Chapter 3
by @khairatup01
***
Follow my watsaap group.
Karamci Writers Association
(Karamci Shi ne tushen mu'amala tagari)
Na
Ummulkhair Sani Panisau
(Khairatup)
No.3
"Habibi ! Kayi min rai Kada ka yarda da batunsu in dai haihuce zan haihu zan yi duk yadda zan yi na ga na baka da ko ya da zaka dinga kalla...."
"Subahanallahi,Aisha wacce iriyar magana ce wannan kike yi? Ya kike son kauce hanya fisabilillahi? Ke za ki bawa kan ki haihuwar? Daman ke kike bawa kan ki?..."
Ka fahimce ni Habibi ba zan iya raba ka da wata ba kai nawa ne ni kadai Wallahi zan haukace in dai ka yarda zaka kara aure.
Ajiyar zuciya Habib ya sauke ya kura mata idanuwansa ya son tana son sa amma bai taba zaton zata iya kokarin kauce hanya saboda shi ba. A hankali ya sa hannu ya kamo hannunta guda ya damke da nasa gam kafin ya soma kwantar mata da hankali."Aisha ke rayuwata ce kin son ina son ki kuma ba zan ci amanar ki ba. Dole ne nayi wa iyayena biyayya kuma kema ina fatan ki tayani yi musu biyayyar. Kar ki ga laifin Hajiya don tana son ganin kwaina a duniya it's been ten years Aisha nima ina son naga dana ina fatan kin fahimta?"
Ji tayi kamar ya maka mata guduma a halin da ake ciki duk ta ji ta tsani kanta kuskure daya tak ya ja mata. Kallonta Habib yake cikin ranta kuwa cewa tayi "ZUCIYAR MUTUM birninsa"
A hankali ta tashi zata koma daki sai kuma ta dawo da baya da sauri tace "Habibi ina da shawara na san kuma zata yi mana amfani."
Laptop dinsa ya kashe ya gyara zamansa yana fuskantarta. "Ina jin ki."
"Kana ji ?"
"Uhm."
Kawai muyi hayar yarinya ta haihu mu karbi dan ita kuma mu sallame ta asiri a rufe.
Idanuwansa ya Karawa girma cike da al'ajabin maganar bai ma gane me take son fada ba.
"Aisha ban gane ba"
"Ina nufin mu samu yarinya ko a kauye ne , sai ka tara da ita,mu dawo da ita gabanmu in ta haihu mu karbi dan ko yar ace ni na haihu kaga babu wanda ya san me muka aikata."
"Aisha kin haukace."
"No da gaske nake yi maka don Allah ka yarda da wannan plan din ita ce kawai hanyar da zan tsira daga kishiya bana sonta."
Tashi yayi ya zari car keys dinsa ya dauki laptop dinsa ya yi hanyar fita. Da sauri ta bi shi ta ja gabansa ta wara hannayenta biyu ta tare mai hanya.
"Ki matsa Aisha".
"Aa ba zan matsa ba sai ka yarda."
"Aisha ban taba nuna miki bacin raina ba yau kar ki zamo silar da zan nuna miki."
"Habib in na gane kafi son kayi min kishiyar ? Kai ma kana bin bayan Hajiya da sauran yayyunka da ba sona suke ba. So kake a kawo wadda suke so ni kuma a guman takaici a bar ni a kwana Wallahi Habib sai ka yarda ."
Hannu ya sa ya tura ta gefe ya fice.
Tsugunnawa tayi ta saki ihu ta ture dankwalin kanta ta kwanta a gun tana kuka. Ta tsani kishiya kuma wannan karon da alamu in bata yi da gaske ba zasu cinnma burinsu a kan rabata da Habibi. Zama bai ganta ba tashi tayi ta koma ciki mayafi da mukullin mota ta dauko tayi waje da gudu a yanayin da ta tada motar ma ya tayarwa maigadi hankali tun kan ya karasa bude gate tayi waje tare da dukan kofar daga barin hagu. Hannu dafe a kirji maigadi ya bude baki yana ambaton sunayen Allah duk wanda ya zo bakinsa.
*
Kwanakin da Nata'ala yayi a Kano ya hadu da wayayyu da suka koya mai abubuwa da dama ciki harda damfarar mutane in Ka fito da mota da gayya zai fada kan mota a bashi kudi.
Yau ma ya fito kuma yayi babban nasara domin kuwa wannan aikin shi ya juya dukanin wata duniyarsa zuwa farin-ciki.
Aisha ko ganin gabanta bata gi saboda tashin hankali bata yi aune ba Nata'ala ya fado Kan motarta tuni ta taka birki da karfi. A kidime ta fito waje ta duba shi tuni mutane suka yo mata caaa a kai.
"Ku bari don Allah,zan kai shi asibitin mijina babu abinda ya same shi."
Jin asibiti Nata'la hankalinsa ya tashi gashi ba halin ya bude baki yayi magana za a rafko shi kuma jikinsa ya gaya masa dole kanwar naki ya dake yana ji aka saka shi a cikin motar.
Sun soma tafiya yaga dai asirinsa zai tonu a can ma kila a kira masa yan sanda.
Kawai Aisha magana taji a kanta. "Hajiya kiyi min rai ki sauke ni a nan lafiyataau ba ki yi mini komai ba sharrin shaidan ne kudi nake so na rasa mai daukata a aiki ko na gyran fulawa ne ta haka nake samun na sawa a bakin salati na bar matata a kauye da iyaye sai na samu zan basu nima..."
Shiru Aisha tayi na wasu yan lokuta ta kura masa idanuwanta abubuwa da dama ke mata yawo a kai.
"Zan dauke Ka aiki kuma zan dinga baka albashi mai tsoka sai dai nima zaka yi mini aiki."
"Zan miki in dai za ki biyani."
Murmushi tayi kawai ta tada mota tayi reverse ta karya kwana ta koma gida.
Daki ta ba shi a BQ ta kuma gaya masa yayi wanka yayi sallah za a aika masa da abinci. Da daddare zata kira shi ta hada shi da mijinta a nan zai ji aikin da zata ba shi.
Nata'ala ya dinga murna kakarsa ta yanke saka. "Uwani ina nan zuwa gareki na dawo da ke birni ki huta ki sha fanka ki ci mai kyau ki kwanta akan mai kyau."
*
Misalin karfe goma sha dare na dare ya koma a gajiye sai dai gana ganin Aisha abin dazu ya fado masa a rai. Tuni ya turnuke fuska ya hade rai zai kauce tayi saurin rungume shi a jikinta da ke tashin kamshi. A kunnensa tace masa "Am sorry kayi hakuri na bar maganar yadda kace haka zan yi mijina."
Hannunsa ya saka ya dawo da ita baya ya sumbaci goshinta yace "Wallahi kin bata min rai amma naji dadi da kika gane da kan ki kika kuma dauki gyaranki. Allah zai kawo mana mafita Aisha ko da akwai aure a kadarar rayuwata Aisha ban zan juya miki bayan ba zan rike amana bakin rai bakin fama mutu Ka raba ni da ke."
Hawaye ta share. Tace muje Ka ci abinci. Sai da ya gama cin abincin yayi wanka. Bayan sun kwanta ta gaya mai ta yi bako daga kauye dan uwansu ne daga nesa ya zo neman aiki kuma ta dauke shi zai dinga yin share-sharen tsakar gida da ban ruwa ga fulawa da yan aike dai haka.
Ba mutum ne mai zurfaffa bincike ba amsa mata kawai yayi ya kwanta.
Habib ya soma bacci ita kuma a lokacin kwakwalwarta ta soma hassafa masa abinda zata yi ta samu da don ba zata yarda ayi mata kishiya ba. Sai ta rufe bakin Hajiyarsa da ma yayyunsa sai ta nuna musu nata ikon.
Kwanaki biyu Nata'la yayi baya aikin komai sai dai ya ci ya kwanta. Aisha ta bada kwangilar a gyara mata shi tsaf hakoran nan kamar ayi amai. An dauki lokaci kafin Nata'ala ya kile ya kuma rike yin brush koyaushe.
Watansa biyu ta fara ba shi aikin wankin mota tana saka kananun kaya sai ya kile ga dagawa da shegen magana a cikinsa ga karya.
Mai aikin Aisha Mariya tunda Nata'ala ya kafa ido a kan ta ya ji fa ta gama da shi sai yaga ashe Uwani ba mai kyau bace. Aisha bata wasa da yan aikinta fannin Kaya haka da tsafta saboda Habib baya son kazanta bare ita kanta. Mariya tayi wayewar da ba ka ce yar aiki bace ba kai kace kanwar Hajiya ce.
Kamar yau yana zaune da gajeran wando da riga mara hannu saboda zafin da ake yi a garin Kano. Gyada dafaffiya yake ci tunda ta fito yake kallonta da ya kasa jurewa kuwa sai da ya tanka mata.
"Mari babban kifi , barka da fitowa. Yarinyar nan ba kya jin garin nan kinga yadda kika yi fes dake."
Tayi wal da idanuwa kamar wata yar duniya ta saki dariya tace "Allah ko Nata'ala? Kai ma ai kayi kyau baka jin zafin nan"
"Kalle ni fa kayan shan iska na saka zo ki zauna ki taya ni cin gyadar."
"Aikin fa Nata'la wa zai mini?"
"Sai na taya ki ai."
Tayi dariya kawai ta gyada kai tayi gaba tana magana "Kai ka sani ba zan biye maka ba Wallahi."
Tashi yayi ya bita yana tsokanarta wani ta maida mai martani wani ta hakura ta kyale shi haka ta gama yana biye da ita.
"Yau me kika dafa a gidan?"
"Sakwara ce aka yi ka san yau maigidan zai dawo."
"Madallah!." Ya washe hakoransa yana dariya
yace "Dan zubo mini man yunwa nake ji daman shi yasa kika gan ni da gyada a nan."
Gaskiya ba zan iya baka ba. Abincin nan dai na Alhaji ne
"Ke naga ba ki iya komai ba ,ai ba zasu sani ba nifa masoyinki ne." Ya fada yana kashe mata ido.
Murmushi tayi tayi gaba tana magana "Zan kiraka in na kammala."
Ya ko wahshe hakoransa ya na muzurai ya koma wurin zamansa.
A Kan idanuwansa Hajiya ta dawo. Bata jima da shiga ba ta saka aka kira mata shi.
"Barka da yanzu Hajiya"
Ba tare da ta kalle shi ba ta amsa. Ta ci gaba da daddana wayarta kusan mintuna goma kafin ta waiwaye shi ta ajiye wayar a gefe ta hade hannayenta wuri guda.
"Ya ma kace sunan ka?"
"Nata'ala nake Hajiya."
Daga wane garin kake?
Daga garin Minna nake.
Minna dai ta Niger?
Eh kwarai.
To naji kana magana akan kana da mata da waye?
Eh akwai matata Uwani ba a jima da aka yi auren ba na taho neman kudi ko auren ma bamu raya ba Innata tace sai nayi kudi.....
"Kaga saurara kaji me zan gaya maka tukuna bana son dogon surutu."
"To Hajiya na bari ina jin ki Hajiya."
Zaka dawo da matar ka nan garin cikin gidan nan.......... Sai da ta kai aya kafin ta kuma ja masa kunne "Bana son kowa ya san da wannan shirin namu in nace kowa ina nufin kowa daga ni sai kai kawai na yarjewa sani. Zan aura maka Mariya nan da sati biyu zaku zauna a nan , zan dinga biyanka kudi duk karshen wata irin kudin da baka taba zato ba amma Nata'ala in sirrin nan ya fita daga bakin ka Wallahi-Tallahi sai ka yi da na sanin zuwan ka birin Kano don sai na sa an batar da kai kuma ka tafi kenan."
Gyara zama Nata'la yayi sosai yace "Hajiya kar ki damu sirrin nan na danne shi daga yau ko ita Uwanin ba zata sani ba."
"Yayi maka kyau ina son muyi komai daga yau Sabo da haka ka san da me zaka fara ai?"Nan da wata hudu kaje ta taho da ita ka kawo ta nan."
"An gama yalabbiya."
Tashi kaje.
Ya fita jiki na rawa. Shi fa kudi yake so kudi bana wasa ba irin kudin da zai koma kauye ana masa kallon Alhaji kowa sai ya sara mai dama ba wasa ya shigo birni yi ba. Ga gida,ga kudi, ga kuma mata an bashi yar birni mai wayewa Mariya. Tabbas Inno zata yi alfahari da shi korafi ya kare.
*
A can Minna kuwa cikin dare suka soma jiyo hayaniya na tashi Kan kace me kowa ya bar kan shimfidarsa an firfito sai dai Jin harbi da gudun mutane ya saka kowa ya shiga taitayinsa ya gane abin da ke faruwa, Yan bindiga ne suke shigo sun jima basu waiwayosu ba sai yau tuni kowa ya soma neman hanyar mafaka suka dunguma cikin daji.Kauyen CIRORO kenan dake garin Minna suna fama da fargabar yan bindiga sosai in suka shigo su kashe na kashewa su tafi da na tafiya mafakar mutane cikin daji ko tsallaka kogi. Akalla suna sati basu koma gidajensu ba saboda fargaba.
Haka za a zuba guragu a wilbaro ayi ta yi dasu ba babba ba yaro,ba tsoho ba tsohuwa.
Cilla kafafuwanta kawai take yi ba ganewa take ba saboda yunwa ta gama cinye ta dama. Kwananta biyu tana azabtuwa da yunwa Yaya Habun ma karfinsa ya fara gazawa ya daina bata abincin, daman matarsa ba so take ba na cikin gidan kuma in an yi ba bata suke yi ba musanmman ma da Suraja ya kone da tuwo tun daga nan Inno ta kara nata matakan tsanani a gidan ga zagi da cin mutunci da take fuskanta sai dai tayi kuka kawai. Akalla anyi wata biyu yanzu da tafiyar Nata'ala babu mai labarinsa ta ma fara tunanin ko dai guduwa yayi ya manta da alkawarin da yayi mata. Tana can tana gudu taji an fizgi hannunta ta fada wani wuri ta ko dage zata kurna ihu aka sa hannu aka toshe mata bakinta. Ta dinga wulla idanuwa tana zaresu.
"Ke nutsu kiyi shiru kar su ji mu su yo kan mu mafaka ce nan inda kika nufa duk suna can a tsautsaye sun tare hanya.
Hannu ta saka ta dafe kirji saboda yadda yake bugu kamar zai fado kasa.
A hankali tace "Na gode Abida."
"Babu komai". Haka suka zauna a cikin wannan ramin suka yi bakam ko kwakwaran motsi basa yi saboda gudun kar a jiyo su.
Kwanansu biyar kafin suka soma fitowa daga maboyarsu ba ci ba sha komai sai dai su yi a inda suke. A kwana na shidda suka isa gidajensu an kwakwashe musu dabobi da kayan abinci anyi watsi da komai ko ina dai kaca-kaca.
Haka aka soma maida magana in abun dariya ya shigo a dara in abin kuka yazo ayi. Haka rayuwar mazauna kauyen take kullum cikin zullumi da fargaba. Wanda suka kasa dauka sun yi kaura daga garin wasu kuma suna ganin ba zasu iya barin garinsu ba saboda garin akwai yalwar arziki saboda noma da kiwo.