17&18
by @mommuhseen
SAHAAR
ADABI WRITER'S ASSOCIATION.
BY
MOM MUHSEEN
🅿️....17&18
Haka Feedo tazo ta iskeni kwance ko kayan dake tsakiyar d'akin ba wanda na kauda,ita ta shirya su kowenne ma ajinsa sannan na tashi na shiga toilet don na canza pad, bayan na gama na fito ta zubo mana abinci da tai kafun ta fita class, yadda taga inaci kamar bana so ban maci da yawa ba nace na k'oshi, "Tunda na shigo naga yana yinki kamar bakida lafia ko Mp d'inne?"
Na kwanta ina lumshe idona nace, "anmun allura bana jin ciwo sosai, kawae dai banda kuzari jikina"
"Daren jiya Hamma F yakirani wai yana neman ki, yaje dakin ki bakinan kuma ya kira wayarki baki dauka ba,daga karshe yaji a kashe"
"Na kwana da tunanin to ina zakije haka?"
Sai kawae na fashe da kuka sosai bata hanani ba saida nai mai isata sannan tace, "Miya faru dake ne?"
Ina shashshekar kuka sosai nace, "Oga Uhaimid.......sai na sake fashewa da kuka sosai, hankalinta ya tashi sosai "miya miki ne Sahaar?"
"Bansan ta inda zan fara ba,na rasa dame zan misalta abun daya mun jiya zuwa yau,kinga duk kayan nan shine ya siya mun,wannan wayar ma shine ya siya,bayan ya gama mun rashin mutunci yamun barazana sosai kuma yadda ya fad'a xai aikata, Feedo bansan ya zanyi ba taya zan nesanta kaina da Hamma F,"
Ina kukan na ke bata labarin abunda ya faru har zuwanmu makaranta, jinjina kai tayi tana murmushi sosai tace "Ya kike maida kanki yarinya wai Sahaar?yanzu wannan har yakai ki zauna kiyita kuka kina cewa bakisan ya zaki ba?"
Kallonta nai sosai jin abunda tace, "wannan d'in ne baikai nayi kuka ba,tsirai cina fa yagane mun sannan yana mun barazana da fyad'e,sannan kice bazan kuka ba"
Murmushi tayi tana gyara zamanta, "To bari kiji wani abu wannan kuke kuken da tsoron da kike nuna masa shine abu na farko da yasa zai ringa miki barazana, dole saikin cire tsoron sa a ranki kin kwaci kanki, wai shin tsaya ma tukun ke a tunanunki miyasa yake miki hakan??"
Girgiza Kaina nayi ina share hawayena, "Ban sani ba,tunda na dawo nake kwance ina sak'awa da kuncewa da tunanin miye amfanin abunda yai mun,Miye matsalarsa da Hamma F?"
Feedo ta gyara zama tana kallona sosai,kafun ta fashe da dariya, "wallahi bansan dame zan kiraki ba,yanzu duk wannan haukan nashi baki fahimci komi ba?"
Girgiza mata Kaina nayi, "Ban sani ba Feedo,nidai nasan ko a k'afa aka daura masani zai kunce tass,saboda wutsiyar rak'umi tayi nesa da k'asa,bayan haka kodayaushe uwargida tana mun kashedi da d'anta bansan amfanun hakan ba,kuma aure zayyi satittika masu zuwa"
Feedo tace "ture duk wadannan hujjojin naki,Oga Uhaimid SONKI YAKE ba kuma yau ya fara sonki ba,ba jiya ba bazan iya cewa ga lokacin ba,kishi ne ke neman ya haukata shi kema ya sanya ki haukace d'in, hallau Oga Fauzan shima abunda ke d'awainiya dashi kenan domin babu ta yadda za'ai su ringa miki hidima irin wannan ba dangin iya babu na baba, iya wannan wayar taki kad'ai ya isa ki shaida cewar wallahi sonki yake ba komi ba,ya kuma rasa taya zai furta miki kamar yadda Hamma F shima lalube yake yana son samun damar hakan"
Koma wa nayi na jingina bayana da bango na rufe idanuna,inajin yadda sautin bugun xuciyata yake shiga har cikin kunnuwa na,bawai don ban yarda ba bakuma don zuciyata bata kawo hakan ba Aa,tabbatar mun d'in da tayi shine shock d'in daya bugan,taya hakan zata faru?
"Kar wannan abun fa ya tada miki hankali Sahaar"
Bude idanu na nayi ina kallon ta nace, "Karya tada mun hankali fa kika ce?ya kike so inyi Feedo?kin kosan wacece UWARGIDA HAFSA? shin kin san matsayi irin na Fauzan da mahaifiyarsa? Duk bama wannan ba saboda me zasu nemi hargitsa lissafina?wai So lallai toni dukansu ba wanda yai mun,ni na iya talaucina ba kuma zasu jefani cikin matsala ba"
Feedo tace "Kin kai a sokin ne Sahaar,duk abunda ake nema jikin mace wanda namiji keso kin mallaka,kina da wani sirri wanda ke ba zaki iya ganeshi ba kuma wannan sirrin shine ya siyo miki zuciyar zaratan maza kamar su,wlh ko sarki baki fi karfinsa ko shugaban k'asa bakifi karfinsa,ke inmiki ta babban mahaukaci bakida wani namiji a aduniyar nan da yafi karfin aurenki,wannan wata nasara ce da sa'ar rayuwa Allah yana sonki da gata da rahma da jin dad'in rayuwa,karki butulce masa bance kiso wannan ki k'i wancen ba,amma ki natsu ki iya ganewa idonki wanne yafi dacewa da rayuwarki,"
Girgiza kaina nayi "bazan iya ba Feedo,su dukan bazan iya kwatanta son kowa ba ai banma san miye Son ba balle har na iya cewa xan iya gwadashi akan wani,ni zamana haka shine kwanciyar hankalina saboda koda zan iya d'in duk wanda na so banso d'ayan ba wata fitinar ce, ya kike son inyi?ni tashin hankalina shine ace Anna taji wannan labarin, wlh dana bani saboda ita kanta nesa take dasu balle ni.
kuma kullum mgnrta itace inyi nesa dasu in iya talaucina, kawai sai taji lbrin ina tare dasu?"
Feedo tace, "bakida hanyar gujewa ko wannen su,nayi imanin cewa ko binin sin kikaje sai Uhaimid ya biki a yadda kika gaya min shi to zai Iya komi akanki,haka zalika oga Fauzan aganina babu aibu don kinso dayansu kawae matsalar shine bakisan yadda zaki tafiyar dasu ba,tsoronki yai yawa ga kuka komi akai sai ki kama kuka,kefe yanzu ba yarinya bace aji biyu muke hari saboda me zaki bari namiji ya susutaki,mgnr Anna kuma ai bazai yuwu kibari tasan komi ba,kibarma lokaci in lokaci yai komi tafanjama fanjam,matsalar kawae kisan yadda zaki bida kowa cikinsu amma sai kin cire tsoro wlh"
"Feedo Uhaimid fa Aure zai nake gaya miki,taya zan ringa mu'amala dashi bayan nasan aure zai,bazan iya cutama Anti Jamila ba tayi min hallacci na rayuwa"
"Hmm,toshikenan sai ki cigaba da b'oye kanki kina shiga fargaba da sauran su,nidai shawarar dazan baki ki iya takunki banga alamun cikinsu akwai wanda zai iya hkr dake ba saboda wani kalubale"
*******
Haka na cigaba da zama cikin makaranta dakin Feedo muna lectures,Na kasa had'a wayar daya bani saboda bana son ya kira ink'i dauka ya min wani abun,gefe guda Kuma Hamma F yana kirana ta layin feedo bai nuna min komi ba,zamu gaisa sosai har fira muyi bai dai ce min zai zo ba,nima hakan yafiye min kwanciyar hankali ina adduar Allah yasa hasashen Feedo ne babu wani abu mai kama da soyayya ta cikin ranshi,duk da wani abun ni nasan dole akwai wata a k'asa to amma na bishi a yadda yazo mun,haka na kashe sati biyu har aka kafe mana time table,karatu baji ba gani haka muka fara shi inaso in kara point d'ina akan na waccen semester d'in,don yanzu kam alhamdulilla kaina yana d'auka sosai,har nakan wayar ma da wasu kai akan abunda basu gane ba,
Kwatsam rannan saiga Jidda tazo ashe sun dawo, mun fito daga exam karfe hud'u kiran waya ya shigowa Feedo tana dauka akace mata "Please kiba Sahaar waya"
Ta miko mun na ansa ina yin sallama, "Habawa Sahaar ashe zaki iya mantawa dani ko"
Inajin ta na gane nayi dariya "Kiyi hkr Jidda Ban san ta yadda xan magana dake ba,yaushe kuka dawo?"
"Jiyan nan wlh,gani cikin makaranta kuna ta ina"
Kwatance muka mata sai gata da mota,amma kamar driver ne ya kawota, ta fito tazo ta rungumeni "Nayi missing d'inki,ya sch d'in"
Na nuna mata question paper ina bata fuskata, "Ga sch nan ba dad'i jarabawa muke"
Tana dariya tace "Wayyo sorry kinji"
Suka gaisa da Feedo sosai sannan nace tazo muje dakinmu, muna tare har magariba saida tayi salla sannan tace Bari ta kira Hamma Uhaimid inya tashi aiki ya biyo yatafi da ita tunda dazun sallamar driver tai.
Rasss gabana ya fad'i sosai, nace "ki kira driver mana"
"Banda no. Dinsa ai,bari kawae inkira Hamma Uhai"
Feedo na mun dariya aboye,gaba d'aya naji duk na dame nasan bazai min ta dad'i ba,kuma dole infita rakata in yazo,inaji ta kirashi ya kuma ce mata to zai biyo.
Ana gama sallar isha'i kuwa ya kirata yana cikin get din area classes,Ba yadda banyi Feedo tazo muje ba tace ai nidai inje kamar zan kuka haka na fito don ma akwai hasken sola ko ina,sai kawae naji tace mun "Tsoron Hamma kike jiki ko?"
"Aa waye ya fad'a miki?"
Dariya tai tace "Nagani a fuskarki tun dana anbaci sunan shi,Hamma baida matsala kece kika kasa fahimtar shi,He's very nice kidaina tsoronsa"
"Hmm"
Kawai na fad'a har muka iso inda yake fira take mun ni kam na kasa cewa komi, yana tsaye jikin motar tashi tun daga nesa daman kamshin sa ya sake tabbatar da wanzuwar sa, dan danan bugun xuciyata ya karu akan na da,addua nakeda fatan Allah yasa mu rabu lfy, "Hamma kayi kyau sosai"
Wayar ya maida aljihu yace "Daga Office fa nake"
Tana dariya tace "Ehy mana,ai bakai daud'a ba ko Sahaar?"
Ta tambayeni tana kallona, murmushin yak'e nayi na d'aga kaina, a lokacin ne nace masa "Ina wuni Oga Uhaimid"
"Lafia lau ya sch"
Ya fad'a cikin sakewa irin wadda bazan iya tuna ranar dayai mun mgn haka ba,inajin tun muna karatu dashi kafin dawowar Oga Fauxan, "Lafia lau alhamdulilla"
"Ya exam d'in,yaushe kuke karewa?"
Ina wasa da yatsuna nace, "Next week insha Allah"
"Allah ya bada sa'a"
Ya kalli Jidda yace "muje ko"
Ta bude gaban ta zauna tana cemun, "Zakizo weekend jibi ko?"
Girgiza kaina nayi "Anya?nafison sai mun gama gaba d'aya sannan indawo"
"Ayya Allah ya kaimu ya bada sa'a..........Shigo muje na siya miki ice cream"
Naji ya fad'a yana kallona, girgiza kaina nayi "Nagode Oga Uhaimid karatu zan fita yanzu"
"Ai bazamu dad'e ba"
Jidda tace "Please kizo muje nima inci albarkacin ki"
Na rasa yadda zan doje ma fitar,bazan iya ture alfarma Jidda ba dole na shiga bayan motar muka fita,surutun ta kawae ke tashi a motar shi kuma yana biye mata, mamakinsa yana kamani daman yana raha haka?daman yana sake fuska har haka?
Tamabayar da naita ma kaina kenan,sau uku muna had'a ido ta madubi,duk na tsargu na kasa sakewa na matsu aje inda za'a, amma ga alamun ma sun mance dani amotar, saida yashigo titin unguwar yace "Ohhh sheet,Jidda kin mantar dani"
"Ya salam Sahaar baki tuna mana ba munata magana"
Kamar inyi kuka amma bance komi ba, "sauka ki idasa gida in maidata mkrnta parrot kawae"
"Wayyo Hamma to kasiyo dani kaji"
"Bazan siyo d'in ba"
Rigima ta fara mashi saida yace zai siyo mata d'in sannan ta fito tana mun bye bye,cikin wani irin gudu yaja motar muka koma baya, saida ya daidaita kan titi sannan ya rage gudun.
"Ina zamuje?"
Ya kallan a madubin motar yana tambayata, Kain d'ago kaina nayi nace "ka maidani mkrnta kawae nace daman karatu zanyi"
Baice dani komi ba har muje shagon kayan lashe lashen, katuwar robar ya siya mun da shawarma, ya ajemun ledar gabana ya koma ya tada motar muka dauki hanyar makaranta,ya tsaya inda zaifi mun saurin isa Hostel.
Kafin na bude ya zagayo ya bude mun,amma bai bani hanyar wuce wa ba ya tsaya gabana sosai, zuciyata ta soma tseren bugawa, muryarsa naji tayi sanyi sosai tayi kasa fiye da dazun, "Miyasa kika k'i hada wayanki"
Kasa magana nayi, ya sake cewa "Bakiji ba?"
"Kayi hkr"
Abunda nace masa kenan, huci ya fesar yace "Zaki iya mun alfarma daya?"
Dago idanuna nai ina kallonsa kamar daman hakan yake buk'ata, ya sauke mun kyawawan idanunsa masu fitar da wani kalar abu mai fizgar mutum zuwa garesu, "please"
Saurin aje kaina nayi k'asa muryata na yar rawa nace "Allah yasa zan iya"
"Ki had'a wayanki pls ba danni ba"
Mamakinsa kamar zai kasheni na dago ina kallon sa, yana dafe da murfin k'ofar yana kallona cikin hasken dake wajen yana kallona sosai, "Please"
Zuciyata kamar zata fito waje nakeji, yadda yake begging d'ina cikin taushin murya yana kara kasheni anan zaune, "Kinji"
Kaina na d'aga masa Ina son cewa wani abu, "Wayar yafi karfina tsoron anfani da ita nake"
Sumarsa ya shafa yana fesar da iska yace, "Ke kike ganin tafi karfinki,amma tunda kince ta miki girma ki bayar zan sake siya miki wata"
Girgiza kaina nayi, "Ni Aa"
Siririn murmushi ya kubce masa bai shirya ba,wani abu na mintsinanisa cikin kirjinsa zuwa zuciyarsa, "To ya kike so ayi"
"Karka siya wani wayan zan maido waccen ka maida,Zan siya wani da albashina.......albashin da kikace a rik'e a madadin na Humaira?"
Tsaresa nai da ido shaff na mance,sai na d'an sako k'afata Zan fito,yai saurin tare hanyar "kina saukowa Zan rungumeki gara ki koma mu gama mgnr mu"
"Don Allah Oga Uhaimid ka rabu dani"
"Saboda me?"
Kamar zan kuka nace "Na gaya ma karatu zanje nayi"
"In kinaso na barki ki tafi ki ansa mun alfarma ta zaki had'a wayarki,kuma dakin had'a ni zaki kira"
"Miyasa Zan kira ka?banda lokacin kiran waya......shiru nayi ganin yana kokarin shigowa inda nake, "kayi hkr Zan had'a"
"Yaushe?"
"Yau d'in koda safe haka"
Girgiza kanshi yake, "bazan iya hkr safe ba,duk dare ina saurarenki,.......To zanyi"
Har na sauko ina rik'e da ledar ice cream d'in ya jiyo yana kallona "Zamuyi rigimar da tafi ta wancen karon in kika sab'a alkawari"
"Zan had'a nace ai"
"Ohk goodnight"
Saida na b'acewa ganinsa naji tafiyarsa,ina zuwa dakin Feedo da wata qawarta suna karatu basu fita ba tace, "daga rakiya naji shiru"
Ledar na aje nace, "mun fita ne"
Na shige toilet na barta kawai.
*********
Ban shirin bacci ba sai karfe shabiyu na gama karatuna na tabbatar ya zauna banda wata matsala,nayi wanka na shirya na kwanta sai na tashi a firgice na dauko wayar Ina dubata, daker na iya had'ata daman anyi cajin d'inta tun rannan, sai na kunna ta cikin sim card d'in no. D'aya ce nasan kuma tashi ce banma san ya akai ya sakata ba, kira nayi kuma ta shiga alamun akwai credit ciki.
"Kin bani wuya tun dazun nake kallon wayata"
Abunda yace kenan, nace "Zan kwanta inada exam da safe"
"Wai haka kike ma shi mgn shi?kina mun mgn wani tsaitsaye"
Na masa shiru kamar banaji, "Dake nake mgn fa"
"Oga Uhaimid ya zance ma"
"Ya kike fira dashi a waya to?"
"Waye shi?ni bana fira da kowa"
"Dagaske?"
Ya fada cikin rainin hankali, "To da wane wayar zanyi firar?"
"Ni kike tambaya?karki jawo ma kanki rigimar da bakisan karshen ta ba,shiyasa kika watsar da wannan wayar saboda kina mgn dashi data yar dakin ki,ba abunda ban sani ba na barki kiyi mai isarki ne"
Kutmar k'aniyar can,wai miyake son zama ne haka taya yasan ina waya da wayar Feedo? Na shiga ukuna,gaskiyar Feedo kenan da tace ko birnin sin naje sai ya ganoni.
"Kina mamaki ko?,kibar mamaki zanyi abunda yafi wannan ma,na hkr ne sbd kina exam amma sai kin biya bashi nan,ki kwanta kiyi isashshen bacci MATAR AHMAD"
daga haka ya kashe wayar ya barni da ita kamar hoto ina kallon ta,nama rasa miye zanyi tunani akai!
Ayi hkr ba yawa banda lokaci yau sosai
Mom muhseen✍🏻