace "Uhm akwai magana fa Sahaar,wannan ogan naki fa kamar.........kallonta nake sosai sai ta fashe da dariya, "Muje dai zuwa maji inda aka kwana"
"Gara kifito mun a mutum Feedo,miye kike zargi don Allah nima kaina zuciyata tana cikin tararrabi"
Murmushi tayi tace, "Dad'ina dake har yanxu kanki a kulle yake,kenan ba zaki iya gane cewar in kare na shinshinar takalmi ba dauka zai?"
Tsareta da ido nayi zuciyata tana bugawa da sauri-sauri, "Muna nan dake zaki fahinta ahankali"
Daga wannan lokacin Alakarmu da Hamma Fauzan ta kara wani irin sauyawa, tun ina d'ari-d'ari harna sake duk da cewar cikin zuciyata inajin tsoron wani abu,amma kuma zuciyar ta kasa dakatar da kanta,ko kiran sa na gani faduwar gaba nake shiga balle yace mun yana jirana inzo,har mu rabu bugun zuciyata baya dai-daita,kodayaushe muna tare a waya sai idan karatu nake wani lokacin ma tare mukeyi yana kara mun lectures akan wanda akai mun,cikin sati guda bakina bazai iya fasalta sabon da nayi dashi ba,saboda har lokacin Anna bata dawo ba ta kirani da wayar wani rannan tace mun sai anyi arba'in zata dawo,na kama mata kuka nace nidai yayi tsawo taita lallashina haka nan na hkr,dole na shirya na koma gida saboda kayan dana dauko bazasu isheni ba.
Shi yazo ya d'aukeni muka taho gidan yana ta jana da fira,muna fitowa daga motar Oga Uhaimid shima ya dawo daga Asibiti, rabona dashi har na mance kuma ko tunawa dashi banyi ba,kallon daya mana sai naji na wulakanta a wajen ganin sun tsaya suna magana sai nai wuff na fece daga wajen, nayi wanka na sauya kaya na d'an kwanta ina hutawa saiga Humaira.
Anan mukaita fira tace yanzu ba ayyuka sosai zaman banza suka cika yi tunda Oga Uhaimid inya fita aiki yana kai dare,abincin su kawae suke girkawa shikenan sai gyaran gidan, tace "Tunda kika tafi kullum sai yazo ya tambaya baki dawo ba,ince masa ehy saboda karya na mashi nace kinbi Anna Kauye"
Zaro ido nai nace "Waye yace kice masa haka?yanzu idan yasan karya kikai fa Humaira?"
Tace"wallahi nima saida na fada masa naji nadamar hakan,Allah dai ya kub'utar dani..........kwatsam sunan sa ya fad'o a wayata yana kirana, cikina ya bada k'ulululu,na nuna mata kiran ta zaro ido "shikenan karya ta ta kare"
"Bazan dauka ba,ni nasan na shiga hannunsa mai k'watata sai Allah......wallahi gara ki dauka rashin daukar kamar karin laifine?"
"Yo mina masa?gyaran dakin sa ne kuma yasan ai makaranta yanzu bata barina......wani kiran ya sake shigowa,duk da gabana fad'uwa yake hakan baisa na dauka ba, "Sahaar ki dauki kiran nan karki jama kanki wani tashin hankalin"
"Bakisan waye Oga Uhaimid ba,gara mun rashin dauka da in dauka ya sauke mun kwandon masifarsa............sallama mukaji bakin kofar dakin,muka kalli juna nida ita, tace "Ado ne wallahi,kuma nasan aiko sa akai"
"Sahaar Oga Uhaimid na nemanki keda Humaira yace minti biyar ku samai a sama"
Jinai yan cikina sun bada wani sauti,Humaira tace "Shikenan aikina yazo karshe gidan nan,Sahaar tashi muje"
Na dad'e ban iya tashi inda nake ba,tashin hankalin da nake ciki saka Hijab ba hka muka fito zuwa cikin gidan, tsitt kakeji saboda ba kowa sai muka nufi saman Humaira duk ta rud'e sosai,nima d'in a rud'en nake amma ba zakai saurin ganewa ba.
Falon saman muka nufa inda Uwargida ke yawan xama,da sallama muka shiga yana ta tab'a system bai ansa ba muka zube k'asa Humaira na cewa, "gamu Oga Uhaimid"
Wani kallo daya wurgo mana saida zuciyata ta ansa, bai tanka ba haka ya banzatar damu tsawon lokaci kamar ya mance ma muna wajen,yaita ansa wayoyinsa hankali kwance sannan ya cigaba da aikinsa,kafafunmu sunyi sanyi sosai har dayi suke,munfi awa durkushe kafin ya dago yana kallon mu.
"Ke rannan dana tambayeki ina wannan yarinyar mi kikace mun?"
Bakin ta na karkawar tace, "Na.....nayi nayi kuskure a gafarceni Oga Uhaimid"
Jinjina kai yai yace "kin anshi laifinki kenan,ita tace kimun karya?"
Da sauri take girgiza kanta, "Aa Oga Uhaimid ka gafarceni don Allah"
"Ban tab'a miki hukunci bane shiyasa kika rainani kika daukan shashasha,tashi kiban wajen amma wannan watan karki jira albashinki don bakida shi,gobe ma idan na tambayeki kumun karya"
Kuka ta fashe dashi tana rok'onsa afuwa, "kagafarceni Oga Uhaimid,nayi kuskure ka yafe mun don Allah........kar kibari in sake miki magana kibar nan wajen"
Har tatashi sai naga ni dana jaa mata bai dace ace ban saka baki ba, cikin d'ar d'ar nace "Kayi mata hakuri Oga Uhamid.........wani jakkin kallo daya auno mun dole na hadiye mgnr tawa, haka Humaira ta fice tana kuka saboda ita kad'ai tasan irin taimakon da albashin yake mata,nima kuma shaida ce itace ke dawainiya da kanta harma marikiyarta su anfana dashi.
Tana fita ya tashi yana cewa cikin wani irin miskilanci da izza dana jima ban ganshi dasu ba, "Ki biyoni dakina da wadannan tarkacen nawa"
Wani mugun faduwar gaba ya rufto mun, ban gama tararrabin abun ba ya sake cewa "kar kuma na rigaki isa"
Cikin hanzari na tattata kayan da computer na bisa dasu kusan tare muka isa,nai tsaye bakin kofa bayan na rufe ta, abunda ya d'imautani ganin ya soma watsi da kayan dake cikin dakin,tun daga kan madubi zuwa wadrope dinsa da wajen adana takalma da kan gado da wasu takaddu,duk ya warwatse dakin dasu cikin wani irin fushi har ina iya ganin jijiyar kanshi yadda ta fito sosai idanunsa tamkar an zuba attarugu ciki, wani irin rawa k'afafuna suka soma yi mun jikina kanshi ya ringa kerma sosai, ya jiyo yana nufo inda nake tsaye runtse idona nai jikina yana b'ari sosai, hannunsa yasa ya daki jikin k'ofar da nake tsaye jikinta wlh kadan yasa fitsari bai fito mun ba, takkadu da computer suka zube k'asa na bisu ina kerma hannu yana rawa ina tattarawa, ya durkoso gabana yana fizgo gashina ya dago fuskata, saida na saki k'arar azaba "Minty goma na baki ki gyara mun dakina"
Sannan ya sakarmun kan,ban samu damar kuka ba na soma kokarin farawa,sai na rasa ta ina Zan fara d'in dakin ya haukace sosai yana cewa minty goma yabani,taya Zan gyara shi cikin wadannan mintocin, "Idan na fito wanka baki gama ba........sai na hau gadon na fara gyaran zuciyata sosai take bugawa, tashin hankali yana kamani zamana cikin dakin akwai damuwa,Duk da cewar ban tab'a ganin wani abu mai kama da alfasha tattare dashi ba amma ina matukar tsoron kusanta kaina da inda yake,tun fil'azal daman tsoron zuwa dakinsa nake to balle yau da yana yinsa yai mun kama da wanda yasha kayan maye suka masa yawa,
Karkarwar jikina bata hanani aikin ba amma bana sauri sabida ba anatse nake ba,kuma sai zufa nake duk da Ac dake kunne dakin agogo na kalla naga har na cinye minty goman amma gado da madubi na gyara, jinai kamar Zan saki kuka amma ba lokacin sa bane, fitowar sa toilet d'in yai daidai da bugawar zuciyata, tsaye yai yana kallon dakin sanan ya kallan da jirkitattin idanunsa da basu dawo daidai ba, sai kawae naga ya sake birkice gadon ya wargaje gyaran madubin tass, ya zauna cikin wata kujera dake dakin yana shafar shi hankali kwance, kwalla suka ciko idona zasu zubo yace "Five minutes na baki"
Wlh ko ina jikina rawa ina ta sharb'en hawaye da majina,haka na raba kaina inyinan inyi can amma yana gama shafa man shi ya tashi ya k'ara lalata komi, jinai kamar aradu ta rufto mun akaina muryata ta na wani irin kerma nace, "Don Allah.......wata zaburowa yai yayo kaina cikin fushi, ban san sadda na durkushe na boye kaina cikin guiwowina ba ina sakin siririn kuka, fizgoni yai na mik'e fuskana kaca-kaca da hawaye, "five minutes na baki kigama wannan aiki"
Ya wancakalar dani gefe har ina tangal tangal Zan fad'i, ya dauki kayansa da xai saka anan inda ya watsar dasu, ban ankara ba kawae naga ya saki rigar wankan daya sanyo, wata kara na saki ina juya baya kafafuna da jikina karr karr karr kawae suke, wani mugun fitsarin tashin hankali naji ya daure mun marata jinake inayin wani motsin kirki zai iya kubce mun.
🤣🤣🤣dramer alqur'an Uhaimid kishine ke neman ya zautar da yar mutane sauk'i dai.
Mom muhseen✍🏻