SAHAAR

15&16

by @mommuhseen

*_SAHAAR_*

ADABI WRITER'S ASSOCIATION.

BY

MOM MUHSEEN

🅿️....15&16

Wata irin makerketa k'afafun keyi saboda

Fitsarin daya cika marata tafff,tunda uwata Anna ta haifan ban tab'a jin inajin fitsari irin haka ba,hawaye wani na koro wani fuskar tai kaca kaca a hakan na cigaba da gyaran d'akin, yana cikin sofa yana wayarsa cikin wata yar iskar murya yana zuba ma Anti Jamila shagwab'a son ranshi, na gama gyara gadon da madubi da drowers dinsa, duk da yadda nake rawar d'ari ko ina kerma yake jikina, na soma gyara closet d'in nashi, Ina mammatse k'afafuna zufa na cigaba da karyo mun, ina jan majina da hawaye kwatsam wayata dana jefar bakin k'ofa d'azun ta soma kara sosai, jinai kayan hannuna sun zub'e kasa saboda firgici, na kalli k'ofar inda wayar take na juya ina kallon shi, bude idanunsa yai akaina sun lumshe sosai sun Kuma rik'ede ainun, jinai fitsarin ya zubo k'adan na matse k'afafuna sosai, na fara takawa cikin karfin hali don isa ga wayar, kamar kyaftawar ido na ganshi gabana, kallon yadda nake rawar jiki yake bakina yana makerketa hawaye na zubowa nace, "Don...don...don girman.....girman Allah,a fusace ya dauko wayar yana kallon wanda ke kira, na rubuta HAMMA F......runtse idona nai Ina rufe bakina, kukan na son kwace mun saboda yadda ya tsareni da jajayen idanunsa, "miye tsakaninku?"

Ja baya na rink'ayi yana biyoni kamar wani zaki, wlh jikina kamar an jona mun electric shock, "kiran mi yake miki?"

Kai na kurin nake girgizawa ina hawayen bakina ya kasa mgn, bangon da nake jiki ya kaima wani irin bugo sai ga fitsarin yana zubo mun a pant, "ba zaki gaya mun miye tsakaninku ba!!"

Ya daka mun tsawar da naji komi nau ya tsaya fitsarin kuma yana idasa kubce mun yana biyo kafafuna zuwa k'asa, silalewa k'asa nayi ina fashewa da wani irin rikitaccen kuka kaina cikin guiwata.

Bin wajen yai da kallo tsikar jikinsa ta wani irin tashi,runtse idonsa yai kafun cikin wani irin zafin zuciya yai jifa da wayar ga bango ta tarwatse,ya durk'usa inda nake ya fizgo kaina yana kallon fuskar yadda tai jajir ga hawaye da majina, "Ko kigaya mun miye tsakaninku ko kuma na miki tabon da ba zaki tab'a mancewa dani ba"

"W....wa...wallahi......ta...tallahi babu komi....komi babu komi,na rantse maka......na rantse da Allah babu komi,kayi mun rai ka gafarceni Oga Uhaim........Shittttt, ya fada yana zaro mun idanunsa waje,wani fitsarin yana sake kubce mun, "Uban waye yace kimun fitsari a d'aki?yai kama da kazamin toilet d'inku?"

Girgiza Kai kawae nake"Aa,.....Aa....kayi hkr kubce mun yai"

Har lokacin ban daina sashshekar kukan ba,kirjina yana ta d'agawa saboda tashin hankali,ban tab'a ganin bala'i da fitina irin wanna tun bayan barowa ta daga wajen inna sahura, Tashi yai daga gabana yana shiga cikin Toilet d'in, naji yana tab'a ruwa jimm ya fito yana kallona har sannan rawar d'ari nake, sai kawae naji ya d'aukan zuciyata tai tsalle kamar zata fad'o, bai tsaya dani ko ina ba sai cikin toilet d'in cikin komin wanka kawae ya sakani,na zabura saboda na tsorata ya watso mun wani kallo "koma ciki"

Na koma Ina sauke numfashi,ya juya ya fice yana ja mun k'ofar na dad'e ban iya yin komi cikin ruwan kumfan daya sani ba, wani irin kamshin sabulai yake dana shower gel, kayan na zare a hankali sun jik'e sharkaf na wanke jikin sama-sama na fito nayi alwalla, waige na fara inda zan samu towel amma bangani ba, anan naji hankalina ya sake tashi daman kuma ban shigo da Hijab tun farko, jikin k'ofar na tsaya muryata tayi wani irin sanyi ba karfi cikinta, "Babu abunda zan d'aura anan"

Shiru baice komi ba,na sake maimaitawa kamar zan fashe da kuka sai zuwa can naji alamun an bude kofar dakin, "Don Allah kabani wani abu na daura"

"Kifito haka mana"

Dass zuciyata ta bug'a sai kawae na soma daukar kayana zan maida,ko zai kasheni bazan tsaya gabanshi tsirara ba, bud'e kofar kawae naji na saki kayan na durkushe kasa ina k'an k'ame jikina, kaya nagani ya aje ya sake jan k'ofar.

Na sauke ajiyar zuciya nai saurin dauko su doguwar rigace ban san ina ya samota ba,ban tsaya ganin ya take ba kawai na sanya burina in fito in ganni dakinmu cikin bargo na kudundune.

Na matse kayana na dunk'ulesu waje d'aya na fito dasu, sadda na fito naga d'akin kamar sadda na tadda shi da farko need ko tsinke babu k'asa, tsaye nai bakin k'ofar na kasa motsawa kwance yake bisa gadon hannunsa bisa goshinsa idanunsa rufe, hasken dakin ya rage amma ana iya ganin komi.

Bude idanunsa yai yana kallonta dasu, wani irin tsalle zuciyarsa tai ta doka da karfin gaske, yayin da idanunsa suke hango masa komi na jikinta cikin rigar, ban san mikenan ba saboda ni a sanina na saka kaya, "koma da wadannan tsumma kisasu dustbin"

Komawar nayi saboda yanzu wani fitinannen tsoronsa ne ke kamar zai hallakani, na ajesu cikin sharar kamar yadda yace duk da kaunar kayan da nake haka na barsu na fito, wayata na hanga bisa madubi,amma tashin hankalina isa inda take in d'auka, tashi zaune yai daga kwancen idanunsa ni d'in kawae suke kalo kaina babu ko hula balle d'an kwali,ruwane ki d'iga ta gashin nawa dis dis dis, "zoki busar da gashinki"

Takowar nai na iso ga madubin,ya tashi ya dauko dryer ya jona mun yana bani,idona ya sauka akan madubin ina kallon kaina,ban san sadda na fasa kara ina matsawa baya da sauri na kankame jikina idanuna sun firfito sosai, "Na shiga uku na lalace ban saka kaya ba"

Idona ya ciko da kwalla da rawar murya na kalleshi kamar yadda yake kallona, "Ka taimakeni na tafi dakinmu,don Allah kayi hkr nayi alkawarin bazan sake sab'a maka ba"

Wani irin lumshe idanunsa yai yana budesu akaina, muryar cool ba kuzari cikinta "Zoki busar da gashinki nace"

Girgiza masa kaina nayi ina kuka ahankali, "Don Allah na rok'eka,kabarni na tafi inje insaka kaya"

"Karki bari na sake miki magana"

Kafafuna suna kerma na tako na tsaya nesa dashi, nuna mun stool d'in mirrow yai "Sit here"

"Oga Uhai........inkika sake mun musu wallahi billahi saina rabaki da wannan rigar ma gaba d'aya"

Na had'iye wani irin busasshen miyau a mak'oshina, na iso da sauri na zauna amma hannuwana rungume a kirjina na boyesu, zare ribbon din kaina yai gashin ya sauka bayana, ya soma busar mun da gashin cikin natsuwa,sanyin AC yana huda fatar jikina yana haifar mun da zazzabi sosai, nan na cigana da rawar sanyi uffan baice mun ba har ya gama mayukan shi na gashi ya dauko yana shafa mun,yasa mataji ya taje mun sosai ya maida mun ribbon d'in.

"Wuce ki hau gado ki kwanta"

Na girgiza kaina Ina shashshekar kuka, "ka rufa mun asiri Oga uhaimid na tafi dakinmu,bazan iya.........jinai kawae ya daukan tamkar jaririya na fashe da kuka ina kokarin sauka, "Kai mun rai,don Allah ka saukeni na tafi dakinmu"

"Inkika sake mun gardama zan baki mamaki wlh"

Hadiye maganata nai amma hawaye basu tsaya ba,inaji ina gani ya shimfed'eni bisa lallausan gadon shi wanda tsawon rayuwata ban tab'a hawan gado mai azabar laushi da dad'i irinsa ba,mai cike da kamshi da sanyin ni'ima, ya rufa mun bargonsa kamar gashin mage don laushin sa, ya wuce ya kara rage hasken d'akin ya kwanta cikin sofa wadda ya kwanta kanta d'azun.

Wannan dare ban tab'a riskar irinsa ba a rayuwata, tsoro da tashin hankali sun baibayeni duk yadda bacci yakai ga iya sata kasa saceni yai a wannan daren, ji nake na takura na matse sosai duk da fad'in gadon kuma,amma ko juyawa in canxa hannu na kasa gani nake shikenan yau rayuwata ta jirgice sama zuwa kasa kasa zuwa sama,ban tab'a tunanin gari zai waye ba tare da yayi mun wani abuba,kawae ina tunanin ta inda zai farmun ne hawayena har suka k'afe saboda zullumi da yadda zuciyata take bugu irin bugun da bata tab'a yimun shi ba.

Akan kunnena liman yai kiran farko na sauke wata ajiyar zuciya dana kyalla idona na hango shi takure kan kujerar yana bacci sadidan, na sauko ahankali cikin wata irin sand'a da nufin zuwa in bud'e kofar in fice,duk da yadda nakejin tsoron hakan amma na kasa hana kaina, jijjigar duniya naima k'ofar ko motsi batai ba jikina yai sanyi na jiyo na dawo na kwanta,daga hakan kuma baccin ya saceni ba tare da raina yaso ba.

******

Ruwan da naji kamar an yarfomun yasa na bud'e idanuna daker saboda baccin bai isheni ba, hasken daya hasko ta window yasani rage idanuna, kafun na idasa bud'esu daker ina kallon inda naji yarfin ruwan, zaune yake bisa stool yana taje lallausar sumar sa mai azabar sulb'i baka sid'ik da ita, nan take kwakwalwata ta dawo mun da movie d'inmu na jiya, wata zabura nai da karfin gaske sai gani tsaye bisa k'afafuna, na mance wace irin rigace jikina, jiyowa yai jikinsa sanye da rigar wanka yana karemun kallo sama zuwa k'asa, idanun nan sunyi wani irin kala bansan dame zan misalta color d'insu ba, sun lumshe suyi masa wani irin kyau na ban mamaki, sakale nai ina kallon sa yadda yake kallona dasu, "ba ki iya gaisuwa ba?Ina zaki da kika zabura kika tashi?"

Alokacin ne hankalina yakai ga rigar, idanuna kamar zasu fad'o ganin yadda duk halittuna suka fito sosai,wanda za'a iya cewa da ita gara babu wani tsalle na daka na koma bisa gadon naja bargon na k'udundune ciki har kaina.

Wani kafirin murmushi da bai shirya masa ya kwace masa, ya gama shafarshi ya dauki kaya ya wuce inda akai masa wata cover don shiryawa, cikin minti biyar ya fito zazzafar saurayi mai jini a jika mai tashen k'uruciyarsa,yana fidda wani daddaden kamshi mai rikita zuciyar duk wanda ya shak'a, gaban gadon ya iso ya fizge bargon na sake zabura na dunk'ule waje guda.

"Miye kike b'oyewa?banga wani abuba da zaki boye mun ai?ni kallon namiji nake miki da kin sauko kinje kinyi salla kizo ki gyara mun dakina"

Banji haushin mgnr ba kamar yadda banjin zan sauko yana kallon jikina, girgiza kaina nayi nace "Zan...zan sauko,amma kaje waje don Allah"

Waro idonsa yai yana mun wani dan iskan kallo, "Nan d'in dakin kine ko nawa?"

Na girgiza kaina "naka ne"

"Tunda nawa ne nine Zan baki doka da order akansa,oya get up malama"

Yasha murr sosai ya koma wani daban irin fuskar basawan nan,jikina na rawa na sauko na nufi toilet d'in,jingina bayana nai da k'ofar ina sauke numfashi, "Allah na rok'eka ka fitar dani daga tarkon mutumin nan"

"Five minutes na baki"

Naji ya fad'a a dake,cikin sauri nahau nayi fitsari na kora shi,nayi alwalla na bude zan fito ya watso mun harara "Koma kiyi wanka"

Zanyi magana dole na maida abuna,na dawo na soma yin wankan inajin kamar inyita ihu ko wani zai fahimci ina cikin matsala ya kawo min agaji,ban dad'e ba na fito rigar na jikina na yafa towel din dana gani a ciki, "ga kaya nan ki shirya kiyi sallah"

Kayan na dauka na koma toilet na soma shiryawa, "Nashiga uku na ni Sahaar"

Na fada Ina zaro ido ganin hadda pant da bra kuma nau ne,to taya akai ya dauko su? Ya salam wane irin mutum ne shi wai?lallai na yadda tataccen dan iska ne Uhaimid (🤣🤣 nidai ba ruwana in yajiyoki ato)

riga da siket ne na atamfa na sanya sannan na fito na saka hijab din daya had'o da ita, na hau abun salla na kabbara zuwa can naji fitar shi ko addua banyi ba na mik'e na ruga zuwa k'ofar da fatan ta bud'e in fece amma inaa bata bud'u ba, kwalla suka ciko idona "miyake so a fahimta ne?ya na son kawae yajawo mun masifa ni Sahaar...........budewar yasa nai saurin rufe bakina, tire ne hannunsa yai tsaye dashi da kayan kalaci a cikinsa, "zagina kike?"

"Wallahi Aa"

Takowa yai yana nufoni da tiren, naita ja baya ina girgiza kaina "wallahi Oga ban zageka ba Allah ya sani"

"Inaso in jawo miki masifa ko?"

Idanuna kamar zasu fito waje na waro su jin cewar yaji minace, "Kayi hkr don Allah Oga Uhaimid,kabarni na tafi kar a fahimci na kwana dakin ka Zan shiga matsala..........aje tiren yai kasa yana dafa bangon da nake tsaye jikinsa, kallona yake da fusatattun idanunsa, "Baki son ya fahimci kin kwana dakina ko?tsoro kikeji kar hankalinsa ya tashi nayi iskanci dake.........Na shiga uku na,Wallahi Aa na rantse maka ba haka bane,ka yarda dani babu wata alaka tsakanin.....ya tsarsa ya dora bisa lips d'ina,na hadiye mgnr ina matsar kwalla sosai, "jiya ma naji sadda kike harin guduwa ai,kina tunanin zaki iya tsere mun?"

Na girgiza kaina ina hawaye, yai murmushin gefen baki yace "Har ni Zan kiraki a waya ki k'i dauka,halan shine yace karki kuskura ki ringa dauka wayata"

Nan ma girgiza kai nayi, "In baki tsaida wadannan yan iskan hawayen ba zaki sani"

Nasa hannu cikin sauri na goge su, lips d'in nawa yake zagayewa da yatsar sa, runtse idona nai Ina girgiza masa kaina magana na bakina ban iya furtawa, "inda nayi niyyar iskanci dake da nayi jiyan nan,kar yar karamar zuciyarki ta dauki wannan wani abu,horaki kawae nake yadda nan gaba zaki kiyayeni,inaso ki gane waye UHAIMID ATTAHIR kin fahimta"

Kaina naita d'aga masa idona rufe rufff, "bude wadannan idanun naki"

Na bud'e ba jayayya,kallon idanuna yake kamar Allah ya aiko shi,yayin da fuskar sa tayi kusa sosai da tawa,har saida na dauke numfashina na wucin gadi,jin hancin sa bisa nau yasa na rufe idanun ban sani ba, hannunsa yasa ya tallabo bayana ta gefen cikina, mukai kusa sosai dashi har ina jin sautin zuciyarsa nima kuma nasan yaji nawa bugun zuciyar.

Magana yake silently gently calmly a bisa fuskata, "Ranar da duk na kara ganinki dashi a waje ko a cikin gida,ko a mota ko a makaranta.........bazan kara b"......ya dora yatsar sa still a bakina "ban gama magana ta ba ai"

Ba bakin mgn sai dai kaina da naketa faman daga mashi, hucin numfashin kawae naji ya sakar mun a fuskana da hancina, "innalillahi wa inna ilahir raju'un" kawae na furta cikin raina yayin tsigogin jikina suka tashi yarrrrrr, na damki siket d'ina jikina ya soma rawa sosai.

"Idan na kuma ganin ya siya miki wata wayar,idan na kuma kiranki baki ansa mun ba,idan kika kara mun rashin kunya ko sab'a umurnina,kin san miye zaifaru?"

Girgiza kaina nayi cikin sauri ina numfashi da sauri-sauri, wanda yake haduwa da nashi suna gauraya waje d'aya, yatsan sa yasa yana nuna gadon shi sannan ya kalli cikin idona sosai, yace "Acan abisa wancen gadon zanyi shagalina dake,zan miki fata fata yadda bazaki ma moru ba,bana jin wani d'a namiji zai moreki kaff rayuwar nan..........bansan sadda kuka ya kubce min ba, "Shiiiiiiiit"

"Kimun shiru malama,ai ba yanzu nace ba da zan miki daren jiya da an wuce wajen saidai wata bake ba, wannan warning ne ya zama na farko kuma na karshe kin jiya?"

"To....to....to"

Nake ta fad'a idona na zubar da hawaye, sannan ya matsa daga kusadani yana cewa, "zauna muyi kalaci"

Inani Ina sake masa gardama ni kam, zama nai sosai ya zuba komi ya aje min sanan yace muci tare cheeps d'in, karfi da yaji yana mun finkarfi a rayuwata saida yasa muka cinye tass muka ci naman kai da bread sannan na shiga na wanke bakina,shima ya shiga ya don ya wanke na soma gyara dakin sosai da yake akwai kayan shara dana mop a d'akin,dan danan na gama na wanke bayin na saka turarukan dana sakawa a toilet din, na kunna masa bonner turaren wuta,dan danan dakin ya sake fitowa fess dashi yadda yake burgeni a kodayaushe.

"Zan barki ki tafi amma kisani cikin magana ba wadda nake yi da wasa wallahi,sabida ke din ba abokiyar wasana bace"

"Zan kiyaye,Amma.....Amma don Allah"

Tsareni da ido yai sosai "What?"

"Karka hana Humaira albashinta nice nace ta gaya ma hakan"

"Ohk,naki Zan dakatar kenan?"

Cikin sauri nace masa "eh na yadda"

"Wuce muje na saukeki makaranta,idan na sake ganin kin dawo gidan na ba tare da Anna ta dawo saina miki abunda ba zaki mance dani ba"

Cikin yardar Allah har na isa dakinmu ban had'u da kowa ba,fad'awa nai bisa katifarmu nai kuka na gode ma Allah, "Da wani abu ya faru dani ina Zan saka kaina?mizance da Anna?"

Nafi minty goma ina kuka na tashi na hada kayan dazan dauka na kulle dakin na fita naje nabawa Humaira mukullin, tana ganina ta rud'e sosai "Miya faru?Ina kika kwana?banyi bacci ba Sahaar hankalina yana kanki,don Allah miya miki"

Hawaye suka ciko idona nace, "Bamun wani abu na lalata ba,amma ya mun abunda ko daga nesa na hangoshi jinina sai yahau"

"Hazbunallahu wani imal wakeel,nashiga uku daman hakan yake?iskanci ya miki halan"

Girgiza kaina nayi ina share hawaye, "Ya dai kusa,zamuyi magana yana jirana waje"

Daga haka na fito na wuce can wajen get ina hangen motar Oga Fauzan a cikin compound,amma na kasa juyawa ma na kalleta sosai,yana cikin motar yasa kid'a kadan yana tashi na bude bayan na saka kayana, na dawo gaban Zan xauna "Mijinki ne ni da zaki jera dani?"

"Kayi hkr"

Na koma bayan na zauna inata murzar yan yatsuna na kasa ko d'aga kaina, zazzab'i nakeji cikin jikina marata tana ciwo kadan kadan nasan Mp na yana tafe,zazzab'in yana dafa k'asusuwan jikina.

Asibitinsu naga ya nufa dani,banda bakin tambayarsa me zamuyi haka na bisa har office dinsa, sai naga ya bud'e wani dan akwati duk kayan magani ne da allurai, hankalina ya tashi watau allura zai mun kenan, to ya akai ya fahimci banda lafia?

Lallai lamarin Oga Uhaimid azimunne kamar wani mai duna?,bai saurareni ba kawae ya juyo dani muna fuskantar juna, kawai naji ya tsira mun akan siket d'ina, idon runtse har ya gama sannan ya fiddo wasu magunguna ya ballo ya bani ga hannu, yaje ya dauko ruwa mara sanyi yaban nasha daker kamar zan amai, wasu yaban yana cewa "Safe da dare zakisha kwana uku"

Kaina na d'aga masa, "baki iya godiya ba"

"Nagode"

"Rike kayanki ba abunda zata mun ai"

Haka muka fito muka sake tafiya, wani shago mukaje yace karna fito na jirasa, inata zaune har yaje ya fito ya dawo yana d'ora mun kwalin waya bisa cinyata,saida tsoro ya dabaibayeni ganin irin wayar daya siyo?

Wayace ta dubu daruruwa,bayan mun dauki hanya nace da sanyin murya "Oga Uhaimid bazan iya rike wannan wayar ba,tayi tsada Anna zata mun fad'a kowa zai tambaya ina na sameta"

"To ki jefar mana,in antambaya bakida bakin fad'in wanda ya siya miki"

Cikin rawar murya nace, "Anna zatai fad'a sosai tace miyasa na ansa"

"Shiyasa nace ki jefar ai"

"Kayi hkr baxan iya jefarwa ba,amma ka maida ni basai na rik'e waya ba"

Ya watso mun harara "saboda na fasa miki wadda Saurayinki ya baki.........girgiza kaina nayi "Ba saurayina bane wallahi,ni banda saurayi Oga Fauzan Yaya na..........dole nai shiru ban sake cewa komi ba,naga ina niyyar kaishi bango.

Wani mahaukacin shopping yai mani kamar wata yar masu manyan kud'i,amma ina fara magana naga zai balbaleni da masifa wai don ba Fauzan ne ya siya mun shiyasa zan rena mai wayau,ban kuma cewa kala ba har muka shigo makaranta,da kanshi yasa aka daukar mun kayan zuwa dakinmu na gaya masu dakin da zasu kai,da yake muna da masu mana wannan hidimar mata ne kuma.

Sim card ya mik'o mu sabbi yana kallona, "In kika kira wani dasu Allah ya isa,ba sai nace ga wanda xaki kira ba ruwanki ne ki kira kowa"

Kud'i ya fiddo rafar yan dari biyar ya mik'o mun, "ki rik'e hannunki saboda siyen handout da pad"

Kasa kallonsa nai saboda nauyin abunda ya fad'a, "nagode Allah ya saka da alkairi"

Haka muka rabu na wuce hostel d'in Ina zuwa Feedo na class,banda karfin jiki dana zuciyar dazan iya zuwa lectures,gaba d'aya banda kuzari na kwanta katifa nai shiru abubuwa suna cunkushe mun akaina,na rasa a wane mizani zan d'ora abunda nan daya faru,mi hakan ke nufi?wace manufa yake da ita.

Sahaar na bukatar fashin baki akan dan ATTAHIR MUKTAR🤩😄

Banjin dadin rashin comment har raina🥺😩

Mom muhsen ✍🏻