Raina!

Chapter 1

by @ayshashafiee01

Bismillahir rahmanir rahim.

Kowa ya san cewa I'm going to dedicate this book to you Ayunie, the one who always believed in my stories even when they were only scattered thoughts.

Yau baka nan, baza ka ga wannan rubutun nawa ba, but I wrote this with your love still holding my hand, and every word carries the part of me that still aches for you. Allah ya jikanka da rahamarsa, Ameen.

~ * * ~

If there's journey written in my destiny, then why should I stop anywhere, just moving with my own colour without any destination or strings... - Aliyu

New GRA, Phase 2, Porthacourt.

09:00 AM.

Safiya ce, amma idan mutum ya rufe idanunsa ya buɗe, zai ce yanayin na yamma ne bayan rana ta fadi, a lokacin da lumshin duhun dare kewa al'umma sallama kafin baiyanarsa, kuma hakan ya kasance ne sakamakon mamakon ruwan saman da aka kwana aka tashi dashi tun daga daren jiya, wanda duk da a yanzu ruwan ya tsaya sai yayyafi kawai dake sauka hakan bai sa garin ya washe ba.

Kuma sai mutane ma suka daɗa bada gudunmawa ta hanyar rashin fitowar su, duk da cewar ranar juma'a ce, ba ƙarshen satin da kowa ke mararin huce gajiyar jikinsa ba, amma duk da haka ɗaiɗaikun mutane ne kawai a waje, da yawa na gida lulluɓe cikin bargo da bacci mai daɗi.

Motar ƙirar accord ce, kalar makuba, ta wanku tas cikin yayyafin ruwan sai faman ƙyalli da ɗaukar ido take, tayoyinta a hankali suke motsawa har zuwa wata kwana da allon gefe ya kafe sunan 'Lawson Street' inda kamar koina na cikin unguwar ta sabuwar GRA, layin mai tsananin kyau ne ɗauke da haɗaɗɗun gidaje kala-kala da kuma mikakken titi baki-ƙirin da shima ya wanku cikin ruwan.

A cikin motar mutane biyu ne, matuƙin mai suna Jamilu, wanda ba zai wuce shekaru talatin da biyar a ƙiyasce ba sai kuma wata dattijuwar mata dake zaune a baya, Hajiya Laila. Fara ce ƙal! Yafe da wani mayafi kalar ruwan madara da ya ƙara fito da haske da kuma kwarjininta, ga mai kallon da bai san ko wacece ba kenan.

Amma ga wanda ya santa, kallo ɗaya ne zai nuna masa irin tsananin fargaba da kuma hanƙoron dake kan fuskarta, don manya-manyan idanun nata basa taɓa iya ɓoye halayen zuciyarta.

Hannayen ta duka biyu suna damƙe ne da ƴar jakar hannunta mai cike da tarin takardu da kuma adadin kudi mai yawa, wataƙila kuma ta riƙe jakar ne don kar rawar da jikinta ke yi ta fallasa a idanun Jamilun da tun fitowar su daga hotel ɗin da suka kwana a garin yake bin ta da maganganu na cewar ta kwantar da hankalinta, komai zai tafi kamar yadda suka tsara.

Kamar yadda suka tsara.

Wani tsari da aka shafe fiye da shekaru tana zana shi a allon cikin ƙwaƙwalwarta, tana hango shi a idanunta sannan kuma tana kawata shi a mafarkin ta... Amma me akace ne? Wai babu wani abu da yake ɗorewa a duniya, a yau duk wannan tsarin da shirye-shiryen ya wuce, yau itace ranar da take ganin zata fuskanci komai. Ta gyara zaman mayafinta wanda har a yanzu take tantamar dacewar sa da wannan yanayin, don bata san me yafi dacewa ace macen da ta fito neman ɗanta ta sanya ba.

"Hajiya, mun karaso Block E ɗin, let me call him."

Muryar Jamilu ta ratsa cikin kanta lokacin da ya bar leƙe-leken da yake yi ta window ya tsayar da motar a gefe, sai ta juya ta kalli gefen inda suka tsaya din ɓangaren dama, sannan ta kalli takardar dake riƙe a hannunta, layi na ƙarshe a jiki shine...

'Block E, Lawson Street, New GRA Phase 2.'

Sai daga ƙasa kuma suna ne da nambar wayar mutum na ƙarshe da zai zama jakadan su ga ɗan data shafe shekaru cikin bulayin nemansa... Aliyu! Aliyun ta!

'Emmanuel Eliotepe, 0803375....'

A lokacin da ta ɗago da idanunta har Jamilu ya kara waya a kunnen sa wajen kiran layin, ta sani cewar tun farko ya riga ya zuba nambobin duk mutanen da suka mu'amalanta a tsawon tafiyarsu tun daga farko har zuwa nan. Wani irin mutum ne shi mai himma da kuzari, abinda ta nazarta kenan game dashi wanda yasa har ta tsallake kowa ta jawo shi cikin fafutukar da suke yin ta shekara da shekaru.

"Okay, we're outside waiting." (Muna waje muna jira.)

Amsar da Jamilun ya bayar cikin wayar kenan bayan ƴar gajeriyar maganar da aka yi a ciki, sai kawai tayi saurin sake buɗe jakarta ta damƙo kuɗin da bata san adadin sa ba ta miƙo masa.

"Idan ya fito, ka ƙara masa da wannan akan waɗanda zaka bashi."

"Haba Hajiya..."

Cewar Jamilun yana girgiza kansa.

"Su fa mutanen nan abin tsoro ne, yanzu yana gani mun ƙara masa wani abun sai ya yi tunanin da sauran kudi da yawa ne a jikin mu, kuma abubuwa su zo su canja akala. Ki barni dashi da iya waɗannan ɗin da akayi yarjejeniya kawai."

Babu musu sai ta gyaɗa kanta, ta mayar da kudin jaka don ya riga ya faɗi abinda ko da wasa ba zata iya sake cewa komai ba. Kuma bayan hakan tsawon wucewar mintuna biyar, ƙafafunta na ta kadawa cikin tsananin jira da hanƙoro sai wata kofa daga jikin ginin Block E ɗin ta buɗe, wani ƙaton mutumi ya fito daga ciki sanye da ƙananun kaya, kuma cikin ɗan gudu-gudu na kaucewa jiƙewar yayyafin ya karaso da sauri ya buɗe ƙofar motar ta gaba ta shigo. Ƙamshinsa na daban ya gauraya da iskar cikin motar a take, yasa cikin Hajiya Laila kadawa tare da ƙara tsurar da tunaninta.

"The place is just two corners from here, lets move." (Wajen layi biyu ne kawai daga nan, mu tafi.)

Abinda ya fada kenan ba tare da ya damu da kallon kowa a cikin motar ba, kuma babu musu Jamilu ya tada injin motar tayoyinta suka shiga murzawa akan jikakken titin, Idanun Hajiya Laila suka bi kafaɗun mutumin nan da kallo a lokacin da taji kwalla na neman cika idanunta.

Ta ya ya zata taba tunanin cewa ta sanadiyar wannan arnen ne zata yi fatan sake ganin fuskar ɗan ta? A baya zata ƙaryata duk mafarkin da wani zai gaya mata hakan balle ta yarda da faruwarsa... Rayuwa kenan! Zuciyarta ta ambata a lokacin da hawayen daya taru a idanunta ya sauko, taji shi mai ɗumi akan fatar ta yayin da ƙwaƙwalwar ta ke tuna mata da wani zamani daban, wani lokaci da kalmar 'baya' ta shuɗe dashi.

Sanda take ɗauke da su Aliyun a cikinta, sanda motsin su ke sukar marar ta, da lokacin da bayan sun zo duniya yatsunta ke kasa fita daga hannunsa idan ta riƙe shi, da sanda zata manna shi da ƙirjinta yayin da yake tsallara kukan da babu gaira ba dalilinsa alhali danuwansa na kwance yana bacci, haka zata shafe awannin kowanne dare tana zagaye gida rike dashi a ƙirjinta har sai addu'oin da take furtawa a kunnensa sun kwantar da kukan nasa ta fara jin bugawar zuciyarsa akan tata... Sai gashi wai a yau yayi mata nisan da sai ta hanyar wannan inyamurin take fatan lokaci zai sake haɗa su, a lokaci guda idanunta suka cika da kwallar da take jin tsananin zafi da kuma yajinta.

Kuma cikin dishi-dishin hawayen, ta hango fuskarsa, fuskarsa a ranar da tayi masa gani na karshe... Ranar da duniyarta ta tarwatse, Ranar rasuwar Ahmad, ranar da ya shigo ɗauke da gawarsa a kafaɗarsa, ta tuno yadda ya haɗa da ita da gawar ya riƙe a wancan lokacin yana irin wani irin kuka da ko a gaban ubangiji zata rantse Aliyu bai taba yin irinsa ba, sai kawai ta karasa rufe idanun nata yayin da a hankali hawayen ya shiga sulalewa akan kuncinta.

A cikin duhun fatar idanun nata ta hango fuskokin ƴaƴan nata su biyu wannan karon, su biyun da tun farkon wanzuwarsu ubangiji ya halitta su a cikinta kuma suka zo duniyar a lokaci guda, sai dai idan ba mutum ya sani bane babu ta yadda zai canki cewa su ƴan biyu ne, don tun daga kan siffa har zuwa halayya kowa yasha banban da ɗanuwansa.

Ahmad fari ne tas kamar ita, mutum mai raha da son mutane, mai saukin kai, mai saurin sabo ta hanyar yalwataccen murmushin da ba ya taɓa barin fuskarsa a kodayaushe sannan kuma mai tsokana, yana da ƙoƙari da kuma son ganin ya farantawa mutanen dake tare dashi da zuciya ɗaya, irin mutanen nan ne da idan ka hadu dasu a rana ɗaya zasu kama zuciyarka, idan ka saba dasu kuma sai kayi mamakin yadda rayuwarka ta baya ta tafiyu babu su.

Aliyu ba fari bane amma kalar fatarsa mai duhu ce kuma mai haske idan zaka kwatanta ta da sha'anin hutu, kuma wataƙila lissafin nasa halayen zai iya cika wani guntun littafin da mutum zai shafe awanni yana karantawa.

Don tun a lokacin yarintarsu a kallo ɗaya ne mutum zai banbance su kamar yadda zai banbance yatsun hannunsa, Ahmad zai shiga cikin yara a koina, a yi wasa kamar ba gobe amma Aliyu zai tsaya ne a gefe kawai yana kallon kowa, kuma in dai Ahmad din yana waje to kuwa zai jira shi ne ya gama duk abinda zai yi ko da kuwa hakan laifi ne.

Babu adadi ta sha saka yayansu (ɗan mijinta) Muhammad ya zane su a duk lokutan da Ahmad din ke tsayawa wasa ko kuma yabi yara su tafi yawo musamman bayan an tashe su daga islamiyya, kuma duk inda za'aje din tare da Aliyun zasu je amma zaiyi ta binsu ne kawai har san da Ahmad din zai gaji ya juyo yace su tafi gida, kuma da sun dawo a kallo ɗaya kawai ta ke yi musu ta gane me ya faru don Ahmad zai dawo da kayansa ne kamar mai haƙan rijiya amma Aliyun ba ya taɓa yin datti da jikinsa, ƙarya ne ace an samu wata rana da kayansa zasu yi futu-futu da dattin da ido zai ganshi, ya iya killace duk wani abu da yake nasa da kuma tattala shi saɓanin Ahmad ɗin da duk wani abu nasa baya taɓa yin ƙarko.

Mutum ne shi mai zurfin ciki, kafaffen ra'ayi da wata irin zuciya mara misaltuwa, abinda yake so ya kan sha banban da wanda tarin jama'a suka taru akansa, kuma idan ya furta magana babu wanda ya isa ya canja shi akanta, babu kuma tana nufin babun da gaske! sannan idan ransa ya ɓaci baya shakkar kowa kuma baya shakkar gayawa kowa maganar dake bakinsa, don haka halayensa a bauɗe suke ta hanyar ƙara tunzura shin da mutane ke yi sakamakon rashin fahimtarsa.

Shi yasa a kullum shima yake janye jikinsa daga cikin mutanen, yana yin nesa dasu yana kuma sauke fushinsa akan duk wanda ya taɓo shi, wanda hakan wani abu ne da kullum yake ƙara ɓantare rusashshiyar alaƙar dake tsakaninsa da mahaifinsa, wata alaƙa da ta riga tayi rauni tun kafin ya gama tsayawa da ƙafafunsa a duniya.

Mahaifin nasu Alhaji Abdurrazak mutum ne mai tsananin ra'ayi da kuma son juya ƴaƴan sa zuwa abinda zuciyarsa ta raya masa, don tun daga kan yayyen su Aliyun biyu maza shi ke zaɓa wa kowa abinda zai yi daga harkar karatu har zamantakewar rayuwa, kuma babu wanda ya isa ya bashi shawara akansu balle a ƙalubance shi.

Wannan halinsa ne tun a zamanin da bai ma mallaki ƴaƴan ba, ya iya juya duk wani abu dake ƙarkashin ikonsa zuwa wani abu da zai haɓɓaka ta hanyar daya juya shi ɗin, kuma wannan tambarin nasa shi ya jawo masa tarin buɗi a harkar kasuwancinsa da yake yi ta kayan katako har ta kai ya mallaki hadadden kamfanin kansa wanda suke ƙera duk wani nau'in kayan katako kowanne iri cikin tsari da kuma haɗuwar da ya fitar dashi ya zama zakka a cikin ire-irensa.

Sai dai shi kansa ya sani cewa ba'a koina wannan halin nasa ke aiki ba, don tsatstsauran ra'ayin nasa shine sanadin rabuwarsa da matarsa ta farko wadda ta haifa masa ƴaƴa biyu, Muhammad da Bello... Amma bayan ita ya aure ta sai komai ya cigaba, don ya same ta ne mai tsananin sanyin hali da kuma haƙurin da duk abinda zai ce ba zata taɓa buɗa baki ta ƙalubalance shi ba.

Don haka sai ya cigaba da yarda cewa duk wata hanya da zai bi daidai ce, zata ɓulle dashi zuwa gaɓar da zata amfanar, ya yarda Allah ya bashi tunanin da yasha banban da al'umma, ya tabbatar cewa abinda yake iya hange ba idon kowa ne ke ɗauko shi ba kuma babu abinda zaiyi wanda ba daidai bane.

Sai Aliyu sai yazo daban, daban da ɗanuwansa kuma daban da kowa, kowan ya haɗa har ƙannensu biyu mata Zahra da Nusaiba da ta haifa bayan su. Shi kaɗai ke baiyana ra'ayinsa a duk lokacin da abu bai yi masa ba, shi kaɗai ke ƙin yin abu idan baya so, shi kaɗai ke ƙalubalantar mahaifin nasa, shi kaɗai ke cewa

"Wannan ra'ayinka ne Daddy, ni a bar ni inyi abinda nake so..."

Wasu maganganu da tun lokacin yarintar sa, suka zama mafarin ɓata shi a idanun mahaifin nasa, ya zama baya janyo shi a jiki kamar sauran ƴaƴan sa, baya sanya shi cikin lamuran sa, zai ce mata

"Yaron nan yana da matsala nace ki kai shi asibiti a duba shi.."

Don har ga Allah a tunaninsa Aliyun yana da matsalar ƙwaƙwalwa ne, sai bayan da ya fara girma sannan ya fahimci halinsa ne daban, don haka sai yayi ƙoƙarin amfani da karfin iko a matsayinsa na mahaifinsa ya tanƙwara shi, amma hakan bai yi komai ba sai ma ɓata al'amura da yayi.

Ya buɗe tarin wasu shafukan na halayyar Aliyun da ba'a ma sani ba, ya sanya zuciyar yaron ta ƙeƙashe akansa, ya yarda baya son sa shima kuma ya fara tabbatar masa da hakan tun daga wata rana da aka dawo da Aliyun daga makaranta bayan yayi wa malamin su duka akan cewa ya dake shi bayan baiyi masa komai ba.

Shekarun sa goma a lokacin, yana tsugunne a gabansa bayan tafiyar malaman nasu hannayensa a ɗaure da rigar makarantar sa da aka cire, Alhaji Sa'ad ya girgiza kansa yana kallonsa cike da takaici, sannan ya faɗi maganar da itace farkon lissafin da Aliyu zai iya riƙewa.

"Allah wadaran haihuwarka Aliyu!"

Kuma duk da kanƙantar shekarun sa a wannan lokacin, shima kallonsa yake da wani irin yanayi mara fasaltuwa yayin da ƙwalla ta cika idanunsa, ƙwallar da bata taru a duk dukan da yasha na makaranta ba sai a wannan lokacin da ƙwaƙwalwarsa ta tabbatar masa da hasashe da kuma waswasin daya daɗe yana jerawa akan mahaifin nasa.

Kuma bayan ya ƙara girma sai komai ya ƙara rincaɓewa maimakon abubuwa su yi sauki kamar yadda take lallashinsa a kodayaushe, sai kowa ya kara yin nesa dashi sakamakon rashin fahimtarsa da akeyi, ya zama daga ita sai ɗanuwansa kawai ke da kusanci a rayuwarsa.

Ahmad ke lauya kansa zuwa daidai da ra'ayin Aliyun a kodayaushe, baya taba damun kansa da banbancin halayyarsu balle har ya ji wani abu game da ɗanuwan nasa, hasalima idan har kana son ganin ɓacin ransa to ka furta laifin Aliyun koda kuwa abinda ka faɗa ɗin laifi ne, wannan dai ƙaunar da ubangiji ke halittawa a tsakanin kowaɗanne tagwaye itace zaren dake jan alaƙarsu.

Amma mutane da yawa ma tsoronsa suke ji, don sautin muryarsa kaɗai mai zurfi da zaƙi kan sa kowanne irin mutum ya tsaida abinda yake yi ya ɗago ya kalle shi, idan ransa ya ɓaci kuwa sautin ya haɗu da ɗagawar muryar, zaka tsinci wani abu na rawa a ƙirjinka duk sanda yake magana.

A daidai wannan lokacin, a wajen duniyar da Hajiya laila ta tafi cikin tunaninta,  Jamilu yasha kwana ta ƙarshe a kwatancen da Emmanuel yake yi masa, don haka ta ajiye dukkan tunanin nata a gefe ta bude idanunta a hankali sannan tasa hannunta guda daya ta share hawayen da ya fara bushewa a fuskarta, kuma duk da ɗokin dake cikin zuciyarta sai ta kasa ɗagowa har sai da muryar Emmanuel ɗin ta furta wani abu da ya daki tsakiyar kanta.

"The house is there, the one at the far end..." (Ga gidan nan, wancan na ƙarshen.)

Ya fada a lokacin da Jamilu ke tsayar da motar daidai ƙarshen layin, a lokacin ne ta dago da kanta idanunta na turawa ƙwaƙwalwarta sakon hoton gidan... A duk layin, ginin shi kaɗai ne daban, shi kadai ne babu irinsa don yawanci gidajen duka estates ne, amma shi wannan yana tsaye ne shi kaɗai a gefen kowanne. Har abada Aliyun ta daban ne, baya taba haɗa kansa da kowa kuma baya taba jiɓantar kowa, komai nasa daban ne a rayuwa, daban ɗin da ke sawa kowa ya ɗaga idanu ya kalle shi.

"Nace Aajiya a wannan gidan ne yaron da na gani a photonku yake."

Muryar Inyamurin ta fada a lokacin da shima yake bin haɗadden ginin gidan da kallo. Hajiya Laila bata ko ji shi ba saboda yanayin da zuciyarta ta gama fadawa, sai kawai ta ajiye jakarta da sauran takardun data fito dasu a gefe sannan ta bude ƙofar motar a lokacin da Jamilu ke bude wajen dashboard yana nunawa Emmanuel kuɗin sa.

Iskar farko mai sanyi da danshi ta daki fuskar ta da wani irin yanayin da ya shiga haska mata komai kamar ba a gaske ba, sai taji kamar tana zarmewa ne cikin irin mafarkan data sha kwana tana tashi dasu a shekarun baya, da takalmanta suka miƙe cikin danshin wajen kuwa, sai ta fahimci cewa ba hannayenta kaɗai ba har ƙafafunta rawa suke.... Ga kuma yanayin garin na lumshin dake ƙara nuna mata kamar komai ɗin ba gaske bane, kamar komai ɗin a mafarki ne yanzu kofa zata buɗe muryar ɗaya daga cikinsu Nusaiba ta tashe ta, amma sai ta ture komai ta motsa zuciyarta tabi ta kan slope ɗin ya tsallakar da ita kwalbatin wajen sannan ta tunkari gidan daya kara tsawo a idanunta.

Tana jin yadda yayyafi ke sauka a mayafinta da kuma sanyin iskar dake ratsa ta amma bata damu da hakan ba, zata fassara yanayin da take ciki ga mutumin daya taba rasa wani makusancinsa, uwa, uba, ɗan'uwa ko kuma wani abokin rayuwar da mutuwa tayi muku yankan kauna, idan har aka shaida maka cewa wanda kake kewa din bai mutu ba, kaje ga wata ƙofa zaka ganshi... to zata kwatanta maka abinda take ji ne da makanancin wannan.

Hannunta ya tura ɗan ƙaramin gate ɗin gidan ta shiga, kuma bata kula da komai a harabar ba bayan ƙofar shiga gidan da idanunta suka manne akai. Kalar yalo ce, ta isa gare ta bayan takalmanta sun cire a rashin sani, don sai da ta taka baranda ƙofar inda babu danshin ruwa sannan ta fahimci tun daga gate ɗin suka zame daga ƙafafunta.

Babu ɓata lokaci hannunta ya sauka akan makunni mai alamar kararrawar dake ƙwanƙwansa gidan, ta danna sannan ta ja baya tana ƙare wa ƙofar kallo da zuciyarta mai zurfi... Wai a bayan ƙofar nan Aliyu ne zai baiyana! Aliyu! Aliyun ta! Wannan ɗan da ya girma a jikinta! Wannan ɗan da yasha gaya mata cewa ba zai iya rayuwa idan babu ita ba, itace ƙarfinsa kuma itace rauninsa! Wannan ɗan da take so fiye da dukkanin ƴaƴanta!

Sai kawai ta sake matsawa jikin ƙararrawar ta shiga danna ta ba ƙauƙautawa, yi take hannunta baya Tsayawa kuma zuciyarta bata tsayawa da gaya mata cewar zata kwana tana hakan har sai ƙofar ta buɗe...!

**

I live like an ascetic and my mind wanders around, now where will this vagrancy take me? -Aliyu.

Primecare Hospital. Plot 8, Sultan Dikko Way, GRA, Kaduna State.

02:30pm

Kofar ta buɗe kai tsaye, don Dr. Aliyu bai ƙwankwasa ba, baya knocking kowa ya riga ya san wannan a asibitin, kamar yadda yake bude ƙofar dakin tiyata ya shiga kai tsaye haka yake bude kowacce ƙofar da zai shiga, kowacce kuma na nufin kowacce.

Wannan dabi'arsa ce da ba wai ya tsara ta bane, kawai tunanin yin knocking din ne ma baya zuwa kansa, shi yasa a yanzun ma kawai murda kofar ya yi ya shigo duk da cewar wannan ƙofar ta banbanta da kowacce a cikin asibitin, don a samanta harafai ne da aka rubuta da wani ƙarfe mai ƙyalli da suka hadu suka bada sunan 'Professor Ibrahim Ɗanladi' yayin da daga ƙasa kuma aka rubuta matsayinsa da muƙaminsa wanda kowa ya kwana da saninsa a asibitin 'Owner / Proprietor.'

A lokaci guda ƙamshin takardun litattafai da ya hadu da turaren da Aliyu ya haddace saninsa a matsayin tambarin Professor Ibrahim ɗin ya isa hancinsa kafin idonsa ya sauka akansa, yana zaune daga can kan makeken teburin cikin ofishin, mai dauke da tarin takardu, desktop screen da kuma wasu kayan amfanin da kullum suke nan.

Daga kowanne ɓangare na bangon jikin office din akwai wasu hadaddun shelfs da yadda aka tsara su da kuma katakon da aka yi su kadai ya ishe ka kallo banda tarin litttafan dake jere cikin tsari a cikinsu, litattafan da ko a ƴar wasan canki-canki zaka bada yakinin cewa mai su ya kai ƙurewar mataki a al'amarin boko.

Sai kawai ya yi karfin halin ƙarasawa cikin a hankali bayan ya furta sallamar da Profesorn ɗin ya amsa ba tare da ya janye idanunsa daga kallon screen din computer dake gabansa ba.

Ƙafafunsa suka tsaya a daidai gaban teburin kuma maimakon ya sami daya daga cikin kujeru biyun dake wajen ya zauna sai kawai ya durkusa har kasa akan gwiwoyinsa sannan muryarsa mai zurfi ta furta.

"Sir Barka da yamma."

"Barka ka dai Aliyu, muna lafiya?"

Tasa muryar mai cike da kwarjini ta amsa  ba tare da ya kalle shi ba har yanzu."

"Alhmdlilah mun gode Allah."

Sai ya gyada kansa sannan ya juyo ya kalle shi. Dogwayen kaya ne kaftan a jikinsa, na wani lallausan yadi a jikinsa farare tas! Gugar jikinsu na kara sa yadin kwanciya a jikinsa sosai, wanda hakan ya fito da fadin kafadunsa dake kara masa kwarjini a idon mutane, babu hula a kasa sai gashin kansa baki sidik wanda ya taho har cikin fuskarsa ya kuma hade da sajen da ya zagaye fuskar tasa gabadaya, bakin gashin na sake fito da hasken fatarsa wanda ke fallasa hutu da kuma jin dadin da lokaci ya kawo masa.

Idan ka kalle shi ba zaka ce wai likita bane ko kadan, likitan ma na tiyata, wanda in dai a cikin asibiti ne to ana sa ran ganin likitan tiyata ne da korayen kaya da safar hannu tayi kaca-kaca da jini, musamman a dazu da ya tura a kira shi ma aka shaida masa cewar yana cikin wata tiyatar, to amma shi kansa Professon ya sani zai tsaya a koina ya bada shaidar cewa tun daga ranar da ya san Aliyu, bai taba ganinsa cikin wata shigar dake nuna datti ko makamancin haka ba har kuwa a zamani da rayuwa take baibai a wajensa.

"Tashi ka zauna, taso."

Aliyu ya mike, ya nemi daya daga cikin kujerun ya zauna, har yanzu idanunsa a kasa, gashin jikinsu sun hade da junansu kamar ma idanun a rufe suke gabadaya.

"Ranar Monday ma na shigo bamu hadu ba."

Aliyu ya gyada kansa.

"Ai kowacce Monday bata zuwa da sauki Sir, don wani lokacin har patient biyar muna samu a rana daya."

"Kuma ka tabbata dai in an samu patient biyar din nan baka yi musu mantuwa a ciki ko?"

Ba shiri Aliyu yayi murmushin da ya tala lebbensa, ai ba'a taba yin ranar da zasu hadu bai tsokane shi ba dama.

Prof ya gyada kansa shima fuska a sake.

"To Allah ya taimaka, I'm proud, really."

Ya fadi abinda ya saba fada masa a kodayaushe, Aliyu ya gyada kansa shima alamun amsawa ba tare da yace komai ba.

"Ko zaka hado mana tea, don maganar da zamu yi ina ga dole muna bukatar shayin nan."

Wani abu a cikin kirjin Aliyu ya motsa a lokaci guda, dama ya sani tunda yaji kiran Proff ya san ba wani abu bane ƙarar sa aka kai, idonsa ya hasko masa fuskar CMO (Chief Medical Officer) don ko lalube zai yi ya san aikinsa ne wannan. Sai kawai ya mike ya nufi can kan wani dan karamin fridge a gefe da aka jera kayan tea din, akwai kettle a gefe jone a jikin socket, ya tsiyayo ruwan zafin cikinta ya zuba a mugs guda biyu ya hada tean, sannan ya dauko ya kawo.

Ya ajiye masa daya akan teburin sannan ya koma ya zauna rike da nasa a hannu ba tare da ya sha ba, don bai ma sani ba idan zai sha din.

Prof ya dauki nasa kofin ya kai baki, ya zuka a hankali sannan ya mayar ya ajiye,  a cikin takardun gabansa ya zaro guda daya ya mikawa Aliyun, yasa hannu ya karba a lokaci guda da idonsa ya sauka akan sunan da a ka rubuta baro-baro da jan inki.

'Surgical Recovery & Reintegration Initiative.(SRRI)'

Sai kawai ya hadiye wani abu a makogwaron sa a hankali sannan yace.

"Sir, sun tuntube ni kuma na riga na basu amsata."

Proffessor ya gyada kansa.

"Exactly, sun gaya min cewa you turned them down. Twice.”

Aliyu ya cije lebbensa kadan.

“With respect sir, I’m a surgeon. (Ninlikitan tiyata ne) I don’t lead social programs. Ka sani, bana son duk abinda zai hada ni mu'amala da mutane.”

Ya fada muryarsa a hankali amma kunnen Professor ta fito ne da wani irin kaifi ɗaya.

Shiru ya ratsa na wasu sakanni kafin Professor Ibrahim ya kai hannu ya dauki shayinsa ya sha sannan yace.

"Wannan program din ba harkar NGO bace ko wata kungiya ta daban , program ne da yazo daga gwamnatin tarayya, federal Ministry of health kuma a private hospitals ɗari biyu kawai za'a fara gudanar dashi a duk fadin ƙasar nan, na samu labarin program din tun wancan shekarar da aka fito da aim din kafin ma request yaje wajen shugaban ƙasa, I don't have to sit here in gaya maka irin fafutukar da na sha kafin in samu sunan asibitin nan nawa ya shiga cikin jerin wanda za'a fara gwada wannan program din a cikinsu.

Yanzu mun samu tare da alkawarin idan har muka yi achieving result din da ake nema, za'a bamu permanent licence na gudanar dashi har abada a asibitin nan, zamu zama daga cikin asibitoci na farko a arewa da zamu fara gudanar da wannan tallafin, kuma ba sai na gaya maka irin nasarorin da zamu samu da hakan ba kai ma ka sani, Partnerships, funding, visibility a duniya bakiɗaya, It's just something that will put us in the map."

Aliyu ya gyada kansa.

"Na sani Sir, shi yasa nima nake suggesting cewa a zabi wanda zai iya, akwai wasu surgeons din a asibitin nan bani kadai bane, wanda suka saba da irin wannan aikin na duba patients, a tunani na su zasu fi dacewa akan ni ɗin da tun fara aikina babu abinda yake hada ni da mara lafiya.

Ka sani Sir, I only meet my patients unconscious anaesthetized, bana jin akwai mutum daya da na taba yiwa tiyata wanda ya san ni, sannan ko meeting bana attending."

Ya dago da kansa sanda ya fadi hakan, ya kalli idon dattijon da shi kansa ya san karfin hali yake yi na dagewar cewa ba zai karbi aikin ba don kawai da gaske baya so ni din ne.

"Bukata ta ba ta wanda ya saba da mutane bace Aliyu, bukatata ta wanda zai jajirce ce yayi wannan aikin da dukkan kokarinsa don mu samu mu yi scaling wannan siraɗin, and when it comes to that bana ganin kowa sai kai, saboda na san you'll do it right no matter what."

Ya fadi hakan yana kallon idanun Aliyun da har yanzu bai ga alamun cewa maganganun da yake yi suna shirin shawo kansa ba.

Allah ya sani idan za'a tsayar dashi a tambaye shi menene taurin kai a duniyar nan to tabbas fuskar Aliyu zai fara hangowa, ya riga ya san wannan tun a rana ta farko da ya fara ganinsa, kawai anyi sa'a ne a cikin kwakwalwarsa ɓangaren da yake da hankali yafi rinjaye akan akasin sa shi yasa ma ba kowa ne yake fahimtar hakan ba.

Sannan duk wadannnan bayanin da ya zauna ya yi masa ya riga ya sansu daman, kawai yana maimatawa ne a kokarinsa na kare kansa, don da gaske baya son yin irinwannan aikin ya sani, kuma  a tsawon shekarun da ya shafe yana aiki a asibitin nan bai taba takura masa da wani abu makamancin haka ba, Duk abinda yace ga yadda zai yi, zai bashi goyon baya ne ba tare da ya ƙalubalance ba.

Ta haka ne yake aikinsa hankali kwance da kuma jajircewar da ya san idan har za'a zauna a tebur a raba nasarorin asibitin daga shekarun da ya fara aiki tare dasu, to tabbas Aliyu zai dauki kaso mafi yawa a ciki, don sunansa ya riga ya yi suna a bangaren tiyata, kuma tun dawowarsa asibitin ne aka san su a matsayin asibiti mafi shuhura wajen yin tiyata mai inganci.

Shi yasa ko da wannan damar tazo ma babu wanda ya fara zuwa kansa sai Aliyun, don ya san jajircewa irin tasa ce zata sa a cimma abinda ake so.  Shi yasa ya shiryawa kansa dukkan irin tirjiyar da ya san Aliyun zaiyi ya kuma ya sa a ransa cewar dole yasa ya karbi tayin nasa ko yana ko baya so.

Don haka sai kawai ya ajiye kofin hannunsa sannan ya cire gilashin idonsa.

A karo na farko tun bayan da suka fara magana ya kira sunansa.

"Aliyu..."

"Idan har duk wadannan bayanan da nayi basu gamshe ka kayi accepting offer din nan ba, to ina ga lokaci ya yi da zaka biya ni bashin da nake binka kenan."

A lokaci guda kalaman suka taho tamkar saukar mari, don Aliyu zai iya rantsewa ya ji zafin saukarsu a kuncinsa, numfashinsa ya katse a kirjinsa, komai ya tsaya cak a cikin kansa, abinda yake gani a gabansa ya dauke, wasu tarin hotuna suka maye gurbinsa... Yana ganinsu tar! Tamkar a lokacin komai yake faruwa... Wannan daren, wannan daren da ƙaddara ta kawo shi cikin asibitin nan, ƙaddarar da ta zama sillar faruwar matsayin da yake kai a yanzu.

A ranar an yini ana ruwa, koina ya jike sharkaf! Hasken fitulun asibitin suna haskawa a cikin ruwan da ya taru a ƙasa.

A cikin idonsa ya hango kansa, lokacin da ya tsaya a jikin wata mota baƙa, ƙirar Camry, hannayensa suna rawa yayin da yake kokarin zura ƴar siririyar wayar hannunsa a jikin gidan mukullinta, rawar da hannunsa yake bana tsoro bane ko na rashin sanin abinda zai yi, illa na yunwa, yunwar dake bin kowacce jijiya ta jikinsa a sannan.

Daga bayansa wata murya ta tsaida shi kafin ya kai ga ƙarasa buɗe motar.

"Haka kake so ka kare rayuwarka?"

Ya juyo a hankali, ba don ya gudu ba sai don ya saduda ya karbi hukuncin da ya san abinda mai maganar yake shirin yi masa kenan.i

Amma maimakon wani yunkuri na duka ko zagi, sai Professor Ibrahim na wancan lokacin ya miko masa lemar dake hannunsa, yayyafin da ake yi ya koma shi yana jika shi.

"Daga ina kake?"

Tambayar da yayi masa kenan a wancan lokacin, tambayar da bai bashi amsa kai tsaye ba, amma bayan wucewar wasu watanni ya tsinci kansa a ofishinsa rike da takaradar ɗaukar karatun likita, don tun kafin ya ji labarinsa ya gaya masa cewa bai ga sata a tare dashi ba, ya ga wani matashi ne da yayi kuskuren ɗaukan hanya mara kyau don neman yadda zai rayu!

Kuma tun daga wannan ranar zai rantse da Allah Professor Ibrahim bai taba wata maganar da zata tuno masa da wannan ranar ba sai dai shi ɗin ma ya tuna a lokuta da yawa idan ya ɗaga ido ya kalle shi, amma bai sake yi masa zancen wannan taimakon da ya yi masa ba, har yayi dukkan fafutukar karatun da duk da yayi sana'a kala -kala wajen rike kansa da ma dawainiyar karatun, Proffessor Ibrahim din bai fasa taimaka masa ba lokaci bayan lokaci, don har yanzu yana da tarin envelope ɗin da yake aiko masa dashi dauke da kudi da rubutun 'Dont waste it!' ɓaro-ɓaro a jiki.

Shekaru goma da ɗoriya bai taba cewa komai ba, bai taba nuna ma yana kallonsa da wannan abin ba har ya gama yawon bin garuruwa yana aiki a asibitoci mabanbanta a matsayin kwararren likitan tiyata mai lasisi kafin daga baya ya dawo nan Kadunan kuma ya kawo kansa asibitinsa da zummar neman aikin, aikin da ya dauke shi kai tsaye ba tare da ya ko kalli takardunsa ba.

Sai kawai yayi karfin halin saita tunaninsa sannan ya juyo ya kalle shi.

Professor Ibrahim ya gyaɗa kansa shima yana kallon sa.

"This is me collecting on that old debt Aliyu, lokaci ya yi."

Lokaci yayi!

A cikin kan Aliyu, sai yaji kamar wannan kalmar ba iya ma'anarta kenan ba.

*

Allah yasa dai kun rike sunan program din nan...😅

Don shi zai zama silar duk wani danshi-danshi da labarin nan zai yayyafa a zuciyarku...

Cox you’re not walking into a story… you’re stepping into a heartbeat!

*lnsha'Allah!*

*Aysha shafiee.*

*©Rai Na!*