Chapter 1
by @khairatup01
Karamci Writers Association.
(Karamci Shi ne tushen mu'amala tagari)
ZUCIYAR MUTUM
NA
Ummulkhair S Panisau
(Khairatup)
No.1
"Ina son ki gane ,ba wai tafiya zanyi na bar ki ba har kullum kece bugun zuciyata ba zan manta da alkawarin da muka yi wa juna ba." Ya fada idanuwansa nayi mini yawo a jikina.
A hankali na bude baki zanyi masa magana tuni kukan da nake ta dannewa ya kwace min nayi sunkuyi da kaina Allah Ya sani bana son ya tafi kuma ina ji a jikina akwai abinda yake bibiyar rayuwarmu ni da shi.
"Haba ke kuwa a haka kike so nayi tafiyar nan? Ina kallo kina irin wannan kukan? In na ci amanar ki ai sai zumunci ya tambayeni ki gaya mini me kike so nayi miki ki yarda zan dawo mu tafi tare?"
Cikin shasheka jikina bari nace "Bana yi maka kallon Wanda zai iya cin amanata sai dai ina tsoron matan birni da rayuwar birni da ake fada kar ka tafi ka bar ni ,Ka sani Allah ne gatana Kai ne gata na bani da kowa kusancinka a gareni ya saka na samu sassaucin ukuba yanzu kuma zaka tafi neman kudi taya Zan saba babu kai a tare dani?
Kiyi hakuri kamar yau ne zanje zan dawo kuma ba zan ci amana ba.
Da rinannun idanuwa da suka ja tamkar gauta na kalle shi nace "Ka sani in Kaci amanar soyayyata Allah ba zai bar ka ba,kar ka tafi ka bar ni da dakon aurenka a kaina.
Kar ki damu In Sha Allah zan rike amana. Na gayawa Habulle komai duk abin da kike da bukata ki gaya masa kinga zai ma dinga kawo miki ni dai kar ki roki kowa komai kamar yadda na alkawarta nine kowa da komai naki.
Hannayemu biyu ya hada a wuri guda ya rike gam kafin ya tashi ya gyara yamushashiyar shaddarsa ya gyara zaman hularsa ya kalle ni yace "Muje muyi sallama dasu Inno kar dare yayi min."
"Allah Ya tsare Nata'ala ya kai Ku lafiya zanyi kewarka."
Haka muka fita jiki duk a salube. Koda muka fita tsakar gida duk su Inno na waje Yadda suke kallona ma jikina tuni ya fara rawa amma haka na daure na bi shi a bayansa.
"Yau naga wani sabon fi'ili manne mishi za ki yi ne? KO kunyar idanuwanmu ba kya ji kin hito rakiyar miji." Lantana matar Yaya Sabi'u ta fada.
Sauran suka saka dariya..Inno ta bantari goronta tana yatsina fuska tace "Ni ban ga wani amfanin tafiya wani birni ba a nan ma zaka samu arzikinka amma dake so kake ka farantawa yar gwal ai ka kafe sai ka tafi."
"Haba Inno kiyi hakuri ba fa jimawa zanyi ba da ni da ku zan je na samowa arzikin nan. Ni dai kuyi hakuri da juna ku rike min ita amana."
Inno ta kama haba tace"uh'uhm" ikon Allah yau naga abinda ya ishe ni.
Gabadaya duk sai suka saka mini dariya. Shi kuma ya kalleni ya fita. Har yau in na tuna kafin idanuwansa a kaina sai nayi kuka.
*
Da daddare ina kwance a tsakar dakina. Dakin da ko katifa babu arzikinsa a ciki bare leda simitin ma duk ya kukurje. Wani tsohon zani ne kawai a malale a tsakar dakin kawai.
Jikina duk a mace saboda yunwar da nake ji, hawaye ne kawai ne yake tayi min fareti,ina cike da damuwa da tashin hankali da kewa na jima da sanin bani da farin jini wanda nake kalla nake jin dadin ma ya tafi ya bar ni da kewarsa. Daga waje ina jiyo shewa da karadin sauran mutanen gidan da ace zan tashi in shiga cikinsu duk sulalewa zasu yi su bar tsakar gidan ko suyi ta yi min habaici haka nake cijewa nake daurewa na yi zamana a dakin.
Ciki-Ciki na soma jiyo muryar Yaya Habulle a kofar dakina. A hankali na tashi na isa bakin kofar na daga buhun da na yi labule da shi.
Bakinsa ya kasa rufuwa da leda a hannunsa ya miko mini. "Kiyi hakuri na jima ban kawo miki abincin ba na je wajen gari ne ban dawo da wuri ba daga yau in kika ga haka ki shiga gidana wurin Indo ki amshi abincin kawai."
"Na gode Allah Ya saka da alkairi." Ya yi min sai da safe ya koma nima na koma cikin dakin. Rabona da abinci tun Koko da kunun safe shi ma Nata'ala Inno ta aikowa shi ya bani naci. Hannu baka hannu kwaraya haka na dinga zuba shinkafa da taliyar nan dafaduka a bankina ina gamawa na sha ruwa na yi gyatsa na jingina da garu abincin ya sayaya mini tukuna kafin na kwanta ban san ya akayi ba sai baccin ya dauke ni a nan.
*
Tunda ya shiga garin Kano yake kalle-kalle akan hanya motoci,da mashina da yan adaidaita Sahu duk sun birkita shi asalin bakauyen shi ya fito jiri ma yake ji gashi ya kasa ma tsallaka titin da ya yi yunkurin tsallakawa sai ya koma a guje ga kullin kayanshi ya manna a hamatarsa tuni ya jike sharkaf da gumi ga yunwa ga wahala.
Wasu daga gefe da ke kallon abinda yake faruwa suka dinga yi masa dariya iyakar kauyanci ya buga shi kuma dole ayi masa dariya.
Daga karshe da yaga wasu zasu tsallaka yayi kundunbala ya tsallaka tare dasu. Suna ko tsallakawa ya saki ajiyar zuciya hadda kama kirjinsa gana haki.
"Kai jama'a tabbas Kano babban gari ne Kan bu yau naga masifa ni Nata'ala haka dama ake dama?" Maganganu ya soma yi da kan sa ,yanzu ina zai nufa? Ina za shi ta ina ma zai fara neman aikin?
Tun daga tasha wani matashi yake bin sa a baya. Yaga dan kauye ga kullin kaya a hammatan shi a tunanin shi tarin dukiya ce a ciki shi yasa yake rike da kayan gam kamar ran sa.
Shi kuma gashi barawo daman aikin sa kenan zama a wajen tasha In ya ga mutum dan kauye ko bagidaje sai yayi masa aiki ya wuce wurin kawai.
Nata'ala kuwa yana ganin inuwar mutum ya tsaya cak ya juya suka yi ido biyu da barawon nan har ya zaro wata yar karamar wuka daga jikinsa ya nuna Nata'ala da wukar yana karkarta bakinsa wanda hakoran sun dafe da kayan shaye-shaye.
"Kai yane? Miko mini duk wani a dake a wurinka ka gane ai?"
Nata'ala ya hadiyi yawu makwat ya zaro idanuwa waje ya juya hagu ya juya dama ya Kalli gaba ya Kalli baya ya ga dai layin babu kowa sai kawai ya sunkuya ya debi sillifas dinsa ya kwasa a dari uku da sittin yana ihun "Wayyo Allah a taimaki ni barawo zai illatani bani baka ko sisi alquranin Allah kurwata kur"
Shi ma barawo ya bi shi da gudu tabbacin Nata'ala na tare da tarin dukiya Kenan.
Yana cikin gudu yaga get din wani gida a bude ai kuwa ba tare da shawara ko Jira ba ya afka ciki da gudu da karfi ya maka kofar get din ta rufe ji kake ta bada wani kara "Bam" karar da ta jawo hankulan jama'ar gidan gabadaya kenan suka fito suna tambayar waye? Waye?.
Nata'ala kuwa yana ganin idanuwan mutane ga tsoro daman yana ji ga yunwa kawai sai ya sulale ya fadi a wurin a sume.
"Waye ne yake yi mana bugun barayi? Mati kana ina ake yi mini irin wannan hayaniyar a cikin gidana?"
Kansa a kasa Mati ya isa gaban Hajiyar yana mata bayani. "Hajiya Wallahi kawai ji muka yi Bam an buga kofa dama Alhaji ne ya shigo na bude masa kofa kafin na dawo wannan bawan Allahn ya fado cikin gidan kuma ya ma suma kin gan shi can."
"Suma ? Wane irin Suma? Daman nan gidan na shirme ne ku Kula fa. Ku kwashe shi Ku jefar can ya karata."
"An gama Hajiya." Mati ya fada yana juyawa.
Daga sama ya ji muryar Alhaji yace "Mati a kai shi BQ ku bashi taimakon gaggawa bamu san me ya faru da Shi ba in ya farfado ya ji dama sai ya tafi Hajiya ki zo."
Taji haushin hakan da yayi mata a cikin yan'aikinta bata kara cewa komai ba ta buga tsaki ta shige ciki.
Sauran ma suka koma bakin aikinsu. Iliya ne ya debo ruwa ya yayyafa masa aiko Nata'ala ya ji ruwan sanyi sai kuwa ya dage ya zabga wani uban ihun ya kuma rungume kullin kayansa yana surutai "Wallahi ba zan bada kayana ba Wallahi barawo sai dai kayi hakuri" ya dinga dai sambatu.
Mati da iliya suka dinga dariya don yanzu sun gano bakin zaren. Barayin bakin hanya ne suka biyo shi ya fado musu gida suka taimaka masa su kai Shi BQ kamar yadda Alhaji ya fada. Aka bashi magani da abinci ya ci yayi nak saboda dadin abincin ma kunnensa kamar ya tsinke ga nama.
"Kai ko dai mutuwa nayi a aljanna muke? Wannan abincin wai hannu ne yayi shi ko aljannu?"
Mati yace "Kai da Allah ba fa mutuwa kayi ba da ranka. Wannan abincin kuma mutum ne ya dafa. "
"Kai da gaske? Lallai a bawa wannan hannu kyauta babba ta iya girki."
"To yau ka zauna gobe Ka kama gabanka kafin Hajiya ta kore ka,yau ma Alhaji ne ya tare maka." Inji Iliya.
Nan da nan kwakwalwar Nata'ala ta soma hasasho mi shi daular da zai mora ta gara a gidan dama Allah Ya hore masa iya magana da tsara zance shi kam ya ga wuri kuma bai tafiya. Bai ce musu komai ba ya koma ya kwanta kullin kayansa yayi matashi da shi.
*
Washegari na cika ko ina da ruwa a gidan kowanne daki sai da na cika musu randa da bokitai uku -uku. Na koma nayi wanke-wanke sai da na gyara gidan tsaf babu Wanda ya raya ni daman ba mai taya ni Nata'ala ne kuma baya nan. Sai nayi za a bani abincin da zan sa a cikina .
Sha biyun rana na hada wuta na soma kokarin dora sanwar rana tuwon masara ne miyar kuka abincin kusan mutum hamshin ake dafawa kullum saboda yawan gidan. Gidan gandu ne kowanne bangaren akwai Mata biyu ko uku ya danganta dai da karfin namiji. Ya'yan wa ne da ya'yan kanne Maza da ya'yansu da jikoki da ma matan jikoki daddaden gidan gandu ne tun shekara da shekaru. A haka dai suna da hadin kai amma a badini ta ciki-na-ciki.
Idan mijinki yana da halli to za a marawa matarshi baya gidan dai a rabe yake kowacce da akwai uwardakinta in kuma ta kwabe ayi ta tashin hankali da bala'i a gidan kamar ba ayi mutuncin ba har sai iyaye maza sun taka birki tukunna ake samun sa'ida sai kuma a janye tallafin taya girki a bar ki da aikin ki ke kadai haka gidansu Nata'ala yake.
Tsofaffin hudu suka rage a kakanin gidan da iyaye masu zafi da ake jin tsoronsu sosai ciki harda Inno mahaifiyarsu Nata'la. Sai Gwagwagon Zaure da Hajiya Iyye da Umma Marka. Aurosu aka yi amma suna fada aji. A tsofaffin gidan kuwa Maza akwai Baffah da Alhajin Zaure sai Baba Jabiru da Alhajin Sama.