Chapter 3
Raina!
Aysha Shafiee
03
~ * * ~
The doors you thought were closed might be waiting for the courage you’ve just found.-Safina
"To wai Safina don Yaya ya samo miki aiki meye abin mamaki a ciki? Kin san irin mutanen da ya sani kuwa a Abuja da irin connection din da yake dashi? Ni kaina ba don ina son wajen aikina ba ai da tuni nace ya samo min wani."
Aunty Hajiyayye ta faɗa tana zaune daga kan kujera a cikin falon Gwaggo tana sawa ɗanta Naim da Ukthi tayi masa wanka pampers.
Ƙarfe tara na dare ne lokacin, kuma duk da cewar ranar sallar ce amma kusan gidan ya koma yadda yake, kowa ya tafi, su Kawun Abuja ma duk amma sun ka can gidansu da suke sauka duk lokacin da suka zo.
Aunty Hajiyayyen ce kawai ta rage bata tafi ba zata kwana, itama da uzurin mijinta baya gari yana can Kebbi wajen aikinsa, hutun kwana biyu kawai ya samu ya ga ba zai iya jigilar tahowa har ya koma ba ya bata hakuri kawai ya yi zamansa, sai kuma su Hisham da Hameed ƴaƴan Kawu Sulaiman da tun jajiberan sallar suka zo kuma suka nace anan zasu sake kwana saboda Ukthi mutuniyarsu ce, don haka Kawu Sulaiman din ya barsu da cewar gobe da safe zai zo ya tafi dasu tunda zasu je can gidan kakanin mahaifiyarsu a goben.
Gwaggo tana zaune akan sallayarta inda ta gama lazimin sallar Isha'in da tayi, yayin da Ukhtin ke can bandakin dake cikin daki tare da su Hisham tana musu nasu wankan daren, don dabdalar wasan da suka sha a gidan tun safe bata da iyaka.
Safina tana tsaye daga can jikin wata drawer da aka kafe a kusurwar dakin (corner cabinet) inda suke jera ƴan kayan ajiyarsu, irin su turaren wuta da yan tarkacen magani, ta canja kayanta daga na safe zuwa wata doguwar rigar baccinta mai laushi kalar purple, ta nade gashinta da wani ɗan ƙaramin mayafin Pashimna kalar pink, laushin mayafin ya kwanta da irin yadda ta daure shi a kan nata, a hannunta kaskon turaren wutar ne da ta samo garwashi da ƙyar a cikin tokar murhu, don yau ba'a dora abincin dare ba, tarin abincikan da aka yini ana ci tun safe suna nan har yanzu.
Ta debo turaren wutar ta saka sannan ta juyo ta kalli Aunty Hajiyayye da ta gama bayanin cewa bata yi mamakin takardar aikin da ta yini tana mata yawo akai tun bayan da ta koma wajen su Kawu ta sake neman ƙarin bayani ba, don Allah ya sani bayan ta dauko ta, ta kuma gama karanta dukkan abinda ke ribuce a jiki, ji tayi kawai bata gane ba, ta gane ma'anar dukkan abinda aka rubuta, abinda bata gane ba shine yadda ma'anar ta hade da sunanta dake manne a jikin takardar.
A cikin kanta ta nemi guraben amsa wasu tambayoyin ta kasa, yaushe suka taba maganar neman aiki ita da Kawun Abuja? Babu. Yaushe ya karbi takardunta har akayi screening din da aka ce ta tsallake a cikin takardar? Babu. Aikin na menene a ina ma asibitin yake? Babu. Sannan ita za'a dinga biya har har dubu ɗari da tamanin da biyar a wata? Tashin hankali... Ai bata san lokacin da ta rufe kofar motar ba ta koma wajen su Kawun.
Kuma idanunta kawai ya kalla ya ganta a diririce ya kyalkyale da dariya, kasancewar shi mutum ne mai fara'a sosai dama, ba irin Kawu Rabi'u da zata rantse ko kyallin murmushibbata taba gani ya gifta a fuskarsa ba, kuma ba wai don zaka sa shi a sahun mutanen da basu da kirki ba, kawai haka halittarsa take.
Sai ya shiga mata bayanin cewa abokinsa da yake minister of health na kasa bakidaya shi yake da alhakin kwangilar wannan aikin da za'a gudanar gabadaya a Nigeria, don haka ya bashi sunanta yace a saka ta a ciki tunda akwai asibitoci guda biyu a cikin Kadunan da suka shiga jerin lissafin asibitocin da aka zaba don gudanar da aikin.
Yace shi har ya manta ma don an kusa wata biyar da suka yi maganar a lokacin komai na project din ma bai kammala ba sai a shekaranjiya tukunna yasa aka kawo masa takardar har gida da cewar an kammala komai ga posting din tasa candidate din da ya bayar.
Kuma shikenan iya bayanin da ya yi mata yace duk wani abu da bata gane ba kuma idan taje can asibitin da aka kaita zasu yi mata bayani.
Ta san ta gamsu da duk wannan bayanin, amma abinda ya kasa zama akanta shi ne wannan tarin kudin da aka lissafa a jikin takardar da kuma screening din da aka ce anyi wanda ita bata san komai akansa ba, don haka take hangowa ko ma wane irin aiki ne to za'a iya samun matsala da ita tunda bata san komai ba.
Tun safen kuwa duk wanda ta nunawa sai taya ta murna yake yi da fatan Allah ya sanya alkhairi. Ukthi da ta karbi takardar ta karanta haka ta dinga washe baki cike da farin ciki, da idonta ya kai kan adadin kudin da aka lissafa kuwa ba shiri ta kalle ta tana zare ido, don ita ce babbar shaida yadda ƴar dubu ashirin din da take samu duk wata a inda take aiki take rufa musu asirin ƴan buƙatunsu da ba sai sun tunkari Gwaggo dasu ba... Tare da lissafin Wannan kudin kuwa ta tabbata Ukthi kashe ta zata yi da jerin bukatunta da take taka mata burkinsu, musamman a yanzu da take kan gigin cewa itama ƴanmata ce.
Ta taho saitin Aunty Hajiyayyen tana cewa.
"Ni fa mamakin da nake Aunty na yadda ma suka karbi sunana ne alhali banyi screening ba, kuma na yi searching yanzu naga kusan wata guda akayi ana yiwa wadanda duk aka dauka training din aikin."
Aunty Hajiyayye tana kallonta tace.
"Shi yasa na gaya miki Yaya yana da connections ai, minister fa da kansa yace miki ya bawa sunanki, to wane screening kuma za'a miki?"
Gwaggo daga kan sallayarta ta juyo tace.
"Nan ma fa na gaya mata kwanaki yazo tana wajen aiki yake tambayata ina duk suke nace masa Ukthi ta tafi makaranta ita tana wajen aiki, yake tambayata aikin da take yi na gaya masa har da albashin da suke bata. Ya zauna yana ce min wai kudin ya yi kadan ai kawai bauta take musu ta daina zuwa nace masa aa'a, da babu gwara ba dadi, ba zata zauna a gida bata komai ba, yo ko don wannan ma ai ya san yadda zaiyi ya samo mata wani aikin ba."
"Rabu da ita Gwaggo, dadi ne ya mata yawa taga mu da muka yi shekara da shekaru muna aiki ta kamo kafar mu a albashi."
Ba shiri Safina tayi murmushin da ya kara haska fuskarta, murmushinta da mutane da yawa ke fadin suna son su ga tayi, don wai daban yake da yadda mutane da yawa ke yin nasu, yanayin fuskarta yana tsayawa a tsakiya ne tsakanin wani abu kamar kuka da kuma dariya a lokaci guda, amma kuma kana kallonta ka san cewa murmushin take yi.
"Kai Aunty, Kai Aunty... Ni bance haka ba."
"A'a to gashi nan kina ta maimaita abu tun safe, ni wane turare ne wannan kike ƙonawa dan Allah? Tun jiya da nazo gidan nan nake jin wani sabon ƙanshin da ya kasa fitar min a hanci."
Ta fada tana miko mata Naim din da ta gama saka masa kayan bacci.
Safina ta ajiye kaskon a kasa ta karasa da fara'arta ta karbe shi tana fadin.
"Ni dai duk wanda yaji tuaren nan sai yace ya masa dadi, har Kawu Sulaiman fa sai da yasa na siyo masa don duk sanda ya shigo sai yace me kuka sa a dakin nan haka mai daɗi."
Ukthi da ta fito daga cikin dakin a lokacin su Hisham biye da ita, ta naɗe kowannesu da ɗankwalin kayanta tace.
"Aunty Hajiyayye turaren wutar nan ko? Ai ki bari kawai tunda Hajiya Taata (wata ƙawar Gwaggo; tsohuwa ce da shekarunta basu sa ta daina tsirfa da iyayi ba) da tazo ta rikice akan turaren nan sai da aka ɗebar mata na san to turaren nan duk inda aka kaishi zai wuce."
Gwaggo ta girgiza kanta daga gefe.
"Allah ya shirye ki Ukthi, ni ban san me Hajiya Taata ta tsare miki a duniyar nan ba kika hana ta rawar gaban hantsi."
Aunty Hajiyayye tace
"Ni dai dan Allah ku san min, in baɗe gidana dashi kafin Abban Na'im ya dawo."
Safina ta tafi ta dauko robar tana fadin.
"Ai ya kusa ƙarewa ma don ya sha ɗiba, sai dai a siyo wani kawai."
Aunty Hajiyayye ta karɓi robar ta karanta rubutun dake jiki."
Meens Incense!
*Dollor Halluth*Sai ta dauko wayarta ta kwafi number da ta gani rubuce a kasa, ta mai turaren...
***
"Wai Safinatu kin kaiwa su Hajiya Umma sun ga takardar aikin ma kuwa?"
Gwaggon ta tambaya tana tauna ɗata a bakinta.
Safina ta girgiza kanta yayin da Ukthi dake bade su Hisham da hoda ta ɓata rai a ƙasan numfashinta tace 'Meye amfanin nuna musun...'
Safina ta fahimci abinda tace amma bata kula ta ba ta cigaba da kallon Gwaggo.
"To dauki yanzu ki kai musu tun kafin ma dare ya gama rufawa... Bana son kananun maganganu, su ce ba'a fada musu ba tunda har Iya Nana kin nunawa."
Safina ta goya Na'im a bayanta sannan ta nufi cikin ɗaki, a cikin wardrobe dinta saman kayanta ta jawo brown envelope din nan, sai kawai hannunta ya sake jawo takardar ta shiga sake maimata karatun dake jikinta.
Ta sani rayuwa kamar hawainiya ce...
Hawainiya mai canja kaloli a lokuta mabanbanta...Idan ta raɓi abu mai duhu sai ta disashe. Ko ma ta koma baƙi, ɓaƙiƙƙirin!
Watarana kuma sai ta tunkari abu mai haske, watakila ma kore shar! Sai ya haska ta, zanenta ya fito raɗau a idon duk wanda ya kalle ta.
Abinda bata sani ba a yanzu shi ne, wace irin kala rayuwarta take shirin tunkara?
***
"Na gaya miki ba kudi ne dani ba Rashida don haka ba zan iya baki har dubu talatin kiyi ankon kawa ba, idan zaki je bikin a haka ki wanke kafarki ki tafi tunda ba kaya ne baki dasu ba."
Cewar Aunty Hajar, tana zaune a daya daga cikin kujerun falon nasu yayin da ƴarta Rashidan ke kallonta fuska a hade tana rike da kofin shayin dake tiriri a hannunta.
"Haba Mama kin fa san idan banyi ankon nan fa ba zan zauna a cikin ƙawayena ba, sai dai muyi ta baya-baya, kamar ba gaiyatarka aka yi ba."
Maganar babu ladabi a ciki ko kaɗan ace mahaifiyarta take faɗawa, amma daga Aunty Hajar ɗin har Hajiya Umma dake zaune a gefe tana ɓare bayan adduwarta babu wanda yaga rashin dacewar hakan. Sai ma Hajiyan Umman ce ta kalle ta tace.
"Ni wannan yawon bikin ne ma ya fara isa ta, ke kenan kullum biki? Kina ganin dai Safina daga wajen aikinta sai gidan nan, ni sai in dade banji ance taje wani waje ba."
Rashida ta sake haɗe ranta fiye da kima tana gyada kai.
"Nifa nace ki daina hada ni da yaran nan a gidan nan Dan Allah, wallahi kunne na ko sunansu baya son ji."
Aunty Hajar ta karbe itama nata ran na shirin baci.
"Ai shine Hajiya ita Rashida da take ƴar dangi, banda tarin ƙawayen da take dasu ma, su kuwa wa suke dashi a garin nan, kai a duniyar ma gabadaya bana jin zasu iya zakulo mutum biyar daga dangin iyayensu, to ina zasu je?"
"Ni Mama dan Allah kar ma a fara zancensu, yanzu sai ayi ta magana daya, kawai ki taimaka ki min ankon nan dan Allah."
"Wallahi ba zan bayar ba, shi wannan Yusuf din ba zai baki ba? Ɗan abinda yake baki ai bai kai zaman kujerar da kike kina maƙe masa murya ba. Haka zai zo gidan nan awa biyu uku kuna tare kina zaman tada basir sai dai ya baki abinda gobe ma sai kin nema?"
Rashida ta sake ɓata rai.
"Mama..."
"Da gaske nake wallahi don na fara gajiya da wadannan samarin naki da babu wani kwakkwaran motsi sannan babu kwakkwarar kyauta. Ga Alhaji Sulaiman nan babu hudubar da ban yi miki ba ki saurare shi kin ƙi, da yanzu tuni kin fi karfin bukatunki amma sai yaran da ba abinda suke amfanar ki dashi."
Rashida ta turo baki gaba haushi goma da ashirin na ƙarawa akan wanda take ciki.
Aunty Hajar ta ja dogon tsaki, sannan ta sassauta muryarta yadda Hajiya Umman ba zata jiyo su ba tace.
"Kina dai kallo yadda daga ni har ke muka kare a gidan nan amma ba zaki wa kanki fada ba ki san yadda zaki nemi wajen da zaki rufawa kanki asiri ni ma ki rufa min ba."
"Mama ni fa na gaya miki ba zan auri tsoho ba, wallahi ba na son wani Alhaji Sulaiman bana son ire-iren sa, kuma ai a samarin ma ana samun masu kudi."
"Me zai hana kuwa, ga kawayenki nan, nawa ne suka auri samarin kuma masu abin hannunsu."
"To ai Mama shi yasa nace ki min ankon nan, wallahi angon Nafisan mai kudi ne kinga definitely abokansa da zasu zo da maikonsu, idan banyi ankon ba ta yaya ma za'a kula dani a wajen, su kansu abokan masu makeup da anko suke kulawa..."
Ba shiri Aunty Hajar ɗin ta sassauta fuskarta tana kallonta, kamar ba zata yi magana ba sai kuma tace.
"To ai shikenan, zan duba in gani..." Ta fadi hakan tana mantawa da ratsuwar da ta furta zaune a wajen.
Rashida ta juya idanunta cikin jin dadi daidai lokacin da sallamar Safina ta amsa a kofar dakin, a lokaci guda ta katse murmushin nata tare da jan tsaki, sannan ta dauki wayarta dake gefe ta cigaba da dannawa.
Safina ta shigo goye da ɗan Aunty Hajiyayye a bayanta, fuskarta kuma da murmushi.
Tana ji tana gaida Aunty Hajar da Hajiya kafin tayi mata magana itama, sai kawai tayi kamar bata ji ba ta cigaba da danna wayarta.
"Aunty dama takardar aiki ce nazo in nuna muku, dazun nan Kawun Abuja ya bani ita da safe, wai wani aiki ne a wani asibiti a can GRA."
Ba shiri ta Rashida ta dago da idanunta daga kallon wayar ta kalle ta sannan ta kalli hannun Aunty Hajar sanda ta karbi takardar fuskarta ba yabo ba fallasa tana fadin.
"Masha Allahu..."
Hajiya Umma kuma ta shiga kwararo addu'a da nuna farin cikinta. Wani abu ya taru ya dankare a kirjin Rashida a lokaci guda, wani abu da tayi tunanin zata dade tana jinsa ba tare da ya fada ba, amma lokacin da Aunty Hajar ta zare idanunta tare da fadin.
"Me nake gani haka Safina? Dubu dari da tamanin zasu dinga biyanki?"
Ai bata san lokacin da wani gingimeman abu ya taho ya ture abinda take ji ba yayi nasa mazaunin a kirjinta, taji kamar cikinta ma ya murda, kafin nauyin ƙirjin nata yasa ta daina gane komai.
Sai kawai ta zari kofin shayinta ta mike ta nufi cikin dakin dake manne da falon, wanda nan ne wajen kwanansu kamar yadda a bangaren Gwaggo itama cikin dakin nata ya zama nasu Safina.
Allah ya sani idan zata lissafa rayuwarta kaf! Tun daga farkonta har kawo i-yanzu, abinda zata kira ƙalubale mafi girma a cikin rayuwar tata shine Safina.. Bata san me yasa ba, tun daga ranar da idonta ya ci karo da ita a duniyar nan ko da da gilmawar sakanni bata taba jin sassauci game da tsanar da take mata ita da ƴaruwarta a cikin zuciyarta ba.
Sun tare mata abubuwa da dama a rayuwarta, sun hana ta samun abubuwa da yawa, saboda su ta disashe a idon mutane da dama, ciki har da tarin yan uwanta da ma mutanen da itace ƴa a gurinsu ba su ɗin da basu da wani cikakken asalin da za'a kafa ba.
Amma tun a zamanin yarintarsu kowa kawai su yake kallo, in dai suna waje daya tare to sai mutum ya yi da gaske ne ma yake lura da ita, bata taba mantawa ko lokacin da suna bi gida-gida yawon Sallah duk inda suka sa kafarsu to Safina da Ukthi (marayun Gwaggo da labarin dawowarsu hannun Gwaggon ya karade koina) su ne kawai a idon kowa, sai daga baya zaka ji ance "Rashida har dake da ma?"
Wani wajen ma ba'a taba ambatar sunan nata har su juyo, kamar ƴar rakiyarsu kawai take zama a koina, akwai ranar da aka kunna talabijin ana kallon wata rawar India a gidan, tun a lokacin da hankalinta ma bai gama hafuwa waje gida, amma haka kurum sai zuciyarta ta ayyana mata cewa rayuwarta bata da banbanci da ƴan rawar da take kallo suna taya jaruman, gasu dai ana kallonsu suna rawar iri daya da jaruman amma babu wanda yake lura dasu, hankalin mutum ma baya kaiwa kansu kwata-kwata.
Mahaifiyarta ta sha gaya mata cewa ita fara ce mai kyau, kai ko a gari ma ai tana ji ana fada 'Farar mace alkyabbar mata, fara ko mayyace, inda duk mace fara tazo sai hankalin mutane ya koma kanta...'
Amma ita a nata labarin, in dai zata jera kafadunta da na Safina a waje guda to kamar yadda iska ke shafe rubutu a sahara haka waɗannan kalaman suke, hasalima kamar juyin waina suke su koma kan su din da ko makaho ba zai kira ta fara ba.
Ta ajiye kofin hannunta akan drawer jikin mudubi a cikin dakin sannan ta bude kofar bandaki ta shiga, a jikin sink ta tsaya tana kallon fuskarta yayin da kunnenta ke jiyo mata muryar Safinan da ke cigaba da bayanin aikin da ta sam.
Sai kawai ta bude fanfon ta debo ruwa a hannuta sannan ta watsa a fuskarta, tunani kawai take na ranar da zata samu irin mijin da take so ta yi aure ta sami ƴancinta ta bar gidan nan, rayuwarta ta ɗaga, darajarta ta ƙaru a idon kowa, tayi nisan da daga su Safinan, har mutanen da duk basa bata muhimmanci zasu ɗaga ido su kalle ta su san tabbas ta kerewa sa'arsu.
Abinda bata sani ba shine, ƙalubalen da take ganin zata kai ƙarshe a lissafinsa, bai ma fara ba tukunna!
***
Sometimes the scariest part isn’t losing hope, it’s daring to find it again.-Aliyu.
Motar baƙa ce, baƙa wuluk da sabuntarta ke haskawa a cikin kyallin baƙin fenti, gilasanta a rufe suke gabadaya da bakin tint wanda ya sake sakawa tayi dundum baki daya, don ko ta gilashin gaba a rufe samansa da baƙin tint din, abinda kawai idonka zai iya hangowa shine hannun matukin motar dake murza sitiyarin cike da sanin inda ya nufa.
Wajen da watakila ko a cikin barci zai iya kawo kansa ido rufe ba tare da ya ɓace hanyar dake zane a cikin kansa shekara da shekaru ba, don bayan kan dardumar sallarsa, wannan wajen shi kadai ne inda ke yin ma'ana a cikin kwakwalwarsa a lokacin da komai ya rikice masa.
Ya kashe motar a lokaci guda da tayoyinta suka tsaya a cikin jerin gwanon motocin dake ajiye, Hannuwansa na rataye a kan sitiyari idanunsa suka yi gaba yana kallon kofar wajen da zai shiga, kofar da idan ba mutum ya san wajen bane ba lallai ne ya ganta a kallon farko ba, don tana maƙure ne a tsakanin wata kofar da kuma bangon ginin wani banki da ya juyowa wajen baya.
Idonsa ya tsaya akan allon signboard din sunan wajen dake kafe a sama.
TitanFit Gym.
Hanyoyin samun saukinsa a rayuwa guda biyu ne, na farko saukin zuciya da ruhinsa shine sallah da addu'oin dake rike da shi a kowacce rana, na biyu kuma samun saukin gangar jikinsa shine wannan wajen, wannan wajen da ya dade da yiwa tambarin mafakarsa tun lokacin da rayuwa ta fara koya masa karatun rashin tabbacinta, anan zai zo ya fitar da dukkan wani nauyi da yake jin yana bin kowacce jijiya ta jikinsa, nauyin da har yau bai san ta yaya zai fassara sunansa da yaren da shi kansa zai gane ba.
Kamar yadda yake jinsa yanzu, yadda yake jin ya na fitowa tun daga cikin zuciyarsa yana watsuwa a waje-waje na cikin jikinsa, nauyinsa na cika kunnuwansa da wata irin kururuwar neman sauki.
Ya rufe idanunsa a hankali ya fitar da wani numfashi mai nauyi sannan ya sake bude su ya kalli wajen kafin ya ɗauke hannunsa daga kan sitiyarin ya bude kofar motar ya fito, kayan jikinsa wata farar T-shirt ce mai gajeran hannu da kuma bakin wando.
Ya rufe kofar motar ba tare da ya kalli wayoyinsa dake zube akan kujerar gefe ba, ya danna lock da mukullin hannunsa, fitulun motar gabadaya suka kawo suka ɗauke alamun ta rufe kanta ruf! Sannan ya juya ya karasa wajen kofar ya kutsa ciki, faɗi da yalwar wajen ya cika idanunsa kamar kodayaushe, kamar ba ta wannan ƙofar ne zaka tsinci kanka a cikin ba.
Kuma kallo daya mutumin dake zaune a ɓangaren receiptionist ya yi masa ya juya ya cigaba da aikin da yake yi a jikin fuskar computer dake gabansa. Shima idanunsa basu bawa mutanen da ya gani a ciki muhimmanci ba ya nufi bangaren hagu inda lokar kayansa take, da yatsu biyu ya zare rigar farar T-shirt din dake jikinsa ta sama, sannan ya murda mukullin ya lokar ya janyo wani farin bandeji ya shiga nade hannayensa duka biyu dasu.
Bayan mayar da ragowar bandeji tare da rigarsa cikin lokar sannan ya sake murda mukullin dake jiki kafin kafafunsa su juya zuwa ɓangaren dama, can karshe, wani waje da ya dade da zama nasa, tun da ya riga ya dankarawa masu wajen kudaden da dole suka mallaka masa shi.
Ya tsaya nesa kadan yana kallon baƙar jakar dake rataye daga sama, (Punching Bag) a tsaye take ƙyam! Kamar yaddda yake zuwa ya same ta kodayaushe don an dade da daina zamanin da zai zo ya tarar dashi yana lilo tare da ragowar fushin wani.
Nasa ne shi kadai! Haka yake son duk wani abu da zai sami matsugunni a zuciyarsa, ya zama nasa shi kadai kar komai ya raɓe shi, ya san wannan kalmar sunanta kishi, kuma ya yarda yana da kishin fiye da dukkan yadda zai iya misaltawa ma, don a yadda yake jin matsayin Punching bag ɗin nan a zuciyarsa, ko yanzu masu wajen nan suka ce sai ya sake biyansu kudi zai iya sake siyansa da kwatankwacin abinda ya basu a baya, don zai iya rantsewa cewa kusan kaso hamsin na bakin cikinsa a rayuwa tare da wannan jakar ya raba shi.
Kafafunsa suka karasa gaba a hankali, ya tsaya yana cigaba da kallon ta yayin da kwakwalwarsa ke karanto masa abubuwan da ta saba.
A nan wajen, shi ba likita ba ne.
Ba shi ne ƙwararren likitan tiyatan nan mai hannayen dake ceto rai ba.
Ba shi ne likitan da duniya ke yabawa kokokarinsa ba.A nan, shekarunsa suna zabgewa ne zuwa wannan matashin...
Wannan matashin da mahaifinsa baya ƙauna.
Wannan matashin da ƙaddara ta yage daga jikin mahaifiyarsa,
Wanda ya yi dukkan wata fafutuka kafin ya zama wani abu.Ba shi da wani matsayi.
Ba shi da wani girma.
Bashi da komai illa yatsunsa dake cike da rauni da kuma amon dukkan wani abu da ba zai iya furtawa ba.Kuma wannan jakar a yanzu ita kadai ce abinda bata damu da karatunsa kuma abinda ya iya ba,
Ita kadaice abinda ba zata ja baya dashi ba ko ta mayar masa da martanin fushinsa ba...Sai kawai ya dunƙule duka hannayensa biyu sannan ya ja baya kadan.
Dukan farko ya sauka akan jakar ne tamkar tsawar dake girgiza duniya a lokaci guda, don sai da tayi baya ta daki bango sannan ta sake dawowa.
Ya kara kai mata wani dukan sannan wani.
A lokacin ne kuma hotunan nauyin dake manne a ƙirjinsa suka shiga haskawa a idanunsa bi da bi,...daren da ya dauko gawar farko, fukskar yarinyar ta haska tar a idanunsa, sanye da farar rigarta da tayi kace-kace da jini.
Ya rufe idanunsa yana cigaba da kai dukan, wani bayan wani, da iya karfi da kuma saurinsa, tamkar lasisin cogaban rayuwarsa a duniya ya rataya ne akan ganin ƙarshenta.
Hoto na biyo ya taho, ya sake nuna masa kabsa rike da gawa ta biyu.... Ɗanuwansa... Ahmad! Yana rike da kansa dake zubar da jini yayin da tarin jama'a ke kewaye dasu a tsakiyar titin...!
Numfashinsa ya shiga hawa da sauka yana cigaba da dukan jakar da dukkan karfin da zai iya tattarowa a jikinsa.
Hoto na uku yazo dauke da idanun mahaifiyarsa, idanun dake daukan kaso mai yawa a ƙwarin gwiwar da yake samu tsawon wadannan shekarun, hasken idanun ya haska a cikin kansa tar! tamkar hasken tocilan din da ya ratsa duhu a lokaci guda, kuma maimakon ya ji nauyin dake cikin ƙirjin nasa ya ragu kamar kodayaushe, sai yaji yana nan daram babu ko gezau.
A hankali kuma sai ganinsa ya koma kan fuskar dake tsaye a gefen idanun, fuskar mahaifinsa... Yana tsaye a cikin duhun yana kallonsa, da irin kallon da yayi masa a ranar da komai ya kare, ranar da komai ya tarwatse....
Ya cigaba da dukan jakar nan kotaina kuma ko ta yaya, dukanta kawai yake da duk abinda za'a iya kira da duka... Ta yadda idan wani yana tsaye a gefe yana kallo idanunsa baza su iya tsayawa akan hannayensa ba saboda yada suke kaiwa da dawowa da tsananin sauri.
Kuma bai san iya lokacin da ya shafe a haka ba kafin a karshe ya kai wani irin dukan da ya girgiza gabadaya sarkar dake rike da jakar tun daga sama tamkar zata balle.
Sannan ya tsaya.
Ya jingina kansa da bangon dake gefe, numfashinsa na fita da tsananin saurin dake sa ƙirjinsa ɗagawa, gumi na gangarowa daga bayaansa kafinya bude idanunsa a hankali ya kalli hannyensa dake dunkule har yanzu, dukansu rawa suke, rawa sosai.
A lokaci guda, wani abu mai kama da tsoro ya shiga zuciyarsa, Irin tsoron da ke sa zuciya ta tsaya cak! Kafin tayi ƙarfin halin cigaba da bugawa.
Saboda a yadda yake jin jikinsa har a lokacin babu wani abu da ya canja.
Nauyin da ke ƙirjinsa bai ragu ba.
Guguwar da ke zuciyarsa bata lafa ba.
Duk tarin dukan da ya kai, bai fitar da komai ba face gumin da yake ji akan fatarsa.Sabanin a lokutan baya da tun kafin ya kai ga tsayawa ma komai yake zubewa, ya watse, ya zazzage daga zuciyarsa tamkar garin da aka tankade.
Ya sake kallon hannayensa dake karkarwa har yanzu, me yake shirin faruwa da shi ne? Me yake shirin faruwa?
Idan hanyar dake zama mafitarsa a kodayaushe ta daina aiki to me zai kama kuma?Ya dago da idonsa a hankali ya sake kallon jakar dukan dake lilo a hankali gabansa, kamar itama ta fahimci cewar a yau wani abu ya canja, kamar zata bude baki ta fadi abinda shirun wajen ke kokarin fada masa...
Cewar watakila lokaci ya kai shi makurar da samun saukin yafi ƙarfin wannan wajen, ya karkata zuwa wani bigire daban, wani bigire da zuciyarsa bata taba saninsa ba!
Kuma a daidai wannan lokacin ne daga cikin motarsa, inda ya baro wayarsa a yashe, a cikin akwatin email dinsa, sako na goma sha hudu mai ɗauke da taken.
'Surgical Recovery & Reintegration Initiative.(SRRI)'
Sakonni irinsa sun saba shigowa wayar tasa tun daga lokacin da ya amsa kiran Professor Ibrahim ya kuma amsa tayin aikin da bai isa ya tankwabe daga hannunsa ba, don a wannan gabar ya yarda cewa idan duk duniya zata taru a bangare guda , Proffessor Ibrahim ya tsaya a bangare guda tare da wannan aikin to zai mara masa baya ne ba tare da tunani na biyu ba, don ya riga ya gama daure shi da jijiyoyin jikinsa, ya fadi abinda ya ratsa ta cikin zuciyarsa da yake jin ya rufe da karfe ya narka duk wata kafiyar da ya tsaya akai na cewar ba zaiyi aikin ba.
Don haka tun daga wancan lokacin yake samun sakonnin dake tanadar masa duk wani bayanin da zai nema game da aikin, kuma tun baya bi ta kansu har ya soma karantawa daya bayan daya yana fahimtar abinda zaiyi.
Sai dai sakon yau daban ne, don yana dauke ne da ranar da aikin zai fara da kuma jerin sunayen dukkan mutanen da zasu yi aiki a karƙashinsa.
A cikin layi na uku na jerin sunayen...
Safina Sadiq Kallah.
**