Chapter 2
Aliyu! Sunan character ɗin littafin nan yazo ne daga sunan marigayi Aliyu Abdu Gusau, ɗan uwa ga Aisha Abdu Gusau. Ku taya ni addu'ar Allah ya jikansa ya gafarta masa tare da dukkanin makusantan da muka rasa a rayuwarmu. Ameen.
~ * * ~
I have learned not to expect too much from life. Still, somewhere inside me, I carry a quiet hope... that life holds another kind of happiness. One that feels whole. Not something I must earn or borrow… but something I can softly call mine.- Safina.
No. 24, Gidan Sarkin Ruwa Street, Unguwar Rimi, Kaduna State.
09:15pm
Walkiya ta haska baƙin duhun dake sama, hadarin dake haɗuwa ya shiga ruri alamun shirinsa na zubowa, wata iska mai sanyi ta shiga busowa, tana kaɗa duk wani abu da bai fi gejin ƙarfin ta ba... Abubuwan da a cikin lissafinsu ya haɗa har da mayafin Safina da ta nade kanta dashi zaune akan sallaya bayan tayi sallama a sallar da ta yi.
Daga inda take zaune, tana fuskantar katuwar tagar dakin ne inda sassayar iskar dake shigowa ke daga labulen jikinta a hankali tana wasa dashi.
Idanunta a rufe suke kwayar cikinsu na motsawa a duhun da take gani yayin da dogwayen hannunta ke mike a gaban fuskarta cikin rokon ubangijin da ta rike a matsayin gatanta, zuciyarta a bude take wajen kwararo dukkan buƙatunta ga jalla wata'ala.
Sassanyar iskar ta sake tahowa ta sauka akan fatarta taji yadda sanyinta ya ce ta cikin hijabin da take sanye dashi ya ratsa fatarta, lokacin da ta kai ƙarshe a ddu'oin nata ta shafa, sannan ta bude idanunta a hankali, yanayin hasken ɗakin da bata kumna fitila ba sai hasken fitilar falo da waje dake shigowa ya washe a idanunta. Ta kai karshe a addu'ar, ta shafa siraran yatsunta akan fuskarta sannan ta mike a hankali.
Daga inda take zaune, hawa bene na farko a gidan, kuma can cikin dakin Gwaggo tana iya jiyo hayaniyar dake tasowa a can kasan gidan inda ke cike da hada-hada cikin aikin tarar idin ƙaramar sallah a washegarin gobe... Daren wannan ranar shine cikar kwanaki talatin cif na watan ramadanan da aka shafe ana azumtarsa, don haka ba iya gidan nasu kadai na, garin gabadaya a tsaye yake cike da hada-hadar shirye-shiryen Sallar ta yadda baka ko iya gane nisan dare ma, a dazu da ta raka Iya Nana suka fita siyayya, kusan koina a garin hada-hadar yankan kaji ake da kuma siyar dasu, kasuwar kayan miyan da suka je kuwa babu masaka tsinke, duk inda ka juya mutane ne ke ta faman ciniki.
Gashi tun safe an tashi da sa'ar barin wutar da Nepa suka yi don haka koina tar yake da haske, haka ta dinga kallon yadda masu kantina ke baje kolin cin kasuwarsu da yadda mutane suka rude wajen yin siyayya tunda kusan kowa ya riga ya sakankance cewar azumi talatin za'ayi sallar sai jibi, don haka ba-zatan ganin watan ya sake ruɗa kowa, go-slow kuwa ba'a maganarsa akan hanya don tun yamma da suka gama siyayyar nan basu suka samu suka dawo gidan ba sai dab da sallar Isha'i, a haka ma wai Baba Alhaji (driver) ya yi mutukar kokari wajen biyowa ta cikin lungunan unguwanni sun bar kan titi.
Don haka bayan sun dawo din gidan ya sake rikicewa da aiki, kasancewar akwai abubuwa da yawa da ba'ayi ba na girke-girken da aka saba kowacc shekara a ranar idin da ahalin gidan ke taruwa ƙwansu da kwarkwatarsu bakiɗaya.
Don haka kowa a gidan ta kokarin ganim ganin an kammala abinda za'a iya a daren ne tunda jerin abincikan da ake yi yawa ne dasu ba kadan ba, hatta ƴan tsofaffin matan gidan kuwa Gwaggo da Hajiya Umma da ba ruwansu da sabgar abincin gidan yau su ma suna ƙasan ana yi dasu, ana yi ana hira cikin raha da jin dadi don kusan duka jikokin gidan tuni sun hallara tun da yamma, maza ne manya kawai babu da kuma su Kawu tare da matayensu (sirikan gidan)shi yasa a dazu ma sallar isha kawai ta samu tayi ta koma wajen aikin, sai a yanzu sannan ta sami sararin dawowa ta gabatar da nafilarta.
Dogwayen yatsunta suka ninke sallayar da tayi sallar akai cikin ninki hudu, ta cire mayafinta ta ninke shi shima sannan ta dauke su ta mayar dasu can saman bedside drawer dake dakin.
A daidai lokacin Ukthi ta shigo dakin dauke da wata katuwar fanteka cike da soyayyen naman kaza, ta juyo ta kalli kanwar tata daga inda take tsaye.
"Gwaggo tace ki ɗora mata wannan a saman wardrobe saboda su Hisham anan dakin zasu kwana."
Wani dan karamin murmushi ya sauka akan lebbenta sanin irin fadan dake tsakanin Gwaggon da jikokinta, musamman a irin wannan lokacin da suke kafa mata ƙahon zukar tsokana, duk abinda suka san zata yi magana to shi zasu yi.
Ta ƙaraso ta karbi fantekar da siraran hannunta da baza ka ce zai iya rike nauyin kwanon ba.
"To Ukthi ina murfin? Haka za'a ajiye?"
"Aunty Hajar ce fa ta yanka albasa akai, kuma tana ji sanda Gwaggo take cewa a zuba mata naman a ciki, yanzu in ta kwashe ma sai ta sani ƙara wankewa..."
"Ukthi..."
Bata bari ta kai karshen maganar ba ta katse ta, ta hanyar zare idonta kadan.
"Idan kin sake wankewa mene a ciki? Ba na hana ki irin wannan maganar akan Aunty Hajar bane?"
Ukthi ta dan bata ranta sanin cewar duk abinda zata fada akan Aunty Hajar ɗin dama yayar tata ba biye mata zata yi ba, a cikin kanta ta rasa wane irin rubutu aka wanke aka bata ne na yadda bata taba ganin laifin mutane a idonta, ko meye mutum zai yi sai ta nemo hanyar da zata yi masa uzuri ta ƙi ganin laifinsa.
"Koma ƙasan, idan ta gama ki karba ki wanke sai kizo ki rufe."
"Toh."
Ta amsa sannan ta juya ta fita daga dakin. Safina ta juya itama, ta taka gadon ta dora fantekar akai sannan ta sauko itama tana nufi can kasan.
Tana sauka kuwa a cikin tarin jama'ar dake wajen nan idon Aunty Hajar ya sauka akanta.
"Ina kika tafi tun dazu Safina? Ga ƴanuwanki nan suna ta faman yanka alaiyahun can da yaƙi karewa."
Ta fada tana nuna can gefe wajen da ƴaƴan Maama ke tsinkar alaiyahun kamar ba zasu yi ba suna hirarsu.
"Sallah nayi Aunty, bari naje mu karasa."
Ta fada tana wucewa ta gaban Aunty Hajiyayye dake zaune akan karamar kujera tana bawa ɗanta Na'im non, a kusa da ita tabarmar da Gwaggo da Hajiya Umma ke kai ce suna bare agushi cikin hirarsu.
Aunty Hajiyayye ta bi Safinan da kallo sannan ta juyo ta sake kallon Aunty Hajar tace.
"Wai ina Rashida ne? Ni tun dazu ban ganta ba."
Rai a bace Aunty Hajar ta kalle ta tace.
"Ta tafi daki, kanta ne yake ciwo. Ko a taso miki ita ne?
Ta karshe maganar cikin gatse.
Aunty Hajiyayye ta girgiza kanta.
"Ni a wa? A taso min Rashida sarauniyar mata? Ta sha zamanta Allah ya sawwake."
Ran Aunty Hajar a ɓace ta furta 'Amin' sannan ta cigaba da juye naman.
Daga can inda Safina ta sami kujera kusa dasu Ni'imah, tana jin su Aunty Hajiyayyen, kuma kamar yadda Aunty Hajar ta gaya mata magana haka itama ta mayar mata da magana itama, sai kawai tayi wani guntun murmushi tana cigaba da aikinta.
Itama Aunty Hajiyayyen don ba a gidan take bane, amma su yanzu duk sun saba da halin Rashidan ai, babu wani abu da zaka ga tana sa hannunta ayi da ita a cikin gidan, kullum tana daki ne taba danne-danne a waya ko kuma ta tafi bikin wata kawarta, balle yanzu da a cikin samarinta ta sami wani dake ɗan kashe mata kudi, shikenan halin nata ya kara tabarbarewa, ya zamana dan tsawatarwa ma da Aunty Hajar din ke mata ta daina.
A hankali idanunta suka juyo, ta kalli yadda Aunty Hajar din ta kai naman gabansu Gwaggo tana faman bayanin da da gani ba gamsar da Iya Nanan dake tsaye a bayansu yake ba, sai kuma can gaba inda sauran ma'aikatan gidan ke fama da manyan-manyan tukwanen kayan miyan da akayi markadensa, da kuma sauran ayyukan su masa da sinasir da kayan fried rice din duk da ake shirin yi a safiyar gobe, ga yan kananun yaran suna ta wasanninsu a tsakanin ayyukan da ake yi, Kawu Muhammadu yana daga saman wajen tanki shi da wani mai gyara suna duba dalilin da yasa ruwa yaki hawa tun da yamma, ta hango Ukthi ma ta karbi Naim tana goya shi.
Kamar kullum, kamar koyaushe a tsayin shekaru goma sha hudu, wani abu ya murda a cikin zuciyarta, ba sabon abu bane, ta san shi tun da dadewa, ta san shi tun daga ranar da ta yiwa mahaifiyarta kallo na karshe a duniya da kuma ranar da ta yiwa Gwaggo kallon farko a rayuwarta.
Yana tare da ita a kullum kuma kodayaushe, amma duk tsawon shekaru da daɗewar lokaci bai rage nauyinsa ko kadan a cikin zuciyarta ba, duk sanda ya motsa tana jin kamar a sannan ne ya dira a cikin zuciyar tata da tarin lissafin kalubalen dake bibiyar rayuwarsu ita da ƴaruwarta, ƙalubalen da ba wai rana tsaka suka tsince shi ba, wani abu ke dake bibiyarsu tun daga lokacin da kowaccensu ta shaƙi numfashi na farko a duniya har zuwa yanzu da suke rayuwa tare da iyalan gidan Alhaji Dan Isa.
Alhaji Ɗan isa wani babban mutum ne da ya kasance hamshakin mai kudi a lokacin da yake raye, yana daga cikin mutanen da Allah ya arawa dama na samun wadatar arziki da ma suna da daukaka a tsawon rayuwarsa kafin Allah ya karbi ransa, inda ya bar iyalansa mata biyu da kuma yara takwas.
Uwargidansa da ake kira da Gwaggo tana da yara biyar hudu maza da mace guda daya yayin da ta biyun da kowa yake kira da Hajiya Umma yaranta uku ne kawai, biyu mata da kuma namiji wanda shine karaminsu.
A yanzu da babu ransa manyan ƴaƴan uwargidan tasa Gwaggo wato Kawu Abdullahi, Kawu Salisu da kuma Kawu Rabi'u su suke rike da duk wata dawainiya ta gidan, wani abu kenan da ya zama mafarin haddasa rashin jituwa a tsakaninsu daga bangaren Hajiya Umma, don nata ƴaƴan mata Bilkisu da Hajar kullum cikin zugata suke da cewar ana yi musu mulkin mallaka a gidan saboda su mata ne kuma danuwansu Muhammadu karami ne a cikin mazan gidan tunda har a yanzu ko aure baiyi ba.
Kullum cikin kananan maganganu suke cewar su basu da ƴanci a gidan tunda bayan an raba gado, gidan gabadaya ya fada hannun ya'yan Gwaggo ne amma Gwaggon da kanta tace su cigaba da zamansu tare ba inda zasu je, don haka sai suke ganin kamar ana musu kallon suna zaman yan karo ne a gidan tunda su kusan sun cinye nasu kason gadon ma.
Bilkisu da ake kira da Maama itace babbar ƴar Hajiya Umman, tana aure ne nesa kadan da gidan nasu don da kafa ma ake zuwa gidan nata, yayanta biyar, namiji guda daya Aminu sai mata hudu Ni'imah, da Aisha, sai ƴan biyunta Mami da Nana. Daga Mama sai Aunty Hajar wadda ita yarta guda daya ce Rashida wadda take sa'ar Safina, aurenta ya mutu tun da dadewa don haka a gidan take zaune tare da yar tata, sai kuma Muhammadu wanda shi ya gama karatu har ma ya fara aiki amma baiyi aure ba har yanzu.
Gwaggo kuwa ƴaƴanta manyan hudu duka maza ne, Kawu Abdullahi wanda kowa ke kira da Kawu Babba yana da mata daya da yara hudu, maza biyu mata biyu Muktar da Haruna (dukkansu sunyi aure), sai Amina (itama tayi sure) Sannan Sadiya wadda itace Sa'ar du Rukayya da Safina itama bata yi aure ba.
Kawu Salisu da ake kira da Kawun Abuja, shine na biyu kuma shi a can abuja yake da mata daya da yaransa uku, mata biyu Sahla da Sultana da kusan dukkanninsu sa'annin Ukthi ne ƴan secondary sai namiji karami Ahmad da bai fi shekara bakwai ba, yana da kudi sosai don a cikin duka ƴaƴan Gwaggon yafi kowa samu kuma matarsa ma daginta masu kudi ne, don haka in ba lokacin sallah irin wannan ba ba ganinsu ake ba, sai ma shi lokaci-lokaci zai zo ya gaida Gwaggon. Ƴan gayun ne na gaske shi da iyalinsa da suke taƙama da gayunsu.
Daga shi sai Kawu Rabi'u wanda shi anan cikin gidan yake zaune da iyalansa, bayan rasuwar mahaifinsu Alhaji ɗan Isan ne ya dawo nan bangaren mahaifin nasa da matarsa Aunty Iya da kuma yayansa su uku, Fatima, Auwal da Salim, saboda a sami wani namiji babba da zai rike gidan.
Bayan su sai Sulaiman wanda shine sa'an ɗan Hajiya Umma na ƙarshe wato Muhammad, ma'aikacin banki ne yana da aure da matarsa da yara biyu ƙanana duka maza Hisham da Hameed, sai autar Gwaggo Aisha ta da ake kira da Hajiyayye, ita shekarunta basu da yawa sosai don a lokacin da Gwaggon ta haife ta ma kowa ya cire mata rai da samun haihuwa, don haka bata dade da aure ba tana da yaro daya Naim.
Wadannan sune iyalan gidan Alhaji dan Isa, gida mai mutukar mutunci da kuma daraja tun a zamanin rayuwar Alhaji dan Isan har i-zuwa yanzu bayan rasuwarsa, kuma a haka Safina da Ukthi suka shigo cikinsu da tasu rayuwar mai cike da giɓi kala-kala.
Tarihinsu ya fara ne shekaru arba'in da biyar da suka wuce baya, a lokacin da Gwaggo take goyon danta na uku Rabi'u, lokacin da Alhaji Dan isa ke kan ganiyar kudinsa kuma itace kadai matarsa, akwai wata ƴar matashiyar yarinya dake taya ta aikace-aikacen gida da kuma kula da yara mai suna Rabi'a.
Asalin Rabia ƴar karamar hukumar Gaya ce, marainiya ce da take zaune a hannun kanin mahaifinta wanda shi kadai ta sani a dangin mahaifin nata, mahaifiyarta kuma bata da wasu dangi na kusa masu yawa sai yan'uwa na nesa kawai.
Bayan rasuwar ƙanin mahaifin nata ne shima sai aka raba gado kowa a cikin yayansa ya kama gabansa kasancewar dama shi mutum ne mai aure-aure, don haka matarsa ta gidan wadda take da kananan ya'ya ta koma gidan iyayenta itama, tun daga nan sai rayuwar Rabi'ar ta shiga watangaririya har a gidajen makota ta koma zama kafin da kyar a samu wani danuwan mahaifiyarta da take kira Kawu Bala ya dauke ta.
Kasancewar shima Kawu Balan talaka ne mai karamin karfi bai ko yi shawara ta biyu ba ya turo ta aikatau kamar yadda yake tura ƴaƴansa suma, kuma gida na farko da ta fara tsintar kanta shine wajen Gwaggo.
Rabi'a yarinya ce mai hankali nutsuwa da kuma tsananin tsafta, wadannan su suka kara akan kyawun da take dashi ta yadda ba zaka taba kallonta kace yar aiki ce ba, sannan tsananin biyayyarta da sanyin halinta shi ya siye zuciyar Gwaggo da ma mijinta tun a lokacin suka maida ita kamar ƴarsu, ta zama itama wani ɓangare na gidan, ƴanuwa da abokan arziki kowa ya santa, yaransu sun dauke ta kamar ƴaruwarsu sannan duk wani bakin ciki da farin ciki na rayuwar gidan tare ake rabawa da ita.
Su Gwaggon ne suka sanyata tayi karatu a kowanne bangaren boko da islamiyya, sai dai a yadda suka so ta cigaba da karatu kamar nasu yaran hakan bai yiwu ba don tun kafin ta gama sakandire masu neman aure ke bibiyarta hatta Alhaji Dan isan ba'a barshi ya huta ba, wasu ma har can ƙauyen da Kawun Balan yake suke zuwa da alkhairinsa, don haka bayan yazo ya kafe kan cewar dole aure zaiyi mata, su Gwaggo basu da wani zabi illa ba shi hakuri aka samu ta gama sakandirinta a daddafe tunda dama shekarunta sun haura ashirin a wancan lokacin.
A haka bata da zabi Kawu Balan ya zabi wani wanda sikelin alkhairinsa yafi yawa a wajensa mai suna Sadiq Kallah ya aura mata shi, kuma bayan auren ya tafi da ita can garinsu Kebbi.
A can ta haife su su biyu ita da Ukthi, kuma Ukthi na da shekara biyu a duniya ne Allah ya yi mata rasuwa, rasuwar tata da tazo da tarin ƙalubalen da suka sa karfi da yaji su Gwaggon suka karɓe su suka dawo dasu hannunsu tunda a lokacin shima Kawu Balan ya kwanta dama, ya zama babu wani danuwa kwakkwara da zai rike su.
Akwai shakuwa mai karfi tsakaninta da ƴaruwarta Maryam da ake kira da Ukthi duk da banbancin shekarun dake tsakaninsu har guda bakwai, sunan bata kuma na Ukthi ya samo asali ne daga wajenta, don tana tunawa tun a ranar da a ka haife ta da mahaifiyarsu ta miƙo mata ita ta ɗora ta akan hannayenta, ta kalle ta furta mata sunan 'Ukthi' ma'ana 'ƴaruwa' shikenan sunan ya bita kuma har sanda rayuwarsu tayi juyin waina ta dawo dasu hannun Gwaggo, sunan bai canja ba, Maryam ya ɓuya, Ukthi kuma ya zauna a bakin kowa.
Duk wanda ya san mahaifiyarta a baya kuma ya kalle ta a yanzu, zai ce ita ɗin tamkar mudubin mahaifiyar ta ce, don komai nasu iri daya ne sak babu banbanci, hatta kalar fatar ta wadda take ba fara ba amma mai wani irin hasken dake kara fito da kyakkyawar halitarta tun daga kan fuska har zuwa dirin jikinta, ko wani abun ta yi, Gwaggo zata gyada kai ta ambato sunan Rabi'a tare da addu'ar rahama a gare ta, don zata ce ta tuna mata da ita be, ta tuna mata da Rabi'atun ta.
Gwaggo tana mutukar son su, musamman ma ita don ta sha gaya mata idan ta kalle ta sai ta ga kamar Rabi'ar da ta rasa a baya ce ta dawo, don zata rantse tun daga lokacin da shi yasa tun daga ranar da ƙafafunsu suka tako cikin gidan, Gwaggo bata taba wani abu da zai ɓata ransu ba.
A wancan lokacin, Ukthi tana da shekaru biyu ne kawai yayin da ita kuma take shekara tara, don haka kusan dukkan rayuwar karatunsu anan gidan suka yi shi har zuwa yanzun da Ukthi ke matakin aji uku a sakandire ita kuma ta kammala karatun zama Nurse a wata private makaranta ta koyon aikin Nursing ɗin.
Su Kawu Babba sun so University ma tayi, to amma sai aka sami matsala har sau biyu wajen samun admission ɗinta, a shekara ta biyun ne kawai aka samo mata wata private school of Nursing din mai kyau tunda lokaci yana ta tafiya tana zaune a gida.
Kuma tun da ta shiga makarantar har ta kammala bata taba samin wata matsala ba, don bayan sanin da kowa ya yi na cewar tana da kokari, ita kanta ta san tana da ganewa shi yasa ma tun farko hankalinta yafi karkata ga yin karatun da ya shafi ɓangaren lafiya.
A yanzu bayan ta gama din ne ta samu wani aiki kamar na voluntary a wani asibiti nan kusa dasu, don duk wata dubu ashirin suke bata, amma tana mutukar jin dadin kudin don duk da babu wani abu da take nema ta rasa, kuɗin yana kashe mata wasu ƴan buƙatun ta da na ƙanwarta.
Don haka daga ita har ƴaruwarta hankalinsu a kwance yake sosai yanzu, tarin giɓin da suka zo dashi ya cike gabadaya da irin karamci da kuma kyautatawar da suka samu tare da iyalan gidan Alhaji Dan Isa, gida mai mutukar mutunci da kuma daraja tun a zamanin rayuwar Alhaji dan Isan har i-zuwa yanzu bayan rasuwarsa, don ba iya yanuwa kadai ba hatta jama'ar unguwa kowa yana danganta kalmar mutunci da daraja wa duk wani ahalin gidan saboda tarbiyya ilimi da kuma nutsuwarsu tana fita daban a duk inda suka shiga.
Sai a yanzu da karfi da yaji su Aunty Hajar ƴaƴan Gwaggon ke son ɓullo da wata ɓarakar a tsakaninsu, kusan ma za'ace Aunty Hajar ɗin itace ja gaba wajen tada duk wata husuma ta gidan, tun kafin tayi aure kowa ya san halinta na son abin duniya da baƙin rai wajen tsanar duk wanda zuciyarta bata amince dashi ba, shi yasa tunda ta dawo gidan ta zama umul-abasin zuga mahaifiyarta Hajiya Umma kan cewar ba'a darajarsu a gidan hatta ƴaƴan bare wato su Safinan sun fi su muhimmanci a gidan don kowa na kaunarsu kuma Gwaggo bata taba ganin lafinsu.
Ɗaɗin daɗawa kuma dama ita mijinta wani ɗan duniya ne da har yanzu suna rigima a kotu kan cewar ta cinye masa kudinsa kafin rabuwar aurensu, ita kuma ta rantse cewar bata san da hakan ba hasalima karayar arzikinsa ce tasa ta rabu dashi.
Kuma duk da kowa ya san halinta da kuma irin abubuwan da take yi kawai ana kawar da kai ne bisa shawarar Kawu Babba da cewar shi baya son duk wani abu da zai ta da husuma tsakaninsu don mahaifinsu da zai bar duniya shi ya barwa amanarsu bakidayansu, don haka iyaka idan tayi abinda dole sai anyi magana sai shi ya kirata da kansa yayi mata fada wanda baya wani tasiri akanta.
Gidan Alhaji dan Isa gida ne irin na masu kudin da, ƙato ne kuma babba mai dauke wajaje da yawa, ɓangare-ɓangare, da farin fenti mai maiko wanda ba'a taba canja shi a duk lokacin da za'a sake shafawa.
Gida ne wanda ko daga nesa zaka shaida kyau da kuma ingancin gininsa wanda ya banbanta da irin na yanzu, gini ne mai yalwa da kuma fadi wanda tun a wancan zamanin aka kashe kudi wajen yin sa.
Idan ka shigo daga gate din katuwar haraba ce mai girma a tsakiya, daga bangaren hagu gida ne guda mai girma wanda shine bangaren Alhaji dan Isa a lokacin da yake raye, a yanzu kuma ya koma bangaren Kawu Rabiu da shi da iyalansa, sai daga bangaren dama shine ginin cikin gidan mai hawa biyu, akwai katon tsakargida a kasan wanda aka malale shi da tarazo da kuma kitchen kala biyu na dahuwar itace da kuma na ajiye kwanuka da girkin gas, sai dakunan masu aiki duk a kasan.
Hawa na farko shine bangaren matan gidan Gwaggo Hajiya Umma, dakunansu da suka hada da manyan falo da kuma dakuna biyu da bandaki a ciki suna kallon juna sai zagayayyiyar barandar data raba su wadda ake hango kasa idan an leka.
Su Kawu Babba ba irin shawarar da basu bayar ba kan cewar a canja tsarin gidan su Gwaggon su dawo kasa saboda tsufa da kuma kafa amma kowacce daga cikinsu ta kafe akan cewar sun fi son dakunansu haka ba inda zasu.
Hawa na biyu wannan dakunan ya'yan gidan ne da kuma na baki ko ajiyar kaya haka, wanda yawanci yanzu ma ba'a fiya amfani dasu ba a kulle suke kawai.
Don ko Aunty Hajar da yarta duk a dakin Hajiya umman suke rayuwa tunda dakuna biyu ne a cikin falon, kamar yadda Safina da Ukthi dake zaune tare da Gwaggo suma suke dakinta, ba bukatar wani ya hau sama ya bude dakinsa daban. Kusan ma a yanzu cikin dakunan saman duk kayan ɗakin Aunty Hajar ɗin ne wanda ta loda su ana ta rigimar ta siyar a sami waje ko don sha'anin biki amma ta ki.
~ * * ~
Sometimes, your whole life stays quiet, until one moment whispers, and you're standing in a story you never saw coming...- Safina.
Ƙarfe tara daidai na safiyar ranar idin ƙaramar sallah, a wannan lokacin ɗaukacin gidan Alhaji Dan isa ya ɗinke da tarin zuri'ar gidan baki daya ƙwansu da kwarkwatarsu, tun daga kan ƴaya har ma da jikoki.
A ɓangaren Kawu Rabi'u, ɓangaren da yake wajen AlhajinDan isan kafin rasuwarsa, akwai ƙaton falon da yake karbar baƙinsa, kuma shine inda yake tara dukkan yayan nasa idan har zaiyi wata magana, a shekarun da suka biyo bayan rasuwarsa, wajen a rufe yake, ba'a ko bude shi kayan ajiya kawai ake jera masa.
Shekaru biyu baya duk sanda za'ayi irin wannan taron na sallah, sai Aunty Hajar da yayarta Maama suka fara cece-kucen cewa su kawai ana ware su gefe ne amma babu su a cikin taron don wai su Kawu da yayansu gabadaya tarewa suke a bangaren Gwaggo da sun shigo sun gaida Hajiya Umma shikenan ba wanda zai sake waiwaiyarsu sai iya su da nasu yaran, magana ce da suka so su tada hayaniya da ita amma sai Kawu Babba ya basu goyon baya da cewar suna da gaskiya don haka a bude wannan falon ya zamana ana taruwa a can gabadaya.
Tunda dama su daga masallaci ne suke zartowa nan gabadayan su idan suka zo suka gaida su Gwaggon suka ci sbinci kowa harkarsa yake tafiya sai a bar yara kuma suyi ta zagayensu.
Don haka a yau ma kamar kodayaushe bayan dawowar sallar idin wannan falon a dinke yake da al'ummar gidan, an shimfide shi tsaf da tausasan darduman da irin na wannan lokacin ne dama, Gwaggo da Hajiya Umma zaka fara hangowa idan ka shigo, suna zaune cikin ankon sabuwar atamfar su iri daya kamar kowacce shekara yayin da ƴan jikokinsu har ma da yayan jikoki sun zagaye su Auwal da Salim (ƴaƴan Kawu Rabi'u) suna ta ɗaukarsu hotuna a wayoyi, Ukhti ce mai alhakin gyara su da tsara su cikin layi.
Daga can gefe guda kuma su Kawu Babba ne su uku suna tattauna zantukan da suka shafe su, musamman a yanzu da suka hadu har da Kawun Abujan da ba kasafai aka cika ganinsa ba, su biyu dai da suke gari daya Kawu Rabi'u da Kawu Babba sun fi haduwa a kodayaushe, don yawanci juma'a-juma ma Kawu Babban kan shigo ya gaida su Gwaggo.
Kawu Sulaiman da yake karaminsu yana daga waje shi kadai yana waya don tunda yazo yake bada uzurin cewa aiki ne dashi don ma ba zai iya ƙin zuwa bane gabadaya. Muhammad ɗan autan Hajiya Umma, yana tare da Mukhtar da Haruna (manyan ƴaƴan Kawu Babba) suna hira kasancewar ma'aikatarsu guda a inda suke aiki.
Ni'imah da Aisha ƴaƴan Mama suna tare da Rashida suna nasu hotunan su ma ba tare da sun tafi can kitchen inda ake hada-hadar zubo abinci ba, yayin da ƙannensu ƴan biyu Mami da Nana ke zaune a gefensu sun ƙi zuwa wajen ƴaƴan Kawun Abuja Sultana da Sahla dake hirarsu tare da Fatima (ƴar Kawu Rabi'u) da suke sa'anni daya, sai kallonsu kawai suke suna ƴan kananun maganganu a tsakaninsu kamar yadda iyayensu suka koya musu.
Matan Muktar da Haruna (yayan Kawu Babba) suna tare da Amina (yar kawu Babban) da kuma matar Sulaiman suna nasu hirarrkin su ma irin na sirikai.
Manyan sirikan kuma, matar Kawu Babba, matar kawu Rabi'u da matar Kawun Abuja suma suna zaune a wajensu ana hirar yaushe gamo.
Idan ka baro nan ka taho bangaren cikin gidan, inda ake ta faman hada-hadar abinciccikan da za'a ci, bayan Iya Nana da sauran ma'aikatan dake ƙarƙashinta, akwai Aunty Hajiyayye, wadda kusan itace ke ta faman faɗin yadda za'ayi da komai tana goye da danta Na'im a baya, sai kuma Aunty Hajar da Maama, wanda kusan duk iya na bangarensu kawai suke warewa suna yi suna fadin a kara yawan komai.
Iya Nana ta dauki wani flask dake cike da sinasir fari tas! Sai ƙamshi yake, tayi baya can wani gefe na kitchen din, inda Safina ke tare dasu Atu da kuma Safiya (ƴar autan kawu Babba da take sa'arta) suna shirya abincin su Kawun.
"Uwata ai sai yanzu na lura ba'a saka sinasir ɗin anan ba."
A lokaci guda Safina ta dago ta kalle ta, idanunta a zane suke radau da baƙin kwallin da ya kara foto da farimsu da kuma kyawunsu, kuma bayan kwallin babu komai a fuskar ta sai man lebben da ta saka a saman bakinta mai kyalli, amma idan ka kalli fuskar tata zaka ce ta shafe lokaci ne tana kwalliya sakamakon yadda fuskar tayi raɗau! Da ita, kayan jikinta wata doguwar riga ce mai budewar umbrella daga kasa sosai kalar lemon green light sosai da kuma silver.
Daurin dankwalin kanta yayi crossing bangare biyu daga tsakiya wanda hakan ya fito da duhun bakin gashinta ta gaba, sai ta yafa wani dan karamin mayafi silver ta gaban rigar, hannayensa biyu suka sauka ta baya a gefen kowanne hannunta, sai ta sa wasu kananun pills a saman kafadunta duka biyun ta matse shi yadda ko da ta sunkuya ba zai fadi ba saboda aiki.
Idan ka kalli kowa a gidan zaka ga cewar yayi adon Sallah ne da irin nasa kyan kayan, amma idan ka kalli Safina zaka kalle ta ne ka kara da irin simple kyan da tayi babu wata hayaniyar kwalliyar a tattare da ita.
Bakinta ya tale da murmushi da ya kara fito da yadda ɗan ƙaramin lebbenta ya yi kyau da lip balm din da ta shafa tana kallon Iya Nanan tace
"An zuba fa Iya Nana, tun dazu na ɗiba na zuba a wancan flask din, ai nan an gama komai, kawai zuba sugar nan zanyi mu dauka yanzu mu kai."
Cikin jin dadi Iya Nana tace.
"Kai Alhmdlilahi, sannu da kokari Uwata, yau ba don ke ba ai da rikicewar ta min yawa, yanzu bari ki ga inje inji da zuba tuwon su Gwaggo kuma..."
Da haka ta juya da flask din sinasir din a hannunta.
Safina tasa dogwayen yatsunta ta bude gwagwanin sukarin da kyar, ta zuba shi a wani dan tangaran na gilashi, irin tsofaffin kayan Gwaggo da tace tun na jeran aurenta ne wanda bata taba fito dasu sai Sallah-sallah idan za'a zubawa su Baffa a ciki.
Ta juye sukarin da dan yawa a ciki sannan ita da Safiyya da Atun suka shiga dauka suna tafiya can falon inda zasu kaiwa su Baffan.
Da yake Safina ce daga ƙarshe saboda tana tafiya ne a hankali don kar budaddiyar rigar tata da ta baje a ƙasa ta ta, idonta na hango mata su Aunty Hajar da ga can gaba shaƙe da nasu farantin abincincike taf da abinda ko a ido yafi karfin cikinsu, haka suke yi duk sallah, sai sun debi abinci fiye da cikinsu wani lokacin ma har su boye wasu a daki da uzurin zasu yi baƙi, su hana wanda ake rabawa mutane ya isa, sai washegari da safe yawanci su fito dashi ya lalace.
Suna dab da shiga falon idonta ya hango Aminu, babban ɗan gidan Maama dake tsaye a gefe yana danna wayarsa, daga can inda yake ya kadhe mata ido ɗaya tare da yin wani murmushi da tajinkamar amai zai taso mata, bata san lokacin da tayi wani siririn tsaki ba ta juyar da kanta, wai a haka ma ta sami sauki dashi kenan, a baya idan akwai abinda bata so shine ta ganshi yazo gidan, don ya dinga bibiyarta kenan da magana yana neman ta kula shi karfi da yaji.
Tun wata rana da Maaman ta ritsa shi a kitchen yana binta yana mata magiyar ta kula shi, da ta rafka salatin da wani zai rantse mutuwa akayi ta kuma jawo rantsuwa ta kara da tabbacin cewa zata tsine masa muddin ta cigaba da ganinsa da ita shikenan ta sami saukinsa, musamman ma da aka ce KawunBabba ya samo masa wani aiki shikenan kowa ya huta ya rage yawon gararambar da yake yi.
Bayan sun sauke farantan a gaban su Kawun da suke ta musu sannu da aiki da sa albarka, ita da Safiyya ne suka zuzzubawa kowa abinda yake so, a lokacin gabadaya falon ya kaure da ƙamshin abinci kala-kala kowa na faman zuba abinda yake so.
Lokacin da ta mikawa Kawun Abuja kofin kunun gyadar da ta zuba masa, a lokacin ne ya miko masa mukullin motarsa da daya hannunsa. Da murmushi fal a fuskarsa yace.
"I've a suprise for you, kar in zo in shiga hayaniyar garin nan in manta... Ki bude cikin mota a drawer jikin dashboard akwai wani brown envelope ki dauka naki ne."
Ta kalle shi, ta kalli su Kawu Babba sai taga su ma duk sunyi murmushin alamun sun san da maganar, musamman ma Kawu Babba da ta san babu wani abu da zai faru da babu saninsa a ciki.
Mamaki ya dan ratsa kanta, don ta san banu wani abu sosai dake hada ta da Kawun Abujan banda gaisuwar juma'ar da take turawa wasu jerin mutane ciki har dashi, ko kuma idan an ɗan kwana biyu sosai ta kira ta gaishe shi. Don haka, haka kurum sai taji gabanta ya fadi, wani abu mai nauyi ya fada can ƙasan ƙirjinta da nisa, amma sai tayi saurin gyada kanta kawai sannan ta amsa.
"To Kawu madallah."
Ta fadi hakan sannan ta mike, kuma duk da taji lokacin da Aunty Hajiyayye ke bata sakon ta dauko flask din wata miya daga cikin gidan, haka kurum sai bata kula ba, kai tsaye ta mufi parking space inda kowa ya ajiye motocinsa, bata taba maida hankali ta san motar Kawun Abujan ba ma, don kwata-kwata sanin motoci ba a cikin lissafinta yake ba, don haka sai da ta tambayi Baba Alhaji da ta hango shi suna cin nasu abincin shi da wasu mutane a gefe sannan ya nuna mata motar.
Kuma bata san ma zata iya bude kofar ba sai da taga ta sa mukullin kuma ta bude din, da yake ta wajen mazaunin driver ta bude sai ta shiga ta zauna sannan ta mika hannunta ta bude aljihun dashboard din, brown envelope din kuwa yana zaune a ciki kamar ita yake jira, wani abu ya kara nauyi a kirjinta, ta sa siraran yatsunta ta dauko shi sannan ta jawo takardar dake ciki. Wata takarda mai kauri da taji kamar ta cika hannunta ne, kamar ta cika hannunta da alƙawuran tarin abubuwan da take dauke dasu.
Kuma babu wani shamaki, idanunta suka shiga bin duk wani harafi dake rubuce a jiki wadanda suke cikin rubutun dake dauke da kaloli mabanbanta.
Surgical Recovery & Reintegration Initiative (SRRI)
In Partnership with PrimeCare Private Hospital
Plot 8, Sultan Dikko Way, GRA, Kaduna State
*Email: *** | Phone:* 080-123-45678
*Ms. Safina Sadiq Kalla
No. 24, Gidan Sarkin Ruwa Street
Unguwar Rimi, Kaduna State.
Dear Ms. Sadiq Kalla,
LETTER OF APPOINTMENT
We are pleased to inform you that following your nomination and successful screening, you have been selected to serve as a Nurse Secretary under the Surgical Recovery & Reintegration Initiative (SRRI) at PrimeCare Private Hospital.
Your duties will involve both clinical nursing support and administrative coordination, working closely with the SRRI Lead Consultant Surgeon, Dr. Aliyu, and reporting to the Project Coordinator. You are expected to demonstrate professionalism, compassion, and attention to detail, as SRRI is a high-impact program focused on post-operative recovery, patient reintegration, and healthcare innovation.
This appointment is project-based and shall run initially for six (6) months, subject to renewal based on performance and project funding.
Terms of Appointment:
Commencement Date: Monday, 19th May, 2019
Reporting Time: 7:30 AM daily
Location: SRRI Office, PrimeCare Private Hospital
Monthly Stipend: ₦185,000 (One Hundred and Eighty-Five Thousand Naira)
Dress Code: Official nursing scrubs and ID badge (to be issued on Day One)
Probation Period: First 30 days of active duty
Please report to the SRRI Coordinator’s office no later than 7:15 AM on your start date for documentation and induction.
We congratulate you on your appointment and look forward to your meaningful contribution to the success of this initiative.
Warm regards,
Dr. Binta Shehu
Program Coordinator, SRRI
For: Ministry of Health & PrimeCare Private Hospital.
Idanunta suka kai ƙarshe wajen karanta harafan da su ne mafarin abonda zai raba duniyarta zuwa wani tsallake da bata taba hangowa ba, wannan abu dayan shi zai kaita gabar da alkalami ya bushe akan ƙaddararta... Ƙadarar dake hadowa da tarin mutanen da su kansu hasashensu bai taɓa hango wani abu makamancinta ba...
Don tabbas anan gaba idan za'a tambaye ta sanadin faruwar komai, sanadin faruwar tarin abubuwan da bata san adadinsu ba... wannan ranar, wannan lokacin shi zata nuna!
*
I think na gaya muku dama sunan Program din nan zaiyi amfani ko?😊
Now... The story is starting.
Raina!
©Aysha Shafiee.